Showing 132001 words to 135000 words out of 139381 words
yi irin wannan sammako Inna" Inna ta kallesa da sauri tace "Ni dai Ahmadu ne yace in taho da sassafe, bayan jiya ya shigo da daddare mun yi magana" Imaan ta xaro ido tana kallon Inna, Murmushi Mujaheed yyi yana gyada kai, Jin taku a stairs ya juya, Safeenah ce ke sakkowa sanye da doguwar riga damamme, Still tayi tana kallonsu, Inna ta kankance ido tana kallonta da kyau ita ma, Safeenah ta hade rai ta karasa sakkowa ta shigo cikin parlon, Mujaheed ya kalleta yace "Meet my grandma and my lil sis Imaan...." Inna na washe baki tace "Sannu Amarya, da fatan dai an tashi lafiya" dauke kai Safeenah tayi ta tabe baki murya can ciki tace "Ina kwana" Inna tace "Lafiya lau, sai dai ko sunanki ban sani ba" Mujaheed yace "Safeenah" Inna tace "Toh madalla, to safeenah Mujaheed dai gashi nan a gabana aka haifesa, kuma ni nayi wahala da shi tun yana tsummarsa, ke wahalar da nayi da shi wllh kare baxai ci ba, Tabb banda nakudarsa me Rukayya tayi???" Hade rai Mujaheed yyi yana kallonta, Safeenah tace "Toh maa sha Allah, ina d'an yi abu ne a sama Hajiya...." Xaro ido Inna tayi kafin tace komai Mujaheed yace "Mind you, Inna is what we call her..." Safeenah ta d'an tabe baki tace "Toh xan je in yi abinda ke gabana a sama Inna" Inna tace "Ba xancen kije kiyi abinda ke gaban ki ba Yar nan, ko karyawa fa ba mu yi ba, Imaan ma ina jin ko wanka bata yi ba don da naje ma bacci na tarar tana yi...." Imaan na kallon Inna tace "Ni bance maki ban yi wanka ba inna" wani matsiyacin kallon Safeenah ta jefa mata sannan ta kalli inna bluntly tace "Ba a kai ga sauke min gara na daga container da ya kawo ba, ba komai yanxu haka s gidan" Wani kallo Mujaheed ya dinga mata trying hard to control his temper, inna ta rike ha6a tana kallonsa tace "toh me ku ke ci a gidan ba a sauke gara ba ni 'ya su?" Safeenah tayi wucewarta sama, Mikewa Mujaheed yyi ya bi bayanta, yana shiga dakin ya kulle kofar yana nunata da yatsa cikin tsawa yace "Let me give you this warning Safeenah, idan baki son na fito maki da the other side of me you've got to respect that woman to the fullest, she is my grandma kuma albarkacin ta yasa kike gidana, wllh wllh xan yi taking action din da xai baki mugun mamaki idan baki maida hankalin ki ba, sannan breakfast ni nace ki tashi ki fita kije ki girka masu yanxun nan...." A tsawace ya kare maganan yana kallonta, Gaba daya ta gama tsorata sai kallonsa take tana komawa baya, lkci daya hawaye ya kawo idonta sai kuma ta fashe da kuka tace "Is this the real you dama Mujaheed?? me yasa tun farko baka yi encourage dina wajen ganin nayi kokarin hakura da kai ba, you are always telling me xaka koyi sona I shouldn't worry, dama ka aureni ne to make life a living hell for me, kasan irin mutanen da na ki amincewa da nace sai kai?? Kasan mutanen da na watsa ma kasa a ido nace sai kai, dama laifine son mutum da xuciya daya?? Tun da aka kawo ni gidan nan ka ki ko da xama na minti ashirin a dakina balle ka kwana, wllh ina sonka Mujaheed, ban aure ka saboda komai ba sai saboda Ina son kasancewa da kai, ka dai san irin gidan da na fito balle kace saboda wani abu naka na aure ka" dauke kai Mujaheed yyi xuciyarsa na bugawa, right from time a rayuwar sa na duniya ya tsani ganin hawayen mace, a hankali ya karasa inda take ya xauna gefen gadon ya jawota jikinsa cikin sanyin murya yace "I won't make my home a living hell for you Safeenah, and sure I will create a soft spot for you soon, but you've got to respect my family, duk abinda nace bana so kuma plss try to avoid that, Kinga ke yan uwanki baxa su xo in masu gaisuwar walakancin da kika ma grandma dita ba...." lamo tayi jikinsa tace "Amma kana ganin wannan yarinyar fa bata gaisheni ba ma" Shiru ya d'an yi, Sai kuma yace "Mind you sunanta Imaan, and kar ki