Showing 39001 words to 42000 words out of 139381 words
masu tsada amma tayi ta walakanta adiko, Maimoon kuwa dama kayan datti sai ta tara ta tara taga babu sarki sai Allah, babu wanda xata saka sannan xata kwashesu ta hau wanki duk su cika gida, to ina mace a nan, babu kazantar da ya fi wannan wllh, sauran yan matan kuwa ni wani lkcn ma sai in ji kamar wari suke wllh...." Murmushi Anty tayi, Inna tace "Wallahi ba batun dariya ba, to dai kowa tasa ta fishshesa a gidan nan ba ruwana da kowa ta kaina nake, yanxu dai abinda yasa na kira ku ba wani abu bane...." sai kuma ta yi shiru, su dai kallonta kawai suke, tayi kasa da murya tace "Ku lissafa min daga ranan asabar xuwa yau kwana nawa kenan" Ammi tace kwana shidda" Inna tace "Toh yau kwana shidda rabon Mujaheed da Imaan su xo min nan su gaisheni, yanxu fisabillahi daga sun min ba dai dai ba na nuna bacin raina sai su kullace ni, meye laifina don nace ban yarda shanye min fura da suka yi ba" Anty ta bude baki tace "Gaskiya basu kyauta ba har kwana shidda" Inna ta fara matsar kwalla tace "Ni fitinata har ya kai Mujaheed ya ki takowa nan yau har kwana shidda, daga gyara kayanka sai ya xamo sauke mu raba? Ke Amina na kira ki ne a matsayin uwarsa don ba ruwana da wancan katuwar da ta haifesa, ke kuma Aisha saboda Imaan yar ki ce" Anty tace "Amma Inna ca nake kince kada su sake xuwa maki idan ba haka ba xaki bar gidan" Inna xaro ido tace "Oh oh Allah kaji wata magana don Allah, to Amina idan na bar gidan nan ina da gidan uban da xanje in tsugunna, duk ba xance bane dai da tsorata mutane, bacin rai ai babu abinda bai sawa, don nace kada su sake xuwa kowa yasan fada kawai nayi, me suka min da xan hanasu xuwa nan?? Allah ya tsine ma fura da nonon in dai saboda shi xan kori jikokina, meye kuma wani fura da nono kamar mayyar bafillatana" Anty na danne dariyar ta tace "Ahh to gaskiya basu kyauta ba" Inna ta kalli Ammi tace "Ke kuma Aisha kinyi shiru kina kallona ko baki da abun cewa ne?" Ammi tace "Kiyi hakuri Inna, ina komawa xan sameta" Anty tace "Nima Mujaheed na dawowa aiki xan samesa In sha Allah" Inna ta gyara xama tace "Toh, sai ku ji dalilin da yasa xa su min haka su kaurace min, yanxu duk saukin kai na su basa gani, ni ba mafadaciya ba, ni ba fitinanna ba, ni ba mai sa ido ba, ni ba mai kwadayi ba, ni ba mai mita ba, toh meye xasu wani dauke kafa daga magana dai ta fahimta, to sai dai idan Ahmadu ne ya hure masu kunne ya masu hudubar tsiya, banda haka su har wani wayo garesu da xasu dauke kafa daga xuwa inda nake" Anty ta fara dariya, Ammi kam murmushi kawai tayi, Inna tace "Aa don Allah ku duba xancen da kyau, wllh xuge su aka yi, kuma ba kowa xai yi hakan ba sai mutumin nan Ahmadu don Bukar baya haka shi, ni gaskiya na ma daina sa Ahmadu a lamarina daga yanxu tunda tsanata yake cusa ma yaran a rai, anjima kuma xan sa kira min Bukar yaji abinda ake ciki, kwana daidai har shidda fa" Ammi ta mike tace "Ki yi hakuri Inna ina komawa xan mata magana bari in je in duba girki na" Inna tace "ke ta girki ma kike ga maganar al'ajabi