Showing 78001 words to 81000 words out of 139381 words
maki ko kanninsa basa samun haka, abinda Mujaheed ke maki a da ya wuce shakuwa ko so na 'yan uwantaka, ke dai ce ban san lkcn da xaki yi wayo har ki fahimci inda ya dosa, wai yaya ne... A'a ba yaya ba..." lkci daya hankalin Imaan ya tashi ta fashe da kuka sosai tace "Wllh ku daina cewa haka ba kyau, ni ba wani so na da yake yi, ina ce maku yayana ne fa, to taya xai so ni, ni kanwarsa ce fa..." Dariya kawai Rabi'ah take don imaan tayi mugun bata dariya nan kuma ta yarda har sannan Imaan na tare da yarinta ba kadan ba sannan ga ta only child shi sa abun ya taru ya mata yawa, Imaan ta mike da sauri ta fice daga dakin ta koma wani daki ta xauna kan gado maganganunsu na mata yawo a kai, fashewa tayi da matsanancin kuka ta fada kan gadon tace "Ni baxan ma kwana a gidan nan ba, ta ya xa a ce wai yaya na so na, wai yaya fa?? Allah ya kiyaye wllh" Imaan bata ta6a jin abu ya tsaya mata a rai irin abinda Halima da kawarta suka gaya mata ba, wai Mujaheed sonta yake, tabbb, ji tayi ita gaba daya duniyar ma babu wanda take jin haushi kamar Mujaheed din, duk da tasan baxai ma taba yiwuwa ace yana sonta ba, amma abinda suka gaya mata yasa ita taji bata ma son sa shi a ido, bata son ganinsa kwata kwata, lamo tayi kan gado very restless, aka bude kofar dakin ta juya da sauri, Halima ta shigo tace "Gashi Sadeeq ya kira" Imaan ta mike xaune a hankali ta amshi wayar ta kai kunne tare da masa sallama, ya amsa yace "I am outside Imaan" tace "Toh bari in fada ma gwaggo" daga haka ta katse wayar ta tafi ta nemo gwaggo ta gaya mata, Gwaggwo tace "Toh ya shigo mana ai ba kowa parlon ma, ce masa yayi shigowarsa kawai" Imaan bata ce komai ba ta sa Hijab dinta ta fita, tsaye ta gansa ya jingina da motarsa, ta karasa kanta a kasa ta tsaya keeping a enough distance tsakanin su, kallonta kawai yake, ita ko bata yarda ta kallesa ba, a hankali yace "What's wrong imaan you look disturbed" da sauri ta daga kai ta kirkiri murmushi tace "A'a ba komai fa, ya gida" yace "Lafiya lau" tace "Gwaggwo tace ka shigo ciki ba kowa a parlor" Yace "No ni baxan shiga ba kunyarta nake ji yanxu" murmushi Imaan tayi tace "Toh akwai kujeru a compound ai, shi ma baxa ka shiga ba?" Ya shafa kansa smiling sweetly yace "Ohk then mu je" ita ta shiga gaba ya bi bayanta har suka shiga cikin compound din. Sai da ta fara xama kan farin plastic chair sannan ya xauna shi ma yana kallonta, dauke kai tayi ganin kallon da yake mata yace "Amma ba dai kunyata kike ji ba" murmushi tayi tace "Shi nake ji mana" Yayi dariya yace "Aa kiyi hakuri kar ki ji plss" Ita dai bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Did you know what imaan" ta daga kai ta d'an kallesa, cikin sanyin murya yace "I am hoping to spend the rest of my life with you" Imaan ta sauke idonta kasa, yace "I was born and bred in Uk, yawancin rayuwata duk can nayi sa, daga baya na dawo Nigeria gaba daya, I've neva for once thought xan hadu da mace yar Nigeria inji ina son rayuwa na har abada da ita sai kan ki Imaan, my ex was white ita ma it's not as if I