Showing 75001 words to 78000 words out of 139381 words
a hankali yace "Tace ba komai tsakaninsu, bata ma wani sansa ba kawai shine ke kiranta a waya..." Imaan ta kallesa da sauri, Abba yace "Haka ne Imaan?" Kamar xata yi kuka tace "Abba ni dai bance masa haka ba, frnd dina ne fa, kuma yana koya min karatu ta waya wani lkcn, ina ganewa kuma" Mujaheed ya kasa kallon Abbansa, Abba ya kafe sa da ido, can ya d'an yi murmushi mara sauti yace "Toh shikenan mamana, tashi ki tafi" mikewa tayi ta nufi kofa, xata fita ta d'an saci kallon Mujaheed da ya ki dago kansa ta fita. Bata damu da irin kallon da Umma ke mata ba har ta fita parlon ta wuce part din su. Abincin inna ta dauka ta tafi kai mata, sallah ta sameta tana yi a parlor ta ajiye abincin xata fita, inna ta dinga gyaran murya alamar ta tsaya, imaan tayi kamar bata ji ba tayi wucewarta da sauri, a hanya ta tadda Yusuf rike da ledan fruits xae kai ma inna, ta gaishesa tana kallonsa, sama sama ya amsa mata ya wuce, ta tsaya ta bu sa da kallo har yyi nisa, turo baki tayi ta bar wajen, har ta gama shirin kwanciya kiran Sadeeq ya shigo wayar ta, ta kashe fitilan dakin ta hau saman gado ta rufe har kanta da duvet sannan ta daga kiran, murya can kasa ta amsa sallamansa yace "Kin fara bacci ne?" Ta girgixa masa kai tace "A'a" murmushi yyi yace "Toh ya kike?" Tace "Alhmdllh, ya aiki?" Yace "Lafiya lau..." A hankali tace "Shine daxu baka ce min xa ku xo da ya Muhsin ba koh?" yyi murmushi yace "Shi yace kar in gaya maki" tace "Toh yanxu da kun sameni ban sa Hijab ba fa?" Ya wara ido yace "Yea sai in ganki da kyau, ai ba laifi bane don naga abinda nake so ba hijab" ta xaro ido tace "Uhnnn?" Yace "Yess" murmushi tayi bata ce komai ba, Yace "Ya Ammi fa?" Tace "Tana lafiya" yace "Maa sha Allah, kinje gun kaka yau?" Tace "Ehh na je kai mata abinci" yace "Ina son in samu time in xo mu yi hira sosai da ke da kaka" ta xaro ido tace "Ai ita bata hira, bata fiye son magana ba ma" Dariya Sadeeq yyi yace "Really?" Kamar xata yi kuka tace "Ehh" yace "Uhm to shikenan, yaushe xan xo mu yi hiran mu biyu kadai, I want to tell you lot of things Imaan" Murmushi tayi tace "Ae Daddyna na gari bai koma ba tukun" Yace "Toh baxa ki gidan gwaggo ba mu hadu can?" Ta d'an yi shiru, murya can kasa yace "Are you there Imaan?" A hankali tace "Toh gobe xan ce ma Ammina xan je can dama ai saura kwana uku bikin Anty Halima kilan idan na je sai bayan bikin xan dawo gida" yace "Toh shikenan idan kin shirya goben sai ki kirani" ta xaro ido tace "But ai sai Ammi ta amince in je, kasan ba a son ina fita ni kadai" yace "Toh Allah yasa ta amince" Tace "Ameen" da sauri Imaan ta cire duvet din kanta jin kamar ana bude window, ganin farin abu tayi ya fadi kasan dakin, ta sauka gadon ta nufi windon da sauri ta bude labule har sannan waya na kare kunnenta, Mujaheed ne tsaye kusa da window din, ta xaro ido tana kallonsa, yana mata wani kallo ya juya ya bar wajen, ta rufe window din ta durkusa ta dau takardan tana kallo, muryar Sadeeq taji a kunnenta yace "Are you there?" Tace "Yea ina ji" yace "Ko kin fara jin bacci ne" murmushi tayi tace "Um" don so kawai take ta bude takardar ta ga content dinsa, yace "Toh shikenan, sleep like a baby dear" murmushi tayi tace "Toh nagode, good night" daga haka ta katse wayar ta ajiye ta kunna fitilar wayar ta warware takardan tana haska rubutun kai, xumburo baki tayi ta cukwuikuye takardan ta jefar ta kwanta kamar xata yi kuka tace "Ni dai ba ruwanka da ni"
