Showing 90001 words to 93000 words out of 161239 words
kalloni a lokaci ɗaya , hawo saman gadon Hafsa tayi tana ƙoƙarin riƙe hannuna ta ɗaure , kallonta nayi kamar wata sakara sannan nace dake da Amina ku tabbata idan har kuka min wani abu kasheni shine kawai mafita a rayuwarku , amma na rantse da girman Allah wanda ya halicceni ya halicceku dani daku dukanmu shi muke bautama , mutuwa ta ko taku zata iya zuwa ko wane lokaci yanzu ko anjima , ko kuyi ko ku bari yanda kuka buɗemin sirri saina buɗe sirrin uban kowa a cikinki ,
Bayan buɗewa saina tona musu asirin da ku kanku sai kunsha fiya² kun mutu saboda baƙin ciki , kar wacce ta ɗauremin hannu ko ƙafa kuyi duk iyakar iskanci da kuka iya , bashi ne kuma bazaiyi kyau ba a lokacin da zan biyashi akan iyayenku ,
Muni , baƙin ciki , firgici , tashin hankali gaba ɗayanku zaku fuskance su yayin dana shigo rayuwarku , ina da illa kuma ina da bala'en haɗari haka nake dasa baƙin cikin da baya mantuwa a zuciyar duk wanda ya nemi ya dasa baƙin ciki a rayuwata , ciwo gareni haka nake da ɗaci kuka akemin kamar mutuwa yayin da na shigo gida dan ruguza farin ciki zuri'a ɗaya , ku lasa ku maida miyanku tunda kun buɗa ni kuma nayi alƙawari daga yanzu rayuwar farin ciki ta ƙare gareku ,
Kallan kallo suka tsaya yi kowa da abinda take saƙawa a zuciyarta , tsoki nayi tare da cewa kuna ɓatamin lokaci domin ni ruwan ƙorama ce zuwa nake da ƙarfi na tafi idan kuma na tashi tafiya nakan tafi da abu mafi soyuwa ga al'ummar gari za'ayi ta tunani na har shekara ta zagayo ba'a gama wani kukan ba zan sake caɓar wani abun inyi gaba dashi haka mutane zasuyi ta kuka dani har ranar da mutuwarsu zata riskesu , dake da dake duk wanda na bari a cikinku ya huta ban yafewa kaina ba...
Dukan ƙofa akayi da ƙarfi tare da cewa Hafsa me kukeyi kuma ? A shagwaɓa tace Mom ya akayi kuka dawo ne ? Ƙara dukan ƙofar tayi tare da cewa ni banje ba tunda na shigo nakeji ana ihu *kwarata* wai me ke faruwa ne ...?
Dukansu shiru sukayi , ci gaba tayi da dukan ƙofar tana cewa wallahi idan kika bari na buɗe ƙofar nan da kaina zaki ci ubanki.... Cikin yanayin ɗacin rai Hafsa ta kalleni sannan ta sauka ta fara ƙoƙarin saka rigarta a lokacin har Mom inta ta zuro makulli ta waje ta fara buɗe ƙofa...
Murmushi nayi da gefen bakina nima na sauka daga saman gadon na ɗauka towel in na ɗaura , ban gama ɗaurawa ba ta shigo ɗakin , kayana na ɗauka da makullin motar na raɓa ta gefenta zan fita , riƙoni tayi tare da cewa ke daga gidan ubanwa kika zo nan ke kuma....?
Ko kallonta banyi ba da nace mata daga gidan ubanta nake , bakiji ina miki magana ? Kema nan dako haihuwarki ba'a gama ba har kin iya iskanci haka ? Kallonta nayi sannan na faɗa mata kaf abinda ya faru na ɗaura da cewa kuma na rantse da girman Allah saina rama ,
Haƙuri ta fara bani , niko nace dama kin adana kalmomin haƙurinki kila zasuyi tasiri a lokacin da "yarki ta fara halbe²n mutuwa , ina faɗin haka nayi gaba , a palo naga wata ƙatuwar hijabi dan haka na ɗauketa nayi gaba , a ƙofar palo na saka sannan na wuce inda na ajiye mota ta , ina zuwa na shiga naja cikin gudun tashin hankali nabar gidan kamar babu rai a cikin motar...
Tuƙi nake bansan inda nake bi ba , domin idona cike yake da hawaye yayin da hankalina da zuciyata suka tafi tunanin hanyar da zan samo iyayensu Amisty dan babu hanya mafi muni da zan saka musu inba inyi iskanci da iyayensu ba kuma in ɗauka vidio in tura musu...
