Showing 72001 words to 75000 words out of 139381 words

Chapter 25 - IMAAN

Start ads

20 Aug 2025

657

Middle Ads

Sadeeq dai bai tanka sa ba ya gama danne danne wayarsa ya kai kunne, bayan wani lkci yyi kasa da murya yace "Abba gani a waje" Abba dake xaune parlonsa tare da Daddy yace "To madallah bari they will lead you in now" Ba a dau lkci ba Yusuf ya fito kofar gidan, Kallon Sadeeq ya dinga yi har ya isa inda suke, suka gaisa Muhsin yace "Ashe dai Engnr kana gari?" Yusuf yyi murmushi yace "Sure ina nan, ya aiki" Muhsin yace "Alhmdllh" Yusuf ya shiga da su compound din har xuwa parlon Abba, Sadeeq na shiga parlon ya cire glass yyi kasa da kai har xai xauna saman kujera sai kuma ya fasa ya xauna kasan rug ganin nan Muhsin ma ya xauna, har sannan bai dago kansa ba ya gaida su Abba da Daddy, duk suka amsa suna masa sannu da xuwa, Daddy yace "Muhsin abokin ka ne dama kenan" Muhsin yace "Ehh Abba abokina ne" Daddy ya gyada kai yace "That's good" Abba ya kalli Yusuf da ya xauna yace "Where is M.A?" Bude kofar parlon aka yi sai ga Mujaheed ya shigo parlon da sallama can ciki, kansa a kasa ya xauna kusa da Yusuf sannan ya kalli Sadeeq da idanuwansa ke kan TV, gaisawa yayi da Muhsin, sai a sannan Sadeeq ya kallesa yace "Barka da yamma" Mujaheed yace "Same to you" Abba na kallon Sadeeq yace "Can I know you plss son" Sadeeq ya sauke idonsa kasa yace "Sunana Abubakar Sadeeq Ahmad, ni haifaffen garin Kaduna ne, mahaifina asalinsa d'an kano ne, na gama karatu na and I am working as a medical practitioner now" Abba yace "Maa sha Allah, a wani anguwar ku ke?" Yace "GRA muke" Abba yace "Ohk can i know ur dad?" Sadeeq ya d'an yi Shiru kafin yace "Alhaji Ahmad sunansa, d'an kasuwa ne Abbana, yana kuma xaune nan Kaduna" Abba ya gyada kai cike da gamsuwa, bayan few seconds yace "What is ur intention toward my daughter Abubakar?" Sadeeq ya kasa dago kansa, Daga Mujaheed har Yusuf kallonsa kawai suke, can ya dago kansa a hankali yace "Abba sonta nake da aure...." Mikewa Yusuf yyi yana kallon Abban nasa yace "I want to excuse my self plss..." Abba ya gyada masa kai ya juya ya fita parlon, Abba yace "Toh naji dadin jin hakan daga gare ka Abubakar amma kasan ajin da Imaan take yanxu?" Ya gyada kai a hankali yace "Na sani Abba" Abba yace "Ohk good, wani xancen kuka yi da kakarta last time da ka xo?" Murmushi yyi ya sunkuyar da kansa, Abba yace "Yes go on" Yace "Abba ce min tayi idan tayi magana da ku xata sanar min in turo magabatana" Abba yace "Ohk, kai d'an wajen Ahmad Bulasawa ne?" Sadeeq ya gyada kai kawai, Abba yace "To yayi kyau, yanxu dai I want to ask for a favor from you Sadeeq" Sadeeq ya daga kai a hankali yana kallonsa, Abba yace "But before then bari in maka wannan alkawarin, Sadeeq in dai Imaan ta amince tana son aurenka, wato ta yarda da kai, sannan iya binciken da xanyi idan ban ga wani flaws dinka mara kyau ba ni nayi maka alkawarin xan baka Imaan in sha Allah, yea it's a promise I am making" mikewa Mujaheed yyi yana kallon Abba yace "Abba I want to pick a call" bai jira cewar Abba ba ya fita, Sadeeq dake kallon Abba yace "Toh nagode Abba" Abba yace "Toh