Showing 3001 words to 6000 words out of 161239 words
shiga, fitsari nayi na fito, a tsakar gida na wanke cinyoyina, nayi alwallah na dawo daki.
Tun ina sallah Babana yake kirana tare da cewa uwar masu gida kiyi sauri mun makara naga har 7:30am, bana so Baba yana bina makarantar boko saboda duk kawata daya gani sai ya bita gidansu ni wannan abun yanamin ciwo.
Tsaye na ganshi a kofar dakin mu yana daura agogo sai zuba kamshi yake yasha farar shadda sai daukar ido yake, murmushi nayi a zuciyata nace Baba kenan ko ba'aba ciki ba aba kaya,
Katsemin zance zuci yayi da cewa maida hankali Mama mu tafi, mikewa nayi ba tare da nayi magana ba naci gaba da shiri, a gaggauce na shirya, tare da shafa "yar madara nace zan rago miki, Babana ya rikemin jakar makaranta muka fito daga gida.......
_Gaba daya kaine sile, dan iska domin ni kai zan kira da kwarto, kaine silar rushewar rayuwata_
Cikin farin ciki muka fito daga gida, ina fadawa Babana yabi sannu karya bata jikinsa kasancewar ruwan daya kwanta saman kasa,
Cikin jin dadi muke tafe muna fira, har mun kusa fita bakin titi ya sheko da gudu tuki na rainin hankali, tuki na gadara, tuki na wulakanci da rashin arziki, tukun da basa kaucewa mutane saidai mutane su kwauce masa, duk lokacin da zai shigo anguwar nan haka yake shigowa idan ya taka mutum ya taka banza, ko dabbobi gareka saidai ka daure abunka amma badai maganar ka sakesu ba.
Tunda na hango motar nake cewa Baba dawo ta nan, amma kafin Baba ya hayo inda nake tuni yabi takan ruwan ya wuce shaddar baba ta koma brown, iya wuya raina ya baci kuma nayi alkawari ko zai kasheni tunda har ya tabomin Babana sai naci uwarshi a safiyar nan.
Da gudu nabi motar ina watse hannuwa na yanda ake zagi dakkuwa, ina zaginsa, shima Baba biyoni yayi da gudu cikin tashin hankali, yana Mamana dawo, wanda yayi nisa bayajin kira, a kofar gidanshi da yake kiwon dokunan shi anan Baba ya sameni ya rikeni, shi kuma ya fito daga motar da bulala dorina irin wacce ake dukan dokuna da ita.
Zagin dana taho inayi shi ya jawo hankalin mutane yasa duk mutane suka fito daga gidajen su, wanda ke waje suka iso wurin da muke dan ganin kwam,
Rikeni sosai Babana yayi tare da rufemin baki saboda yasan ban iya zuciya ba, shima abokansa da sauri suka rikeshi tare da cewa *Dikko* karka daketa dan Allah yi hakuri, Babana kuma cewa yakeyi ranka ya dade kayi hakuri don Allah bata san kaine ba,
Raina baci yayi ganin kamar mahaifina yana bawa yaron da haifa hakuri, dan haka na bambare hannun Babana daga bakina nace, nasan kaine kuma na zageka, ban kara maganar ba Babana ya wanka min mari.
Tunda nake a duniya magana mai daci ko muni Baba baya fadamin ita, yana tattalin rayuwata yana kaunata amma yau saboda wani sakarai ni Babana ya daka,
Ina cikin wannan bakin cikin Baba ya bashi hakuri da taimakon abokansa ya hakura suka ja banza suka shiga gidan da yake kiwon dokuna,
A raina na dauka alkawari yanda Baba ya dakeni saboda Dikko saina rama dukana a wurinshi...... Hannuna Baba yaja muka taho yana bani hakurin marin da yayi min, wai yayi haka ne saboda Dikko kar yayimin wani abu, saida ya sakani napep sannan ya koma gida,
Cikin bacin rai na tafi sch amma tabbas Dikko sai yaci kaniyarshi.........
{{{}}} {{{}}}
30/07/2019
Meelat Musa ce 🤙🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 2
Duk sanyi sanyin da akeyi saboda ruwan da aka kwana kwararawa a daren jiya hade da wani irin iska mai dadi amma Baba zufa yake kamar an tsare mai jegon da a saman gadon kara......