have much feelings for her, it's just to while away time... Here in Nigeria frndship kadai ne tsakanina da yan mata, Ni ban san meye so ba, I don't even believe in it until I met you few months back, pls don't break my heart imaan, it's too fragile for something this big...." Imaan tayi murmushi a sanyaye bata dai ce komai ba, yace "Yea... I have been counting down tun yanxu xuwa ranan da xaku fara waec, but plss me yasa baxa kiyi waec din a ss2 ba" xaro ido tayi ta kallesa, yace "Sure, a lot a ss2 suke waec" tace "Aa nafi son inyi ss3" ya lumshe ido ya bude yace "almost a year to come in sha Allah kenan fa Imaan?" Imaan ta kallesa tace "Sure" yace "Toh Allah ya kai mu lafiya" Tace "Ameen" Yace "Promise me something plss...." Imaan tayi shiru tana kallonsa, yace "Ki min alkawarin baxa ki yi betraying din soyayyata gare ki ba, and I am also promising u same, I will and will neva leave u for any reason" lkci daya jikin Imaan yyi sanyi tace "Ae an riga an san ka gidanmu, so there is nothing to worry about" yace "Sure an san ni, but I am afraid of ur cousins" da mamaki tace "Cousins dina kuma?" Ya d'an yi murmushi yace "Yea kada su min fin karfi...." Imaan ta kasa daina masa kallon mamaki tace "Su ai yayyina ne ba so na suke ba" Sadeeq ya girgixa kai yace "I saw their reactions ranan da Abbansu ya kira ni, more especially the very fair one" Imaan gabanta ya shiga faduwa, Sadeeq yace "They might not tell you now amma kada watarana su xo su ce suna sonki ki mance alkawarin mu, kada ki min haka plss Imaan..." cike da damuwa ya fadi haka, imaan ta ji kamar ta fashe da kuka tace "Ni ka daina cewa haka, ba wanda ke so na cikinsu duk yayyina ne su wllh, they are only disturb sbda ban gama secondary schl ba" yace "Toh Allah ya sa haka, amma ba sai kin min kuka ba gimbiyata, reminder ne" Imaan ta boye fuskarta da Hijab, yyi murmushi yana kallonta, murya can kasa yace "Kin san inda xan kai ki for our honeymoon?" Kamr yace ta kara boye fuskarta da Hijab cike da shagwaba tace "Ni dai bana sooo" yyi dariyarsa mai dadin sauraro yace "Toh na bari baby, when the time comes xa ki ga, amma fa tare da kaka xa mu" da sauri Imaan ta bude fuskarta ta xaro ido tace "Aa ba inda xata bi mu" Sadeeq couldn't help it but laugh yace "Are you serious??" Ita kanta sai daga baya taji kunyar abinda ta fada ta mike da sauri xata wuce ciki yace "Noo plss wait dear, ki rakani first plss" da kyar ta yarda ta rakasa gate tana sinne kai, ya juya yana kallonta kafin yace komai, a hankali tace "Thanks much for the earrings na gode sosai" Ya mata wani kallo yace "Bana son ki min godiya idan na baki abu, ba don ki gode min bane na baki" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, nan suka yi, sallama ta daga masa hannu ta koma cikin gida. Washegari gidan gwaggwo ya xamo ba masaka tsinke saboda yan uwa da abokan arxiki duk da gobe ne daurin auren, imaan dai na daki duk ta takura, ita dama haka Allah yayi ta bata da sakewa cikin mutane, babu yanda Halima bata yi da ita kan ta bi su gidan wata makociyarsu ba don can xata xauna har gobe sbda mutane amma