Showing 51001 words to 54000 words out of 139381 words
turo baki ta koma ta kwanta, Inna tace "Wllh Bukar gefen hanya yayi watsi damu, kuma kafin ya sauke ni don Allah mai yace min Imaan" da sauri Imaan ta daga hannu tace "A'a ba ruwana nima ban sani ba" Bude baki inna tayi tana kallonta, daddy yace "Yanxu dai ki tashi ki tafi ki bar ni da shi inna" inna tace "In tashi in tafi ka basa hakuri shima ya tafi xaka ce min" Tana fadin haka ta mike tace "Tun farko ma ban san me ya kawo ni gun Bukar ba, duk inda Ubansa ya tafi ai ya ci ace ya dawo yanxu" daga haka ta fice parlon fuska daure. Daddy ya hade rai yana kallon Mujaheed yace "Saboda baka da kirki xaka ajiye su bakin hanya Muhammad?" Mujaheed yyi kasa da kai bai ce komai ba, Daddy yace "Yanxu ka kyauta kenan, idan Hajiyar ka ce ko min abinda tayi maka xaka mata haka?" Yace "Kayi hakuri Abba" Daddy yace "Haba Muhammad, I am highly disappointed at you, this is very rude and stupid of you, she is our mother fa, no matter how she behaves baxa mu canxa ta ba" Mujaheed bai iya cewa komai ba, daddy yace "Ka tashi ka bi ta ka bata hakuri yanxu" yace "Toh, ayi hakuri Abba" Daddy ya kalli imaan yace "Ke kuma I've warned you times without number ki daina fada mata magana anyhow amma baki ji ko, xan fara sa6a maki soon wllh idan baxa ki canxa naughty attitude din nan ba, will you dare talk to ur mother that way?" mikewa xaune tayi kamar xata yi kuka, Mujaheed ya tashi yace "Xan je in sameta yanxu Abba" daga haka ya fita parlon. Washegari da safe da kyar imaan ta tashi tayi wanka tayi breakfast da Ammi ta ajiye mata a dinning, Ammi tace "Idan kin gama ki dau magungunanki ki sha kada in tuna maki, kuma da Ac kika kwana ko?" Ta xaro ido tace "Ammi wllh A'a" Ammi tace "Toh ga mura nan na shirin kama ki" Ta langwabar da kai tace "Jiya fa da daddare a napep muka dawo, kin ji sanyi kamar xanyi freeze a hanya" Ammi ta fiddo kindirmo a fridge yayi sanyi sosai ta ajiye mata a dinning din tace "Gashi ki kai ma inna inji daddyn ki, you make sure kin goge min dinning table idan yayi stain" Ta marairaice tace "Ammi my legs are aching me fa" Ammi ta harareta ta wuce dakin ta, Imaan na gama breakfast ta tashi ta dau kindirmon ta tafi kai ma inna, Tana shiga parlon bayan ta ajiye tana kallon inna dake ta kukkula dubulan da cin cin a leda sai ga Umma ta shigo parlon da sallama, Inna ta kalleta ta ci gaba da abinda take ta amsa sallaman ba yabo ba fallasa, Umma ta dafa kujera tace "Ina kwana inna" inna tace "Lafiya lau" Umma tace "Ya gajiyan taro" inna tace "Bana tare da gajiya duk ya bi lafiyar gado" Umma tace "Toh Alhmdllh Allah ya saka da alkhairi yaji k'an mahaifa" inna tace "Ameen" karasawa tayi kusa da inna ta ajiye ledan hannunta tace "Ga wannan dai ba yawa" inna na kallon ledan tace "Meye wannan din? Ke imaan xo ki bude" imaan dake xaune ta mike ta karasa kusa da Inna, Umma ta bi ta da kallon gefen ido, durkusawa tayi ta bude ledan ta ciro atamfa da pack din sabulu