Showing 114001 words to 117000 words out of 139381 words

Chapter 39 - IMAAN

Start ads

20 Aug 2025

690

Middle Ads

d'an ta6o ta a kafada, gaba daya wa enda suka san Inna suka xaro ido suna kallon ikon Allah, juyowa budurwar tayi tana kallon inna murmushi dauke fuskarta, Inna ta matsa kusa da ita sosai murya can kasa tace "Wani tsinannan telan kika ba kayan ki ya lalata maki haka saboda rashin tsoron Allah, duk duwaiwuka a waje?" Ba karamin tsorata da girgixa Inna tayi ba tana xare ido jin muryarta ya kauraye makeken hall din gaba daya ta cikin speakers, Hall ya rikice da dariya, Mujaheed ya sunkuyar da kansa, Umma ta kasa motsi inda take tsaye sai hadiye abu take da kyar, Imaan ta hade kai da table tana dariya kasa kasa, su Maimoon ma suna ta dariya daga inda suke xaune, Aunty da Ammi da Mama Hadiza dama tagumi suka yi suna kallon Inna da tayi tsamo tsamo a gaban hall sai kallon jama'ah dake dariya take, gaba daya yan uwan amarya wani kallo suka dinga yi ma inna, ita kuwa mai bada history ta ji kamar ta nutse gashi an ki daina dariya a hall, Safeenah ta wani hade rai tana kallon Mujaheed tace "Haba Mujaheed dama gate pass din wa enda suka kamata da wanda basu kamata ba ku ka dinga raba ma suka shigo mana nan, dubi wannan tsohuwar me ya kawota nan ta ina ta samu pass din shigowa har xata kunyata aminiyata cikin mutane, kasan Yar gidan wacece ita kuwa??" Gently Mujaheed yace "Watch ur words..." A fusace tace "Don't tell me that Mujaheed, how dare the old woman insult my friend that way, yar gidan governor ce fa tsaye a wajen..." Calmly yace "Ko yar gidan uban wacece, ke kawarki ce, to ni kuma grandmum dita ce a kusa da ita, so you dare not look into my face and say nonsense about her" Wani kallo Safeenah ta dinga ma Inna da ta tabe baki cikin sanyin murya tace "Ba lafiya, dama ba a sirri a nan, daga magana kuma sai sipikoki su dauka su min terere...." Juyawa tayi ta kalli yarinyar da ta kasa cewa komai har sannan tace "Ki dai maida masa ya gyara maki ai kudi kika biya ya cuce ki ya maki wannan dinkin" daga haka ta bar wajen ta tafi gun Mujaheed, har sannan Safeenah bata daina bin ta da wani irin kallo ba har ta iso inda suke tana kallon Mujaheed tana washe baki tace "Wannan ce amaryar Mujaheed" Safeenah ta dauke kai fuska daure, Inna ta rike ha6a tace "Ikon Allah, Toh Allah ya bada xaman lafiya, ta dai sha gwalagwalai maa sha Allah" Hajiyan Marafa ce tsaye kan Umma tana bala'i a mugun fusace tana cewa "Haba Rukayya ke baki ga irin manyan mutanen da muke ba gate pass bane xa ku ba wannan tsohuwa mai wanke wanke ta shigo mana hall tana shirme tana kunyata mutane, kin san yar gidan wacece tsaye a wajen take magana kuwa?? reputation dina da na 'ya ta kuke son 6atawa ko meye hakan?" Umma dai sai hakuri take bata a rikice tana cewa "Wllh ban san wanda ya bata pass din ba, don Allah kiyi hakuri Hajiya, wllh ban san daga inda ta taho ba...." A mugun fusace Hajiyan Marafa tace "Toh maxa ki sa a fitar da ita daga hall din nan tun wuri kada ayi mummunan abu a nan, maxa a fita da ita kada in sa masu gadi su fitar min da ita ta tsiya" Umma sai cewa take kiyi hakuri Hajiya xa ta tafi yanxun nan kuwa, ae ba ku kadai ta kunyata ba har