Showing 12001 words to 15000 words out of 161239 words

Chapter 5 - KWARATA

Start ads

28 Aug 2025

574

Middle Ads

gidan kai tsaye, a kofar get in gidan nayi ma mai gadin gidan sallama, ya ansa cikin sakin fuska, nace mishi dama wani mutum ne da jajayen kaya a jikinshi yace in turo mishi kai yana can yana jiranka..... Na nuna mishi hanyar da Dikko ya wuce da hannuna ,

Cikin sauri ya wuceni ya tafi, yana wucewa na shiga cikin gidan, doki d'aya ne kad'ai wato shine dokin da Dikko ya dawo dashi, an d'aureshi a gefe kuma an cika bokiti da ruwa an ajiye shi kuma dokin yana ta bubbud'a hanci yana maida numfashi,

Da sauri na kinkimi bokitin ruwan nakai gaban dokin na ajiye, aiko ina ajiyewa ya duk'ar da kanshi yaci gaba dashan ruwa, a daidai lokacin da mai gadi ya shigo dan yabi hanya baiga Dikko ba ya dawo,

Kay kay kay ba'a bashi ruwa yana k'ok'arin isa dan d'auke ruwan na tareshi tare da cewa anshi yace ka ajiye mishi wannan takardar idan yazo da daddare zai karb'a, bai tsaya ansar takardar ba kuma baimin magana ba ya wuce,

Murmushin nasara nayi daga cikin nik'af ina sannan naje na ijiye masa takardar a saman kujerar da yake zama na wuce abuna.

Kafin ya isa tuni doki ya shanye ruwan dana ajiye mashi, sai dai abinda ba'a rasa ba, cikin tashin hankali ya ciro wayarshi daga cikin aljihu ya fara kiran wayar Dikko,

Mai gida kazo akwai matsala dokin daka dawo dashi yanzu, gashi nan zai mutu, yana fad'in haka ya kashe wayarshi,

Cikin k'ank'anin lokaci Dikko ya iso, a k'ofar gidan yayi parking ya fita da sauri ko murfin motar bai tsaya rufewa ba, lokacin daya shiga cikin gidan tuni dokin ya kwantar da kanshi k'asa yana ta zabura irin na fitar rai.

Meya faru haka ne ? Dikko ya tambayi mai gadin shi ! Cikin daburcewa ya fad'awa Dikko duk yanda mukayi dashi , sannan ya d'ora da cewa ga takardar can daka bata ta kawo ta ajiye, ajiyar zuciya Dikko yayi tare da furta wace ce ita tayimin k'arya ?

'Daukomin takaddar kila tana da wata manufarta a ciki, d'aukowa yayi yakai mishi, ya warware ya duba, cimimiye takardar Dikko yayi bayan ya gama karantawa ya dink'uleta wuri d'aya sannan ya jinjina kanshi, ya fito da sauri daga cikin gidan,

Wurin motarshi ya tsaya, tare da kaima gaban motar duka sannan yace wallahi cikin k'ank'anin lokaci duk inda "yar iskar yarinyar nan take cikin garin nan ku d'auko min ita, yana fadi haka ya shiga mota yaja fa fafa ya tafi kamar zai tashi sama.......

Har yayi nisa ya dawo, har yanzu mai gadin bai koma cikin gidan ba yana nan tsaye a wurin, yanzu daya dawo bai fito ba ya sauke glashin motar shi sannan yace, ku kawota wurina zan nuna mata nid'in d'and'an Babana ne wallahi wallahi wallahi sai tayi nadamar zuwanta duniya.

Yana fad'in haka ya juya a guje ya tafi, lallai da ganin yanayin shi gaskiya ranshi a b'ace yake, tabbas idan har aka kamoni aka kawai Dikko ni a cikin wannan yanayin lallai Dikko kasheni zaiyi,

Lokaci d'aya jikina ya d'auki kyarma naji fitsari ya kamani sosai, "yan hanjina suka juya ai bansan lokacin dana bar wurin ba, cikin tashin hankali na hau napep na nufi filin gidanmu, tun kafin mu isa na dire nayi gida da gudu........

Da sallama na shiga, Babana na gani zaune dashi da abokanshi kuma sune suka amsa min sallama, cikin farin ciki ya kalleni tare da cewa daga ina kike Mamana ?

