Showing 54001 words to 57000 words out of 161239 words

Chapter 19 - KWARATA

Start ads

28 Aug 2025

617

Middle Ads

mukayi sallama ya shiga mota tare da cewa karfa kiyi wasa da takardun motar nan ki adana su kinji ko ? Sai yanzu na gane abinda takardun suke nufi godiya nayi masa suka wuce ni kuma na koma gida...

Ina shiga gida Hafsa na ba makullin nace kije ki ajiyemin zan ɗauko ta ƙarshen satin nan insha Allah, ansar mukulin tayi taci gaba da maganar ta, kallonta nayi sannan nace saurara kiji, kije ki ajiyemin mota ki dawo, tashi tayi ita dasu Saude suka tafi ni kuma na shiga ɗakina, ban daɗe da shiga ba Nana ta shigo tare da bani number matar Bello amma bata samo na ɗanshi ba , ansa nayi da nayi niyar bata 500 sai wata zuciyar tace kawai in bata 1k in ka nema ma ka samu ai arziƙi ne...

Jakata na buɗe na bata 1k nayi godiya, itama godiya tamin ta fice a ɗakin, tana fita na kulle ƙofa na kwanta saman katifa na fashe da kuka mara sauti , duk duniya babu wanda ya taɓa wulaƙanta ni kamar Dikko nice zai bawa cingom in bakinshi da yawun bakinshi na haɗe a cikin cikina , duk duniya babu abinda yakai miyau saurin sadar da shaƙuwa, shi yasa masu wayau ko bariki suke basa yadda suna haɗa bakunansu da na wasu, waccan ranar bai haɗa bakinmu ba amma shine yau ya ciro abu daga cikin bakinshi ya bani, yana da wata manufa ta daban shine dalilin da yasa yace ma Al ' Ameen bara suga magani na, wato wannan dalilin ne yasa kowa ya juya mana baya ko ? Saida na goge hawaye na sannan nace ƙarya kakeyi yawun bakin ka bazai taɓa zama hukunci a gareni ba...

Nayi kuka har na gode Allah daga baya kuma bacci ya kwasheni wanda bansa lokacin daya zo ba kuma baiyi shawara dani ba,

Washe gari koda na tashi nayi sallah bacci na koma bayan na gama kwashewa Dikko karama , misalin 09:30am Alhaji yasa aka kirani a waya, bayan na ɗauka nayi sallama dakel Alhaji ya amsamin sallamar cikin nishi yace Sultana ina federal medical center { F M C } saida ya sake yin nishi cikin yanayin wahaltuwa sannan yace ina nan Accident & Emargency kizo yanzu don Allah inasan zanyi magana dake....

Har a zuciyata banji daɗi ba cikin muryar tausayi nace kayi haɗari ne ? Hawaye ya gangaro masa daga cikin idonshi yace kizo dai dan bana tunanin zan ƙara awa ɗaya a cikin duniyar nan....

Subahanalla da Allah ka daina wannan maganar gani nan zuwa insha Allah, cikin rawar jiki na kashe wayata, da sauri na sauko daga saman katifa na zuba ruwa, a gaggauce naje nayo wanka tare da wanko bakina, mai fauda da kwalli kaɗai na shafa, baƙar riga ta jallabiya na saka na yana gyalen a saman kaina na zagoyo dashi har gashin kaina saida ya fito ta ƙasan gyalen jallabiyata, gilashi mai saukin duhu na saka sannan na wanke jikina da turaruka masu sanyi ƙamshi, masha Allah na faɗa a lokacin da naga kaina a cikin madubi, nayi kyau sosai na fito kamar baƙuwar balarabiya a nigeria,

Wayata na ɗauka da jakata, na fito ina tsaye ina kulle ɗaki Hafsa ta shigo, ita ɗaya ce babu abokan nata su Saude, su Nana ma duk basa tsakar gida, ɗan gangarowa tayi da wani irin salon tafiya, ta wutsiyar idona na kalleta sannan na ɗaure fuskata na kallota dukanta a daidai lokacin dana gama rufe ɗakina...

Wow uwar ɗakin karuwai kinyi kyau fa kamar dai ba'a mutu ba, share maganar nayi tare da cewa da mota kika zo ne ? Eh ta faɗa tare da bina da kallon cin wanka , gaba nayi tare da cewa muje ki saukeni f m c biyoni tayi muka fito a tare, a ƙofar gida muka haɗu dasu A ` i hada Amisty da Saudatu....

Amisty tace wurinki zamuje munji shiru har yanzu, kuma mun rubuto takarda an tsara jaddawalin yanda zai ƙawatar ya kuma tafi da hankalin maza gaki kuma zafi fita, buɗe gaban mota nayi na kame sannan nace ku shigo muje kuma, baya suka shiga, Hafsa kuma ta zauna mazaunin tuƙi taja muka tafi....