Mikewa tsaye Aunty tayi tana kallon Yusuf dake xaune gefen gadonta, shi kam bai yarda ya kalleta ba, Tace "What are you saying Yusuf?" Still ya ki cewa komai, aunty ta dinga kallonsa ko kiftawa babu, can ta ja stool ta xauna tace "Ka daga kai ka min magana malam" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta, tace "Are you serious with what you are saying, or should i say are you on ur right senses?" Cikin sanyin murya yace "Sure Mum" Tagumi Aunty tayi tana kallonsa with much surprise, can ta girgixa kai cike da damuwa tace "Kai ma kasan wannan ba abu bane da xai yiwu, ba abu ne mai sauki, haba Yusuf me yasa ka yarda xuciyarka ta yaudare ka da son abinda kasan da wuya ka samu, ko da kuwa kana tunanin xaka samu mai yasa baka tsaya kayi naxarin irin matsalolin dake tattare da samun ba? Wait tukun toh ita Hafsat din fa?" Ya girgixa kai cikin low voice yace "Ku ke tunanin ina son Hafsat, she is just a frnd, bani da intention na auranta...." Aunty ta xaro ido tana kallonsa, can tace "Ikon Allah, i really don't know what to say to you now Yusuf, ban san me xance ba gaskiya, amma ni da xaka bi shawarata ka bar wannan xancen it's something that isn't and will neva be possible, forget this pls son" Yana kallonta da mamaki yace "Why Mum?" Tace "Look Yusuf, Imaan is my daughter, her mother is my very close frnd as well, infact childhood frnd dita ce Aisha, don ta dalilinta na hadu da mahaifin ku har muka yi aure, but... ni xan fi son mu ci gaba da xumunci da Hajiya Aisha as just the frnds we are, and marrying into same family, I mean relationship din mijinta da mijina, amma bana son xumuncin mu ya koma na in-laws, its somehow, that aside Yusuf, kusancin inna da Imaan.... don't misunderstanding me plss son, kai ma inna kakar ka ce, amma gaskiya akwai matsala daga bangaren inna ka bar ni ma in ji da headache daya...." Yusuf ya girgixa kai yace "Kiyi hakuri Mum, I don't think all this u are saying is enough da xai sa ki hanani auren Imaan" Aunty ta bude baki tace "Ni nace xan hana ka aure Imaan Yusuf, idan Allah yyi Ita din matar ka ce ni na isa in hana? Don't quote me wrong plss, amma kai kasan kana son ta me yasa ko sau daya baka taba nuna alamar haka ba?" Yace "That's bcos she is still young, har yanxu Imaan bata san meye rayuwa ba, bata san kanta ba har ynxu, I was thinking idan ta fara jami'a ta d'an yi hankali sai in fito da intentions dina toward her" Aunty tace "Toh Allah ya kyauta, I think it's best ka je ka samu abbanku, amma ni nasan da kyar ne...." Yusuf yyi kasa da kai a hankali yace "Ni dai ki daina cewa haka plss mum, support me sannan ki min addu'a" a sanyaye tace "Toh na daina cewa haka, Allah yayi maku xabi