Showing 126001 words to 129000 words out of 161239 words
fito na ɗauko mishi kayan da zai saka dan naga kayan a gefen katifar ɗakina , ɗakinshi nakai mishi da turare shima a kusa da kayanshi na gani turare mai shegen tsada da ƙamshi , yana fitowa ya saka kayanshi ya shafa turare sannan yayi alwallah dan magrib ta gabato , abin sallah na shinfiɗa mishi ya hau sama , nima na fito nayi alwallah na wuce ɗakina...
Duƙe yake saman bayan kujera ya ƙurawa waya ido yana kallon hotunan Sultana , murmushi yayi a bayyane yace da wannan kyakkyawar zan kere sa'a na kasace na daban abina , amma dai ya kamata na bata shawara ta daina ciki baki akan cewa baza ta taɓa so na ...
Zagayawa yayi ya zauna saman kujera yana cewa dani dake yau zanga waye tunani zai hana bacci , kwanciya yayi saman kujera ni na kwanta kuma bacci zanyi ya ƙarasa maganar yana murmushi , saida ya lumshe idanuwanshi yace ki kasance cikin farin ciki na barki lafiya....
Saida na gama duk abinda nakeyi na kwanta saman katifa a gajiye , a hankali naja bargo na lulluɓe tare da ƙurawa wayar dana ɗauko ido kira sai shigowa yakeyi babu ƙaƙƙautawa , uhum murmushi nayi tare da kashe wayar gaba ɗaya na rufe idonuwana danyin bacci....
_Ƙarya kike..._
Wannan kalmar itace ta fara zomin a cikin kwalwar kaina , ɗan jujjuya kaina nayi a hankali na gyara kwanciya ta ,
_Zuciyata ta faɗamin cewa ko kin tafi sai kin dawo , bata taɓa faɗamin ƙarya akanki ba duk abinda ta faɗamin gaske ne_
Murmushi nayi har yanzu idanuwana a rufe nace tou ya akayi ban dawo ba ?
_Zaki zo zuwa gareni kina roƙon na baki soyayya ta , tabbas ranar zata zo , murmushin shi yazo ya tsayamin a rai kalmar ƙarya ta sake dawomin a zuciyata..._
Da sauri na tashi zaune nace wallahi ƙarya kakeyi na tsaneka....
Murmushi yayi ya gyara kwanciya , nasan baki tsaneni ba ɓacin rai yasa kike faɗar wannan kalmar , idonshi a rufe yayi magana ...
Wallahi a daren ranar banyi bacci ba , tun daga ranar dana fara ganin Dikko har zuwa yau da muka rabu ko ta ina Dikko ya zargemin zuciya , nayi juye² wallahi bai fita ba , ganin dai baccin bazai zo ba yasa na haƙura na fita nayo alwallah naci gaba da sallah !
***
Yau laraba kuma itace jibin da nake jiran zuwanta , bayan hantsi ya ɗaga na dafa ruwan wanka wa Babana , kafin ya fito na gyara mishi ɗakinshi na share na goge fess na zuba mishi turaren wuta , bayan ya fito wanka ya shirya cikin shiga ta kamala ya baɗa ƙamshi ,
Sama ² ya yagi abin kalacin dana kawo mishi , bayan ya gama ya umurceni dana fitar dashi ƙofar gida saman dakali , ɗakina na koma na ɗauko kafet na naje na shinfiɗa mishi sannan na dawo na kamashi dan har yanzu yanayin abu irin na wanda yasha jiya harya gaji ,
A hankali muka fito dani da Babana muna lallaɓawa , saman dakalin na samu Amisty zaune ita da Hafsa , ko inda suke ban kallaba na taimakawa Baba ya zauna , a dai² lokacin da Umar yake tsugunniya a gaban Baba yana gaishe shi cikin girmamawa tare dayi masa sannu da jiki ,
Naji daɗi sosai dan haka nima na gaishe shi , ya ansa cikin kulawa tare da cewa wurina yazo ya faɗi maganar yana miƙewa , bayanshi nabi mukayi nisa da Baba , bayan mun samu madakata yace mai gida ya aikoni wurinki , kallonshi nayi banyi magana ba , wayarshi ya ciro daga aljihu ya kira Dikko bayan ya ɗauka yace mai gida gata , ya faɗi maganar tare da miƙomin wayar ,
Cikin jin daɗi na ansa na kara a kunne na tare dayin sallama , ansawa yayi cewa ya kike ? Lafiya qalau kaima kana lafiya ? Alhamdulillah , tun shekaran jiya nake so nai miki ya hanya Umar yace yazo ² bakyanan ina kike zuwa ne ? Banje ko ina ba , tou da kyau , na sake cewa banje ko ina ba , yace ai shine nace hakan yayi kyau sai anjima , shiru nayi dan bana so wayar ta tsaya hakanan , shi kuma kashe wayar yayi abunshi...