Cikin tashin hankali ya fara cire kayanshi yana dorawa a saman katanga, sai bakinshi dake motsawa babu wanda yakejin abinda yake fada saidai lokaci bayan lokaci yakan goge zufar data bulbulo daga jikinsa..
Ganinshi cikin wannan yanayi ya dagawa kowa hankali, gashi ya fita da farar shadda amma ya dawo da shadda kamar miyan goro,
Idan yana cikin yanayin fushi baya so kowa yayi masa magana haka kuma bayasan ganin kowa kusa dashi, mata da "ya "ya suka gane haka shi yasa babu mai shiga sabgarshi, idan yana cikin yanayin damuwa Sultana kadai ke zuwa wurinshi ta bashi hakuri kuma ya sauka saboda soyayyar dake tsakaninshi da ita,
Har na isa makaranta tunanin yi hakurin da Babana ya bawa jakin dana manta sunanshi nakeyi, sunanshi ya bacemin kwata kwata na manta sunan da aka kirashi dashi, nidai Allah yayi min jakar kwalwa, saboda ko "yan gidanmu ba dukansu nasan sunansu ba, amma na alakanta abun da yawan da muke dashi, yayin da wasu suke ganin rainin hankali ne......
Ko a aji naso na bawa Amisty labari amma na manta sunan wanda zan fada mata, Amisty itace kadai abokiyata duk a ajinmu, abinda kuwa yasa na zabeta tana da kokari sosai kuma idan ana jarabawa tana bani satar amsa,
Amisty irin yaran nan ne da idonsu ya waye tun suna cikin zanin jarintaka, bata da labari sai labarin maza, bata da aiki sai kallon B F, duk hotunan da zaka gani a cikin wayar Amisty hotunan tsiraici ne, walau nata walau na wasu, babu mai tarayya da ita saini kadai domin an dade da canfata cewar tana lesbian, nikam babu abinda ya dameni idan dai zata bani shayi nasha a tashi jarabawa ta bani satar amsa idan anyi rubutu nima tayimin a littafina shikenan banda wata damuwa.
Lokacin dana shiga aji har malami ya shiga ya fita, ga rubutu nan a saman allo, bana gane sunan subject haka nan kawai na kalli allon nadan basar tare da cewa ashe malam harya fita.
Da Eh kusan rabin ajin suka amsamin dan ina da masoya sosai, wasu saboda kyauna suke sona yayin da wasu kuma gashin kaina yake daukar musu hankali, okey shine abinda na fada kamar wata shegiyar baturiya dan itama okey din na dade ina koyonta a bakin Amisty dakel dai na samu ta zauna ram a cikin kaina, idan na fadi okey zakayi tunanin nasha turanci na koshi, amma babu abinda nake ganewa duk duniya sai sallolina biyar da Allah yasa na iyasu saboda nacin zuwa islamiya.
Ina zuwa mazauni Amisty tace yau ina kika baro mana Baban namu ? Wata irin faduwar gaba naji dan nasan Babana shima ba karamin tantirin dan iska bane, kodai itama Amisty Baba ya zagaya ne ?
Kinyi shiru, Amisty ta katsemin tunani na, maganata daukewa takeyi duk lokacin da ake tambayata abu, ina da nawar magana akan magana karama sai inja lokaci sosai, inayin in ina kadan wannan dalilin yasa ban cika yawan magana ba.
Dan gajeren murmushi tayi tare da matsawa, zauna tacemin tare da maida hankalinta akan allo taci gaba da kwafar note. Zama nayi tare da cewa wane malami ne ya shigo ?
Malama dai , wace malama ce ? Malamar English ! Me take koyawa na tambayi Amisty, turanci ta fadamin a takaice, murmushi nayi tare da cewa yarinya ai na gane dama dan inji idan zakiyi min karya.
Kedai kika sani, ni ciro littafinki na rubuta miki idan kin gama rainin hankalin naki, Amisty ta fada........ Bude jakata nayi sawon wani lokaci na kasa gano littafin da Amisty tacemin, tun ina dubawa a cikin jaka har na fito da duka littafan banga littafin turanci ba, dan gajeran tsoki nayi tare da cewa Amisty inajin nabar littafin a gida gaskiya.
Daukar littafin tayi domin shine a sama, ajiyar zuciya nayi dan nima ta gane wata jar wuya ce , nace da yake jiya nayi karatu na dauka na barshi a gida ne, tou kawai tacemin bata sake magana ba,
Haka malamai mata da maza sukaci gaba da shigowa har aka tashi daga makaranta, a bakin get din makaranta na tsaya ina jiran isowar Babana , tabbas nasan zaizo duk inda yake naji yana kusa dani yana zuwa bada jimawa ba.