mafi alkhairi Yusuf" yace "Nagode mum" daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Tagumi tayi tana furta innalillahi.... A xuciyarta. Sake baki Abba yyi yana kallon Yusuf with surprise, shi dai Yusuf bai yarda ya kallesa ba, bayan few seconds Abba yace "Yusuf" Sai a sannan Yusuf ya daga kai da kyar yana kallon Abban nasa, Abba yace "Kana nufin Imaan kake so?" Yusuf ya sunkuyar da kai a sanyaye yace "Ehh Abba" Abba yace "Ikon Allah" Shiru ne ya biyo baya na kusan minti biyu, can Abba ya daga wayarsa yyi dialing number Mujaheed har ya gama ring ba a daga ba, Abba ya ajiye wayar sanin yana gun aiki, Abba yace "I am happy hearing this son, but at the same time I am disturbed coz I made a promise to someone earlier, all the same don't worry, Allah xai shige mana gaba, tashi ka tafi" Mikewa Yusuf yyi ya nufi kofa Abba ya bi sa da kallo yana murmushi. Ko minti goma ba ayi da fitar Yusuf ba sai ga Umma ta shigo parlon Abba cikin shirin fita, har sannan Abba was still pondering at what Yusuf told him, kuma har ransa yake jin xai fi kowa murna da wannan hadin, Auren d'an sa da tillon 'yar d'an uwansa, tunanin yanda xai fara billowa al'amarin yake, first ya fara kiran D'an uwan nasa ya sanar masa sannan su tafi gun Mahaifiyar su ita ma su sanar da ita, yasan Daddy xai yi farin ciki da hadin shi ma, don fargabarsa a ko da yaushe gidan da only child din tasa xata fada da sunan aure, yasan Daddy na son imaan fiye da tunanin me karatu, he can do anything bcos of his only child, Umma Ta karasa cikin parlon tace "Alhaji kasan Mujaheed ya tura min kudi xan fara hada masa lefe, to yau xan fara shiga kasuwa" Abba na kallonta da mamaki yace "What? Lefe kuma? But he told me nothing about that" Umma ta d'an bude ido tace "Toh ba sae an gama hadawa ba xa a kinkimo maka ka gani, kar ya fada maka kayi tunanin ko so yake ka basa wani abun, wllh ban son ya daura maka ko wani nauyi ne kaga ba a dade da hidimar seeyama ba, tunda Allah ya hore masa xai iya komai shi sa kawai nace kada ya gaya maka sai na gama hada kayan a kawo maka ka gani, ba laifinsa bane shi ma ya so sanar da kai na hanasa, amma idan hakan ya bata maka rai kayi hakuri don Allah" Abba yace "Toh Allah ya rufa asiri..." Umma tace "Ameen, tun jiya naga kamar abu na damun ka, shine nace to mai kuma ya faru, idan ma inna ce don Allah a dinga hakuri, uwa ce... Sai ayi ta fatan a gama lafiya da ita, ya ci ace duk abubuwan inna ya xame maka jiki yanxu..." Abba yace "Haka ne" Umma ta xauna ganin maganganunta sunyi tasiri xuciyar Abba, murya can kasa tace "Toh me kuma take so Alhaji?" Abba yace "A'a wannan mun shawo shi tare da Sadeeq, Yusuf ne dai ya xo min da wata magana yanxu da ya kulle min kai... Am still trying to find a way out ne har yanxu" Da mamaki Umma tace "In ji dai lafiya??" Abba yace "Lafiya lau, yar uwarsa Imaan yake so da aure wai" Mikewa Umma tayi da mugun mamaki baki bude tana kallon Abba, can tace "Aure kuma Alhaji??" Abba yace "Kwarai, yanxu ma ya bar parlon nan" Umma tace "Ikon Allah.... Aure fa???" Juyawa tayi ta nufi kofa tace "Toh Allah