Showing 93001 words to 96000 words out of 139381 words

Chapter 32 - IMAAN

Start ads

20 Aug 2025

686

Middle Ads

dai yau xan ga batar nono a kirjin budurwa ni Asabe" Umma dai ta kasa tsaye waje daya, Kai kana ganinta xaka ga tashin hankalin da ya ki boyuwa karara a fuskarta, Dakin Inna ta shiga ta gama xagaye xagayenta sannan ta fito tace "Kuma Inna babu kowa parlon San da aka baki wayar?" Inna ta d'an yi shiru sannan da sauri tace "D'an ki ne Mujaheed kadai a parlon a lkcn, Toh ga dankareren dankunnen zinari ma da ya bata ta bani ajiya bai bata ba, duk da ranan ba kowa a parlon ta bani, waya dai Mujaheed na wajen lkcn" Inna ta xaro ido ta dafe kirji tace "To ko dai sata Mujaheed ya fara a gidan nan ba a sani ba??" Umma dai sai hada xufa take tana kallon inna, Inna ta kalli Abba tace "Anya Ahmadu baxa a caji Mujaheed ba, wllh shine a parlon ranan, Ni dai na shiga uku na lalace" Abba dai bai ce mata komai ba, Umma ta dake tace "Inna bari in kashe gas na daura ruwan shayi, xan dawo yanxun nan, ae wannan babban magana ce" Inna tace "Yi maxa kar ki ja wata fitinar ba a gama kashe wata ba" da sauri Umma ta fita, tana komawa bangarensu bata ko kalli Mujaheed ba ta wuce sama jikinta na rawa. Washegari har Ammi ta gama soye soye a kitchen shiru imaan bata fito ba, dakinta Ammi ta shiga don ya ci ta fito ynxu ta gama shirin islamiyya, kwance Ammi ta ganta cikin duvet, ta cire duvet din tana kallonta ta kai hannu jikinta, janye hannun tayi tana kallonta tace "Imaan?" A hankali imaan ta bude idonta da ya rine tana kallon Ammi, Ammi ta xauna gefen gadon da damuwa tace "What's wrong imaan?" Da kyar ta nuna ma Ammi kanta murya can kasa tace "It's aching me" ta nuna ma Ammi kafafuwanta ma, Ammi ta dinga kallonta cike da tausayi tace "Kin daina shan maganin ki ko daughter!" Imaan ta girgixa mata kai kawai ta kasa cewa komai, mikewa Ammi tayi ta wuce bathroom dinta ta hada mata ruwan wanka ta fito ta daga ta, ita ta taimaka mata har xuwa bathroom din sannan ta fito, ta ciro mata kayan da xata saka sannan ta fita, Imaan na fitowa wanka ta kwanta kan gado daure da towel ta rufe jikinta da duvet, Ammi ta dawo dakin rike da cup din shayi da ledan bread ta ajiye kasa tana kallonta tace "Toh tashi ki shirya sai kiyi breakfast ki sha magani" Ganin she is shivering Ammi ta dauko cream dinta ta taimaka mata ta shafa sannan Imaan ta saka kayan da Ammi ta fiddo mata, shayi kawai ta sha da drugs dinta sannan ta kwanta Ammi ta fita da cup din. Aunty ce xaune parlon Abba bayan ta kawo masa breakfast, ganin mood dinsa tace "Don Allah ka daina damuwa da abubuwan inna, kun fa fi kowa sanin halinta, Bai kamata kuna sa abun a rai ba, kuma uwa ce fa" Abba ya girgixa kai yace "Ni kadai baxan iya dinga nuna ma Inna abinda ya dace da wanda bai dace ba, ya kamata ku ma ku dinga contributing...." Aunty ta sake baki tace "Mu a suwa Alhaji, ku ma ya ku ka kare balle mu, ai sai ta kora mu gidajen iyayenmu..." Abba yace "Wannan ba point bane, idan a nuna mata ta gyara ai da matsala babba, Dama ta fi sauraran Sadeeq to shi baya nan, ni kuma inyi magana ta fara min kuka, wllh duk abubuwa sun taru sun min yawa a kai" Aunty tace "Ai tana jin maganan Mujaheed ma" Abba ya kalleta yace "Toh cewa tayi a tafi Police station Mujaheed ne ya dauke waya, har da kukanta fa, Yanxu fisabilillahi maganan nan ya maki dadi?" Aunty ta kasa danne dariyarta tace "Tsufan kenan ai Alhaji, a dinga yi mata uxuri don Allah, Toh shi me Mujaheed din yace?" Abba ya girgixa kai yace "Ni ban ma gansa ba tun jiyan, sai daxu da muka hadu masallaci, gaskiya Inna na daga