Banfi minti 2 ba Babana ya iso cikin wata irin kafirar mota yanzu ma yasha wanka ya murza wata irin dakekiyar shadda, sai kasaita yakeyi, murmushin jin dadi nayi domin dai Babana ya kankaro min mutunci na idan yayo wanka saboda dan gayu ne na koyi a idon duniya.....
Cikin farin ciki na isa jikin motar na bude gidan gaba na wani kame abuna, zugar kawayena ne sukayo kanshi suna gaishe shi kamar yanda suka saba idan yazo daukata,
Dan murmusawa kawai yakeyi tare da karkacewa cikin izza ya jawo wasu irin "yan dubu dubu wanda shi kanshi baisan ko nawa bane , Amisty ya mikamawa tare da cewa ku saka kati.
Yana basu bai jira godiyar da suke mishi ba yaja mota muka tafi......, ba'a hana alkairi amma inajin bakin cikin abinda yakeyi, yabar gida da yunwa yazo waje yana alkairi, gida bai koshi ba yakai ma na waje banda gori da zagin iyayenmu babu abinda akeyi a cikin anguwa cewa Babanmu yana tsaye akanmu amma duk mu tsinannin Allah ne mu , haka zaisa ayi ta shiga da buhun na, na shinkafa gero masara katin katin na madara sugar da komai na sarrafawa idon duniya sun gani haka zai biyo dare ya kwashe abinshi yaje ya siyar wannan rayuwar zalinci ce, kuma bai sani ba kanshi kawai yake yaudara,
Kasa hakuri nayi nace gaskiya Baba ni kadaina zuwa daukoni makaranta daga yau, ba tare daya kalli inda nake ba yace miyasa Mamana ? Kawai banajin dadin abinda kake ne , me nakeyi wanda bai miki dadi ba ? Wannan kudin da kake bayarwa dama gida kabawa su Inna sukaci abinci gidan kowa yunwa ta kamashi babu mai wani sahihin abinda zaici maganar daya ce kullum daga gari sai kanzo.
Dariya yayi sosai tare da cewa Mamana kenan, aisu wannan mutane basa godiyar Allah, kima daina biye musu dan kona basu kudin cefane makalewa sukeyi, duk wanda kika gani a cikinsu daga mai tumaki goma sai mai shanaye babu adadi, idan na basu kudi boyewa sukeyi su hana ku abinci, suna can sun sayi dabbobi sunkai kauyika an boye musu, idan kuma kina magana akan abinda akayi ma wani kuma wannan halin shi ake kiran da hassada idan kikaga anyi ma mutum alkairi koya samu wani abu kikaji bakin ciki a zuciyarki shima hassada ne, kuma ita hassada tana cinye kyawawan ayyuka ne kamar yanda wuta takecin karmami, kuma yawan surutu yana sa mutum ya zama sakarai , ki daina hassada kuma bakinki shiru akan fadar wasu maganganu akaina idan kinki ji kuwa jahannama tsaye ko kina san ki shiga wuta ne uwar masu gida ?
A , a Babana, amma zan fadawa su Inna gaskiya su daina irin abinda sukeyi zalinci ne, abun tausayi Baba kaji yaran nan suyi ta kukan yunwa wallahi ni har tausayinsu nakeji, kyalesu Mamana kina iya fada musu gaskiya suji haushinki barsu da halinsu................Maganarsa ta kare ne a daidai lokacin da muka tsaya wata majalissa.
Fita muje, fitowa mukayi daga cikin motar muka tunkari taron dandazon mazan, kallo daya zakayi musu kasan cikakkin "yan tasha ne ko wannensu ya koshi da iskanci,
Gaishe su nayi tare da matsawa daga gefe na zauna, kai bata abincin nan taci mu wuce, Babana yayi maganar a daidai lokacin da yake zama,
Mikomin abinci akayi a cikin ci ka yada, { take away } gyara zamana nayi tare da juyawa inda babu mutane naci gaba da aiki, daga nan bansan abinda yaci gaba da faruwa ba, saidai naji hayani tayi yawa sosai anata bawa Babana hakuri ana rirrikeshi.