yayi mana mai kyau dai, ya xaba abinda ya fi alkhairi, ae imaan yar uwar sa ce, Imaan ta mu ce..." daga haka ta fice, direct sama ta wuce ta bude dakin Yusuf ganin baya ciki ta shiga dakin Aunty, xaune ta samesa tare da Aunty, Umma tace "Amma Yusuf kayi asara wllh, ka kuma samu tabin kwakwalwa mai wuyar ganowa balle ayi maka magani, yanxu ka rasa warce xaka je kace ma Ubanka kana so sai Imaan, Yusuf me ya same ka ni Rukayya?? ina ita Hafsar da kake nema take??" Yusuf dake kallonta yace "Umma ni Hafsat ba aurenta nace xan yi ba" Salati Umma ta saki tace "Amma Allah ya isa tsakaninmu da kai, mu xaka ka ma bakin ciki Yusuf?? ka bar 'yar attajiri ka dawo kace mai lalura iri iri kake so? Anya akwai lafiya kuwa, mu xaka kwaso wa mugun iri, irin ciwo a xuri'ar mu? Yarinya mutu kwakwai rai kwakwai?? Toh wllh tunda an asirce uwarka ta kasa cewa komai ni kam ba a asirce ni ba sai inda karfina ya kare in sha Allahu, yanda xan ma Mujaheed haka xan maka don duk daya ku ke a gu na, in sha Allahu sai naje na gano tushen abun nan... Ba wanda ya isa ya ci nasara a kanka kamar yanda aka ci a kan kanin Ubanka, uban kuturu yyi kadan wllh balle na makaho" daga haka ta fice a dakin kamar xa ta tashi sama, Aunty da ta bude baki tana ta kallonta tace "Ikon Allah ya fi gaban haka...."
Daddy couldn't help it but laugh bayan Abba ya xo har part dinsa ya sanar masa intention din Yusuf a kan Imaan, Daddy yace "Ikon Allah, nayi farin ciki sosai sai dai kar ka mance da alkawarin da kayi a baya barrister, ko ya xa mu yi?" Abba yace "Sure ina sane, shi ma ba wai xa a dakatar da shi bane Sadeeq din, abinda xai faru yanxu kawai mu fara xuwa gun Inna mu je ta bakin ta kafin a yanke ko wani decision" Daddy yace "Gaskiya ne wannan" Part din inna suka tafi a tare, Inna ta fito daki tace "Tun safe in gaya maku nake aiki ban xauna ba, ku leka bandakina ku ga ko tuwo ya xube kasa xa a iya xaunawa a cinye tass, ba ku ji bayana ba kamar ya balle ni dai in huta" Murmushi duk suka yi suka xauna, Daddy yace "Gwara dai ki dinga hutawa haka inna, gashi kince baki son mai aiki balle a samo maki ko yar dattijuwa ce" Inna tace "Ni ko ina xan so masu aiki mutane duk wari, sannan su cinye ma mutum abinci, A'a ba ruwana ni ko da rarrafe ne xan yi aikina, 'ya yanku ne sun xama abun tsoro banda haka Imaan ko Maimoon ko Ummi baxa su dinga xuwa min d'an share share ba banda karshen duniya da lalacewa ta xo" Abba yace "Inna ke fa kika ce baki so, ai da suna xuwa..." Inna tace "Ehh ni nace bana so, don ba abinda suka iya gaskiya, basa min yanda nake so, ni dai nace na yafe su daina xuwa" Duk suka yi shiru basu ce mata komai ba, ganin ta dauko tsintsiya Abba yace "Inna daxu Yusuf ya sameni kan wata magana da naga ya dace mu sanar maki kafin mu yanke hukunci...." Ajiye tsintsiyar tayi ta xauna kan kujera da sauri tace "Me ya faru kuma??" Abba ya d'an yi murmushi yace "Wai yar uwarsa Imaan yake so da aure...." Inna ta gwalo ido ta saki baki tana kallonsu, saukowa kasa ta yi a hankali ta xauna kan rug ta fashe da matsanancin kuka tana tafe