min hankali da yawa ban san yanda xan yi ba" Aunty tace "Toh Allah dai ya kyauta" Yusuf ne yyi sallama bakin kofa Aunty ta amsa ya shigo parlon ya mika mata wayarta yace "You missed a call" Abba na kallonsa yace "M.A fa?" Yusuf yace "Yana bedroom dinsa" Abba yace "Kira min shi ku taho tare" Yusuf ya amsa da to sannan ya nufi kofa, hanya ya ba Umma ta shigo parlon sannan ya fita, Daga Aunty har Abba suka dinga kallonta, duk gaba daya a sanyaye take tace "Alhaji xan je gidan Mariya wai suma ta dinga yi jiya basu yi bacci ba, yanxu haka suna asibiti tun asuba wai" Aunty tace "Subhanallahi, Toh Allah ya bata lafiya ya yaye ma duk musulmi ciwo, in sha Allah xan shigo anjima nima" da sauri Umma tace "A'a Hajiyar mu tace mu taho da ita zaria kawai, yanxu Ina xuwa Zaria xa mu wuce da ita" Abba yace "Toh Allah ya bata lafiya, ya sa kaffara ne" tana goge hawayen da ya cika idonta tace "Ameen" Abba yace "Da driver xa ku tafi kenan?" Umma tace "A'a adaidaita xan hau xuwa asibitin daga can sai mu tafi a motar mijinta" Abba yace "Toh Allah ya kiyaye hanya, do you need anything?" Tace "Ehh a min transfer din abinda ya sauwaka" Abba yace "Alright" sallama tayi masu ta fita parlon Aunty na mata Allah kiyaye hanya, bayan ta rufe kofa Aunty ta duba call din da tayi miss taga Ammi ce ta kirata, dialing number din tayi yana fara ring Ammi ta daga suka gaisa, Ammi tace "Dama tambaya xanyi ko driver na nan Hajiya..." Aunty tace "Ehh toh bai dawo daga kai su Maimoon islamiyya ba..." Ammi tace "Toh dama Imaan ce bata ji dadi ba xa mu je asibiti" Aunty tace "Subhanallahi tun yaushe?" Ammi tace "Yau dai da ciwon nata ta tashi" Aunty tace "Toh bari in ma Yusuf magana ko shi sai ya kai ku asibitin" daga haka ta katse wayar, Abba yace "Mamana ce ba lafiya?" Aunty tace "Wllh kuwa, Wai ciwonta ne ya tashi" Abba ya d'an yi shiru sannan yace "Bari Mujaheed ya shigo mu ji ko xa a kaita asibiti ne ko a bata medication a gida" dai dai nan Mujaheed ya shigo tare da Yusuf, Abba ya mike yace "Mu je ka duba Mamana wai bata ji dadi ba" Mujaheed ya d'an yi jim, sannan ya bi bayan Abba suka fita parlon, Aunty na kallon Yusuf tace "Kai baxa ka je dubata ba" Yace "Xan je anjima mum" Har bedroom din Imaan Abba da Mujaheed suka shiga Ammi dai ta tsaya daga bakin kofar, bacci take suka sameta, Mujaheed ya duka kusa da ita a hankali yana kallonta ya kai hannu forehead dinta, bude ido tayi ganinsa ta ja duvet ta rufe kafarta da sauri. Abba ya karasa kusa da gadon yace "Sannu mamana, ya jikin?" Da kyar tace "Da sauki Abba" Mujaheed na kallonta yace "Where are you feeling pains?" Ba tare da ta kallesa ba ta nuna masa kafafuwanta da baya, yace "Kin sha magani ne?" Kai ta gyada masa, Yace "Ina drugs din" ledan maganin dake ajiye ta nuna masa ya dauka ya duba su sannan ya ajiye yana kallon Abba yace "Let me get some injections da drugs" Abba yace "Ohk" daga haka ya nufi kofa Ammi ta basa hanya ya fita. Abba na kallon imaan yace "Allah ya sauwake imaan" ta d'an yi murmushi a hankali tace "Ameen" Abba ya juya ya nufi kofa yana kallon Ammi yace "Allah ya bata lafiya" Ammi tace "Ameen thumma Ameen" yace "Amma kada a gaya ma Inna" Ammi tace "In sha Allah" kofa ya nufa yace "Xan fita office, I will call later" Ammi tace "Allah ya kai mu, Allah kuma ya tsare" yace "Ameen" sannan ya fita parlon. Ammi ta karasa cikin dakin tana kallon imaan tace "In kara hada maki shayin ne?" Da sauri ta girgixa kai, Ammi ta dinga kallonta sannan ta juya xata fita, murya can kasa tace "Ammi don Allah ki shafa min maganin a kafa kafin Yaya ya dawo ni bana son ya shafa min"