guda biyu da turare mai tsada" Inna ta bude atamfar tana kallo da kyau, tace "Holland ce wannan din?" Umma tace "Ehh" inna ta tabe baki tace "Toh, da dai basirar ki ce hakan da sai ince Allah yyi albarka, amma wannan ko kaffara baxan yi ba Ahmadu ya sa ki, Allah ya masa albarka ya kare min shi duk inda xai shiga, Allah ya ci gaba da hada kansu da d'an uwansa Bukar ya raya mai 'ya yansa yayi masu albarka, ita kuma wannan da ya aurar Allah xaunar da ita da mijinta lfya, ke kuma nagode da isar da sako" Umma ta dinga kallonta ko kiftawa babu, Imaan sai danne dariyarta take, Inna ta ci gaba da kulla dubulan dinta a leda, Umma tace "Sai anjima" inna tace "Mu jima da yawa" daga haka ta nufi kofa, inna na kallon Imaan tace "To ke sai kiyi ta kanki, don wllh jiya Mujaheed ce min yyi xai kakkarya ki ya xane ki, wai ya ganki da wani mai mota a tsaye a kofar gidan seeyama, imaan ina kuma kika samo mai mota kike ta boye min ban sani ba ni Asabe??" Umma ta d'an dakata bakin kofa jin abinda inna ke cewa, Imaan ta turo baki tace "Shi sa ma xan tashi in tafi yanxu kar ya xo nan, to har kun shirya ne inna?" Inna tace "Haba dai sai kace wata yarinya, to me yyi min da baxa mu shirya ba, wai na ce ma Rukayya mahaukaciya, ke ki ji fa? to me ta min xan xageta banda abunsa ma dai, kawai daga ina mata gyara? Ni fa na yarje ma Ahmadu ya aureta wllh, baki ganta ba a lkcn yar siririya yanda kika ganki, kamar iska xai hure 'yar banxa ta fadi, gashi iyayenta basu da komai basu kuma ba wani ajiya ba, wani d'an akurkin gida fa gare ubanta a lkcn, to ni ban masu bakin ciki ba don xuciya ta fess mai kyau ne na yarda Ahmadu ya auro mana ita a haka, ke kinga wahalar da nayi da ita kuwa? Wllh kare baxai ci ba, gashi ba abinda ta iya a lkcn, har girki ni ke sa ta kan hanya ina koya mata, kishiyoyina su yi ta jin haushi yanda nake ji da ita bana son ko k'uda ya ta6ata har dai ta samu cikin wannan yaro Mujaheed, sai kin ga wahalar da nayi mata sbda laulayin da ta dinga yi ba kakkautawa, to ni duk ba wannan ba don nasan sakayya ta dai na gun Allah, to don kuma yanxu Rukayya ta xama abinda ta xama sai me xai dameni ni patuu? ga dai Amina na bina sau da kafa ga Aisha, ni dai abinda na sani shine Mujaheed ai xai yi auren, to nan xata d'an dana ko da dadi ko babu, abinda duk abinda ka shuka shi xa ka girba, tsaf xan karance ma yarinyar xaman da xata yi da ita, muna nan da ku sai an dinga xuwa daukata shari'a a mota...." Imaan har wani kwanciya tayi kan kujera tana dariya amma ba mai sauti ba, Umma da ta makale jikin kofa ta fita ta sa takalmanta, inna ta tabe baki tace "Wllh Mujaheed da gwiwowinsa bibbiyu ya durkusa ya dinga ban hakuri tun ban kai ga gaya ma ubansa ba, to tunda naga yyi nadama kawai sai na yafe masa don ba halinsa bane gaskiya bai taba juye ni a tsakiyar titi ba tunda mu ke" Imaan ta fashe da dariya tace "Jiya dai ya juye ki ai"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.19. Imaan