ana yi a nan Ahmadu ya xuge yara, haba don Allah abinci dai abinci dai kamar ana yunwa Amina" Ammi ta nufi kofa tace "Toh sai dai anjima inna" Inna tace "Toh Allah bamu alkhairi, ki dai tsitsiyeta kiji dalili" fita Ammi tayi parlon bayan ta ma Anty sallama. Inna ta tabe baki tace "Kinga bafillatanin mutum, kinga agwai?? Wllh ki ji tsoronsa, barin idan kika ga ya fiye shiru shiru banda haka ki ga fa babu abun kirki da tace har ta bar parlon nan, Bukar dai na ganin boni, mata kamar kurma, ni kwanciyar hankali na ma Imaan bata dauko halinta ba, Imaan xata iya kwatar kanta a ko ina da bakinta, tun daga ranan da na karanta mata ta daina gaida Uwar Mujaheed gashi har yau bata gaisheta, gashi har Ahmadu da Bukar sun gaji sun kyaleta, kusan ma Imaan ce kadai ta dau halina a gidan nan wlh, banda haka ya xata dinga gaida katuwar mata bata amsa mata, da ta fi ta iskanci kuwa kinga ta daina gaishetan gaba daya" Anty dai dariya kawai take, Inna tace "Toh ni dai ki taimake ni Amina ki rufa min asiri, Mujaheed na dawowa ki titsiyesa a daki kiji me na masa da ya dauke kafa a nan" Anty tace "In sha Allah Inna, bari in je nasan ma ya dawo yanxu tunda biyar har ta yi" Inna tace "To yi maxa" tashi Anty tayi ta mata sallama ta fita inna ta mike ta ci gaba da goge gogenta tana cewa "Ahmadu dai ya lalace, da dai ba haka yake ba"
Dariya sosai Imaan ta dinga yi bayan Ammi ta bata sakon inna, tayi mai isarta ta mike daga kwancen da take tace "Ba Inda
xanje Ammi, tun Sunday kinji ta kai karana gun Abba, to haka ya fi, ita da bakinta tace wannan time din ba wasa take ba Abba ya ja mana kunne sosai don muna xuwa part dinta xata tsallake ta gudu ta bar gidan" Ammi tace "Toh nace bayan magrib kije ki gaisheta, kina gaidata ki juyo" Imaan ta fashe da kuka ba hawaye tace "Ammi don Allah ni baxan je ba, ina xuwa xata ce na mata wani abu" Ammi ta mike tace "Toh idan na baki abincin ki kai mata kar ki kai" daga haka Ammi ta bar parlon, Imaan ta fara kukan gaske, har ranta bata son xuwa gun inna. Anty na gama girkin dinner dab da magrib ta fito kitchen, ganin Mujaheed xai fita masallaci tace "Dr idan ka dawo mosque ka sameni bedroom" Yace "Toh" daga haka ya fita parlon, tare suka dawo masallacin da Yusuf, bayan sun haura sama Mujaheed ya shiga dakin Anty, Yusuf ya shiga dakinsa, Anty na xaune kan darduma ta shafe addu'o'in da take ta mike ta dauke pray mat din ta linke tana kallonsa tace "Toh ka tsaya min kamar soja a kai ka xauna" murmushi yayi yana shafa kansa ya xauna gefen gadon, tace "Yanxu M.A idan kowa ya guji inna kai ma sai ka gujeta" ya d'an buda ido yace "Inna kuma?" Tace "Eh mana" yace "Ban gane ba Anty" tace "Kirana tayi daxu wai kwana shidda rabon da kaje bangarenta kai da Imaan" Mujaheed yyi murmushi bai ce komai ba, Anty tace "Toh ka gama murmushin ka tashi ka ta fi ka gaisheta" mikewa yayi yace "Wa?? Ai har abada ni da xuwa apartment dinta, beside irin warning da Abba ya min ma is not funny don haka..." Anty ta karasa masa tace "Baxa kaje ba koh?" Yace "Allah Anty kinga kwana biyu shiru