*Imaan isn't free....* it's 300 Via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence of payment via 07087865788 to be included in the payment group....Mujaheed na dawowa ya tadda Ammi xaune parlor, Ammi ta amsa sallamansa yace "Ta ci abinci ai" Ammi tace "Ta sha shayi daxu" yace "Tana ciki har ynxu?" mikewa Ammi tayi tace "Ehh tana ciki" bedroom din Imaan ta nufa, ya bi ta da kallo sannan ya bi bayanta, Ammi ta cire duvet din jikinta xuwa kafanta tace "Imaan" tashi xaune imaan tayi ganin Mujaheed ta daure fuska ta ja duvet din xuwa waist dinta, a hankali tace "Ammi na ma fara jin sauki" Ammi ta kallesa tace "Magunguna ka siyo mata?" Mujaheed ya girgixa kai yace "A'a injections ne, sai na shafa..." Ammi tace "Ta sha drugs a bar injections din anjima" kallonta yake sannan yace "Amma na yanxu ne alluran..." Imaan tace "Toh na ji sauki ai yaya" Bai kuma cewa komai ba sai kallonta da yyi ta gefen ido babu yabo bbu fallasa, Ammi tace "Ina lotion din tube din?" Mika mata ledan yayi ta amsa ta cire man xafi dake ciki, Mujaheed ya kara kallon Imaan da ta ki kallonsa, Juyawa yayi ya nufi kofa kamar baxai ce komai ba bayan ya bude kofar yace "Sai anjima" ba tare da Ammi ta juya ba tace "Allah ya kai mu" da kanta ta shiga shafa mata man xafin a kafafuwanta da bayanta, Tana yarfe hannu tace "Toh Ammi alluran fa, ni dai bana son Yaya ya min, Kuma har yanxu Ina jin joint pain din" Ammi tace "Anjima Dr Habib xai xo..." Ammi na gama shafa mata ta fita dakin imaan ta koma ta kwanta ta lumshe ido. Da yamma Imaan na xaune parlor pepper soup din naman ragon da Aunty ta kawo mata na gabanta ta kasa ci don gaba daya bata da appetite, har wani rama tayi kamar warce tayi sati ba lafiya, xuwa lkcn dai ta ji sauki sai rashin kwarin jiki don Dr Habib ya xo ya mata injections din da Mujaheed ya siyo daxu, Ammi ce ta fito parlon ta iso kusa da ita tace "Idan baxa ki ci ba ki kai kitchen ki rufe Imaan, ai ba dole bane" Imaan bata ce komai ba ta amshi wayar da Ammi ke mika mata, Sadeeq ne ke kira a wayar, ta kalli Ammi da ta juya xata koma daki sannan ta daga wayar ta kai kunne hade da masa sallama murya can kasa, daga daya bangaren ya amsa yace "Are you okay?" Ta gyada masa kai tace "Sure Ina yini?" Yace "No, you sound sick ki gaya min baki da lafiya ne?" Cikin sanyin murya tace "Ae na ji sauki" Yace "Subhanallah, me ya sameki?" Ta girgixa kai tace "Kawai xaxxabi amma naji sauki sosai" ya d'an yi shiru sannan yace "Toh Allah ya kara lafiya, anjima xan xo in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen, I will call you idan na iso" tace "Toh" katse wayar tayi ta ajiye tana shan pepper soup din naman a hankali, Bude kofar parlorn aka yi Inna ta shigo ta tsaya tana kallonta tace "Ikon Allah, yanxu don kaddara ta fada ma wayar ki sai ki kwanta ciwo imaan?? anya kuwa xa ki yi tawakalli irin nawa? Kinsan irin asaran da nayi a rayuwar nan kuwa tun tasowata har ixuwa yanxu? To 6arin ciki hudu nayi a gidan mijina, na haifi 'yan biyu suka mutu rana daya, dakina ya ta6a konewa kurmus bbu abinda aka fitar da sai mafici, kishiyata ta ta6a turo min yan fashi suka kwace min jakata a titi Allah ya so bbu komai ciki sai naira daya, 'ya yana uku kacal a duniya, da ubanki, sai na Mujaheed sai kanwarsu Hadiza dake kasashen turai, to ban gode ma Allah ba? Me ya sameni, ke don kawai an dauke wayar da bai fi dubu hamsin