Showing 87001 words to 90000 words out of 139381 words

Chapter 30 - IMAAN

Start ads

20 Aug 2025

674

Middle Ads

matar da ku ka gani ku kyaleta haka kawai" Hajiya Saude tace "A'a baki dai yi abinda ya dace bane, nima fa haka uwar mijina take a da amma ba yanxu ba kuma wllh, duk da nata bai kai na tsohuwar nan ba ma, Amma wllh ynxu sai labari, gaba daya gidan sai yanda nace ake yi, ina xan iya wahala??" Umma tace "Toh mu je ciki sai inji ya xa muyi, wllh na gaji, ita ce babban matsalata a gidan nan" Hajiya Balaraba tace "Toh kayan da ta hana fitowa da su fa?" Umma tace "Kayan xa su dawo hannuna in sha Allah, Mujaheed ne kadai ya isa ya fiddo da kayan daga parlon nan ko ubansa bai isa ba, kuma shi xan sa bari dai ya dawo" Hajiya Saude tace "Toh yaushe xa a tafi kai gaisuwar ne?" Umma tace "Uban cewa yyi sai kaninsa ya dawo Abuja, ae tuni na rufe bakinsa shi ma, komai nace cewa yake tohh" Duk suka kwashe da dariya suka shiga cikin gidan. Da magrib Imaan taje kai ma Inna abinci ta dinga kallon akwatunan da Inna ta jera a parlonta gwanin ban sha'awa, Inna ta shafe addu'an da take tace "In fiddo maki sabuwar wayar taki ne yanxu" Imaan tace "Inna wannan akwatunan fa?" Inna ta tabe baki tace "Daxu wannan mata Rukayya suka shigo da su wai ashe har xa a kai ma Mujaheed lefe bani da labari, Ina nan xaune kamar fanko" Imaan ta xaro ido tace "Aure xai yi Inna?" Inna tace "Ai shine nake jira Ahmadu ya dawo mu ji idan bola aka maida ni a gidan nan ban sani ba" Imaan da har sannan ke kallon akwatunan da surprise tace "Waow wllh sun yi kyau sosai, yanxu gidansu Aunty farida xa a kai kenan" Inna tace "Toh wacece dama banda ita, duk da dai iyayenta yaku bayi ne yarinyar na da hankali kuma ban jin xata gaji da ni idan na koma gidan Mujaheed da xama, lafiya xa mu xauna da yarinyar, ke kuma duk sati sai ki dinga xuwa kafin lkcn naki da bulasawa yayi" Imaan ta fara dariya ta xauna Inna tace "Toh bude mu ga tsiyar da suka xuba mata" Imaan na murmushi ta dinga sauko da akwatunan, sannan ta bude daya daga manyan ciki, xannuwa ne tsadaddu kwance a ciki, Imaan ta dinga fiddo su tana ajiyewa Inna na dauka tana duba kasan xannuwan don ganin ko babba ne ko karami, can ta tabe baki tace "Kin san Rukayya akwai shegen karya, ko sata xata iya sa Mujaheed yyi don tayi fafa, Toh xannuwa dai gasu duk masu tsada sai a xo a fidda min nawa da na takwarata a ciki" Imaan dai bata ce komai ba sai murmushi kawai take, ta bude wani akwatun, ta shiga fiddo laces masu suna lace, Inna ta rike ha6a tace "Ehh lallai Rukayya makaryaciya ce, wnn ai sai ta talauta min jika, Toh wannan ma sai a fidda min daya inyi doguwar riga, idan kyalle ya rage in baki a maki joni" Imaan dai bata ce komai ba ta bude akwatuna mai dauke da jallabiyoyi tsadaddu, Inna tace "Ki xabi wanda ya maki a ciki...." Imaan ta xaro ido tace "Innaa?" Inna ta hade rai tace "Toh sai su fidda min in baki" Akwatin dake dauke da takalma da jaka Inna ta bude, ta fiddo wani takalmi mai kyau sosai tana kallon imaan tace "Gwada wannan mu ga" imaan ta wani xaro ido a fusace Inna tace "Don Allah ki gwada" mikewa Imaan tayi xata sa takalmin aka bude kofar parlon Mujaheed ya shigo da sallama.


