Showing 99001 words to 102000 words out of 139381 words
sau daya bai sake kallonta ba ya ci gaba da performing ablution dinsa, ta wucesa ta shiga parlon Inna, Inna ta mika mata abun kwashe sharan hannunta wanda ba komai ciki sai few dirt tace "Xubar min wannan a bola, dubi fa parlon kamar ba komai amma ji yanda datti suka cuceni suka makale, kamar na sani nace bari dai in share in gani, ilai kuwa ga shi har da guntun kasa, kila ma wannan mutumin ne ya shigo min da su, sam datti bai da masugunni a parlona gaskiya" amsa imaan tayi ta fita ta kakkabe abun kwashe sharan ta dawo, ta bi Mujaheed da kallo ganin wucewarsa yyi ta shiga parlon, Inna ta shimfida tabarma ta xauna tace "Ke ki ji ya xo min nan ya kwanta salon ya fara wannan xaxxabin nasa a ce a parlon Inna haka ya faru" Imaan ta xauna saman kujera tace "Ba shi da lafiya ne?" Inna tace "Wai daga anje an kai kudin gaisuwa shine har ya fara tunanin rabuwa da ni bai san tare xa mu tare a can gidan nasa ba" Imaan ta xaro ido tace "Shi yace maki haka?" Inna tace "To sai ya fada?? ko bai fada ba nasan hakan ne ma, ke kinsan shakuwar da Mujaheed yyi da ni kuwa? Nima har na fara jin xaxxabin xai rufe ni" Imaan tayi dariya tace "Yaushe aka kai gaisuwan?" Inna tace "Daxu da safe su Ahmadu da Bukar da Bala da abokan Ahmadun suka kai... jibi kuma xa mu je kai lefe ki shirya tare xa mu dake" Imaan ta xaro ido tace "Har da ke?" Inna ta saki baki tana kallonta tace "Oh oh Allah, ban gane har da ni ba, to dama su waye masu kai lefen idan ban da ni... Ni ana bani mamaki wllh haka Ahmadu da Bukar wai bai dace ba inyi xamana a gida, to a kan me? Ni fa nayi wahala da shi Mujaheed din, sannan ba shi da wata kaka da ta wuce ni a duniya, in har baxan je ba dama sai dai iyayen yarinyar so su dau lefen da kansu ba ruwana" Imaan dai bata ce komai ba, Inna ta mike ta shiga daki sai ga ta ta fito rike da wani takarda, tana kallon imaan tace "Duk cikin jikokina kece kadai xan ce tayi abu tayi, da kyar kiyi min musu, sauran kuwa dama baxa su yi ba, to wannan ba wani damu na yayi ba don kansu suke ma, ga wannan wanka xa ki yi da shi ni dama baxan ba su Ummi su xubar min dukiya ba ba ruwana ba sato kudin nake ba, ke kadai ma amsowa" Imaan ta turo baki tace "Meye shi din?" Inna tayi kasa da murya tace "Wllh garin magani ne, sai kamshi ma yake, ko uwarki kada ki gaya ma ba hankali gareta isasshe ba sai ta hanaki amfani da shi, ki xuba a cikin bokitinki ki tara ruwa bakin ki a leko ki yi ki fito kin ji takwarata" Imaan tace "Ni wllh kaikayi xai dinga min a jiki fa" cike da fada Inna tace "Yau naga jaraba sai kace warce xan ba karara? Meye kuma wani kaikaiyi ni patuu? Garin magani ne fa ba wani abu ba" Imaan ta hade rai tace "Toh bana so baxan yi ba" Inna tayi kasa da murya tace "Toh yi hakuri takwara, abinda ma idan kika yi yau kika yi gobe shkkn, wllh dubu goma kenan kar ki ja min asara ba ramin kudi gareni a dakina ba, ba komai sai tarkacen kwallaye da tsoffin akwatuna" imaan ta turo baki ta amsa tace "Toh wai na meye?" Inna tace "Kaikayi koma kan mashekiya" Imaan ta xaro ido tace "Meye hakan?" Inna tace "Duk wanda xai sa maki ido a duniyar nan idonsa xai tsiyaye tass barsa da jakar idon, idan kuma mugun abu xai maki to fa sai dai ya koma kansa ne ni ruwana, babu wanda ya san ta yanda Bukar ya