Miƙa mishi wayarshi nayi , shi kuma yace min yana zuwa , mota ya koma ya ɗaukomin wata "yar ƙarama leda mai tambarin waya a jiki yace gashi yace a kawo miki kuma akwai layi a ciki anyi mata caji ,
Uhum ni da zanma Dikko cikon kuɗi saina ɓige da ansar waya , cikin farin ciki mukayi sallama da Umar , ban koma wurin Babana ba nayi cikin gida ina zuwa na shige ɗakina na zazzage ledar na ciro "yar kyakkyawar wayata na dudduba bansan sunan wayar ba anma an rubuta a jikin wayar , ban damu da sanin sunanta ba nidai tamin kyau kuma ta burgeni sosai , ajiyewa nayi na koma ƙofar gida wurin Babana dasu Amisty dana baro waje ,
Ina fitowa a daidai lokacin da Mamy ta faka da tsadajjiyar motar ta , tasha wani irin dakeken gilashi wanda ya cinye kaf rabin fuskata , karuwa ce data ansa sunanta karuwa , ba karuwar muje mu dawo ba , ba karuwar wahala ba , ba karuwar ya zanyi ba ? Kana ganin zubin iskancinta kasan karuwanci takeyi mai aji kuma mai matsayi ba iskanci cini inci tuwo ba ,
Tana fitowa ta fara bi bi biyyy 👍🏻 cikin yanayi mai nuni da "yar hannun ce , murmushi Babana yayi cikin jattako da gogewa , wata alama yayi mata da ido irin tasu ta "yan bariki , dariya tayi tare da cire gilashinta tace *BINNA* 👍🏻 , Binna kaci dubu ka binne dubu , binna zaki binna kura binnan ƙarshen ƙarni binna ka taushe ..... Sai kuma ta fasa ƙarasawa !
Dariyar "yan duniya Babana yayi tare da ɗan kauda kanshi gefe cikin jin kunyata , Mamy ta sake cewa Binna wuta , wuta na wurina.... Ba tare daya kalleta ba yace ga Mamana nan da nake baki labari ku gaisa , gaba ɗaya tabi mu da kallo dani da Amisty da Hafsa a wani irin yanayi tace wace ce Uwar masu gida ?
Kakkaɓe idanuwa na nayi nace nice , ƙwalalo idanuwa tayi tana kallona sannan ta sake kallon Babana tace Binna Sultana ɗiyarka ce ? Jinjina kai Babana yayi alamar Eh , ƙara kallona tayi sannan ta sake kallon Baba ta juyo ta tsareni da ido....
Kusa da ita na matsa na duƙa ƙasa² nace matsayin kura daban amfanin labule sirri , huɗɗakir da Babana daban nima tawa dake daban ,
Murmushi tayi tare da kallon Amisty tace Amina kuma tsaf ta kira sunan Hafsa , tace ke kuma Sultana ? Nace sosai suma mu'amular ki dasu daban nima har yanzu nawa daban da nasu.....
Kallon Babana tayi shi kuma yayi murmushi tare da cewa mijinki ya dawo ne ? Miji kuma ? 😳 wane irin miji na tambaya a bayyane , kallona Mamy tayi tare da cewa ya dawo ya koma ta ƙarasa maganar tana murmushi , Babana yace sai kuma yaushe zai dawo ? Har yanzu ni take kallo tace harsai na kirashi.... !
Dama kina da aure ne ? Na tambayeta tace Eh amma auren jeka nayi ka kawai idan yazo miji idan baizo ba sauka lafiya , ƙara duƙawa nayi nace ina kika san Amisty da Hafsa ? Wurin Babanki na sansu , Babana kuma kamar ya ....?