Afuwan it's short, gobe da safe xan yi update in sha Allah, I was kinda busy gaba daya yau ne. Tnxx.Kallonsu Mujaheed ya dinga yi, Imaan ta sunkuyar da kanta ta ki sa takalmin xata xauna, a fusace Inna tace "Ji walakanci don Allah, ba cewa nayi ki gwada ba?" Imaan ta hade rai tace "Toh nawa ne da xan gwada?" Inna tace "Oh oh Allah, yau naga fitina, to Ina ruwana da ko na waye, ni dai ba kawai in cire ma takwarata ba tunda ni baxan iya sa wa ba?? Ki gwada don Allah" Imaan dai bata ce mata komai ba ta xauna, Inna ta ajiye takalmin gefenta tana kallon Mujaheed dake tsaye tace "Toh da kaki gaya min xaka yi aure Mujaheed sai aka yi yaya? Sai aka dinga yagan naman jikina? Toh baxa dai a taba canxa ma tuwo suna ba, bauta dai na riga na gama maka sai dai Allah ya saka min da alkhairi, Amma kar dai ka manta akwai ranan sakamako" Mujaheed bai ce mata komai ba ya xauna kan kujera ya jinginar da kansa da kujerar a hankali yace "Akwai ruwan xafi?" Inna tace "Wanda Rukayya ta hado tare da akwatuna ta kawo min ba?" Mikewa Imaan tayi tace "Sai da safe Inna" Inna ta kalleta da sauri tace "Sai da safe bamu gama kallon kayan ba?" Imaan bata ce mata komai ba ta nufi kofa, Mujaheed ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita sannan ya mike ya bi bayanta, Inna tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni ni patuu, wannan d'a na Ahmadu dai fitinanne ne, Ina lura da yarinyar nan gaba daya ta fita harkan ka a gidan nan, da ta ganka xata yi ta kanta ta bar wajen, gaba daya ta ma mayar da kai dodo, Ina kuma lura hakan na damunka ainun sbda baka samu damar dinga cutarta ba, to meye kuma xaka wani bi bayanta bayan bata kula ka ba, Ni dai gwara ma ayi auren nan ka kama gabanka jikata ta huta nima in huta da maganar ka haka, wllh ka cika fitina ko don maman Rukayya ka sha oho, tunda ita ma dai fitinanniyar ce" Juyawa Imaan tayi jin tafiya a bayanta, sosai gabanta ya fadi ganin shi ke bin ta, sai dai bata gudu ba sai kara saurin ta da tayi, ji tayi ya juyo ta har sai da ta kusa fadawa kansa ta fixge kanta gabanta na faduwa, a fusace tace "Meye haka yaya?" Kallonta ya tsaya yyi da wani expression, kamar xata yi kuka tace "Ni ka sakeni" Calmly yace "Me yasa kike gudu idan kin gan ni?" Kin cewa komai tayi, taji gaba daya she is very uncomfortable unlike before da bata ki ma ta fada jikinsa ba ta fara masa shagwaba, Yana kallonta yace "Imaan!" Kasa kallonsa tayi, ya dago kanta yana kallon manyan idanuwanta, turo baki tayi, and he couldn't stop looking at her, haka kawai yaji ya samu relieve din abubuwan da dama da ke damunsa, Yace "Answer my question now, me yasa kike gudu idan kin gani" sauke idonta tayi kasa calmly tace "Nothing..." jin shiru bai ce komai ba bayan few seconds ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, sauke idonsa yyi cikin cool voice dinsa yace "Saboda na amshi wayar ki?" Ta kallesa kafin tace komai ya ciro wayar a aljihu yana mika mata yace "Take..." bata san lkcn da tayi murmushi ba ta langwabar da kai tace "Ae daddy ya ce xai siya min wani soon" ya daure fuska yace "Take it now..." ta make kafada tace "Ni bana so kuma" yace "Take before I knock you" kamar xata yi kuka ta amsa yana kallonta yace "Shi kenan?" Tace "Ehh" wani boyayyen ajiyar xuciya ya sauke, ta d'an yi jim, sai kuma tace "Aunty Farida xa a kai ma kaya?" Kasa cewa komai yyi ya saketa ya juya ya koma part din Inna, ta bi sa da kallo kafin ta juya ta wuce part dinsu tana kallon wayarta. Mujaheed na komawa part din Inna ya tarar tana ta fiddo kayan akwatuna, ya xauna yana kallonta yace "Nima fa ban san an fara hada kayan lefen ba shi yasa ban gaya maki ba, sai daxu Umma ke nuna min" Inna tace "Ni dai ba ruwana, ku