sameki" Murmushi kawai Imaan tayi, Inna tace "Su Maimoon ma ga nasu can na ajiye masu ba don halinsu ba" Imaan tace "Toh" Inna tace "Ni kwana biyu banji Bulasawa ya kirani ba, ko dai lambar ta bace a wayana ne shi sa baya iya kirana" daukar wayar tayi ta mika ma imaan dake dariya tace "Ke duba min, ba halinsa bane rashin kiran duk kwana biyu kya ga ya kirani mun gaisa har in fada masa damuwata" imaan ta gama danne dannenta ta mayar mata wayar tace "Network ne ya dauke sai bayan sati daya xai dawo" Inna ta saki baki tace "Saboda me toh?" Imaan ta mike tace "Ae haka yake yi" daga haka ta fice parlon tace "Na tafi" Inna ta ajiye wayar tace "Toh Allah ya mana tsari da su masu wayan" Ranan Friday da yamma babu yanda Abba da Daddy basu yi da Inna kan cewar tayi hakuri ta bar yan uwan umma, Matan kawu Bala, Ammi da Aunty sai kanwar umma da kawayenta biyu su kai lefe gidansu Safeenah ba inna tace samm bata san xance ba da ita xa a kai kayan, Daddy dake ta kallonta yace "Yawanci ynxu fa iyaye maxa ne ma ke kai kayan ba mata ba Inna, ke me xaki je kiyi cikin yara don Allah" Inna ta masa wani kallo tace "Toh ko a baka kayan ka kai ne Bukar?" Daddy bai ce komai ba, Inna tace "Yau naga jaraba, to wai ina ruwan Bukar a maganan nan fisabilillahi, Wai xanje cikin yara, A'a gyambo ce ni karewar girma, kawai ayi ta laka ma mutum tsufa, ni din nawa nake gaba daya tukunna ma dai, kamar warce dai ta haifi duniya??" kawu Bala yyi kasa da murya yace "Hajiya Inna da dai kiyi hakuri ki bari su kai kawai, ke fa babba ce...." Inna ta dakatar da shi a fusace tace "Kai rabu da ni Balalau, Ina ruwanka?? Ka san da xamana a kaduna ko ka taba xuwa takanas ka gaisheni? Ko gantalallun matan ka ma ba turo su kake ba balle yaranka, yau da Hurera na da rai xaka mata haka, Allah dai ya mata Rahama ya gafarta mata bata min komai ba, lafiya muka xauna da ita...." Mikewa daddy yyi ya fice a parlon, Inna ta bi sa da kallo tace "Wannan Bukar din dai ba shi da kirki wato ga mahaukaciya na magana shine ya fita, Wai... Ai da Bukar ne ke xaune a kaduna wllh baxan sha ruwa a gidan nan ba, mulkata kawai xai dinga yi da bafillatanar nan da figaggiyar Yar su, Toh sae Allah ya rufa min asiri Ahmadu ne, kwata kwata Ahmadu dama bai son abinda xai ta6a ni a duniyar nan shi da yaransa, kaga inda ya fi Bukar kenan, to meye kuma daga magana dai ta fahimta xai kwashi jiki ya fita" murmushi kawai Abba ke yi da kawu Bala da yyi hamdala a xuciyarsa da ta katse tsigesan da tafara yi ta koma kan daddy, Abba yace "Toh shikenan dai Inna, Allah ya kiyaye hanya sai kun dawo" Inna tace "Toh dama mota daya xa a ware mana da imaan da kawata ta rasulu, tace min tana hanya" Abba ya buda ido da mamaki yana kallonta, kawu bala yace "Toh madallah Allah kawota lafiya" daga haka ya fita Abba ya bi bayansa, Kawu Bala na ta murmushi yace "Ayi ta hakuri Barrister tsufa ne" murmushi kawai Abba yyi yace "Ana ta yi, sai dai Allah ya kara mana hakurin" Kuka umma ta xauna kan gado ta dinga rusawa jin da Inna xa a je kai lefe tana kallon kawayenta tace "Babu abun kirki idan aka tafi da matar nan wllh, xuwa xata yi ta mana tonon asiri, tayi ta sakin xance a gidan"
*The book Imaan isn't free* it's 300
Via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 subscribe and read without been judge by ur conscience.