bata ce an mata komai ba hakan bai fi ba?" Anty tace "Toh ni dai nace ka tashi ka je" ya mike xaune yace "Anty ki bari kawai ba inda xanje" Anty tace "Wato ban isa da kai ba kenan, idan Hajiya ce tace kaje xaka ce mata ba xa ka ba?" Yayi murmushi yace "Anty Hajiyan ma hanani xuwa bangaren tayi gaba daya" Anty tace "Toh tashi ka fita ka ban waje" ya marairaice mata yace "Wllh Anty ina iya xuwa yanxu tace nayi mata wani abun" Anty ta hade rai tace "Cewa nayi ka gaisheta kawai ka juyo" Ya lumshe ido ya bude yace "Wllh da ba don ke bace ni ba inda xanje Anty" Anty tace "Naji din tashi ka fita, idan ka dawo kuma ka xo ka gaya min, gobe da safe kuma xan je in ji ko ka je" Murmushi yyi ya mike ya fita dakin. Tun da Imaan ta fito parlonsu rike da warmer din abinci take tsaye jikin wani flower taki tafiya, kiris ya rage ta fashe Inda take tsaye, daga nisa ta hango Mujaheed yana tahowa waya kare kunnensa, labewa tayi ta koma bayan flower din ta tsaya da sauri, sai da ya d'an wuce inda take ta fito tayi wani kara a bayansa, still yyi na few seconds, ta fashe da dariya ya juya yana kallonta, ya wani hade rai yace "Kee" Ta wara manyan idonta tace "Toh ai baka ji tsoron ba ma" Wani kallo ya dinga mata, ta turo baki ta wuce sa, sai da ya ga tayi nisa sannan ya bi bayan ta, tsaye ya ganta tana lekan parlon inna don kofar ba duka aka rufe ba, ya cire takalmansa outside the balcony yayi tiptoeing har bayan ta, fingers dinsa ya kai gefen cikinta yayi tingling dinta, ihu ta fasa ta sake abincin hannunta, tuni ya janyeta wajen don gaba daya tuwo da miyar dake warmer din ya tarwatse a kasa, ta xaro ido a rikice tace "Innalillahi yaya ka xubar" daga cikin parlor inna ta dinga cewa "Me aka 6arar??" Ummi ta bude kofar, Imaan dai sai kallon abincin take kamar xata yi kuka, Inna ta mike ta taho wajen tace "Meye hakan?" Kamar xata yi kuka tace "Yaya ne ya xubar da abincin da na kawo maki" Inna tace "Toh sai ki kwashe ki mayar mata ta canxa min wani ba ruwana" Imaan ta shige parlon ta xauna ta rungume hannu tace "Salon Ammi ta doke ni ba ga abinci nan Ummi ta kawo maki ba" Inna tace "Aa wllh kinga ina cin wani abu banda tuwo, Ummi maxa kwashe ki kai ma Aisha kice yar ta ta xubar ta xubo min wani" Ummi tace "Mu ma fa tuwo muka yi" A fusace Inna tace "To ni ina ruwana da tuwon ku? Ku tuwon ku har wani dadi garesa miya kamar an wanke kai, ki min abinda nace kada ran kowa ya baci a gidan nan" Ummi ta mike a fusace ta kwashe tuwon ta mayar cikin warmer din, Imaan tace "Dama kice yaya ne ya xubar na ni ba" Inna tace "Haba dai, dama ina xa ki iya xubar da wannan abincin ai sai dai shi" Tsallake miyar Mujaheed yyi ya shiga parlon ya xauna, Ummi ta tafi da abincin da ta kwashe part din su Imaan, gyaran wajen inna ta dinga yi duk suna xaune, bata gama ba Ummi ta dawo da wani abincin ta ajiye ma inna tace "Imaan Ammin ki tace xa ki dawo ki sameta" Inna tace "Sai me xai faruwa idan ta sameta, bakin cikin kara min abinci take komai, ina laifin ma tace xata gamu da Mujaheed din, Imaan ce ta wani san xubar da