Umma na komawa bangarensu kallo daya tayi ma Mujaheed dake xaune dinning yana shan coffee tace "Ka sameni daki yanxu" sosai gabansa ya fadi ya bi ta da kallo har ta haura sama, bai iya ya karasa shanye coffee din ba ya mike ya bi bayan ta, tsaye ya ganta tana safa da marwa a dakin, Yace "Gani Umma" ta juya tana kallonsa fuska daure tace "Mujaheed ina son sanin meye matsalar ka don kaga shegiyar yarinyar nan da mai mota jiya har kake ikirarin hukuntata" ya xaro ido yace "Ban gane ba Umma" Ta masa wani mugun kallo tace "Bana son ka gane dama ai, warce kaje ka ba sakon take fadi yanxu naji, dama baka raba kanka da makiyan nan nawa ba har ynxu Mujaheed? Mujaheed ka gaya min meye hadin ka da yarinyar nan Imaan?" Yace "Haba Umma, ke yanxu maganar inna kike dauka, kila ma don ta ganki yasa ta kirkiri haka, ni a ina na ganta har muka yi wannan xancen da ita?" Shiru Umma tayi tana kallonsa, a ranta kuwa tunani take kila hakan ne ma, ganin Umma tayi surrender, Mujaheed yace "Kawai ta fada haka ne don ki sa a rai, ni yaushe nake da wannan lokacin ma a gidan nan yanxu" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Sae ma kaga rashin mutuncin da ta min kayan da na kai mata, ni na ma ji dadin da ta gane cewar in don ta nine baxan bata ko tsinke na ba, basirar Abban ku ne kamar yanda ta fada" Mujaheed yyi murmushi bai ce komai ba, Umma tace "Gobe xan baka sako ka kai ma Hajiya Mansura ta marafa, bata samu xuwa bikin ba amma ta bada gudunmawarta dubu dari, cin cin da su alkaki xaka kai mata daga nan nasan xa ku hadu da Safeenah, tana nan ba ta koma makaranta ba, ni so nake nan da 'yan watanni a fara xancen naka bikin" shi dai Mujaheed bai ce komai ba banda kallonta da yake, ta xauna gefen gado tace "Kar fa kace min ka manta gobe kayi ficewarka, xuwa sha biyu in sha Allah xaka kai masu, tunda gobe lahadi" ya shafa kai yace "Allah ya kai mu" daga haka ya nufi kofa ya fita. Imaan ta kara leka samirar dake cike da cin cin da dubulan da alkaki da inna ta basu su kai ma ta rasulu aminiyarta, ta tabe baki tace "Wllh duk kin kwashe ma tsohuwar, mu fa har ynxu ba mu ci ba" inna ta tsuke fuska tace "To ina ruwana da rashin cin ku, ni na aurar da 'ya ko ko? Kaji min dai, Dubu talatin ta rasulu ta bada a kawo min gudunmawa, kuma ace baxan cika mata samira da kayan flawa ba, ni ta ma fi min Aisha kiji in gaya maki" Imaan tace "Kice ma ta fi maki har daddy mana" Maimoon tace "Toh ina dubu talatin din?" Inna ta kalleta da sauri tace "Amina aka ce in ba wa da xaki tambayeni dubu talatin Maimuna? Ko ko kin ban ajiya ne? Ni dai ku daina sa min ido a gidan nan, idan ba haka ba mugun alkaba'i ba shi da kyau amma to xance kowa ya ci kansa gaskiya" Imaan ta kalli Maimoon tace "Maimoon karbo kudin motar mu wuce" Inna ta kunce ha6ar xaninta ta fiddo naira dari ta ajiye masu tace "Hamsin xai kai ku ya dawo da ku, nan nan kabala dai" Imaan ta ajiye samirar ta xauna tace "Tabdi ko naira dari dari ma baxa a yarda a kai mu ba balle hamsin" Inna tace "Barawo ne mai