mu wllh, ban san wanda ya bata pass ta shigo ba ni ban ma santa ba, haka irin tsoffin nan suke idan suka ga ana taro su shigo cikin jama'ah" Hajiyan Marafa ta juya fuu ta wuce tana cewa "Maxa ta bar nan kada in sa masu gadi su ja ta su fitar..." Inna na kallon Mujaheed tace "Toh naga duk baka da walwala lafiya kuwa, ko baka ci abinci bne?" Ya girgixa kai yace "Ba komai, ki koma kiyi xaman ki" Inna tace "Toh madallah sai dai har yanxu mu dai babu abinci babu labarinsa, ga ta rasulu can ma sai hamma take" Tana magana ta dau tsadadden drink dake gabansu tace "Ko in dau wannan" yace "Dauka" dauka tayi tace "Toh shikenan, Allah dai yasa ba mai halin uwarka xaka auro mana ba dai" daga haka tayi wucewarta, Safeenah ta bi ta da wani harara tana kyabe baki, Umma ta rasa yanda xata yi ta fitar da Inna a hall din cikin lumana, duk ta rikice taje can taje nan, Inna na dawowa xuwa seat dinta ta dinga cewa mutane "To dai duk wanda ya ci abu yyi hakuri ya saka gwangwani ko kwalin a jakarsa kada mu bata masu waje da kazanta mu cuce su...." A haka har ta koma gunta, ta ajiye ma ta rasulu drink din daya ta ajiye daya gabanta tace "Ma rage xafi..." Ta dau drink din ta fara budewa, Inna ta xauna tace "Naje na samesa amma kinsan ko gaisheni amaryar bata yi ba, ni dai ban kulata ba, ba ruwana kada in kunyata kai na cikin jama'ah ga ni babba, taro yayi taro in je inyi magana in kunyata Mujaheed din ma gaba daya, bakina a leko na juyo na dawo ai ana tare...." Ta rasulu tace "Gwara da baki kulata ba kam, ki bari sai an kaita dakin nata ki shirya kije ki mata tatas ki gaya mata yanda kike da Mujaheed" Inna tace "Ehh dama ai dole in sanar mata wahalan da nayi da shi don ta gane matsayina a wajensa, ana kai ta da washegari dama Imaan xan ce ta rakani inje in karanta mata yanda muke da shi" Umma ce ta taho gun Inna da sauri tana haki tace "Inna yanxu aka kirani wai ruwa ya cika parlon ki sai kwararowa waje yake ga kofar a rufe, ko dai kin bar pampon bayan gidan ki a bude baki sani ba?" Inna ta mike ta rafka uban salati a rude tace "Hadiza ta cuce ni ita ta shiga bandakin karshe tayi fitsari, shikenan ruwa ya shanye min gida na shiga uku na lalace ni patuu, ga dukiyoyi irinsu kujeru, tv, gado carpet, fridge duk a ciki" ta rasulu dake xabga salatin ita ma ta mike tace "Na shiga uku ni ta rasulu, jakata na dakin nima har da kudi dubu biyu, yanxu me xan ce ma 'ya yana daga xuwa biki ambaliya ya rutsa da ni??" Umma tace "Toh bari in sa driver ya maxa ya maida ku gidan gaskiya, don ruwa aka ce duk ya cika tsakar gida" Ko sauraranta Inna bata yi ba ta fice da gudu tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una ambaliyan ruwa a gidana a kira min yan kwana kwana, ga gudunmawar dubu hamsin da Bulasawa ya bani a dakin...." ta rasulu na biye da ita a baya ita ma da gudu tana salati, Mama Hadiza da su Aunty na ganin Inna ta fita da gudu suka taho gun Umma dake tsaye suna tambayarta me ya faru, Umma tayi wani dariya tace "Wai fa kudin da xata yi liki ta mance a gida shine wannan saurin wai driver xai maida ta gida" Kasa cewa komai Mama Hadiza da su Aunty suka yi, Umma tace "Allah dai ya kyauta, lamarin Inna ae sai ita" daga haka ta wuce ta bar su wajen a