Saida muka fara tafiya sannan nace karanto min ina saurarenki, Amisty fa tasan komai tasan bana ganewa bana rubutawa kuma bana iya karantawa amma sai tace kidai duba ki gani Sultana, basar da ita nayi tare da miƙa hannuna ta baya na anso takarda ko buɗewa banyi ba na ajiye shegiya ban sake bi ta kanta ba kuma ban sake magana ba har muka isa asibitin...

Wani irin tuƙin ganganci Hafsa tayi tare da sakin sitiyarin saboda taga D --- K , a tare muka iso dasu sai leƙawa take tana kiranshi, wato abinda na fahimta idanma ka nunawa mutum ka damu dashi sai yayi ta ɗagawa, kallon Hafsa nayi tare da cewa ke kuwa baki da aji a haka kike tunanin zan riƙa haɗaki da zafafan mata babu class, raina ya ɓaci sannan nace uban waye Dikko da kike ta hauka kina kiranshi mutane suna kallonki kamar wata zararriya....

A daidai lokacin da muka fito mu dukanmu daga mota shima Dikko ya fito kuma yaji zagin da nayi masa , bai kallemu ba yayi gaba ana take masa baya nima gaba na shiga su Hafsa suka rufomin baya, murmushi Dikko yayi a daidai lokacin da muka tsaya bakin ƙofar ɗakin kowa da muƙarrabenshi a bayanshi, kallona Dikko yayi tare dayin murmushi sannan yace zaki ci ne an mata yayi tambayar tare da ɗaga gira ? Ya ƙarasa maganar tare dayimin wani irin kallo mai tattare da mugunta, yaci gaba da cin cingom inshi cikin salon jan hankali gemunshi yana motsawa a hankali cikin salon ɗaukar hankali , murmushi nayi saboda gaskiya yanayin da yayi ya burgeni, ƙarshen harshenshi ya kawo cingom in yayi wasa dashi a daidai lokacin da aka buɗe mana ƙofa duk muka shiga, daga waje bai sake kallona ba kuma bai sake murmushi ba babu magana har muka isa gaban gadon Alhaji...

Duk matan da muke tare ihu muka farayi saboda tsoron yanayi da Alhaji yake ciki yayin da wasu suka nufi hanyar fita, dani da A ` i aka bari yayin da A ` i ta duƙushe tana kuka ni kuma na cire gilashi na wurgar a gefe na rufe idanuwa na naci gaba da dire dire ina kuka saboda na kasa gaba na kasa baya....

Shi kuma Alhaji burinshi inje wurinshi in taimaki rayuwarshi na goge vidio sai kirana yake cikin dasasshiyar murya da yayi magana sai jini ya kwararo , Dikko yace ya daina magana amma yaƙi saurarenshi Sultana kawai yake kira,

Kusa dashi Dikko ya ɗuka sannan ya tambayashi me zan mishi ne ? Hawaye na zuba a idon Alhaji yace ma Dikko ya rufa mishi asiri ya kawoni wurinshi magana zamuyi ta sirri, Dikko yace faɗamin na faɗa mata kaga ta firgita wani abu zai samunta, cikin wahaltacciyarar murya Alhaji yace kayi min wannan arziƙin na sauran mintunan da suka ragemin a duniya lokacina yana tafiya zan iya mutuwa ko wane lokaci, yanda yayi maganar ne yasa Dikko ya kallo inda nake tsaye ina ta direre kamar anyi ma lafiyayyan diko allurar hauka.

Ɗauke idonshi yayi daga kaina sannan ya kalli zugar daya zo da ita, Al ` Ameen ya faɗa cikin wani irin yanayi kamar bashi ne yayi maganar ba, gaba ɗaya waje suka fita harda A ` i aka fita, inda gilashina yake Dikko yaje ya ɗauko sannan yazo kusa dani, ta gaban rigata ya jawo ya sagala gilashin sannan yace buɗe idonki, jikina yana kyarma na buɗe na kalli Dikko, dakel ya haɗe yawun bakinshi sannan ya tofar da cingom in bakinshi gaba ɗaya yanayin Dikko ya canza ɗaure fuska yayi sosai sannan yace miye tsakaninki da mara lafiyar nan ? Miye dalilinki na zuwa ganinshi ? Me kikaje yi gidanshi ? Kema "yar iska kike so ki zama ko ?