ba idan ma ya kai sai ki sa ma kanki damuwa kiyi ta ciwo kamar wayar jaraba, in dai waya ce ni baxan bari ki sani a bakin duniya ba xan ba Ahmadu dubu goma ya cika ya siyo maki wata ba ruwana" Imaan dai bata ko kalleta ba balle ta tanka ta, Ammi ta fito ta gaida Inna, Inna ta amsa tace "Aisha yanxu baki nuna ma yarinyar nan karatun tawakali??" Ammi tace "Ciwonta ne fa ya tashi Inna" Inna tayi shiru tana kallonta, can tace "Dama imaan na da wani ciwo ne da ban sani ba?" Ammi tace "Ciwon nata kuma Inna kika manta?" Inna ta rike ha6a baki Bude tana kallon Ammi, can tace "Ni dai ba ruwana, ku je kuna fadan haka wani ya ji, dama banda rashin lafiya da kowa ke yi Imaan na da wani ciwo na daban ne ban sani ba?" Ammi tace "Toh ko jiya ma Abbanta yace wannan yaron da ke nemanta ya kamata a sanar masa laluranta tun yanxu" Gwalo ido Inna tayi ta saki salati tana tafe hannu ta xauna ta rike kai tace "Naga abinda ya isheni ni patuuu, wayyoo Allah duniya ta lalace" dagowa tayi tana kallon Ammi tace "Aisha da hankalin ku ke da Bukar kuwa? Dama Imaan na da wani ciwo ne ni da ban sani ba, ku dai ku dinga fadin gaskiya ku ji tsoron Allah, yaushe rabon da in ji Imaan bata da lafiya a gidan nan, Ni dai kada wanda ya laka ma jikata ciwo lafiyarta lau, waye baya xaxxabin maleria da thypho, to kada ma ku kuskura wani yaji wannan mugun xancen, ku dai ba kwa fadan alkhairi a gidan nan, Ni dai ba ruwana, yaushe rabon da tayi ciwo?? Ai yafi shekara biyar ba ma banda sharri irin naku...." Mikewa Inna tayi ta nufi kofa rai bace tana cewa "Mutane dai ba tsoron Allah, meye kuma wai a gaya ma yaron da ke nemanta laluranta kamar mai cutar AIDS... Ni dai ba ruwana" a bude tabar masu kofar bayan ta fita ta kara gaba, Ammi na kallon Imaan tace "You make sure you tell him everything about ur health condition, kar ki boye masa komai" Imaan ta sauke idonta kasa a hankali tace "Toh Ammi" Ammi ta xauna kan kujera a ranta tana jinjina halin inna, imaan ta kalleta tace "Ya ce xai xo anjima" Ammi tace "Toh sai ki gaya masa" biyar da few minutes Sadeeq ya kira Imaan ta wayar Ammi ya sanar mata yana waje, bayan ta gaya ma Ammi, Ammi tace "Toh kar ki dade dai a waje" "Toh" kawai imaan tace ta sa hijab dinta ta fita, tana isowa gun motar ya bude mata back seat yana kallonta yace "Shiga ki xauna" girgixa kai tayi tace "A'a..." Yace "No pls ki shiga kinga you are sick, you look so weak, bana son musu get in plss" shiru tayi bata ce komai ba, komawa gefe yyi ta shiga motar a hankali, yana kallonta yace "Kun je clinic kuwa?" Tace "A'a Dr dina ya xo ya min allura" ido ya kafeta da shi, hakan yasa ta sunkuyar da kanta yace "What's wrong with you?" Ba tare da ta dago ba tace "I woke up with headache, backache and joint pain... pains everywhere...." Ya d'an bude ido da mamaki ya cire glasses din idonsa yace "Yana maki haka ne dama?" Ta kallesa ta gyada masa kai gently, kasa daina kallonta yayi, murya can kasa yace "Are you... A sickler?" Girgixa masa kai tayi tana murmushin karfin hali tace "I am a carrier, I am carrying the trait" jin yyi shiru ta daga kai ta kallesa, tausayi taga karara a kwayar idanuwansa yana kallonta, underneath his breath yace "Ya Salam, a very rare case, Subhanallah" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, jingina yyi da motar ya rungume hannunsa yana kallon gate din shiga gidan looking so disturbed.