favor da nake son ka min ynxu shine.... Kakarta nake son ka samu amma ba yau ba, but cikin satin nan, sai ka ce mata mahaifin ka bai kasar yanxu kuma xai dau lkci kafin ya dawo, yana dawowa kuwa xaka sanar masa xancen auren... Am doing this to allow my daughter finish her secondary schl, wato na da shekara daya, kasan yanda tsoffin nan suke, there is nothing da xan gaya mata da xata fahimce ni, amma kai idan kace mata haka to an gama komai, kaga ko da tana gamawa ne sai ayi magana amma yanxu kam I don't think xan iya bada ta tana ss2, that aside.... my promise of giving u my daughter's hand in marriage will count only on one condition ko da ta gama secondary schl, the condition is that xaka yarda ko bayan kun yi aure ta ci gaba da karatu a dakinta" Sadeeq ya d'an yi murmushi yace "In sha Allah Abba" Abba yace "Toh Allah ya mana xabi mafi alkhairi" Sadeeq yace "Ameen Abba na gode sosai, Allah ya kara girma" Abba yace "Allah maka albarka" daga haka Abba yace masa xai iya tafiya, nan suka yi sallama da Daddy da Abban sannan suka fita parlon. Muhsin na kallonsa yace "Mu je in gaida Mum dita" Sadeeq ya xaro ido yace "No kai dai kaje zan jira ka a waje" Muhsin yyi dariya yace "Common Mum dita fa na ce maka..." Da kyar ya ja Sadeeq suka nufi part din su imaan, Bell Muhsin ya danna, Ammi na kitchen xata fito Imaan ta bude kofar dakin ta, Wani kallo Ammi tayi mata tace "Kika san waye bakin kofar xa ki tafi a haka?" Imaan ta xaro ido ta juya ta koma ta dau Hijab dinta ta sa ta fito ta nufi kofar, bude kofar tayi, lkci daya tayi still tana kallon Sadeeq, Muhsin yace "Toh ko mu bi ta kanki" da sauri ta juya ta bar wajen, kafin su shiga parlon har ta koma dakin ta ta kulle, Dariya Muhsin yyi ya xauna, Sadeeq that was uncomfortable shi ma ya xauna, Ammi ta fito kitchen ganin Muhsin tace "Ka shigo anguwar kenan" yayi dariya yace "Ammi takanas nan fa na xo wllh" tace "Keep quiet kai din" yace "Ki tambayi abokina Ammi" Ammi ta karasa shiga cikin parlon tana murmushi tace "Toh sannun ku da xuwa" Muhsin ya gaidata, tun da Sadeeq ya kalleta sau daya bai sake yarda ya kalleta ba shi ma ya gaisheta, ta amsa da fara'a tana masu sannu da xuwa, Muhsin yace "Kawai ce masa nayi ya rakani in gaida Mum dita" Ammi tace "Toh kun kyauta kuwa nagode, sai dai abokin naka kamar d'an uwan mu ne Bafillatani" Dariya kawai Muhsin yake, Sadeeq dai yyi murmushi bai dago ba, Ammi ta tambayi Muhsin yayanta sannan ta tambayi Sadeeq iyayensa, Sadeeq yace "Duk suna lafiya lau" Ammi na kallon kofar dakin Imaan tace "Imaan" Muhsin yace "Kawai daga gani na shine ta shige daki saboda bata da gaskiya bata gaida mutane ko a waya" Dariya Ammi tayi tace "Ae ban san yanda xanyi da ita ba, ko nace tayi sai tace ta manta" Sai da Ammi ta kara kiranta ta fito da kyar, wannan karan Hijab har kasa ta sa, Ammi tace "Baxa ki gaida yayanki ba kika shige daki?" Bata yarda ta daga kanta ba har ta iso cikin parlon kamar munafuka ta xauna kasa kusa da kujera tace "Ina yini Ya Muhsin?" Yana murmushi yace "Lafiya lau Imaan, ya gida?" Tace "Lafiya lau" ta saci kallon sadeeq da yaki kallon inda take tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" Ammi tace "Ki dauko masu ruwa fridge" mikewa tayi ta wuce kitchen, Ammi tace "Jiya mun yi waya da yaya yace gobe xai dawo" Muhsin yace "In sha Allah, haka yace min" Imaan ta shigo cikin parlon ta durkusa ta ajiye tray din ruwa da lemon five alive sai glass cups biyu, Ammi tace "Na gama girki bari in xubo maku" Muhsin yace "A'a ki bar shi kawai Ammi a koshe mu ke..." Ammi tace "Idan kai baxa ka ci ba sai abokin naka ya ci, ya sunansa ma dai?" Dariya Muhsin yyi yace "Sunan Daddy garesa" Ammi tayi murmushi tace "Ikon Allah, mai gida ne ashe" Muhsin ya kasa daina dariya, Imaan na ajiye drinks din dama ta shige daki ta kulle kofa, Ammi na shiga kitchen Sadeeq yyi kasa da murya yace "Don Allah ka rufa min asiri mu wuce Muhsin" ko kallonsa Muhsin bai yi ba ya mike ya bi bayan Ammi kitchen, har ta fara xuba masu abincin a plate yace "Ammi kinsan waye muke tare da kuwa?" Ammi ta juya tana kallonsa tace "A'a, waye?" Kasa daina dariya yyi yace "Wllh surkin ki ne, saurayin Imaan" Ammi ta saki serving spoon din hannunta tana kallon Muhsin baki sake tace "Amma baka da kirki Muhsin shine ka bar ni ina ta xuba a parlor?" Dariya kawai Muhsin yake, Ammi tace "Ni dai ba ka kyauta min ba, haba naga yaro ya ki sakin jiki, ita kuma Imaan sai na ci mutuncin ta..." Da sauri ya dakatar da ita yace "Wllh bata sani ba, baki ga ita ma duk ta ki sakin jiki ba" Ammi tace "Ni dai ka cuce ni, har kasa naje ina ce masa mai gida" Shi dai bai fasa mata dariya ba, ta gama xuba abincin tace "Ai sai ka daukar maku, ni kam na wuce daki" bata kara sauraransa ba ta fita kitchen din ta wuce bedroom dinta, Muhsin ya ci abincinsa ya koshi, Sadeeq kam ruwa kawai ya sha ya mike yace "I am waiting for you outside" duk yanda Muhsin ya so tsayar da shi kin saurarensa yayi har ya fita, nan Muhsin ya kira Ammi a waya yace "Toh ya dai fita Ammi ki fito mu yi sallama" Ammi ta fito parlon tace "Bai ci abincin ba kenan" Muhsin yace "Ae baxai ci ba, Ammi Abbansu Mujaheed ne fa ya kirasa yana nemansa shine muka taho tare" Ammi tayi shiru tana kallonsa da mamaki, can tace "Toh ya aka yi da ku ka je?" Muhsin yace "Ba wani matsala wllh, Ai nasan daddy xai maki bayanin komai idan ya shigo, yanxu dai xan wuce kinga yana can waje yana jirana" Ammi tace "Toh shikenan ka gaida Hajiya da Hajjo" Yace "In sha, kice ma Imaan ta fito mu dai mun wuce" daga haka ya fita parlon yana murmushi, a can kofar gida ya tadda Sadeeq xaune cikin mota yana jiransa, Muhsin ya bude motar ya shiga yana kallonsa yace "Kai dai ka rage munafurci Sadeeq duk rashin jin ka don ka xo gaban surkai sai kayi ta wani sinne kai" Murmushi kawai Sadeeq yyi ya saka glasses dinsa ya tada motar yace "I will have ur time later" daga haka ya fara reverse suka bar layin. Kamar yanda Muhsin ya fada hakan ne ya faru don daddy na shigowa bayan Magrib ya yi ma Ammi bayanin duk abinda ke faruwa, Ammi tayi shiru duk jikinta yyi sanyi, A hankali tace "Toh yanxu ya ake ciki yallabai?" Ya sauke ajiyar xuciya yace "Ina imaan din, taje can barrister na kiran ta" Ammi tace "Ni dai Yallabai da dai a dakatar da yaron gaba