Dariya tayi tare da cewa amfanin labule sirri yanzun nan kika faɗa Sultana , saboda haka a sake labulen muje ciki inji neman da kike min ,
Amisty tace Aunty Mamy amana don Allah , cikin rashin fahimta na kalli Amisty nace amanar uwarki .... Dariya Mamy tay tare da cewa ai kinsan ba haka nake ba , kowa da wurinshi ,
Murmushi nayi na nuna mata da "yan yatsuna biyu manuni da mai bi mishi 🤞🏻 kamar ina datsa abu nace kema ...? { lesbian } Tace ina yaran wata ƙawata ne , nace baƙar magana kika faɗamin kenan kikace wurin Babana kika sansu ko ? Tace wallahi tare da Babanki nake ganensu kullum rana ,
Kallon idonta nayi tare da cewa kuma fa da gaske kike ba ƙarya kika faɗa ba , tou amma idan na gano akwai wani abu tsakaninsu da Babana tabbas zaune da tsaye bata ƙare ba , murmushi Mamy tayi tare da cewa ki kiyayi Binna duk macen da kika ga tana manneshi ki mata uziri idan ya gaji da kanshi zai wulaƙansu wallahi babu asiri ba komai idan dai kika faɗa tarkonshi fitarki sai Allah , matan yanzu da kansu suke bibiyarshi , kuma duk mutanen da kika sa nayi musu vidio kwanaki kinsan ko su wayen Babanki ne ?
Nace sai kin faɗa , jinjina kanta tayi tare da cewa gaba zaki sani amma Allah yasa dai wani abu bai shiga tsakaninki da Baban Hafsa ba , ni babu abinda ya taɓa haɗani dashi saidai munayi waya ana maganganu dai irin na gyaran kasuwa , so ɗaya kawai ya taɓa rungumeni ya bani cake a bakin partyn birthday ina , Mamy tace gaskiya an samu matsala shi kanshi Binna da yasan waye Hafsa a wurinshi daya haɗe zuciya ya mutu , itama bata san wayenta ba , shima Baban Hafsa baisan ke wacecen shi ba , kowa iskanci ² gaba ɗayan ahali sun zama *KWARATA...*
Cikin rashin fahimta nace su waye ahali ɗayan ? Murmushi tayi tare da cewa wai dani da mijina shima neman matan bariki yakeyi , murmushi nayi nima dan ban taɓa daukar akwai wani abu ba , saidai tacemin da Baban Amisty da Baban Hafsa na fita hanyarsu tsohuwar motace su koda mai sai an tura , na gane karatunta kalami ne na matan bariki ,
Kallon inda su Amisty suke suna fira da Babana cikin tsantsar soyayya akwai soyayyar Babana mai zafi a cikin kwayar idon ko waccensu , sun tsareshi da ido daga gani sunajin daɗin kallonshi dan Babana yana kyau sosai gaskiya kuma ɗan gayu ne ƙirƙirar farko yana da aji kuma yanayin komai nasa cikin tsari da burgewa , tabbas saboda Babana su Amisty suka ƙyaleni amma da ba haka ba idan duk katsina dangina ne babu wanda ya isa ya kwaceni a hannun su Amisty...
Cikin gida muka nufa da Mamy amma zuciyata tana tamin tariya akan maganar Mamy ,
_Gaskiya an samu matsala shi kanshi Binna da yasan waye Hafsa a wurinshi daya haɗe zuciya ya mutu , itama bata san wayenta ba , shima Baban Hafsa baisan ke wacecen shi ba , kowa iskanci ² gaba ɗayan ahali sun zama *KWARATA...*_
Juyawa naji kaina nayi kwalwata na zakuɗawa wasu abubuwa sunamin yawo a cikin kai da sauri na rufe idanuwana jikina ya fara kyarma lokaci guda zufa ta ketomin kaina da tunanin da nake dashi da wani sauran sani ya juye kwalwata ta sake toshewa , na sake tashi wata kidahuma ta karfi da yaji.....
Gaba ɗaya saina manta maganar da nayi da Mamy nayi ² na tuno amma sai zuciyata tacemin bamuyi wata magana ba , duk yanda naso na tuno wallahi gaba ɗaya komai ya goce daga cikin kaina , amma ban manta na fitar da Babana waje ba kuma na riƙe nabar su Amisty kuma na tuna nayi waya da Dikko amma sauran maganganun sun ɓacemin ,
Ina ƙofar ɗaki tsaye Mamy ta miƙomin waya cewa ana kiranki , da sauri na ansa na ɗauka , An mata Dikko ya kirani a cikin wata irin murya yace meke damunki ne ? Ba komai na bashi ansa , yace karki min ƙarya meke damunki ne ? Tunani na fara yi , sassauta murya yayi yace me kikeyi yanzu ? Ba komai , kina yanayin tsayuwa ko zama ? Nace tsaye nake , An mata zaki iya faɗamin ko wane iri ne Dikko ? Shiru nayi ina tunani , yace tuna ² An matana , har yanzu kaina juyawa yakeyi , yace kin tuno ko wane iri ne Dikko ko ?