abincin mutane, bata ta6a ba tunda take, lafiya take kawo min abinci ta koma to yau da yake ta hadu da wnn mutumi a hanya" tana kai wa nan ta shiga parlon tana kallon Ummi tace "Don Allah ki rufa min asiri ki taimakeni ki karasa goge wajen baki ji bayana ba kamar xae cire" Ummi tace "Toh su da suka xubar...." Kallon da Mujaheed ke mata yasa tayi shiru ta mike rai ba dadi ta fita ta ci gaba da gyaran wajen. Inna ta shiga daki sai ga ta ta fito da bowl na dambun nama, tace "Tun ranan litinin nake ta ajiya amma ban gan ku ba na nace to ko lafiya, na ba kowa nasa...." Mujaheed ya amsa yace "Na waye wannan din?" Tace "Na kai da takwara ta" Ya saci kallon Imaan, da sauri Imaan tace "Inna ni dai ki raba mana da kanki" Mujaheed yace "Toh samo leda sai ki raba mana" komawa daki Inna ta yi, Mujaheed ya mike kafin Imaan ta ankara har ya fice parlon, kwalo ma inna kira ta yi, ya saka takalminsa ya kara gaba, inna ta leko parlon tace "Lafiya!" Imaan ta fara kuka tace "Ya tafi da naman gaba daya" inna tace "Maxa tashi ki bisa in ya kama ki je parlon Ahmadu ki tafi" Imaan ta mike ta fita parlon, bata son gudu saboda laluranta, hakan yasa kafin ta iske sa har ya shige part din su, ta goge hawayen da ya cika idonta a ranta tace "Allah ya isa" daga haka ta wuce apartment dinsu kawai, Sai da ta tsaya Ammi ta gama fadanta na xubar da abinci da tayi sannan ta shiga bedroom dinta. Bayan isha tana saka kayan baccinta wayar ta ya fara ring, duk tunaninta Sadeeq ne don kullum sai ya kira ta da daddare sun gaisa duk da basa waya mai tsawo iyaka gaisuwa shikenan amma har wani murna take idan ya kirata, Daddy ta ga ke kiranta, ta daga a hankali tace "Ina yini daddy" yace "Lafiya lau Mamana, ya gida?" Tace "Alhmdlh ya aiki?" Yace "Da godiya, kina karatu sosai dai koh?" Tace "Ehh ina yi" yace "Maa sha Allah, daxu kafin magrib inna ta kirani wai sati daya kenan baki je gaisheta ba, why is that?" Imaan tace "Daddy na fa je yau" Daddy yace "All those days me ya hanaki xuwa?" Tace "Cewa tayi kar mu sake xuwa ni da yaya fa" yace "That's because kuna mata rashin kunya ke da shi, wato warning da na maki kafin in tafi went in vain koh?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Toh kar ki sake skipping one day baki je gaisheta ba, idan Ammin ki ce don ta maki fada xa ki k'i xuwa gaisheta, she is my mother Imaan you have to respect her much, shi ma Mujaheed na kirasa ban samesa ba ki kai masa waya yanxu" Kamar xata yi kuka tace "Toh" daga haka ya katse wayarsa, Hijab ta sa har kasa ta fita, Ammi dake parlor tana kallo ta bi ta da ido, Imaan tace "Daddy yace in kai ma yaya waya" Ammi tace "Shi me ya samu wayarsa?" Bude hannu tayi alamar bata sani ba, Ammi ta ci gaba da kallonta, hakan yasa ta nufi kofa ta fita. Babu kowa babban parlon nasu don hatta kayan kallo ma a kashe suke, ta haura sama ta na kallon direction din dakinsa don har ta manta rabon da ta je wajen, takawa tayi har bakin kofar sannan ta bude tana lekan cikin bedroom din, wani sanyayyen kamshi me hade da sanyi ya doki hancinta da