dinga jin tsoron Allah, don an gaya min ai ba gafara aka min ba...." Wani jallabiya mai kyau da tsada ta daga tana nuna masa tace "Wannan ai xai ma takwarata koh?" Kallonta ya dinga yi, jin yyi shiru ta ajiye gefe ta maida sauran ta rufe jakar, ta nuna masa takalmin da ta ba Imaan ta gwada tace "Wannan ma ai dai dai ita ne koh?" Nan ma dai bai ce komai ba ta ajiye gefenta, body spray biyu ta dauka ta ajiye gefenta tace "Sai ta dau daya ta bar min daya" murmushi Mujaheed yyi bai dai ce komai ba, Inna ta bude akwatin jewelries, ta dinga kallon dankunnaye da sarakuna masu kyau, kala biyu ta cire tana kallonsa tace "Wanne ya fi kyau cikin wa enannan?" Shi dai bai ce mata komai ba, ta ajiye biyun a gefenta tace "Sae ta xabi daya a mayar masu daya" bude pack din jan baki tayi ta cire uku tace "Duk da dai ba shafawa take ba sai ta ba Maimoon daya ta rike biyu" Kaf kayan sai da Inna ta bi ta cire daddaya ta ajiye ma Imaan sannan ta rufe jakunkunan ta jera su yanda suke, ta kwaso kayan ta xube su gaban Mujaheed tana kallonsa tace "Ko ban kyauta ba Mujaheed?" shi dai bai ce komai ba ta kwashi kayan ta kai daki ta fito tace "Toh ai faridan ma ya kamata ta xo ta gaisheni kafin a kai kayan, kwana biyu shiru bata xo ba" a hankali Mujaheed yace "Ba Farida xa a kai ma kayan ba..." Inna ta gwalo ido tace "Wa xa a kai ma?" Yace "Wata ce daban" Inna ta xauna kan kujera ta saki salati tana tafe hannu tace "Wayyoo.. Amma dai kai shahararren mayaudari ne Mujaheed, yanxu dama yaudarar yar mutane ka dinga yi ba aurenta xaka yi ba? Kasa yarinya ta kashe d'an kudinta ta siyo min turare duk da ba mai tsada bane, Mujaheed anya kana son wanyewa da duniya lafiya kuwa? Ina laifin yarinyar, kyakkyawa ce fa doguwa" Mujaheed dai kallon kasa kawai yake bai ce mata komai ba, ganin ynda ta dage tana kiransa da mayaudari ya dago ya kalleta yace "Umma ce bata son aurena da ita, shine ta hada ni da yar kawarta..." Inna ta xaro tace "Auzubillahi, yanxu Rukayya ce ta hanaka aurenta? Toh kuwa akwatunan nn babu inda xa su daga parlon nan sai gidansu Farida, yarinya mai hankali da natsuwa, tun da naga ynda take ji da Imaan take sonta naji nima ina sonta" Da sauri Mujaheed yace "A'a ita ma fa iyayenta sun riga da sun mata miji har an sa rana" Inna ta saki baki tana kallonsa, can tace "Toh wacece wannan kuma xa ka kwaso mana?" Ya d'an yi murmushin karfin hali yace "Idan anyi auren xaki ganta" Inna tace "Sai ka kawota ai ta gaisheni ba ruwana, Amma dai kun yaudara juna da farida tunda gashi ita ma har an mata miji kace, ohh mutane dai tsoron Allah yayi karanci a xukatansu, yanda ka taso gabana Mujaheed bai ci ace baka da tsoron Allah a xuciyarka ba, Toh ko da yake ai Rukayya ce ta haifeka, Ahmadu da na haifa ai gashi yana tsoron Allah, haka ma Bukar, duk basa yin abinda Allah ke fushi da, banda haka kayi ta xuwa gun yarinya kuna tadi ashe ba aurenta xaka yi ba??" Shi dai Mujaheed kallonta kawai yake, bude kofa aka yi Abba ya shigo, Inna ta tsuke fuska, Mujaheed kadai ya amsa sallamansa, Abba ya xauna yana kallonta yace "Ina yini" tace "Toh ni da aka ki gaya min xa a kai ma Mujaheed lefe sai aka yi yaya??" Abba ya girgixa kai yace "Kiyi hakuri, ni ma ba a gaya min da wuri ba Inna" Inna tace "Kai dai ka ajiye bala'i a gida kawai kuna xaune, banda haka ya xa ayi d'an ka a boye maka xa a hada masa lefe?" Mikewa Mujaheed yyi yana kallonta yace "Sai da safe" tace "Tou yaushe xa a kawo min yarinyar?" Yace "Ehh xa a kawota in sha Allah" daga haka yayi ma Abba sallama ya fita. Washegari Thursday Imaan na dawowa schl bayan ta yi wanka ta ci abinci ta shirya ta tafi part din Inna, Inna dake bakin pampo ta biyota ciki tace "Duk na cire maki kayan na boye maki a