damu xan mata magana" tace "Step sis dinka ce?" Ya girgixa kai a hankali yace "She is my cousin sis" daga kai tayi tana kallonsa, ya gyada mata kai, tabe baki tayi bata ce komai ba, yace "Toh for my sake kiyi hakuri ki hada breakfast din even if it's just Irish and egg, sai ki dafa ruwan shayi" Shiru tayi masa yace "Xa ki yi?" A hankali tace "Toh" murmushi yyi ya manna mata kiss a goshinta, ta lumshe ido don ba kadan ba taji dadin hakan, ya mike yace "Come out soon" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo, Allah yasan so ba na wasa ba take ma Mujaheed, Bata taba yi ma d'a namiji irin son da take masa ba, kuma xata iya yin komai a kansa. Mujaheed na dawowa parlor ya tadda Imaan kadai tana kallo, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai, ya isa kusa da ita yace "Me yasa baki gaida Safeenah ba?" Ta turo baki ta ki cewa komai, ya dafa kujeran da take xaune yana kallonta da kyau yace "Look, duk kika xo gidan nan ko kika ganta a wani waje dolenki ki gaidata coz she is my wife... Kin ji abinda nace??" Ta hade rai tace "Toh ai ita ma ba da respect ta gaida Inna ba da ta sakko, so why will I greet her, why??? beside she is suppose to tell me... Sannu da xuwa kafin in gaisheta, amma ko kallona bata yi ba so nima naki gaisheta din ai ba wajenta muka xo ba...." Kallonta kawai yake ganin yanda take maganar cike da tsiwa tana xare masa ido, ya dauke kai ya d'an yi murmushi, can dai ya mike ya nufi kitchen jin muryar Inna kasa kasa ita kadai tana magana, tsaye yyi bakin kofa yana kallonta tana duke tana fere dankali tana cewa "Idan ba jaraba ba da safen ma ya wani bi figaggiyar mata kamar xabiya daki bayan kwana da yayi a dakin daren jiya, to meye xasu shige daki kuma da safe bayan nace masu ban karya ba ga 'yar mutane na taho da ita, ita ma bata karya ba, dama da ya iyayenta suka yarda ta biyoni, ni dai ba ruwana..." Dariya sosai ta basa, tana ganinsa tayi shiru tace "A'a har ka fito Mujaheed" yace "Dankali kike ferewa da kanki kuma?" Inna tace "Yo baxan fere ba tunda na kwaso yunwar cikina Mujaheed, ga Imaan ma bata karya ba da kyar Bukar ya yarda ta biyo ni... Abu dai da raina da lafiya ta, ita wancan matar dake xaune parlor tace ba ruwanta baxata shiga kitchen din mutane ba, ni ban gane ma wannan abun ba gaskiya" ya shafa kansa yace "Yanxu Safeenah xata xo ta hada maku kayan karin" inna ta ajiye wukar tace "Toh amma anya ka ce mata nice na raine ka kuwa...." Safeenah na sakkowa parlor ta dinga yi ma Imaan wani kallo sak na tsana tana tafiya, suna hada ido Imaan ta tabe baki ta dauke kai.... Tsayawa Safeenah tayi tana kallonta xuciyarta na tafarfasa tace "Beware a gidana kike.... you had better respect ur self ki maida hankalin ki" Kallonta Imaan tayi da sauri tace "Gidan ki ko gidan yayana? Gidan ku na can kin baro sa malama don haka baki isa ki min warning a gidan Yaya ba...." Da sauri Inna ta karasa fitowa kitchen jin muryar imaan, Mujaheed ma ya fito ya tsaya kallonsu da mamaki, Inna tace "Lafiya?? me ya faru??" Imaan tace "Wai inna ki ji ce min take in shiga hankalina wai nan gidanta ne, wllh ba abinda na mata daga sakkowarta ta fara min fada tana min warning" sake baki Inna tayi tana kallon Safeenah tace "Ba lafiya, ta shiga hankalinta kuma? Kinsan wacece ita kuwa yar nan, to bari kiji wllh wannan da kike gani ta fiye ma Mujaheed ke so dubu dari, kaji min mata kamar zabiya dai, ita da gidan yayanta kice ta shiga hankalinta sabida baki da tsoron Allah?? To wllh a kan Imaan sai Mujaheed ya kora ki gidanku yanxun nan, gwara ma ki xageni da ki ta6a min imaan gaskiya, duk da dai kin ma xageni tun daxu kawai dai ni me hakuri ce na ja bakina nayi shiru, kaji min mokadaddiyar mata dai xata sa min jika a baki in shiga uku???" Mikewa Imaan tayi kamar xata yi kuka ta nufi kofa tace "Ni sai kin dawo Inna baxan xauna ba...." Inna ta saki salati tana tafe hannu tace "Na shiga uku ni patuu, Mujaheed ya auri jaraba tunda ta ta6a imaan, ke me ya kai ki kinsan wacece kuwa, ita kenan fa uban ya haifa a duniya, ko kallon banxa ba a mata balle a mata fada... Shi Mujaheed din bai xaunar da ke ya sanar maki bane??" Bin bayan Imaan Mujaheed yyi ganin har ta fice parlon.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