Cikin inda inda na sosa kaina tare da cewa daga gidansu k'awata nake, murmushi Babana yayi tare da mik'ewa yace muje waje muyi magana, naso nayi masa gardama dan gani nakeyi kamar idan na fita zanga Dikko k'ofar gidanmu,

Muna fita na fara tambayar shi ya akayi ya dawo ? Yace min su Bello sukayo belin inshi, akwai wani wasan caca da za'ayi an saka naira miliyan hamsin kin san na kware sosai a wasan caca babu wasan cacar da za'ayi a ci ni saidai ni in ciwo shi yasa ake min hassada.

Gyara tsayuwar shi yayi tare da d'an jan dogon hancinsa, sannan yace Mamana kinsan ba'ayin wasan caca a bashi sai an saka k'addara, bani da k'addara sai kayan sakawata, na saka amma ance ba'asan sutura, tou Bello ya bani shawara wai in sakaki a matsayin k'addarata,

Cikin rashin fahimta nace Baba kamar ya za'a sakani a matsayin k'addara bayn nima banda komai... Murmushi yayi tare da cewa Mamana kenan ai kuwa kece ma mai komai domin keda kanki kece babbar k'addara ta shi yasa na zab'eki a cikin duk "ya "yan hamsin da takwas dana aifa.....

Kiyi hak'uri kawai ki yadda duk wanda yazo ya tambayeki kece k'addarata kawai kice Eh, danni na yadda da kaina babu ubanda ya isa ya ciwo uwata a wasan caca saidai ni inciwo uwarshi wallahi, Mamana ki yadda da Babanki nayi alk'awari baza a samu matsala ba, ki yadda dani kinji Uwar masu gida, ya k'arasa maganar yana mai rik'e duka hannaye na duka biyun yayi kalar tausayi.

Tou Babana idan aka tambayeni zance Eh kawai ko ? Yawwa Eh zaki ce kawai ya wadatar, insha Allah gobe kamar yanzu muna cikin kud'i kuma ga Uwata a tare dani, ya k'arasa maganar cikin farin ciki, murmushi nayi mishi sannan muka koma cikin gida dan in fad'awa su Bello na yadda..........




Allah yasa muyi juma'a lafiya, ubangiji ya sadamu da alkairan dake cikin wannan juma'a mai albarka, mugun ji da mugun gani tsaka mai wuya ubangiji ya tsare daga garesu, Allah ya karemu da jin kunyar duniya da lahira. Am3n,


Jamila Musa ce 🤙🏻



02/08/2019

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 5

Muna shiga ciki tun kafin mu k'arasa inda suke zaune Baba ya fara cewa tou gata nan ku tambayeta kuji, a daidai lokacin da muka iso gabansu.

Ina k'ok'arin durk'usawa Bello yace a , a basai na zauna ba in tsaya a tsaye akwai abinda yake dubawa.

'Dan b'ata fuska Babana yayi tare da cewa kamar ya kana duba wani abu ? Ai a cikin sharud'd'an babu maganar wani dube dube, dan haka kabar yarinya ta zauna ka wani daina yi mata kallon k'urulla saboda rake ba sa'ar tsoho bane ba, dan koya bada kudin sa ya siya saiya ajiye tunda baida hak'oran cizawa, ya k'arasa maganar cikin sigar duniyanci.

Murmushi Bello yayi tare da cewa, ai zamani tafiye yake da ci gaba ko ba'a tauna ba a tsotsa, d'an b'ata rai Babana yayi tare da cewa, kaga da Allah mubar wannan maganar muyi abinda ya had'amu, ya k'arasa maganar cikin nuna rashin jin dad'in zancen nasu.

Gyara zama Bello yayi tare da cewa, haba Aliyu kasanni fa farin sani, kuma haka nima nasanka ciki da wajen ka, wane dare ne jemage bai gani ba ? Na hau tudu nabi ta gangare, kasan ko inacin kwarika wannan kwaron yayi min k'ank'anta shi yasa kaga bana cin shinge saboda na raina girmanshi duk da kuwa yana da mai sosai nafi gane kura ko da kuwa an soyata babu magi ba gishiri, kalmar dai d'ayace ake kira amma wurin hidimar da banbanci karka samu damuwa yaro ne sabon jini kuma bak'one a harka, yasan dad'in komai a duniya amma har yanzu baisan dad'in mace ba shi yasa kaga inata k'ara dubawa dan bana san a samu damuwa,