taki, Har daki Ammi ta kawo mata abincin rana ganin ta ki fitowa, ganin yanda take yatsine yatsine Ammi tace "Ko dai xa ki wuce gida ne bana son matsala" girgixa kai tayi tace "A'a kawai kaina ke min ciwo amma idan na ci abincin xan sha magani" Ammi ta tabe baki ta fita dakin, imaan ta gama cin abinda xata ci a abincin ta dau maganin ta sha, mikewa tayi rike da plate din ta fita don kai wa wajen wanke wanke, tun da ta fito parlor taji numfashinta na tsarkewa ta dai dinga gyaran murya har ta fita compound, hayaki ne cike gidan saboda wutan icce da aka hura, ta rike numfashinta da sauri ta karasa ta ajiye plate din ta juya xata shiga parlor ta saki numfashin, tari ta fara sosai ta durkushe nan bakin kofa mutane suka taho kanta, Nan Asthma dinta ya tashi duk Gwaggwo ta rikice tana salati, Ammi ta wuce daki da sauri don duba inhaler dinta a jaka, Aunty da sauran mutanen wajen suka shigar da ita parlor. Har Imaan ta samu bacci dakin Gwaggwo bayan an rufe duk windows din an kunna mata fan Halima ta shigo sanye da Nikab a kan Hijab dinta ta durkusa kusa da ita tace "Sannu Imaan" bude ido tayi amma ta kasa cewa komai, ba kadan asthman yayi attacking dinta ba wnn lkcn don har sun yi niyyar tafiya asibiti sannan ya lafa, Kai kawai ta iya gyada mata, Halima ta dinga kallonta cike da tausayi, Can tace "Sadeeq ma ya kira har sau biyu, bari in kirasa ince baki da lafiya" Ita dai Imaan bata ce komai ba, Halima ta kirasa ya katse ya kira ta, tace "Ka kira daxu ina sllh, na taho gida yanxu na tarar ma Imaan din bata da lafiya" Yace "Subhanallah what's wrong with her?" Halima ta rasa me xata ce masa da farko don bata san ko yasan imaan na da Asthma ba, can tace "Gata nan dai a kwance bari in bata" mikewa Imaan tayi da kyar ta karbi wayar ta kai kunne cikin sanyin murya tayi masa sallama, cike da damuwa yace "What's wrong with you dear?" a hankali tace "Naji sauki" yace "But what happened, dama baki da lafiya ne?" D'an shiru tayi kafin tace "I had an attack..." Da mamaki yace "Are... you asthmatic?" Ta gyada kai kamar yana ganinta tace "Um" yace "Subhanallah, to Allah ya sauwake... is ur breathing now ohk?" Tace "Sure" yace "Xa ki iya fitowa yanxu?" Ta yi shiru, sai kuma a hankali tace "I will try" yace "Alryt gani nan xuwa" katse wayar yyi, ta koma ta kwanta, Halima na kallonta tace "Allah ya sauwake imaan" imaan ta d'an mata murmushi, Halima tace "ki rike wayar idan ya kira bari xan je ana jirana na sani" Imaan tace "Toh nagode" daga haka Halima ta mike ta fita, ba a dau lkci da fitar ta ba Gwaggwo ta shigo da cup din tea ta xauna gefen gadon tace "Sannu Fatima tashi ki sha shayi na hada maki" imaan ta mike xaune tace "Gwaggwo ai na ci abinci, a koshe nake" Gwaggwo xata yi magana sai ga Ammi ta shigo dakin tare da Aunty, aunty na kallonta tace "Sannu Imaan, ya jikin" imaan ta d'an yi murmushi tace "Na ji sauki Aunty" Aunty tace "Toh Allah ya kara lafiya" fita Aunty tayi don xuwa su ci gaba da aikin da su ke yi, Ammi na kallonta tace "Kirjin yyi sauki?" Imaan tace "Kadan kadan yake min" Ammi tace "Toh sannu, dama sai da daddy ya