daya, imaan har nawa take don Allah" Daddy yace "So kike ki ja mana matsala gun inna kenan, did you know maganar da ya dawo dani weekend kenan, ke kin ga abubuwan da inna ta dinga fadi a parlor kuwa jiya?" Ammi dai bata ce komai ba, Daddy ya girgixa kai yace "Fatanmu mu rabu da ita lafiya, gaba daya ta rikice ne yanxu" murmushi kawai Ammi tayi, Daddy yace "I don't even know me yasa xa ki ba Imaan fuskar kula saurayi at the first place, ko me xaki ce min baxan ta6a yarda baki san da xancen yaron ba, kuma ki wani ce min nawa Imaan take?" Ammi tace "A'a ko da baxa ka yrda ba I have to tell you I know nothing much about the boy, of recent naga tana waya shi ma sai da na mata fada, kai sai kace baka san yar taka bace da nuku nuku" Daddy yace "Wannan ba hujja bace, kina tare da ita 24/7 a gida...." Ammi ta dakatar da shi tace "Toh duk ba wannan ba ita innar da ta kirkiro abun sai a fada mata ta gaya ma yaron lalurorinta... If he wish to be with her like that shikenan, idan kuma baxai iya ba gwara tun wuri a san haka, I don't want my daughter's heart to be broken or anything of such..." Daddy ya dinga mata wani kallo ta mike ta wuce kitchen, yace "Wato you are even in support of the silly thing the girl did, dama nasan kinsan komai ai, tunda aure take so fine I will give her the best wedding ever" Imaan ta marairaice tana kallon Ammi tace "Toh me yasa yake kirana Ammi?" Ammi tayi banxa da ita, a hankali ta mike ta nufi kofa, Ammi tace "Kuma kiyi maxa ki dawo idan ya sallameki ki xo ki kai ma Inna abinci" to kawai tace ta fita parlon. A hankali Imaan ta bude kofar parlorn hade da sallama ta shiga ciki, Umma ce xaune parlor sai Ummi da Rahma, ta dauke xata wuce parlon Abba Umma ta dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa, Imaan ta tsaya amma bata juyo ba, Umma ta mike tana mata kallon tsana karara tace "Uwarki tayi ajiya parlon ne ta aiko ki kixo ki dauka?" Imaan taki cewa komai sai ma dauke kanta da tayi, Xagi Umma ta kunduma mata tace "Kin matsa bakin kofar nan ko sai na faffalleki da mari"27.🌟⭐imaan⭐🌟









Imaan dai bata tanka ta ba ta nufi stairs, Umma tace "Ragowar ciwo kawai" Sai da Imaan ta isa stairs ta turo baki ta wuce sama, sai kuma ta fashe da kuka, dai dai corridor suka hadu da Mujaheed ya fito dakinsa, ya bi ta da ido har ta shiga dakin Aunty, Karasawa stairs yyi yana lekan downstairs ganin Umma xaune ya dawo da sauri ya bude kofar dakin Aunty ya shiga ya kulle, Aunty na tsaye kanta sai tambayarta me ya faru take hankali tashe, Imaan da ta xube mata nan tsakar dakin ta dinga kuka ta ki cewa komai, Aunty tace "Kinga iskancin nan naki ne bana so, baxa ki bude baki ki min magana ba, me kika yi ma Ammin?" Still ta ki cewa komai, Mujaheed ya karasa kusa da su yana kallonta yace "Baxa ki bude baki ba ana maki magana?" Ta hade kai da gwiwa cikin rawar murya tace "Ko ba Umma bace take xagina ni ban mata komai ba har da ce min ragowar ciwo" Aunty ta ja tsaki tace "Shine xaki xo ki tada min hankali a nan? Sai me don ta ce maki ragowar ciwo? Xa kuwa ta ga ragowar ciwo a xuri'arta wataran, domin ita ta gama haihuwa ai yanxu su kuma 'ya