Wani irin wawan burki na taka dan ban lura ba traffic ta riƙeni , tsayawa nayi tare da sauke gilashin mota ta ina kallon wata mace data bugawa wata mota itama dai masiffiyace itace take da laifi amma sai rashin kunya takeyi ,
Kyawawan motoci ne masu tsada kuma ta kashe musu fitilar baya kuma sai zagi takeyi tana cewa idan sunajin su wasu shegune itace maganin "yan iska sai an biyata motar ta data goge , tunda sune sukayo baya , duk wanda ya bata haƙuri sai tace batayin haƙuri uban waye ma ake tuƙawa a motar ?
Daga ciki aka sauke gilashin motar ya sauka a hankali , Dikko na faɗa tare da ƙarasa sauƙe gilashin mota ta dukanshi , matsawa matar tayi taci gaba da zazzagawa Dikko rashin mutunci , kuma ya hana kowa yayi mata magana , murmushi nayi tare da ɗaga kaina na kalli danja har yanzu ba'a sakemu ba , amma waccan wawiya ce da tasan Dikko da bata shiga rayuwarshi ba Allah dai yasa ba a gidan haya suke zama ba suma...
Ina tunani naga ta juyo tana kuka kome Dikko yace mata Oho su kuma an sakesu sun wuce , ɗaga gilashin motar nayi nima ana sakinmu nabi bayan motar matar da gudu dan ina so inji abinda Dikko yace mata take kuka ,
Itama gudu takeyi sosai nima na take tawa sosai , muna samun sarari na shiga gabanta , dole ta tsaya har yanzu tana cikin ɓacin rai , fitowa nayi daga cikin mota ta ko takalmi ban tsaya sakawa ba , na nufo motar matar har yanzu kuka takeyi , gidan gaba na buɗe na zauna , kallona tayi tare da cewa lafiya ?
Cikin yanayin damuwa nace abinda aka miki ne baimin daɗi ba shi yasa na biyoki in baki haƙuri me ya haɗaki dashi ne ? Cikin ɓacin rai tace ɗan iskan yaro ne gashi da siffar mutanen kirki amma baida mutunci , kuma baida kunya ko kaɗan , driver inshi ne yayo baya ya gogi motana ni kuma na kasa haƙuri na fita nayi musu magana shine duk sukamin shiru , ni kuma nace uban waye ma ake tuƙawa a motar ashe yana ji yana sauke gilashi ni kuma naje wurinshi da niyar ce masa bai kyauta ba shine yace min...
Wai kar inmi mishi rashin kunya bayan yasan komai , cukwui da nonon raƙumi nasha aka bani kyautar motar na taho kan titi ina ma mutane ganganci ko an faɗa min titi ɗakin mijina ne ? Ban tsaya naji sauran bayanin shi ba na taho saboda yaci min mutunci da yawa...
Lallai Dikko cikakken ɗan iska ne , haƙuri na bata tare da fita daga cikin motarta na nufi mota ta , wato ya yazo gari kuma hali na nan bai canja ba , mota na koma na shiga naja nayi gida ,
Tun kafin inyi parking naga Nana zaune a saman dakali sai kuka takeyi , ko inda take ban kalla ba na wuce cikin gida , dan har Nana haushinta nakeji saboda abinda su Amisty sukamin....
Wanka nayi tare da sake wanke kayana na bazasu a saman igiya , ɗaki na koma na shirya bayan na gama abinda nake na ɗauko kuɗin Amisty dana sace na fara irgawa , ban gama irgawa ba naji A ` i tana kwalamin kiran cewa kizo ana kiranki a ƙofar gida ,
Abinda raina ya bani Babana ne dan haka na ajiye kuɗin na fito , a tsakar gida Karima ke ƙyanƙyasa min cewa an saki Nana , idanuwa na zaro tare da cewa innalillahi garin ya ? Nayi maganar a sirrance tare da natsawa kusa da Karima ! Karima tace ai labarin sai kin dawo kije kiji kiran da ake miki , har ga Allah banji daɗin mutuwar auren Nana ba kuma na lashi takobin gyara aurenta da gaskiya ,
A ` i ta ƙara cewa jiranki akeyi , cema Karima nayi ki jirani ina dawowa , bayan na fito ƙofar gida nacewa A ` i waye yake nema na ? Filin da aka rushe gidaje ta nunamin kallon motar da akayi parking nayi sannan na kalli A ` i nace waye ? A ` i tace wani dattijo ne , wane kala ne ? Fari ne ! Ya yanayinshi yake ? A ` i tace wallahi ban lura dashi sosai ba yaro dai ya turo yace Sultana taje...