sif" Imaan ta xaro ido tace "Ni dai ba ruwana Inna" wani kallo Inna ta mata ta xauna kan kujera tace "Toh ni da ruwana, sai in ga wanda xai ce min don me" Imaan ta tabe baki ta xauna, inna tace "Daxu Bulasawa ya kirani muka gaisa, ni dai tunda uwata ta haifeni ban taba ganin yaro mai hankali da kirki irin yaron nan ba..." Imaan ta dai yi murmushi bata ce komai ba, Inna tace "Bayan mun gama waya ni dai nace masa iron dina ya lalace" Imaan ta xaro ido tace "Kika ce masa haka Inna?" Inna tace "Toh baxan ce ba, tun yaushe nake bin Bukar da Ahmadu su siya min sai su ce sun mance, dama wannan yaron isuhu kadai ne xan ce ma abu ya min nan take, shi Mujaheed ban ma sa shi a layi, ko ya siyo sai ya kai ma wancan katuwar matar, to wai ni isuhu na gidan nan ma kuwa?" Imaan ta bude hannu alamar bata sani ba, Inna tace "Ikon Allah ni toh bai xo ya ce min xai yi tafiya ba... Kai bari dai inje bangaren nasu inji lafiya, bai taba min irin haka ba da ma dai Mujaheed ne ni baxan damu ba" Inna ta saka Hijabi da ta dauko tace "Tashi ki rakani, ba lafiya yau kusan kwana goma ban ga isuhu ba, to ko bai da lafiya ne" Imaan ta mike suka fita parlon, Inna ta rufe kofar ta da makulli Imaan tace "Inna to meye na sa makulli" Inna tace "Baxan sa makulli ba? Ko datti ya shiga parlon ba a cuce ni, ko Kandangare ya ji shiru yana iya shiga in shiga uku" Imaan tayi gaba Inna ta bi bayanta tana cewa "Don Allah ki dinga cin abinci mai yawa Imaan, kinsan fa Bulasawa mai mutane ne, haka xa a ga amarya kamar tsinken tsire a sa mu a bakin duniya, ni dai ki rufa mana asiri" imaan dai bata tanka ta ba har suka iso part dinsu Maimoon, Inna ta shiga parlor tana kallon Ummi tace "Ke Isuhu na nan?" Bata jira cewarta ba ta wuce sama tana kallon stairs din palon tace "Matan Ahmadu dai kazamai ne, dubi fa yau basu goge nan ba ina ga" dakin Anty ta bude Aunty ta mike ganinta tace "Sannu da xuwa Inna" inna tace "Kwana biyu ban ga isuhu ba ko ke kika hanasa xuwa inda nake" Aunty tace "Ni na isa Inna, ban ma san bai je ba ai, yanxu dai baya nan" Inna tace "Toh yana dawowa kice ya xo ina nemansa" Aunty tace "Toh" Imaan ta gaida Aunty, Aunty ta amsa da fara'a, Umma ta leko ganin Inna ta koma ciki da sauri ta rufe kofarta, inna ta juyo tace "Toh ita kuma mai hada lefe ana ciki kenan, Toh dai baxan shiga ba" daga haka ta fara sauka stairs din Imaan ta bi bayanta. Bayan magrib Imaan na part din Inna Mujaheed ya shigo, xaunawa yyi ya gaida Inna da ke cin abinci tace "Mujaheed ni fa ban ga isuhu ba har yanxu, ban san me ya faru ba" Mujaheed na kallon boxes da ta jera yace "Inna xa a mayar da akwatunan can gida" Inna ta ajiye cokalin hannunta tace "A kan wani dalili?" Yace "Ai ba a gama xuba kaya ba" Inna tace "Toh sai a dinga xuwa nan ana xuba su, in dai kaga an fitar da akwatunan nan daga parlona to gidan amaryar xa mu tafi kai wa, ai ba wani ya min wahala da kai ba, ko Ahmadu da na haifa ban masa wahala yanda na maka ba, Rukayya dai ta shiga hankalinta a gidan nan ta daina shiga hurumin da ba nata ba" Bai kuma cewa komai ba, ya kalli Imaan dake xaune tana kallo, ta gefen ido ta ga yana kallonta ta mike tace "Sai da safe Inna" daga haka ta fita parlon, Bai dade xaune parlon Inna ba ya mike ya fita, yana isa part dinsu Imaan ya shiga balcony ya danna bell sannan ya bude kofar, Ammi dake xaune parlor ta dinga kallonsa har ya shigo, kasa kallonta yayi ya dukar da kansa ya xauna saman kujera yace "Ina yini Ammi" Ammi tace "Lafiya lau ya aiki" yace "Alhmdllh" tace "To maa sha Allah" kasa cewa komai yyi, can yana shafa kansa yace "Ammi dama..." Sai kuma bai ce komai ba, Ammi tace "Dama me?" Yace "Ina son Imaan xata rakani ne" Da mamaki Ammi tace "Ta raka ka ina?"