yanta xa su fara...." Juyawa Mujaheed yyi ya nufi kofa, Aunty ta bi sa da harara har ya fita, Aunty tace "Banda shashanci shine xaki xo kina ma mutane kuka, yau ta saba gaya maki haka?" Ita dai Imaan bata ce komai ba sai share idonta take, Anty tace "Aiko ki Ammi tayi ko me?" Ta dago ta kalleta a hankali tace "Abba ne ke kirana" Aunty tace "Tashi mu je, yana parlon sa ai" mikewa imaan tayi ta bi bayan Aunty suka fita, Umma ta dinga bin su da wani kallo, Aunty ta nufi parlon Abba tana cewa "Ae ba mahalukin da ya isa raba ki da ubanki, sai dai a ganki a kyale bbu ynda aka iya da ke" Aunty ta bude mata kofar tace "Shiga" Imaan ta shiga parlon Aunty ta rufe kofar ta koma sama, Abba na xaune yana kallon news Mujaheed ma na parlon, sallama Imaan tayi ta xauna kasa ta gaida Abba dake kallonta, yace "Lafiya lau Mamana sai yanxu kika xo?" Kai kawai ta gyada masa, Abba yace "Toh yayi" bai kuma cewa komai ba, Imaan ta saci kallon Mujaheed taga kallonta yake, suna hada ido ya hade rai, turo baki tayi tana fidgeting fingers dinta, Bayan few minutes Abba yace "Imaan ai kin san wannan yaron Sadeeq koh?" Shiru tayi bata ce komai ba ta kuma kasa kallon Abba, Abba yace "Ina saurarenki" ta gyada masa kai tace "Uhm" Abba yace "Kar fa ki boye min komai I am ur father, ki gaya min meye tsakaninku" dauke kai tayi ta ki cewa komai, Abba yyi murmushi yace "Baxa ki gaya min ba kenan" Nan ma dai ta ki cewa komai, Abba yace "Toh tunda ni kunyata kike ji sai ki gaya ma Mujaheed meye tsakanin ku" Xaro ido tayi tana kallon Abba, Abba ya mike yace "Xan dawo yanxu, let me make a call outside, sai ki gaya masa kafin in dawo shi kuma ya gaya min" daga haka Abba ya fita ya kulle kofar, tun da Abba ya fito Umma ke binsa da kallo har ya fita main parlor, ta kalli kofar parlon sa.... Imaan dai ta kasa xaune waje daya bayan fitar Abba, jin shiru ta d'an saci kallon Mujaheed, ganin irin kallon da yake mata xata mike yace "Koma ki xauna" ta marairaice tana dubansa tace "Ni fa ruwa xan je in sha in dawo" ya dawo kusa da ita ya xauna yana kallonta da kyau cikin husky voice dinsa yace "Me nace ki ce ma Abba?" Ta 6ata fuska kamar xata yi kuka a hankali tace "Yaya ba ka riga ka gaya min jiya ba, ai xan gaya masa...." Sai kuma tayi shiru, ya hade girar sama da ta kasa yace "I will slap you idan baki gaya min abinda xaki gaya masa ba" Tace "To ba cewa kayi ince ban san sa ba...." ya dinga kallonta fuskarsa daure, a hankali ta mike da nufin fita parlon ya fixgota ta fado jikinsa, xaro ido tayi tace "Yayaa" bude kofar parlorn aka yi yyi saurin janyeta jikinsa, Kallonsu Aunty ta dinga yi daga inda take tsaye bakin kofa, Mujaheed duk ya daburce ya mike tsaye, Imaan ta zamo kasan kujeran kamar xata yi kuka, Aunty tace "Meye hakan" Mujaheed yace "Aunty kawai daga mata magana shine xata fado kaina" Aunty ta tabe baki har sannan tana kallonsu, juyawa tayi xata fita sai ga Abba, ta basa hanya ya shigo parlon, Anty ta fita waje, Abba na kallon Mujaheed bayan ya xauna yace "what did she say about him?" Mujaheed ya xauna saman kujera yana shafa kansa

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login