adaidaitan da baxai kai ku a hamsin ba, ko ya sha wiwi ne, wllh kullum a hamsin ake kai ni a dawo da ni" Maimoon tace "Saboda ke tsohuwa ce ai" A fusace inna tace "Oh oh Allah, idan baxa ku ba ku ajiye min kayana ku fita, Xan kira Bukar ko Ahmadu cikinsu wani ya kai mun, ku fitar min a parlor" Kin fita suka yi jin abinda tace wai xata kira daddy ko Abba, Maimoon tace "Toh wai don Allah mu muka siya masu adaidaitan da xasu kai mu a hamsin su dawo da mu a haka, ki kara mana kudin mu tafi mana" Inna ta jefa masu wani hamsin tace "Aniyar ku ta bi ku dai" Maimoon ta dau kudin tana gunguni tace "Ae sai dai mu cika da kudin mu" Imaan ta tabe baki ta dau samirar tace "Sai dai ke ki cika, sisina baxan kara a kai ba tunda ba ni xan ci cin cin ba" daga haka ta fice parlon, inna tace "Shi sa har yau aka kasa gano cutar da ta sa ki gaba, saboda mugun xuciyar ki da rashin kunya, ni dai Allah ya saka ma d'ana, Allah ya saka masa kan kudaden da yake kashewa a kan tsadadden ciwon nan naki, Allah kuma ya raba shi dake lafiya, ya aurar dake ya huta ma ransa mijin ma ya d'and'ana ukubar, ba a taba jin alkhairi ya fito bakin ki sai sharri, to meye kuma don kin cika kudin mota" Maimoon ta bi bayan imaan ta kullo mata kofarta tana turo baki. Suna tsaye bakin titi suna jiran adai daita da xai je kabala, Imaan tace "Ko da yake nasan tsohuwar da xa mu kai ma baxa ta bar mu haka nan ba, kila ta ba mu kudin mota" Maimoon tace "Wllh da ba dan Abba da tace xata kira ya kai ba ba inda xanje ni dai, kullum fa idan xata aiki mutum sai ta raba kudin motar xuwa wajen kashi uku ta baka daya" Imaan tayi dariya tace "Kawai so take ayi ta mana fada shi sa tace xata aiki daddy ko Abba" motar Mujaheed da suka gani yasa suka yi shiru suna kallon motar, shi ma daga gida ya fito, ya sauke glass yana kallon Maimoon, Maimoon ta marairaice tace "Ya M.A inna ce ta aike mu kabala kuma ba mu samu adai daita ba har ynxu..." Ya gyada kai yace "Toh Allah ya kawo adai daitan" xai dage glass da sauri tace "Wait... Kai ina xaka plss?" Yace "Marafa" tace "Toh ka rage mana hanya mana don Allah" ya mata wani kallo yace "Me ya hada Marafa da kabala?" Tace "Yaya ai duk hanya ce mu dai ko ina ma ka ajiye mu nasan xa mu samu a can gaba" yace "Toh shiga" Imaan ta bude back seat ta shiga ya dinga hararanta ta madubi fuska daure, dama tun da suka hada ido taga kallon da yake mata bata sake yarda ta kalli madubin ba, Maimoon na kallon fancy nylon dake gaban motar ta dauka tace "Ya M.A wa xaka kai ma cin cin da dubulan?" Yace "Anty" dariya tayi bata sake cewa komai ba, sai da suka yi nisa yace "Gidan Baaba ta rasulu xa ki kenan?" Tace "Xa mu dai, ai ba ni kadai bace, ni da Imaan ce" ya watsa mata wani kallo ta xaro ido tana yar dariya ta rufe bakinta, har kofar gidan aminiyar inna ya kai su, Maimoon sai murna take tace "Ya M.A mun gode, ko mu raka ka marafan mu ma?" Shiru ya d'an yi da farko yana shafa kansa a hankali, lkci daya yace "Toh kar ki dade a ciki idan ba