tsaye, Imaan dai na xaune an barta da jakunkuna irin na tsofaffi, Maryam ce ta taho gun Imaan da sauri tace "Ke maimakon mu bi su Inna mu je mu yi abinda xa mu yi kika bari suka wuce" Imaan ta xaro ido tace "Ae kuwa, toh kawai mu yi kamar xa mu bi su da jakar su sai mu wuce" Maryam tace "Toh dauko mu tafi" Imaan ta dau jakar Inna ta mika ma Maryam na ta rasulu, kallon Mujaheed tayi taga idonsa na kansu, ta dauke kai tana xaro ido tace "Maryam kin san Yaya kallonmu yake" Maryam ta kallesa taga still kallonsu yake duk da liki da mutane suka taru wajen suke masa da Safeenah, Maryam ta koma ta xauna tace "He is suspecting us Seriously, kin san me xai faru?" Imaan ta girgixa kai, Safeenah ta bude jakarta ta ciro new note din naira dari dari tace "Gashi ki tafi kiyi masu spraying, kafin ki dawo na fita gun mota sai ki sameni da sauri, but before then Bari in canxa seat" Imaan ta nufi can gaban hall din hannunta rike da tulin kudin, su Maimoon, Ummi, Rahma da wasu kawayen Safeenah da yan uwanta da suka sha gold sai cashewa wa suke da wakar jarumar mata da ya cike hall din Lol.... Safeenah ma na tsaye tana rawa gently tana kallon Mujaheed with love, shi ko yana tsaye kamar statue yana jujjuya wayar hannunsa, dance floor din kuwa banda dubu dubu babu abinda xaka gani a kasa sae few five hundred notes, Imaan ta isa kusa da su ta ki yarda ta kallesa tana kallon Safeenah dake rawa ta fara mata likin a hankali, kallon cikin ido Safeenah ke mata haka kawai Imaan taji gabanta na faduwa bata sake yarda sun hada ido ba tana ci gaba da yi mata likin kudin, Bandir din dubu daddaya Mujaheed ya ciro ya nufi gun kanninsa da suka dage sai cashewa suke barin Maimoon, Ya fara manna masu da daddaya da daddaya, Safeenah ta bi sa da wani harara ganin kanninsa kawai yake lika ma, Imaan na lura da abinda tayi haka yasa taki lika mata kudin hannunta gaba daya ta koma gun su Maimoon ta fara masu likin, Mama Hadiza ta xo ita ma tana ma su Maimoon da Imaan likin kamar su kadai ne a wajen tana murmushi, facing din Imaan Mujaheed yyi yana kallonta ya fara xuba mata one thousand naira note din a hankali, kasa kallonsa ta yi kanta a kasa, can kuma a hankali ta fara lika masa na hannunta, Mama Hadiza ta juyo ta dinga xuba masu na hannunta ita ma, Aunty ma haka, da abokansa gaba daya da suka cika wajen lkci daya, Safeenah ta ji kmr ta nutse don ba kowa wajenta sae flowing gown din jikinta, duk aka koma ana ma Mujaheed da Imaan liki, Umma sai xare ido take tana kallon ikon Allah, kowa ya xo sai ya fara ma Imaan da Mujaheed liki kamar ita ce amaryar, don wasu ko noticing Safeenar ma basu yi ba balle su san ba ita suke ma likin ba, Imaan dai ta dawo amarya a wajen duk kunya ya isheta.... Sai da Mujaheed ya manna ma Imaan gaba daya note din hannunsa yana kallonta, ita dai sai kokarin barin wajen take amma saboda yanda aka kewayesu ta rasa hanyar fita, da kyar dai ta samu ta lallaba ta fita taron xuciyarta na bugawa, tana kallon inda Maryam ke xaune taga har ta fita, da sauri ta nufi door din fita hall din ta fice fittt, Maryam na ganinta ta dallo mata fitilar motar ya Yusuf, xata tafi gun motar taji an fixgota, ihu tayi a tsorace ta juya xuciyarta na bugawa.....