Cikin gatsali nace Ey "yar iska zan zama ina ruwanka da iskanci na ne ? Jinjina kai yayi tare da cewa Allah ya sawaƙe wuce muje yana kiranki, tirjewa nayi tare da juya zan fita da gudu ya riƙoni yace ai ƙarya kike sai kinje, har gaban Alhaji ya jani ya kaini sannan ya zaunar dani saman kujera ya tsaya ta bayana yace gata nan me tayi maka ne ? Ko kaima taci kuɗinka kamar yanda taci na Umar ?

Ɗaga kaina nayi na kallo Dikko ɓacin rai kwance a cikin idonshi zare min idanuwa yayi tare da cewa bari kallona kar fashe miki kwayar ido wallahi, jiki a sanyaye na sauko kaina daga kallon da nake ma Dikko naci gaba da kallon Alhaji ina kuka, dafo kujerar yayi ya duƙo kusa dani sosai saitin kunne na yace na rantse da girman Allah idan na gano akwai wani abu tsakaninki dashi saina kashe ki, ya faɗi maganar tare da shaƙemin wuya sosai na fara ƙoƙarin ƙwalƙwale hannunshi na kasa, tun ina iyawa har nasa wani abu na fara halbe halbe har na faɗo daga saman kujera Dikko bai saki wuyana ba naci gaba da halbe halbe, yanda nake halhalbe ya jawo hankalin mutane suka yo kanmu amma an kasa cire hannun Dikko daga wuyana,

Hayani tayi yawa sosai wanda yasa su Al ` Ameen suka shigo ciki da gudu amma wallahi duk yawan mazan nan suka kasa ɓanɓareni daga hannun Dikko harsai dana suma, riƙe Al ` Ameen yake da hannun Dikko yana cewa don girman Allah mai gida ka ƙyale yarinyar nan karta mutu, zaro jajayen idanuwan shi yayi kamar yaci mutuwa yace fita idona Al ` Amenn ya faɗi maganar yana fitar da wani irin lumfashi kamar ranshi zai fita, Al ` Ameen kuwa ƙin sakin hannun Dikko yayi saboda tunda yaga Dikko a wannan yanayin yasan komai zai iya faruwa....

Yace mai gida karta mutu, Dikko yace ta mutu idan ta mutu kaine ka kashe ta ko kaine zakayi azumi ? Ya ƙarasa maganar tare da kwalalo idanuwanshi waje , sannan yace duk abinda ya faru da ita nine ya ƙarasa maganar tare da nuna kanshi, haƙuri akayi taba dikko dakel aka samu ya sakeni ,

Bakin gadon Alhaji ya koma ya ɗauki wayarshi iyakar bincike Dikko yayi bai samu komai ba, kuma number na dama Alhaji baiyi saving ba, jerin kira ya dawo yaci gaba da binke, saida ya gama sannan ya ajiye wayar , kallo gadon da nake kwance yayi har an sakamin ƙarin ruwa da taimakon Al ' Ameen dayayi tsaye yace a bani taimakon gaggawa,

Kusa da Al ' Ameen yaje tare da cewa bani makullin mota, cikin girmamawa ya ɗauko ya bashi baiyi mishi musu ba saboda yasan Dikko baya san gardama idan yace ayi kawai ayi mishi idan yace a bari barin kawai za'ayi sai a zauna lafiya,

Cingom ya ciro daga aljihu ya ɓanɓare ya saka bakinshi yaci gaba daci, Al ' Ameen kuwa bin Dikko yayi da kallo harya fita daga ɗakin yana mamakin hali irin na Dikko zuciyarshi tayi yawa idan ya burkuce wani lokaci kamar bashi ne yakeyi wasu abubuwan ba...

Ta jikin window ya leƙa Dikko, har ya shiga motar yaja ya tafi cikin tuƙinshi na ganganci wanda baya kaucewa kuma baya ɗagawa kowa ƙafa idan ya tafi sai yakai inda zaije hankalinshi yake kwanciya, Allah ya tsare hanya Al ' Ameen ya faɗa tare da dawowa wurin gado na ya tsaya, su Hafsa da Saude da A ` i da Amisty sunyi jigum kowa yana jiran farfaɗowa ta yaji abinda ya haɗani da D --- K......

Dikko kuwa tuƙi yake amma yana tunanin maganar Alhaji ranka ya daɗe wato wallahi wata yarinya ce muka ɗan keɓe da ita , tou wallahi bansan yarinyar nan ta shirya sharri ba, ashe duk abinda mukayi ranka ya daɗe tana ɗauka cikin waya ban sani ba....

Dukan sitiyari Dikko yayi tare da cewa tabbas yacemin yarinyar nan shekarunta bazai wuce 16 zuwa 17 ba daidai saitin zuciyarshi ya daka tare da cewa kece .... ?