[7/16, 7:46 AM] +234 807 505 4566: 🌟⭐Imaan⭐🌟
39...
Mujaheed dai na tsaye kitchen sae kallon Umma yake har ta kai aya, jin yyi shiru a fusace tace "Wae ba da Mujaheed nake magana bane??" Ya d'an shafa kai yace "Ina ji Umma, Toh ni ya xan mata, kinsan tunda tace sai taje, ba wanda ya isa hanata xuwa ne" Umma ta hade rai tace "Yanxu baxa ka samo dubara da xaka hana xuwan nata ba, wllh idan taje gidan nan tsaf xata iya sa su fasa baka mata, tun da uwata ta haifeni ban taba ganin mutum sakakka irin tsohuwar nan ba, ni dai duk yanda xa ka yi ka rufa min asiri kayi ka hanata xuwa Marafan nan don Allah, ga ta can bakin motoci tsaye sai nuna hali take" Mujaheed yyi murmushin karfin hali yace "Toh..." Juyawa Umma tayi ta fice daga kitchen din rai bace, Inna dai na tsaye an sha super da mayafi da yar jakarta sae xuba kamshi take, duk mutan wajen dama sun bar jikin motar an bar ta ita kadai barin kawayen Umma, ta aika Maimoon ya fi sau uku ta kira mata Imaan amma shiru, ganin Maimoon ta dawo for the 4th time Inna tace "Yau naga abinda ya isheni ni patuu, Ina Imaan din ta shiga ne wai??" Maimoon tace "Inna ni fa ban ganta ba" Part dinsu Imaan Inna ta nufa fuska daure tana cewa "Ni ai xan ganta idan naje" Daddy ne xaune parlorn yana operating laptop dinsa, ta shigo parlon ko sallama babu tana kallonsa tace "Bukar Ina Imaan ta shiga ne wai, ko bata san duk jama'ah sun taru ita ake jira bane?" Daddy ya kalleta yaci gaba da abinda yake yace "Tana daki...." Inna tace "Kaga walakanci ko, wllh tarbiyar 'yar ka kalilan ne Bukar, ce mata nayi fa ta shirya ta fito mu tafi amma don wlknci ta shanya ni a rana ina ta jiran fitowarta, gafara xata min ne ko menene haka??" Daddy ya kalleta yace "Ku je Ina wai?" A fusace Inna tace "Kai lefen mana, ko gwari nake maka" girgixa kai yayi yace "Don Allah ki bari Inna, me xata je yi gidan... cikin manya kuma, kai lefe dai tun daxu ana ta abu daya ya ki ci yaki cinyewa, Ni nace mata baxa ta je ba don babu sa'anta a masu kai kayan, kema kawai don kince sai kin je ne babu yanda muka iya..." Inna ta saki baki tana kallonsa, can tayi kasa da murya tace "Meye laifina don nace xanje kai kayan jikana da nayi wahala da tun yana tsumma, me yasa baka da fahimta d'an uwanka ya fi ka fahimta Bukar...." Sai kuma ta fara matsar kwalla tace "Toh ai shikenan sai in fasa xuwa a kira ta Rasulu ace tayi xamanta, ai ba aikin Allah bane kai lefen na hakura" Daddy yace "A'a ni bance kar ki je ba tun da kinyi niyya kiyi tafiyar ki amma Imaan baxata je ba gaskiya" Inna tace "A'a su tafi, haka kawai in bata maku rai kan tsinannen lefe, dama ai babu sa'a na a masu kai kayan sai ta Rasulu ita ma xan sa a kirata ince tayi xamanta kawai, ae gaskiya ku ka fada, duk wanda kuma ya rasa mai gaya masa gaskiya a duniya yyi asara, ni dai na hakura da in bata maku rai sbda kayan mutane" Daddy dai bai ce mata komai ba har ta fita, Ammi da har ta gama shiryawa ta fito daga daki tana kallon Daddy tace "Kai me ya kai ka yin haka yallabai, maimakon ka barta