Cikin tsananin bacin rai yake cewa da Allah ku sakeni wallahi saina kwakwale mashi idanuwa tunda nayi rantsuwa saina makantashi duk cikar garin katsina babu wanda ya isa ya hanani aikata abinda nayi niyya, da sauri na tashi nayi wurin Babana ina bashi hakuri,
Abokin fadan Babana yake cewa, yo kai "ya "yan wasu nawa ka batawa rayuwa, saini kawai dan na kalli diyarka nace babban lambu zaka nunamin rashin kunya, cewa nayi zan shiga ciki ? Yabawa fa kawai nayi.... Sai kawai hankali ya tashi ?
Sanin kanka ne duk kasuwar data burgeni saina ci ta hanyar shiga inyi siyayya a cikinta, duk gidan giyar daya burgeni idan na shiga saina sha kwalba biyar karanci kenan idan banda kudi, haka kuma idan naga gidan karuwai zan shiga ne inyi ta ciyayyar abinda ya sawwaka ba tare dana gajiya ba,
Ka sani nima nasan haka, tunda saina gama nake ma gwanjon mata, banyi maka shamaki da matana ba haka diyana, kenan yanzu idan nace ka bani aron Sultana mu bata dare haka zakazo bakin kofa kayi tamin babatu ?
Da sauri Babana ya rufe idanuwan shi tare da kauda kanshi gefe guda, tunda ni bansan abinda ya assasa fitinar ba, tou miye b'ata dare ? Kila shaye shayen su suke nufi,
Jinjina kai Babana yayi tare da cewa kaci sa'a Mamana tana kusa amma zan maida ita gida na dawo na nuna maka karyar barikanci, yana fadar haka yaja hannuna mukayi gaba, har muka iso gida baiyi min magana ba, saida ya tabbatar na shiga gida sannan ya koma,
Da sallama na daga buhun kofar gidanmu na shiga, gaba daya gidan suna tsakar gida uwaye da yara, yaran mazansu da matansu sun gurfana gaban wani dakekin mutum bakikkirin da cikinshi kamar ace Allah saukeshi lafiya, ni a tunani na assembly ake musu saida naga Inna na tuna ba makaranta bace.
Saida nazo daidai inda suke nayi musu sallama kamar yanda na saba, ina kokarin wuce yace ke zonan, ban kalleshi ba kuma banzo ba haka kuma ban tsaya ba naci gaba da tafiyata na kusa shiga dakinmu naji yace waccan yarinyar ta raina mutane wallahi da nayi niyar yin hakuri amma na fasa sai kun tashi kunbarmin gidana.
Hayani ta kwace bakajin maganar wani duk maganar ta koma iri daya yi hakuri , Allah ya taimake ka Allah ya kara arziki ka taimaka dan Allah karka tashemu, kaji hauka akan wannan rubabben gidan suke wani hadashi da Allah yayi hakuri, Allah ma yasa ya tashemu nayi addu'a ta a bayyane,
Zainab ce ta tashi taje wurinshi tana wani irin karye karye, sai kace karyar gidan karuwa taga maza, magana tayi mishi babu wanda yaji abinda tace, saidai suka fita da mutumin, ganin tafiyarshi yasa kowa ya tashi yaci gaba da sabgar gabanshi,
Babana da Zainab bansan yanda suka kare da mutanen su ba, haka Dikko bansan inda yake ba, dan an dauki wani lokaci banji labarin yazo anguwanmu ba,
Kwanaki da dama sun shude, rayuwa tana tafiya babu abinda yayi gaba sai ci baya ake samu, amma ni na samu ci gaba na rayuwa domin dai Babana ya siyamin sabon machine kamar yanda yayi alkawari, a cikin matanshi kuwa maman fa'iza ta samu karuwa ta aihuwa, yanzu mun zama mu hamsin da takwas cas a gidanmu,
Zaune nake a kofar dakinmu ina yanke farce na, "yar kyakkyawar magena tana shan madara, Baba ne ya siyomin madarar da yawa nake bata danni yanzu na daina tausayin "yan gidanmu tunda na gane duk munafikai ne, Kuma Babana ina gani duk safiya yana basu kudi amma bansan ko nawa bane,
Kadangare ne ya fado daga saman bango fef, yana ganin mage ya ruga, ita kuma daina shan madarar tayi tabi kadangaren da gudu, nima binta nayi ina kiran "yar madara' dan bana so tana cin kwarika, kadangare ya rugawa mage, ni kuma