Kai tsaye na nufi wurin , tunda mu "yan kasuwa ne ina zuwa na buɗe mota na shige naja na rufe garam , shi kuma ya sanyawa motar lock , ko faɗuwa gabana baiyi ba domin dama raina ya bani za'ayi haka ,
Waye kai ? Na tambayashi domin duhu ya shiga , ni ne , ya bani amsa , kaine wa ? Na sake tambayarshi , *Shekara biyu...* ne ya bani amsa , dama ana ganin shekaru ? Umm idan bakya ganinsu zaki wuce su ? Ɗan gajeran tsoki yayi tare da cewa yanzu ba wannan ba me yasa kike san yawan yin kuka ? Ni banda isashiyar lafiya sai kiyi ta kuka kina taramin damuwa ! Me akayi miki ɗazu ne ?
Tou sai yanzu na gane ko waye , murya nabi na ganoshi , me kuma ya sake dawo dakai cikin rayuwata ? Na tambayeshi , bai bani amsa ba ya fara gangarawa da motar yana saukowa , riƙe sitiyarin nayi nace ina zaka kaini ne kuma ? Janye hannuna yayi daga saman sitiyarin baiyi magana ba a daidai lokacin daya sauko ya juya kan mota ta kalli titi...
Haba wai ina zakaje dani ne haka ? Ba tare daya kalleni ba yace yi haƙuri An mata yanzu zan dawo dake bazan daɗe ba , shiru nayi , kinyi haƙurin ko ? Ya tambayeni cikin sigar lallashi murya mai kwantar da hankali dasa natsuwa , shiru nayi ban sake magana ba , a hankali yayi tuƙi har muka fita bakin hanya , yana hawa titi kuma ya fara falfala gudu kamar yanda ya saba.
Tafiya mai nisa mukayi , sannan Dikko ya sauka daga saman titi yaci gaba da gurzar burji , ganin ɓoyayyar hanya yasa na fara kuka , kallona yayi tare da cewa wai miye ne ? Kina tunanin zanyi miki wani abu ? Ɗan soɓaro baki yayi sannan yace wannan hanyar tafi sauri ne bara mu koma titi tunda kinajin tsoro..
Nidai bana so ka mayar dani gida, kwaikwayo na yayi tare da cewa idan naƙi mayar dake kuma fa ? Sai in barka da Allah.... , murmushi yace An mata kenan waike bakijin kunyar min rashin kunya ? Banaji kai har abunda za'aji ma kunya ne , murmushi yayi bai sake magana ba ,
Wayarshi ya fiddo yayi latse² sannan ya kara a kunne , bayan an ɗauka yace fito na iso , kashe wayar yayi ya faka motarshi gefen wani gida ,
Duk dani dashi babu wanda ya sake magana har mutumin ya fito daga gidanshi , saitin Dikko ya tsaya ya gaisheshi cikin girmamawa nima ya gaisheni cikin mutuntawa , ko kallonshi banyi ba ban kuma ansa ba , gyara zama Dikko yayi sannan ya kalleni fuska a ɗaure yace bakiji ana gaisheki , gabana ya faɗi yanayin kallon da yayi min nace ai nace lafiya lau bakaji ba , kauda kanshi yayi sannan yace ya kukayi dashi ne ? Yake tambayar mutumin , Eh babu damuwa amma sai an koma hutu ,
Dikko yace har yaushe ne hutun zai ƙare ? Mutumin yace saura sati biyar , tsoki Dikko yayi yace ko na barta yanzu ? Cikin girmamawa yace ai matan gidan dukansu basa nan idan dai sun dawo zan kiraka insha Allah ,
Ba komai sai ka kira ɗin , inji Dikko godiya mutumin yayi sosai cewa yaga saƙo yafa gode sannan ya matsa , Dikko yaja mota muka dawo gida ,
A ƙofar gida yayi parking sannan yace ki kiyayi dawowa ta iskanci da rashin kunya cike da kai amma babu ilimi ni bana san zama wuri ɗaya da jahili kina ɗawainiya da fankon kai a haka kike tunanin zaki hareni shakaru biyu masu zuwa ? Dan dai zan fita katsina a daren nan amma wallahi dana zaune dake har tsawon sati biyar saina koya miki hankali bakauya dake kina fitowa ko hijabi babu ke ba ɗiyar kafirawa ba , zama saman dakali yawon banza fira da maza rashin kunya da tara "yan daba duk ranar dana waiwayoki jikinki zai baki labari fice ki ban wuri kafin in fara miki rashin mutunci , ya ƙarasa maganar tare da buɗemin motar na fice...