Dariyar mugunta yayi tare da cewa , wash ashe na manta malamar Babanta jarumin gaske ne a harkar wasan caca, Shima Babana murmushi yayi amma da ganin murmushi kasan na b'acin rai ne, yace Bello kenan, shiga ramin kura ba abu ne mai sauk'i ba, idan har kaga na fad'i a wasan cacar nan tabbas duk wanda yayi k'ok'arin kusantar min Mama saina ga bayanshi, wannan shine sharadi na,

Bello kuma cewa yayi kar muyi haka dakai Aliyu yaron nan d'an rigima ne, mu daina wannan maganar kawai dai muyi fatan Allah yaba mai rabo nasara, kallona yayi tare da cewa kin amince ? Jinjina kaina nayi tare da kallon Babana sannan nace na yadda............ Dariya Bello yayi tare da cewa magana ta k'are mata tacewa mijinta shege,

Kafad'ar Babana ya daka tare da cewa Aliyu muje, juyowa yayi ya kaleni tare da cewa yarinya ki shirya, idan kinga Babanki tou fa lallai an ciki a wasan caca, idan kuma kika ga Bello tou Babanki ya cinye matashin nan, ganinmu shine zai tabbatar miki Babanki yaci caca mu kuma munzo miki murna ne, suna fad'in haka sukayi gaba abunsu,

Bayan tafiyarsu ina zaune suku suku dani kamar asirin mayya ya tonu, ni ba Babana ne damuwata ba Dikko shine tashin hankalina, yace duk inda nake a gano ni, sai yanzu na gane na tafka babban kuskure dana rubuta suna na a jikin takarda, lallai na cika babban dak'ik'iya.

A b'an garen Dikko kuwa nema na sukeyi kamar rai da mutuwa, babu wanda yasan inda muka koma, daga makaranta prymary babu wanda ya sake jin labarinmu,

Rashin gani na yasa suka fara ba Dikko hak'uri, amma fur Dikko yace wallahi kafin sha biyun dare sai an nemoni idan har ba'a ganni ba zai iya sargafe kanshi ya mutu,

Duk iyakar yanda suka so Dikko ya hak'ura ya k'iya, ba nemoni bane wahala a wurinsu suna tausayin irin a zaftuwar da zanyi a wurin Dikko, dan ya fad'a musu ba mutuwar dokin ya b'ata masa rai ba, d'an marasa tarbiya dana kirashi dashi, bama shine baida tarbiyar ba iyayenshi ne basu da tarbiya abinda nake nufi kenan,sai kuma idan ya fasa shi ba d'an Babanshi bane. Wannan sune munanan kalamai masu muni da suke ta zungurar zuciyar Dikko.

Dikko yana da zuciya sosai, kuma fushin shi baya da kyan gani, idan ya nace akan abu sai yayi babu wanda ya isa ya hanashi, idan yace bayayi babu wanda ya isa ya tursasa masa yayi abinda baisa kanshi ba.

Yau Dikko yana cikin matsanan cin b'acin rai, yayin da ni kuma nake cikin fargaba da tashin hankali, dan yanayin dana ga Dikko d'azu ya bani tsoro,

Duk wanda yaji wannan abun yasan nice bani da gaskiya, domin ni naje har inda yake na jawoshi fad'a, ya Allah ka rabani da Dikko daga yau insha Allah bazan sake janshi fad'a ba, ka mantar mishi dani a rayuwarshi kuma ka bashi hak'uri a zuciyarshi, ya daina nemana,

Misalin 10:45pm Babana ya dawo gida, dashi da abokinshi Bello a lokacin har nayi bacci Baba yasa a tadoni in samesu kofar gida......

A waje na samesu, gaishe su nayi tare dayi musu sannu da zuwa, Bello kad'ai ya ansa amma Babana ya kasa magana, Bello ne ya fara magana kamar haka.

Maryam, wannan shine sunan da Babana ya sakamin, wato sunan mahaifiyar shi, darajar wannan suna ne yake kirana da Uwar masu gida ko yace Mamana, Bello yaci gaba da cewa an samu matsala mahassada suka cuci Babanki bandai san yanda abun ya faru ba gab da za'a fara wasa kwalwarshi ta juya, ba buk'atar dogon bayani kawai dai Aliyu ya fad'i wasa.