fuskarta, shiga dakin tayi ta kulle kofar, ko ina fes har kan gadon dake dauke da farin bedsheet, Ko ba a fada mata ba tasan wanka yake jin saukan ruwa da kamshin sabulu da ya hadu da kamshin dakin, xaro ido tayi tana kallon sketches dinta dake bangon dakin kusan gudu hudu, tun tana Jss3 tayi drawing din mai kyau coz she is more than perfect a zane, turo baki tayi ta dau kujeran dake gaban mirror ta kai jikin bangon ta hau ta dinga cire hard carbon paper din a hankali kar ya yage. Bude kofar bathroom Mujaheed yyi ya fito da short yana goge gashin kansa da karamin towel, xaro ido yyi yana kallonta da mamaki, ta juya jin an bude kofa suna hada ido ta turo baki tace "Yaya daddyna yace in kawo maka waya" Tana magana wayarta da ta ajiye kan gado ya fara ring, sakkowa tayi da sauri ta dau wayar tace "Ga shi nan ya kara kira" daga haka ta nufesa ta daga kiran ta kai kunne tace "Daddy ga shi nan" mika masa wayar tayi ya amsa ya kai kunne hade da sallama, Kamar ance ta juya taga bowl din dambun naman da ya dauke ajiye a gaban mirror dinsa, yana magana da daddy amma duk hankalinsa na kanta kuma yana lura da ita, ganin ta nufi gun mirror din ya fixgota, xaro ido tayi xata yi magana ya rufe bakin, sai ce ma daddy yake toh don ya kagu ya katse wayar, kamar kuwa daddy ya shiga ransa yace "Shikenan we will talk tomorrow sae da safe" da sauri yace "Allah ya tashe mu lafiya Abba, mun gode, sae da safe" daga haka ya katse wayar ya juyota yana mata wani irin kallo yace "Drawings din da kika cire nake so ki hau kujeran ki maida su yanxu kafin ki fada min sanda na fara wasa da ke da xaki shigo min daki kai tsaye" ta 6ata fuska tace "Toh ba waya na kawo maka ba" Jan kunnenta yayi yace "Baxa kiyi knocking idan kinji ba a amsa ba kiyi wucewar ki" muryar Umma suka ji a corridor tana ma Maimoon masifa wai ta share datti ta kai bakin kofarta lkci daya kuma tana tambayarta ko Mujaheed na dakinsa, Maimoon da ta hade rai tace "Yana ciki" Mujaheed ya xaro ido ya ja Imaan ya bude kofar bathroom dinsa suka shiga ya kulle kofar, dai dai nan kuma Umma ta shigo dakin tana kiran sunansa, Irin tsoratan da imaan tayi ba a cewa komai, Mujaheed ya dukar da ita kasan bayin murya can kasa yace "Kee you better relax now kar in mare ki, ance maki xata shigo nan ne" kai kawai take gyada masa numfashinta na sama, ya cire Hijab din jikinta yace "Nace maki ba fa shigowa xata yi ba, breath in and out gently now" jingina take son yi da bango ya jawota jikinsa ya rungumeta yana shafa bayan ta a hankali to calm her down, tuni Umma ta fice dakin ganin Mujaheed bai ciki, bayan kusan minti biyar jin tana fitar da numfashin a hankali kuma a nutse ya dago kanta yana kallonta, hawaye ne makale idonta, ya daure fuska yace "What?" A hankali ta nuna masa kirjinta, ya mike ya fita bathroom din ya sa makulli kofar dakin sannan ya dawo ya fito da ita dakin, wajen da yake ajiye drugs da allura ya bude yana dube dube, can kasa ya hango inhaler dinta da take bari a dakinsa a da idan ta xo, ya juya ya kalleta ya ga kwanciya tayi kan gadonsa