Akan titi duk ƙurewar wuri Dikko ya juya kan sitiyarin mota ya koma baya ba abinda ya dameshi da halin da wani zai shiga kanshi kawai yakeji amma baya sauraren talakawansu, da gudu ya ibi shararra ya komo asibiti, a lokacin su Al ' Ameen sun fito zasu tafi ganin Dikko ya dawo yasa Al ' Ameen ya dawo cikin ɗakin da gudu yasa aka ɓoyeni, danshi Alhaji tuni Allah ya anshi rayuwarshi har an tafi da gawarshi, duk zunubin da Alhaji ya cacumar ma kanshi an samu wani marar rabo a lahira ya dira gidanshi yayi mishi caccakar wulaƙanci aka kawoshi asibiti dan ceton rayuwarshi Allah yasa ikar ibar da yayo kenan, Allah ya jiƙanshi yasa mu cika da imani ubangiji ya kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo...

Ana ɓoyeni su Al ` Ameen suka fito, a waje suka haɗu da Dikko yana ƙoƙarin shiga suka faɗa mishi mutuwar Alhaji ni kuma an canja min asibiti, Allahu Akbar Dikko ya faɗa tare da cewa ubangiji ya ƙarɓi baƙuncinka Muntari Allah ya kyautata tamu bayan taku, da Amin kowa ya ansa sannan suka tafi a tattare baki ɗayansu...





25/08/2019


Taku a kullum

*MEELAT MUSA...*


⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 19



Har yanzu kalar idon Dikko bai koma fari ba, idon nan jajir kamar yaci bala'e, amma a hankali yake washewa zuwa kalarshi ta ainahi, fuskar nan a murtuke ya jingina bayan shi da kujerar mota kana kallonshi kasan yana tattare da tsantsar damuwa.

Ɗan gajeren tsoki yayi tare da gyara zamanshi, hannunshi yakai ya shafe gefen fuskar shi, tunanin safiyar haɗuwarshi da Sultana ya fara dawo mishi sabo fitikil kamar yanzu ne abun yake faruwa, da sauri ya rumtse idanuwan shi tare da haɗe leɓunan sa wuri ɗaya ya danne su da haƙoranshi ta ciki, buɗe ƙofafin hancin shi yayi saboda lumfashin da yake shaƙa yayi mishi kaɗan ya buɗe ƙoƙofin hancin ne dan iskan ya yalwace shi.

Har suka isa gidan rasuwa Dikko bai sake ma kowa magana ba, tunda dama shi ba ma'abokin surutu bane, mota nayi parking ya fita cikin damuwa danshi dama kullum haka yanayin shi yake , farin ciki da ɓakin ciki duk yanayin iri ɗaya ne a wurin shi, babu wanda ya isa yasan lokacin farin cikinshi kuma babu wanda ya isa yasan lokacin da yake damuwa.

Tunda ya fito aka fara gyara mishi wurin da zai zauna dan zamanin ga mutane basa abu domin Allah basa darata girma shekaru da mutumci amma suna ba naira matsayi na musamma, Dikko yana da rashin mutunci amma alherinshi yasa mutane basa ganin rashin mutuncin nashi dan Allah yayi masa kyauta idan dai kukayi ido ido dashi tou tabbas zai baki kuma baya da kwauro idan zai bayar mai yawa yake baka, tou kyautar itace ta danne rashin mutuncin shi ga idanuwan al'ummar gari...

Sabuwar tabarma aka amso daga cikin gidan aka shimfida mishi, takalman shi ya cire ya taka tabarmar da safa, saida ya zauna sannan kowa ya zauna kuɗi suka fara nuna ikonsu domin masu neman asan dasu sukayi ta zubewa suna bada gaisuwa, saida ya jinjina kai dan shi kaɗai yasan tsutsar baƙin cikin dake lasar masa zuciya...

Wanda suka bawa duniya gaba ne suka fara bawa Dikko labarin yadda abun ya faru amma a zahirance yana jinsu amma a baɗinance hankali shi yana wurin Sultana so yake kawai a dawo jana'iza yaje ya ganota wallahi sai ta faɗa mishi miye tsakaninta da Muntari, inma banda take daƙiƙiya dan ta tona mishi asiri shine zai haɗa kirji da ita taje ita kuma ta haɗa da yaronshi...

Wayarshi ya ciro yayi "yan rubuce rubuce bayan ya gama ya tura, wayar shi ya maida aljihun gaban riga a zuciyarshi kuwa yana tunani Sultana ta gama barbaɗashi a duniya kowa kallon ɗan iska yake mishi,

Mikewa tsaye sukayi gaba ɗaya dan an fito da mankara, sai yanzu wasu keyin alwalla shidai yana da ita takalmin shi ya saka suka fita sarari dan sallatar

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login