Tou idan ya fad'i sai kayi ya ya kenan ? Na tambayi Bello, sai zamu tafi dake wurin wanda ya ranta masa kud'in, dan a can basu yadda da ansar mace ba, sai wani ya buk'ata dan haka ya bada kud'in yace a kawo mishi ke,

Waye shi ? Na sake tambaya, a tak'aice ya bani amsa cewa idan kinje kin ganshi, zan k'ara magana Babana yace Mamana babu abinda zai faru kiyi hak'uri kuje dan bana tunanin akwai wanda ya isa yayi miki wani abu a cikinsu saboda sun san waye ni, na bud'e bakina zan sakeyin magana a karo na biyu, wanda Babana ya sake tare min numfashi na da cewa idan dai har kare zai iya farautar kura tou lallai wani abu zai iya shiga tsakaninku, idan kuwa kare bazai iya ba tabbas zasu dawo dake, dan duk rashin kunyar kare ta gida ce, bishi kuje.... Yana fad'in haka ya juya da zumar shiga gida,

Da gudu nabi bayan Babana na rik'e hannunshi ina kuka nace haba Babana laifin me nayi maka zaka sayar dani ? Cikin kulawa ya kalleni tare da gogemin hawayen da suka zubo saman fuska ta sannan yace, baki sawuwa Mamana saboda nima bada kud'i nasiyo ki ba, haka kuma bakya satuwa tunda Allah shine ya azurtani dake, hak'ik'a kuma baza ki ciwo ba ta sanadiyar wasan caca ko kun tafi sai kun dawo, dan haka ki zama d'iya mai biyayya a gareni,....

Baba.....Mamana ya fad'a kafin nace komai, yaci gaba da cewa, so guda d'aya ne tal a zuciyar ko wane d'an adam, amma shi wannan san a duniya za'a kasa shi kaso mutane so adadin haka, uwa, uba, d'a da kuma mata, banda uwa banda uba, kuma ni Allah bai d'oranmin ciwon son "ya "ya ba, bare mace da ban d'auketa a bakin komai ba, wannan son nawa gaba d'aya kece na martaba ki dashi saboda ki zamo d'iya mai sharewa Babanta damuwa. Sakin hannu na yayi tare da cewa sai kun dawo, yana fad'in haka ya shigr gida.

Inaji ina gani suka tasa k'eyata gaba suka sakani mota mukabar k'ofar gidanmu, tafiya mukayi mai nisa sosai, sannan Bello da abokinshi daya taho dashi suka fara magana,

Bello yace, alhamdulillah na zurashi rami na gama, kasan Aliyu yana tak'ama da tasha ni kuma zan k'ure mishi tashi tashar shi dan abinda yayi min bazan manta dashi ba nima saina rama akan wannan d'iyar tashi daya d'auka san duniya ya d'ora mata,

Bello yaci gaba da cewa nine na bada kud'in nan cas saida na ajiyesu sannan akayi caca, bana asara zan kaita inda za'a bani kud'ina har a d'ora mani riba, ina tsoron wai wai da bayan da Aliyu zaiyi wallahi da nine zanyi mata kaca kaca da rayuwa amma yanzu zan kaita wurin gwamnati idan zai iya yayi fad'a da hukuma in gani.

Ai kaji shi wai Allah baisa mishi ciwon san "ya "ya ba, nima shi yasa ban zab'i ko d'aya daga cikinsu ba dan nasan duk wacce na d'auka abin bazai mishi ciwo ba, nima ina so in dasa masa irin tabon daya dab'a min a zuciyata wanda bansan ranar da zai gogo ba,

Ajiyar zuciya Bello ya sauke tare da cewa da Allah sake kiransu ni fa ba abinda ya dameni da wani fushin banzar shi, dan ba fushi yakeyi ba ko mutuwa akayi mishi ni kawai tafiya zanyi idan munje can ayita ta k'are, abokinsa yace to idan masu gadi suka hanamu shiga fa ? Daina min ma wannan bak'ar fatar taka da Allah, duba min magungunan nan Allah yasa ban zubar dasu ba wurin wancan sakaran, wata "yar k'aramar leda ya d'auko ya mik'a ma Bello tare da cewa gasu nan, dariya Bello yayi sosai tare da cewa kasan bak'one dole saida "yan rakiya,

A daidai lokacin daya fara magana a waya, nifa dama basai yana harkar mata ba, to dama banda abinka duk wanda kaga yana harkar mata ai koya yayi, nifa taimaka min zaiyi kuma na taimakeshi, saurara ka taimaka mana kazo ka shigar damu gidan idan muka shiga duk nasan yanda zanyi da Allah, tou babu damuwa gamu nan isowa ba jimawa, haka yayi wayarshi har ya gama, yakan d'auke maganar sa danjin abinda abokin wayar tasa zai fad'a, yana fad'in haka yaja

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login