Yanxu xan dinga update twice sbda xan rage tsayin rubutun, sai kuma da daddare in sha Allah.

*The book Imaan isn't free, you read for free ur cup of coffee...*🤷🏻‍♀️

It's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, then you show ur evidence of payment through my WhatsApp digit 07087865788 to be included in d payment group.


Imaan isn't free, it's 300 via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah.♀

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello JiddahMujaheed ya kalleta yace "Ina son xan je gidansu Farida ne" Ammi tace "Wace faridar? Wace ku ka yaudara ko wata daban?" Shiru yyi bai ce komai ba, Ammi ta tabe baki ta maida dubanta kan TV, yace "Ni ban yaudare ta ba Ammi, kila hakan Allah ya tsara we are not destined to be together" Ammi tace "Toh yayi kyau, haka Allah ya tsara" Bai ce komai ba, can ta kallesa tace "Toh me xaka je ka mata?" Yace "Ina son xuwa in bata hakuri ne, idan ta gan ni da Imaan she might listen to me, bana son tayi tunanin yaudararta nayi" Ammi tace "Toh Allah ya kyauta, amma yanxu dare yyi sai ka bari gobe" yace "Gobe da safe xata wuce kano" Ammi ta girgixa kai, tace "Toh ba sai ku tafi har da Maimoon ba" yace "Eh

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login