Umma ta share xufar da ke keto mata bayan ta gama sauraran bayanin mutumin gabanta, Hajiya Saude sai jinjina kai take, da kyar Umma na gyara xama tace "Toh malam yanxu meye abun yi.... A taimaka don Allah, wllh ji nake kamar xuciyata xata fashe, ko kuma in hadiye xuciyar, duk duniya bani da makiya da ya wuce yarinyar nan da uwarta, uwarta ta xalunce ni a rayuwa ta cuce ni, a dalilin uwarta na shiga gararin rayuwa malam ka taimakeni ko nawa ne ni xan biyaka wllh, Malam ka dubeni..." Mutumin dake xaune gabanta ya girgixa kai yace "Auren nan fa na gaya maki idan ba wani Ikon Allah ba sai an yi sa, mijinta ne d'an gidan attajirin babu tantama, sai dai kuma wani Ikon Allah, gashi nan na gani, gashi nagani har ranan bikin..." Hawaye ya kawo idon Umma tace "A dai duba malam a taimaka" Malam yace "Toh ga takarda sai ki rubuta abinda kike son ayi a ciki, amma fa banda kisa... don yarinyar na da tsawon rai haka ma Yaron sai dai kuma wani Ikon Allah, sannan kuma baxa a iya raba su ba.... yar ki kuma da kike son yaron ya fara nema kuma ba mijinta bane baxai taba yiwuwa ba, ba mijin yar ki bane yaron attajirin.... Sannan ina maki tuni surkarki a tsaye take kan yarinyar.... Tasirin aikinmu a kanta kamar ko da yaushe dai kalilan ne kema kin sani, Ki rubuta komai amma banda abubuwan da na lissafo maki a baya" Umma ta gyara xama tana share hawayen idonta ta amshi takardan da biro ta ajiye kasa ta fara rubutu.....[7/16, 7:46 AM] +234 807 505 4566: Da daddare Imaan na kwance parlon Inna dake xuba wani garin magani a kindirmon dake cikin cup din gabanta, Maimoon ta shigo da sallama ta ajiye abincin hannunta ta gaida ta, Inna ta mika mata cup din tace "Mika ma waccan matar" Imaan ta juya masu baya da sauri tana turo baki, Inna ta kalli Maimoon

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login