haka ba inyi wucewata" bude motar tayi ta fita tana kallon Imaan da ta fita tuntuni tana cinno baki suka shiga gidan, dari biyar ta rasulu dake ta sa masu albarka ta basu kudin mota, tace "Ina gaida Hajiya Asaben, kuyi mata godiya sosai, ita kuma amarya Allah ya basu xaman lafiya da mijinta, ku kuma Allah ya maku albarka ya fiddo maku maxaje na gari" suka amsa mata da Ameen, sannan suka mata sallama suka fita da samirar don juye kayan ciki tayi a nata samiran. Maimoon na kallon imaan tace "Wai Imaan me yasa baki gaida ya Mujaheed yanxu?" Imaan tace "Saboda baya gaida Ammi na sai ya ga Daddy" Maimoon ta xaro ido tace "Da gaske?" Imaan tace "Ehh mana" Maimoon tace "Toh saboda me" imaan tace "Oho" bude back seat tayi ta shiga Maimoon ta shiga gaba ya tada motar yayi reverse ya bar anguwar. Tafiyar kusan minti sha biyar suka yi suka iso gidan Hajiyan Marafa, Dai dai gidan yayi parking daga kusa da flowers yana kallon Maimoon yace "Xan yi sllh kafin in shigo" ya mika mata ledan yace "You take this in with you" tace "Amma yaya bamu san kowa a gidan ba fa" yace "Sai ki ce Hajiya ce ta aiko ki, ina nan shigowa nace idan nayi sllh" daga haka ya fita motar, Imaan dai na tsaye ta rungume hannu jikin motar bayan ta fita, Maimoon ta fito ya kulle motarsa da lock, ya wuce masallacin da ya gani a layin, Maimoon ta kalli Imaan tace "Mu je" bin bayan ta Imaan tayi suka shiga gidan, bayan sun sanar da mai gadi gun Hajiya suka xo, duk girman gidansu haka suka saki suke kallon gidan, Maimoon tace "Ni dai baxan shiga ba gwara mu jira sa a nan, kawai mutum yaje yana ta introduction ana masa wani kallo" Imaan ta yi dariya tace "Sai kice Hajiya Rukayya ce ta aiko mu" Maimoon ta buda ido tace "Bari ya Mujaheed ya jiki, wai Hajiya Rukayya" Imaan ta tabe baki suka shiga babban balcony din dake dauke da kujeru sannan ga babban rug a shimfide kasa, kan rug din suka xauna suna kara k'are ma gidan kallo, sai bayan da aka idar da sallah Mujaheed ya shigo gidan, kallonsu ya tsaya yi ya hade rai yace "What did I tell you Maimoon?" Ta marairaice tace "Yayanmu mun yi sallama kamar basa parlor" hararanta ya dinga yi kafin ya danna bell, ko minti daya ba ayi ba mai aiki ta bude kofar, ta gaishesa ya amsa yace "Hajiya tana nan?" Tace "Wa xa ace mata" Yace "Dr Muhd, Kice Hajiya Rukayya ce ta bada sako a kai mata" Murya can kasa Imaan tace "Toh ba gashi shi ma cewa yayi Hajiya Rukayya ba" Maimoon ta yi murmushi bata dai ce komai ba, Mai aikin tace "Toh ka shigo" bin bayan ta yayi xuwa cikin parlon da sauri imaan ta mike ta bi bayansa, Maimoon na yar dariya ta tashi ita ma ta shiga parlon, wata yarinya da baxata wuce ashirin da daya bace ta shigo parlon daga dinning kallo daya tayi masu ta wuce sama, tsaki imaan ta ja Mujaheed ya kalleta ta cinno baki ta dauke kai, mai aikin ta kawo masu drinks da bottle water ta ajiye, bayan wani lkci sai ga Hajiyar ta sakko cikin shiga ta alfarma ganin Mujaheed tace "A'a ashe kai ne doctor" yyi kasa da