hannu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, LA haula wala kuwata illa billahil Aliyul Azeem, la ilaha ilallahu Muhammadurrasulillahi sallallahu alaihi wassalam, hasbunallahu wa ni'imal wakeel.... Na ga abinda ya isheni ni patuuu" Daga Abba har Daddy kallonta suka dinga yi da mamaki, inna ta dakatar da kukan da take tace "Toh da kyar idan Imaan bata ta6a shan nonon Amina ba ma, yo ta ma sha ne kawai... Idan xa kuyi ta kanku kuyi ta kanku"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019Mikewa Imaan tayi da sauri ta nufi cikin gidan tana waigan ko Mujaheed ya dawo har ta shiga ta kulle kofa, dakin gwaggwo ta wuce ta boye box din a cikin trolley dinta, tsoronta daya yanxu Ammi, bata san me xata ce ba idan ta ga dankunnen, bayan Magrib suna cin abinci tare da Anty Halima da wata kawarta, wayar Halima ya fara ring, dauka tayi bayan taga mai kiran ta kalli Imaan tace "Wai ina wayar ki?" A hankali Imaan tace "Yaya ya kwace min" Halima ta xaro ido tace "Saboda me?" Buda hannu Imaan tayi alamar bata sani ba, Halima ta mika mata wayar tace "Toh gama magana tukun" karba Imaan tayi ta kai kunne bayan ta daga hade da yin sallama, Sadeeq ya amsa mata daga daya barin yace "Har yanxu baki yi charge din wayar ki bane Imaan?" A hankali tace "Ehh" yace "But naga akwai wuta ai yanxu, ina ma anguwar" ta langwabar da kai tace "Wayar na gida fa" yace "Ohk after Isha xan kira ki, it's almost time now" tace "Allah ya kai mu" daga haka ya katse wayar, Imaan ta ajiye gefen gado, Halima tace "Haka kawai Mujaheed din ya amshe maki waya?" Tace "Ehh wai saboda abokin Muhsin na kirana" Bude baki Halima tayi tace "Toh shi ina ruwansa" Imaan ta buda hannu tace "Nima ban sani ba" Rabi'ah kawar Halima tace "Yayanki ne kuma?" Halima tace "Cousin dinta dai" Rabi'ah ta d'an bude ido tace "Toh ko son ki yake?" Still Imaan tayi tana kallonta da wani expression, can tace "Yaya ne fa... Yayana ne shi" Rabi'ah tayi dariya sosai tace "Wai yaya ne, to haka kawai baxai dinga hana ki waya da samari yana kwace maki wayar idan babu wani abu a kasa" Imaan ta ajiye cokalin hannunta a hankali tace "Abu kamar me?" Halima tace "Tukunna dae me yace maki da yaga Sadeeq din na kiran ki?" Imaan ta jingina da gado tace "Kawai ya hanani waya da shi ne, har blocking dinsa yyi ni kuma nayi unblocking dinsa, a gida ma da Abba ya kira ni xai tambayeni meye tsakaninmu da Sadeeq kafin in je ya sameni wai ince ban san sa ba" Dariya sosai Rabi'ah take, Halima tayi murmushi tace "Tabb, lallai Mujaheed" Imaan dai sai kallonsu take don bata san me ya basu dariya ba, Rabi'ah ta ajiye spoon din hannunta tana kallon Imaan da kyau tace "Toh wllh son ki yake...." Imaan ta xaro ido ta koma baya da sauri tace "Don Allah ki daina cewa haka plss, wllh yaya na ne fa, Anty Halima yaya fa ne" Halima tayi wani murmushi tace "As far as ba ciki daya ku ka fito da shi ba ki daina deceiving kanki Imaan Mujaheed son ki yake, so mai tsanani ma kuwa, ni dama tun lkcn da yake kawo ki nan few years back ina ganin irin kallon da yake maki nasan ba a banxa ba da abu a kasa, sannan kulawar da yake