Fita nayi daga cikin motar jiki a sanyaye dan duk duniya babu abinda na tsana irin inji an danganta ni da kalmar jahila , kuma ba ƙarya bane jahilarce ni , fita katsina kuma da zaiyi yanzu zaije jigawa saboda an fara shagalin bikinshi ne naji ana ta faɗa ,
Banda tsoki babu abinda Dikko keyi da ana canja hali daya canjawa Sultana hali , duk duniya babu abinda baya so irin mutumin da baya ganewa , wallahi idan har Allah yasa ya dawo lafiya sai an nemi An mata an rasa idan zata shekara dubu saita ta wadata da ilimi , baida inda zai ajiyeta daya tafi da ita , kuma yana so kusanci mai girma da shaƙuwa ta shiga tsakaninshi da ita ,
Rayuwarshi da ita ya fara kuma yana so ya kulle da ita , farin ciki da duk wani jin daɗin shi yana hannun Sultana bai taɓa tunani zaiji soyayyarta ko kaɗan ba a zuciyarshi , daya san wannan ranar zata zo da baiyi mata abinda yayi mata a baya ba ,
Bai ɗauki mace komai ba amma ƙaramar yarinya ta hana mishi sukuni , da girmanshi waishi soyayya zata zo ta dama , kamarshi soyayya zata hana bacci abubuwa suyi ta masa yawo a zuciya , idan An mata tayi fushi ko kuka duk yanaji wannan bala'e kamar asiri.....
A ƙofar gida na samu Nana har yanzu bata daina kuka ba da takardar sakinta a hannu , wurinta na nufa dan jajanta ma......
Dikko kuwa yana komawa gida ya ɗauki abinda zai ɗauka suka kama hanyar jigawa......
12/09/2019
Jamila Musa....
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 31
*_Gaisuwa ta musamman gareki "yar uwa ta gari fatan alkairi da addu'ar Allah ya ƙara zaman lafiya da ƙauna mai girma tsakaninki da mai gidan ki , RABI MUSA ..._*
A damuwance na zauna kusa da Nana dan ina tattare da ɓacin rai da damuwa , ansar takaddar nayi da cewa saki nawa akayi miki ne ? Cikin kuka Nana tace saki ɗaya , tou ina shi mijin naki yake ? Cikin shashshekar kuka tace yanzu ya shiga cikin gida...
Tsoki nayi nace tou me yayi zafi haka har ya sakeki ? Ƙara fashewa da kuka Nana tayi saida tasha kukanta har ta godewa Allah nidai ban bata haƙuri ba kuma bance tayi shiru ba saida ta gaji ta rufe bakinta da kanta na kuma sake tambayarta abinda ya haɗa har akayi mata saki !
Aure zaiyi ! Ba tare dana kalli Nana ba nace tou ke ina ruwanki da auren banzarshi da zaiyi ? Saida Nana ta ƙara goge hawaye sannan tace ba auren ya dameni ba matar da zai aura itace ciwona , wace alaƙace tsakaninki da ita da har bakyaso ta zama abokiyar zamanki ne ?
Rumtse ido Nana tayi tare da ƙara rurewa da kuka tace *A ` I* zai aura fa , ɗan gajeren tsoki nayi tare da miƙewa nace A ` in banza A ` in wofi ! Da saboda A ` i har kika kashe aurenki ? Kiyi haƙuri Nana gaskiya baki da wayau kuma lokacin dana so na farkar dake daga baccin asarar da kikayi dake dasu A ` i kuka haɗu kuka riƙa cimin mutunci , kin watsa mutuncin aurenki kin lalata rayuwarki kika biye musu suka koya miki maɗigo ,{ Lesbian } ta koya miki kika koya kuma kika iya , gashi yanzu zata aure miki mijin kinga zaki tashi a tutar babu , ba abokiyar iskanci babu mijin aure..
Idan kuma zawarcin kika fuskanta ga "yan mata tsalala sabbin zubi suna yawo a gari suma basu samu sun shige ba , idan maza suna kallon lutsa²n zawarawa wankakki "yan gayu masu ƙamshi da gogewar zaman takewar aure , Nana gaki muguwar ƙaza babu sallah babu salati babu biyayyar aure ki faɗamin wane sakaran namiji zai kalleki