Wallahi Dikkon ma ya ɓacemin , An mata tsaya kiji kin tuna nine mukayi fada dake har kika mareni , kin tuna ? Eh na ganeka , amma me yasa kamin wannan bayanin ne ? Murmushi yayi tare da cewa kawai mafarki nayi wai kin manta dani shine nayi sauri na tashi a baccin na kiraki dan Allah kimin adalici karki manta dani kinji An mata , nace tou yawwa An matana..... Muah yai sumbata , murmushi nayi cikin yanayin jin kunya na kashe wayar....
Ɗaki na shiga na ɗauko wayar budurwar Dikko ina zama kusa da Mamy nace ciro layin ciki ki saka a wayar nan.....
27/09/2019
*JAMILA MUSA....* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 43
*_Ina miƙo saƙon ta'aziyya gareki HALIMATU SADIYYA MUHAMMAD { Leema } Allah ya bada haƙuri ya jiƙanta yasa ta huta mu kuma ya kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo..._*
*_Don Allah dan Annabin rahma kuyi haƙuri yadda labarin yazo min kenan haka nake rubuta shi_*
Me za'ayi da layin idan an ciroshi ne ? Shine tambayar da Mamy tayimin , kallo nabi Mamy dashi yayin da nima nake tambayarta wane irin layi kuma...? Mamy tace kina miƙomin waya ne kince na cire layin ciki na saka a wannan wayar shine nace meye ?
A ni ban wani faɗa ba ko dai kin fara ƙarya ne Mamy ? Nifa bana san ƙarya da kika ganni ƙatuwa dake bakyajin kunyar Allah bare kunya na kike nema kijamin sharri ko ? Tou tashi fitar min ɗaki , kamar sakara haka Mamy ta tsaya tana kallona , a hayagagance nace fita....... Da Allah malama , na faɗi maganar ina nuna mata hanyar fita , kallona Mamy tayi sosai tace ke Sultana anya kina da lissafi kuwa ?
A , a banda shi sai ke kika iya malamar lissafi , kila ma kece makarantar boko gaba ɗaga ko ? Murmushi Mamy tayi tabi Sultana da kallo cikin yanayin tausayawa , shi yasa ramuwa ga ramuwar abinda akayi maka babu kyau ka rama sharri ga sharri , Binna kuma idan har na faɗa mishi komai tabbas rayuwar yarinyar nan zata ƙare a gariri ne kawai , tun farko da bai anshi buduricin matar Bello a daren farko ba duk da haka bata faru da tilon "yar shi da ya ɗauki soyayyar duniya da ƙauna ya ɗora mata , dogon tunani Mamy ta tafi , tunanin abinda ya wuce shekaru da yawa shine wani sashe na daban yazo mata a kanta...
_Cikin farin ciki Binna ya shigo gidansu , dan dashi da Bello kowa baya ma kowa iyaka da shiga gidan kowa , kowa kai tsaye yake shiga..._
_Bello yana zaune tsakar gida Binna ya rungume shi cikin farin ciki da in ina yace kai banzan abokina an haifomin balarabiya yanzu na aihu a duniya duk na gaba hoton banza ne , kaga yarinyar kuwa ? Kyakkyawa da ita gata fara , burina akan ta zai sauka , itace Uwar masu gida dama nace sai an haifomin mai kyau zansa sunan mahaifiyata , zan gina mata rayuwa mai kyau dan ina so inyi alfahari da ita..._
_Murmushin yaƙe Bello yayi tare da cewa wane irin farin ciki kake ji a yau ɗin nan ? Binna yace baya musultuwa , Bello yace yanzu alal misali yarinyar nan sai kawai ayi mata fyaɗ...... Ai bai gama faɗa ba Binna yakai mishi wani irin duka harsai da Bello ya suma , duka ɗayan da Binna yayi masa yasashi tafiya duniyar suma , da gudu Mamy ta ɗauko ruwa ta yayyafawa Bello ya dawo , kallon Binna yayi tare da cewa alal misali fa kawai nace ! 👌🏻 Binna baiyi magana ba sai huci yakeyi kamar ɗan matashin zaki , jinjina kai Bello yayi tare da cewe hakan ya nunamin irin soyayyar da kake yi wa yarinyar nan , tsoki Binna yayi ya fice daga gidan..._
_Fitar Binna Bello yayi dariya tare da kallon Mamy yace wallahi tabon da Binna yamin yana nan bazai taɓa gogewa ba , shi a