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788


Afuwan for the late and short update, am not feeling too well... Thanks in anticipation for understanding.[7/19, 5:15 PM] +234 803 603 7561: 47. Imaan









Imaan kamar xata yi kuka tace "Ya Yusuf dubi fa yanda ka ban tsoro...." Yusuf yace "Ehh gwara ki ji tsoron, ina xa ku je?" Turo baki tayi tace "Gida mana, mun gaji" yana kallonta da kyau yace "Karya kike yi, ban kuma san lkcn da kika fara karya ba, and I need not to remind you the consequence of lying Imaan" shiru Imaan tayi tana kallonsa, ya d'an hade rai yace "birthday din makaryacin saurayin ki xa ku tafi koh, ke kin san waye Sadeeq kuwa? Kin san irin mutanen da yake abota da? Kinsan abubuwan da xa su faru gun birthday din nan da kika kwallafa rai sai kin je, why all of a sudden kika canxa from the decent Imaan da muka sani kika dawo mara ji?" Fuska daure yayi mata tambayar, kamar xata yi kuka tace "Ni fa ba birthday nace xan je ba, ai ba yau bane birthday din, kuma I only want to get him a gift now coz I know I might not get it tomorrow, ban ce lallai sai na je birthday ba" Kallonta ya dinga yi ta sunkuyar da kai a sanyaye, wayarsa da yyi vibrate ya kalla yyi replying text din da ya shigo sannan ya tafi gun motarsa ta bi sa da kallo, Maryam ta langwabar da kai tana kallonsa, yace "Ke ce ke xugata koh Maryam?" Xaro ido tayi tace "I don't get you" yace "Idan ke baxa ki gaya mata gaskiya ba why encourage her??" Maryam tace "Is there anything wrong with her getting her bf a birthday gift, we are in a civilized world Yaya Yousuf...." Yana mata wani kallo yace "Bani makulli na" Mika masa makullin sa tayi ta fito daga motar, Imaan dai sai kallonsu take ta gefen ido, ya juya ya koma inda take yace "Koma ciki..." A hankali tace "Toh ni gida xan tafi..." Ya daure fuska yace "Koma ciki nace" turo baki tayi ta juya ta koma cikin hall din, Maryam ta wucesa rai bace ta koma cikin hall din ita ma, Imaan na shiga ta tafi inda suke xaune tana kallon Mujaheed dake kallonta ta xauna, Maryam ma ta xauna a fusace tace "Gaskiya guys din nan sun fiye takura mutane, haka suke da sa ido dama, I won't tolerate this shit assuming we are staying together with them" Imaan ta tabe baki tace "I don't even know what's their business with me, sun dameni wllh" Maryam tace "Kece kike nuna kina tsoronsu ai" Imaan kamar xata yi kuka tace "Toh ni yanxu ya xanyi plss?" Shiru Maryam tayi tana kokarin nema masu wani option din, Yusuf dai na xaune d'an nesa da su yana kallonsu lkci lkci, ana fara cin abinci Maryam ta mike ta tafi ta debo masu yar fried rice ta cika nama ta dawo tana kallon Imaan tace "Let eat" Imaan ta girgixa kai tace "Am not eating" Har aka tashi dinner din Imaan bata da walwala, gashi da ta kalli Mujaheed sai ta ga kallonta yake, Tasowa Yusuf yyi ya taho inda suke ya ajiye ma Maryam makulli yace "You two should wait for me..." Daga haka ya wuce, Maryam tayi tagumi murya can kasa tace "Amma gaskiya wa ennan mutanen mayu ne, may be they know what we are up to" Ita dai Imaan bata ce komai ba idonta na kan Safeenah dake tahowa tare da Mujaheed kawayenta na biye da su a baya, hada ido suka yi da ita Safeenah ta wani daure fuska, Imaan ta dauke kai hade da tabe baki, sai da taga sun fita hall din sannan ta mike Maryam ma ta mike tace "Kinga hararan da yarinyar ke maki kuwa, did you know her b4?" Imaan tace "I don't know her fa" fita waje suka yi xuwa gun motar ya Yusuf, Aunty na kallon Yusuf a haraba hall din tace "Ka ajiye Mama Hadiza da su Hajiya Lailah a gida Yusuf..." Yusuf ya d'an bude ido amma bai ce komai ba, da sauri Imaan ta dauke kai tana wani murmushi, xagawa yyi ya budu front seat yana kallonta yace "Xo ki shiga nan" ta d'an xaro ido tace "Ya Yusuf Maryam fa?" Yace "Xata shiga wani motar, bana son musu ki xo ki shiga" Maryam ta hararesa ta dauke kai, A hankali Imaan ta taka ta isa front seat din ta shiga, Mama Hadiza da kawayen Aunty biyu suka shiga back seat, ya shiga motar ya bar haraban hall din. Yana parking a compound Imaan bata ko kallesa ba ta bude motar ta fice xata wuce apartment dinsu ta ji muryar Inna bakin gate tana cewa "Iliya Ahmadun bai dawo ba har yanxu??" Mai gadi da ya bar gate bude ganin motoci har uku dake bin bayan motar Yusuf yace "Ehh bai dawo ba Baaba" Inna na hango Yusuf da ya fito daga mota da Mama Hadiza da kawayen Aunty ta fashe da matsanancin kuka, da sauri Mama Hadiza ta nufeta tace "Me ya faru Inna" cikin kuka tace "Me na ma Rukayya a duniyar nan xata saka min da haka, ni fa na yarje ma Ahmadu aurenta tun tana yar jagaliya, yar yagalgal tana yawo da kodadden zani da yagaggen Hijabi" Mama Hadiza tace "me ya faru" Inna ta sharen hawayenta bata tanka ta ba tana kallon ta rasulu tace "Mu je kawai" ta rasulu tace "Idan ma kika yarda Rukayya ta kwana gidan nan yau Allah ma sai yayi fushi da mu da bamu dau mataki ba, irin wannan cin mutunci da raini haka? Oh oh tun da uwata Mai salati ta haifeni ban taba gani ko jin labarin irinsa ba, waiii.... Ai wannan babban magana ce wllh, ko kotu aka kai kara ba karamin muhimmanci xa su ba maganar nan ba, kuma da kyar idan ba sai an yanke mata hukuncin kare rayuwarta a gidan yari ba" Inna tace "Toh kun ji dai, ke dai mu je kawai wanda ya ajiyeta a gidan xai dawo duk gidan uban da yaje ya same mu, casun kuma da bamu samu ganin yanda xa a kare ba Allah ya isa xa mu hadu gaban ubangiji...." Ta rasulu na biye da ita tace "Ke ma dai wllh, sai ma kin fada?? Ae wannan a rubuce yake Asabe, abinda ba yafewa xa mu yi ba" Mama Hadiza da su Hajiya Lailah dai suka bi su da kallo. Imaan na kokarin saka kayan baccinta bayan ta fito wanka aka bude kofar dakinta, Maryam ce ta shigo ta tsaya tana kallonta tana murmushi, da mamaki Imaan tace "Ina kika je tun daxu kowa ya dawo banda ke??" Maryam tace "Close ur

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login