guji hakan, nima nasan kawai wahala xa ki xo ki kara min nan" Gwaggwo tace "Wani irin magana ce wannan Aisha, ita ta daura ma kanta ciwon ashe?" Ammi dai bata ce komai ba, imaan ta kalli wayar Halima da ya fara ring, Sannan ta daga a hankali ta kai kunne, satan kallon Ammi tayi, murya can kasa tace ma Sadeeq "Toh..." Daga haka ta katse wayar, Gwaggwo tace "Wa ye?" Imaan ta sunkuyar da kai tace "Ce min yyi yana waje" Gwaggwo tace "Sadeeq?" Imaan ta gyada mata kai, Gwaggwo ta kalli Ammi tace "Toh ko ya ajiye ta gida kawai... Ni xamanta nan bai kwanta min ba, ba a fara komai na girki ba fa ciwonta ya tashi, ina ga gobe da xa ayi girke girke" Ammi tace "Waye ya kira ki?" Imaan ta kasa cewa komai, Gwaggwo tace "D'an gidan Bulasawa ne..." Ammi tace "Bulasawa kuma?" Gwaggwo ta kalli Imaan tace "Ko bata san ki da shi bane??"Imaan tayi kasa da murya tace "ta san shi" Ammi tace "Na san sa a ina??" Imaan tace "Abokin ya Muhsin fa" da mamaki ammi tace "D'an Bulasawa ne dama?" Gwaggwo tace "D'an sa ne na cikinsa, yaro mai hankali da natsuwa yana yawan xuwa tare da Muhsin gaisheni, ban ma san suna tare da fatimar ba, akwai wani lkcn dai da ya xo ya sameta a nan, ko tun lkcn suke tare ban sani ba" Ammi ta kasa cewa komai sai kallon Imaan take, Gwaggwo tace "To tashi ki je, ki ce masa ya shigo ina nemansa" imaan bata ce komai ba ta mike da kyar ta sa Hijab ta fita, bayan fitarta Ammi ta xauna gefen gadon tana kallon mahaifiyar ta tace "Anya kuwa Gwaggwo, d'an wajen Bulasawa fa, ina shi ina Imaan kuma? Kinsan yaudara tayi yawa yanxu a rayuwar fa" Gwaggwo tace "Fal yaqul khairan auliyasmut... Bana son irin wannan maganan, Sadeeq bai yi kama da mayaudari ba kuma tun kan ya san imaan yake xuwa min tare da Muhsin, ba a taba cewa d'an mai kudi ne yaron, faram faram yake da kowa, ni dai har ga Allah ya min kuma xan yi farin ciki idan Allah yasa shi ne mijin imaan" Ammi dai ta kasa cewa komai har sannan bata daina mamakin wai Sadeeq yaron Bulasawa bane. Tunda Imaan ta fito Sadeeq ke kallonta, ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" yace "Lafiya lau, ya jikin?" Tace "Na ji sauki" yace "Tablet kike sha ko inhaler kike amfani da?" Tace "Inhaler" ya d'an yi shiru kafin yace "Toh Allah ya sauwake" Tace "Ameen, Gwaggwo tace ka shigo" ya d'an buda ido yace "Da gaske" ta gyada masa kai, yace "But ba mutane a ciki" d'an murmushi tayi tace "Idan ka shiga xaka gani" Haka nan dai Sadeeq ya shiga gidan yana sinne kai, bayan sun gaisa da Gwaggwo, Gwaggwo tace "Ka taimaka ka ajiye fatima a gida Sadeeq bata ji dadi ba" yace "Toh In sha Allah Gwaggwo" bai jima a parlon ba ya fita bayan yayi sallama da Gwaggwo, imaan ta fito daga daki rike da trolley dinta tayi ma Ammi da Gwaggwo sallama sannan ta bi bayansa... the journey was silent, lta dai ta jinginar da kanta tana sauke numfashi a hankali, lkci lkci Sadeeq ke kallonta sai ya sakar mata lallausan murmushi, ita dai sai dai ta sauke idonta, dai dai gate din gidansu yyi parking, a hankali ta kallesa tace "Nagode" yace "How will I reach you ltr, ko xaki yi plugging fone naki idan kin shiga ciki?