[7/19, 5:15 PM] +234 803 603 7561: Har Imaan ta sauka Balcony ta nufi gate Mujaheed ya rikota da sauri yace "Kee ina xa ki??" Ta hade rai kamar xata yi kuka tace "Ni dai gida xan wuce bayan ta gama xagina, Ni wucewa xan yi" Kallon Eyeballs dinta kawai yake, xata kwace hannunta ya kalli gate, lkci daya ya jawo ta kusa da shi murya can kasa yace "Toh kiyi hakuri...." ta turo baki ta ki cewa komai, ya dauke kai yayi murmushi yace "Toh baxa ki hakura ba..." Bata fuska tayi tace "Xagina fa tayi..." ya xaro manyan idonsa still smiling ya ja dogon hancinta yace "Ni ban ji inda ta xage ki ba, har da sharri...." Kwace kanta take son yi xata wuce ya ki saketa yace "Ai fa nace kiyi hakuri koh?" Kallonsa tayi fuska daure kamar xata yi kuka tace "Toh baka gaya mata ni wacece bane?" Dariya sosai ta basa, and he couldn't help it don har sai da yyi dariyan ganin maganan sak yanda inna ke yi, ya kamo duk hannunta biyu yace "Haba na gaya mata mana lil sis, amma kiyi hakuri xan sake gaya mata da kyau, yanxu mu koma ciki sai ki hada maku breakfast din mu rabu da ita...." imaan ta turo baki bata dai ce komai ba, yana murmushi yace "Idan mun koma sai kice ma Inna kin hakura don ta daina fada kin ji pls?" A hankali tace "Na ji" Yana kallonta sosai yace "Good girl" daga haka suka koma parlon yana rike da hannunta, Inna kadai ce tsaye parlon tana kallon stairs tana cewa "Ka ji min jarabbiyar mata ta ja Bukar ya kullace ni tunda ni na fito masa da 'ya har xa a sa ta a baki... to wllh hir dinki ni ba ruwana, to Wai ma ke baki da tsoron Allah ne?? duk hakurina yau sai da kika kai ni bango, banda haka kin fito daxu kin gaida ni a tsaye sandandan kamar katon soja, ni dai ban kula ki ba don babba da hakuri da kauda kai aka san sa, sannan na maki magana bamu karya ba kince kwantenar karyar da aka maki na gara bai sauka ba, ko ina aka taba gara a kwantena??? Ni dai duk ban kula ki ba ina ta hakuri shine yanxu xaki ta6a imaan baki san ba a ta6a min ita ba, to haka xa mu yi dake tun ban dawo gidan gaba daya ba?? Yau naga abinda ya isheni... Irin xaman da xa mu yi kenan ni patuuu da wannan figaggiyar yarinyar" Mujaheed ya karasa gun Inna yace "Haba Inna daga xuwa kuma, Imaan din fa ta ma ce ta hakura..." Inna ta kalli Imaan da sauri tace "Wai??" Imaan ta gyada kai a hankali, Inna ta koma ta xauna tana share xufar goshinta tace "Toh Alhmdllh... Sai ta sakko ta hada mana karin kumallo, gaskiya Mujaheed Ina ga baka yi dacen mata ba, tun fa ba aje ko Ina ba ta fara nuna hali, ko da yake ai ni me iya saita mata xama ne, ba haka na saita Rukayya ba ma Allah na tuba" Mujaheed ya kalli Imaan ya mata alamar da ta tafi kitchen din, ta rungume hannunta tace "Toh ni kadai?" Kallonta Inna tayi da sauri tace "Ke kadai me?" Mujaheed ya nufeta yace "Toh mu je" Ba musu ta nufi kitchen din ya bi bayanta, dukawa tayi gun dankalin da Inna ta fara ferewa, ya dau wukar ya mika mata yace "Be careful with the knife...." Bata ce komai ba ta amsa ta fara fere dankalin, ya duka kusa da ita yana kallonta, duk wanda ta gama ferewa sai ta sa a ruwan da ke kusa da shi, shi dai kallonta kawai yake, pieces shidda ta gama ferewa tace "Ai dai wannan ya ishemu ni da Inna..." Ya wara ido yace "Toh ni fa...." Kallonsa tayi da sauri tace "Har da kai?" A hankali ya gyada mata kai, ta tabe baki ta ci gaba da ferewa, wani kara tayi ta jefar da wukar sai ga jini a hannunta, ya daga ta da sauri yace "Subhanallah..." yarfe hannun ta fara yi a rikice tace "Wayyoo Yaya zafi...." Pampo dake kitchen din ya nufa da ita ya kunna yana tsaye bayanta ya shiga wanke mata hannun yana kallon cut din that isn't deep, a hankali yace "Sorry lil sis...." Yana gama wanke mata ya juyo da ita, hawaye ya gani idonta, lkci daya ya rikice yace "Yana maki xafi sosai ne??" ta fashe da kuka a hankali tace "Ba kai bane kace in kara bayan na gama namu da Inna" rungume ta yayi yace "Toh yi hakuri plss, we should have use the potatoe peeler instead" ya daga kanta yana share mata hawayenta da fingers dinsa, turo baki tayi tace "Ni dai sai dai kayi slicing din dankalin baxan yi ba" murmushi yayi yana ci gaba da goge mata idonta a hankali yace "Toh naji, sai ki kunna gas ki debi mangyada a pan" daga haka ya saketa ya koma gun dankalin, fry pan da ta gani ta dauko ta bude jarkan sabon man gyada ta deba a fry pan din sannan ta kunna gas ta daura, ta daura ruwan shayi ta sa lipton, ba dai kayan kamshi tunda bata san inda suke ba, tsaye tayi bayansa tana kallonsa har ya gama slicing dankalin ya mike ya ajiye bowl din a sink, ya juya yana kallonta yace "Toh ya xa ayi?" Yar dariya tayi tace "Baka sani ba Yaya" ya buda hannu alamar bai sani ba din, ta karasa inda yake ta wanke dankalin ta tsane duk yana kallonta, yace "Ke da ba ki girki a gida ma...." Murmushi tayi tace "Ehh amma ai ina ganin Ammi na yi, kuma dai na iya...." Shi dai bai ce mata komai ba, suna tsaye kitchen din har dankalin da ta xuba a mai ya soyu ta kwashe a plate, tana kallonsa tace "Toh ina eggs din?" Ya xaro ido yyi yace "Are you sure, kar kije ki tada min Asthma..." Ta turo baki tace "It's just an ordinary egg, sai in sa onion fa, ba yaji ai" Yana murmushi a hankali yace "Ohk...." Eggs din ya fiddo cikin few minutes ta fara soyawa bayan ta yi chopping onion a board, duk yana lura da ita to make sure she is fine din da gaske, can ya karasa kusa da ita ya tsaya bayanta a hankali yace "You are uncomfortable Imaan" ita dai bata ce komai ba don da gaske tsarkewa numfashinta yake yi ko don bata yi lowering gas din bane amma a gida ai tana soya kwai, ya rage gas din sosai ya juyo da ita tana facing dinsa giving her support with his broad shoulder, a hankali take sauke numfashin hade da shakar kamshin sa mai dadi, ya dinga juya kwan a frying pan har ya ga ya soyu sannan ya kashe gas din, gaba daya ya juye a plate din da ta dauko, ya kashe gas da ta daura ruwan xafi ganin yana tafasa, daga kanta yyi yana kallonta a hankali yace "Are you okay?" Kai ta gyada masa, yace "Ki tafi parlor xan kawo breakfast din yanxu" Bata ce komai ba ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, wani plate din ya dauka ya debar ma Safeenah dankali da kwan ya rufe, sannan ya juye ruwan xafin a flask ya dauka da cups biyu da spoon ya tafi parlon, Inna na xaune sai shar6an bacci take har da minshari, ya d'an yi murmushi yana kallon Imaan dake xaune kasan rug ya ajiye flask din hannunsa yace "Are you sure you are okay?" Ta gyada masa kai, kitchen ya koma ya dauko plate din dankalin ya ajiye masu ya koma kitchen din, Tea mai kauri ya hada a cup sannan ya fita da kayan shayin ya ajiye, plate din dankalin da ya bari a kitchen din da cup din shayi ya tafi ya dauka ya fito, sama ya nufa imaan ta bi sa da kallo, can ta tabe baki ta dauke kai, Safeenah na dakinta tana waya da Mahaifiyarta ta sanar mata duk abinda ake ciki tun shigowar Inna gidan da sassafe, rai bace Hajiyan Marafa tace "Ban da ma kin nace sai shi Allah na tuba me xa ki yi da d'an wajen Rukayya, Ni fa da Rukayya kar ta san kar ne shi sa ban so auren ba, ke kuma kika ce ba ki san xance ba kin samu miji, amma duk wannan mai sauki ne wllh tllh, ni nasan ta yanda xan billo ma lamarin, ki kwantar da hankalin ki sai kace ba ni na haife ki ba dai, ai in