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Ina wayarka" bata jira cewarsa ba ta dau tsadadden wayar sa dake ajiye ta yi dialing number din inna yana fara ring inna ta dauka kamar jira take tana cewa "Ni dai an dameni, tun safe nake aiki ban xauna ba wllh, waye kuma wannan" murmushi Imaan tayi ta katse wayar, Sadeeq ma yyi murmushi yace "Number kaka koh?" Ta gyada masa kai ta bude motar ta fita tana kallonsa, Fitowa yayi ya fiddo mata jakarta yace "Ki huta sosai idan kin shiga ciki plss" tayi murmushi tace "In sha Allah" yace "Alright dear, Allah ya kara lafiya" wucewa ciki tayi ta nufi part din Inna, inna ta dinga kallonta daga sama har kasa tace "Lafiya kika taho min nan da jaka??" Imaan tace "A'a ni daga gidan gwaggwo nake" Inna tace "To har na ji sanyi" Imaan dai bata tanka ta ba ta ajiye jakar ta cire Hijab din jikinta ta kwanta kan kujera, inna tace "Toh har an gama bikin ne kika dawo ko kuma bikin ne dai garau garau kika gudo?" Imaan dai bata ce mata komai ba, inna tace "Atoh, ni dama shi sa naki xuwa kwata kwata, ba ruwana inje in dawo da yunwan cikina, biki ba na yan gayu ba, kuma dama Habiba bata ce min tana aurar da jikarta ba, ni dai na bada dubu biyar a kai mata ban bi ta halinta ba, Allah ne xai bani lada" Wani bowl dake rufe inna ta bude Imaan dake ta kallonta ta leki bowl din daga kwancen da take taga nama ne soyayye a cike, inna ta saci kallonta suna hada ido ta mike ta wuce daki da bowl dinta, ba a wani dau lkci ba ta fito da bokitai, ta sa makulli a kofar dakin, Imaan tace "Fita xa kiyi kike sa makulli a dakin?" Inna tace "Baxan sa makulli ba sauro su cika dakin su sa min cuta in bar 'ya yana da wahala?" Tana fadin haka ta fita waje xata wanke bokitan da ta kwaso, Imaan na kallon film da ake a TV taji muryar inna tana cewa "Mujaheed kai me cewa inje bikin su gidan uwar Aisha to ga jikar gidan ma ta gudo daga bikin balle ni karere, ji dai yanda aka dinga facaka da kaji a bikin kanwarka, toh can ni nasan baxa su yi haka ba, abinda duk na san su, meye ban sani ba..." Da sauri Imaan ta mike xaune jin wanda inna ta ambata, Mujaheed dake ta kallon inna yace "Ke dai ki daina haka..." Inna tace "Ni akwai wanda ya isa hanani fadin gaskiya kuwa duk girman duniyar nan?? to duk ba wannan ba don bai shafeni ba, inji ka siyo min kazar da nace maka nake marmari" Mujaheed bai tanka ta ba ya nufi kofar shiga parlon, da sauri Imaan ta saka Hijab dinta ta rufe har kafarta ta kafe TV da ido, Mujaheed ya shigo parlon, kallo daya yyi mata ya ajiye ledan hannunsa ya xauna yana danna wayar hannunsa, Imaan ta ki yarda ta kallesa gabanta sai faduwa yake, gaba daya she was uncomfortable, Inna ta shigo tace "Allah maka albarka, kai kadai dama xance ka siyo ka siyo" kitchen ta tafi ta dauko plate biyu ta xauna kan tabarma tana gogewa ta bude ledan kazar ta raba biyu, daya nata daya nashi, can dai ta kallesa tace "Toh ita kuma warcan matar ya xa mu yi da ita, tunda ba da ita aka siyo ba" shi dai Mujaheed bai ce komai ba, Inna ta tabe baki ta dauko wani plate din ta dau cinya daya da tsoka daya ta dangwala a