tayi tafiyarta tunda ta sa rai" Daddy yace "Gwara ana yi ai ana mata gyara, ba gashi yanxu tace ta fasa ba, Amma komai tace be it right or wrong sae barrister ya biye mata" Ammi dai bata sake cewa komai ba. Inna na xaune parlonta bayan Yan kai lefe sun tafi kai lefen, Umma kam kamar ta xuba ruwa kasa ta sha duk tunaninta Mujaheed ne yyi mata magana ta fasa xuwa farin ciki gunta ba a cewa komai sai murmushi take bayan an tafi kai kayan. Mujaheed ne ya shigo parlon Inna da sallama ta dalilin sawa da Innar tayi a kirasa a waya, ita kadai ce parlon xaune kan kujera fuskarta shabe shabe da hawaye har da majina, Kallonta Mujaheed ya dinga yi da mamaki yace "Mai ya faru kuma?" Ta rushe da sabon kuka tace "Babu abinda Bukar ya mance bai gaya min ba Mujaheed wai daga nace xan je kai kayanka don Allah ya albarkaci kayan, shine ya tsitstsige ni ya gaggaya min ba dadi, yayi ta min bala'i kamar xai ari baki wai xan je cikin yara tsofe tsofe da ni, inda Bukar yake shiga ba nan yake fita ba, yayi min tatasss...." Wani kukan ta kara fashewa da, Mujaheed ya xauna yana murmushi yace "Shine kike kuka?" Cikin rawar murya tace "Baxan yi kuka ba Mujaheed, Bukar ya lalace, yau har nuna min yayi bani da iko da figaggiyar 'yar nan tasa mai ciwace ciwace iri iri kamar warce ta kashe d'an mutum, Ni dai ba Ruwana ba haka Bukar dina yake ba da, duk Aisha ta lalata sa da halinsu na fulani, ta sa ya xama jarababbe ya xama fitinanne, ga bakar xuciya.... Ni dai ban tanka sa ba nayi shiru Ina ta kallonsa don gani nayi abun ba na lafiya bane, Ni Ahmadu baya min haka komai nace sai dai yace min to, kwata kwata bai son bacin raina, Bukar dai ya lalace kuma ni ba ruwana da shi da 'yar sa.... su je can su karata idan Bala ma xai tafi ni bin sa xan yi kawai, duk kwana biyu sai in dinga kiran Ahmadu muna gaisawa" Murmushi kawai Mujaheed yake yace "Kece fa baki fahimci daddy ba ba fada yake maki ba kawai dai gyara ne" Inna ta daga hannu sama tace "A'a wllh fada ya dinga min kamar xai ari baki, ni ba ruwana kar ka xo nan ka karesa.... lalacewa ne dai ta riga ta samesa, har ni xai bude baki yace ma babu inda yar sa xata bi ni" Sai kuma ta fara kuka tace "A karkashin akwati fa na fiddo kayan nan ko sa su ban taba yi ba gashi yanxu babu inda naje sai na wanke su kar su yi warin jiki, kasan mutum ba komai bane facce datti" Mujaheed ya tabe baki yace "Kiran kenan?" Tace "Eh wllh, na rasa wanda xan gaya ma ne na kira ka, gashi har naji sanyi, to wa gareni dama banda Allah sai kai din, sai kuma Ahmadu" mikewa yayi yace "Toh ki shirya sai in kai ki gidan nawa ki gani...." Tace "Gidan da xa mu xauna?" Ta gefen ido ya kalleta bai tanka ta ba ya fita tace "Toh ai kawai bari in fito tunda ban tu6e kayan ba...." Mujaheed na isa part din su Imaan ya shiga da sallama, har sannan Daddy na parlorn a xaune, ya xauna saman kujera ya gaishesa with respect, daddy ya amsa da murmushi yace "Ya gajiya" murmushi kawai Mujaheed yyi yace "Abba dama wai Inna ce..." Sai kuma yyi shiru yayi yar dariya yana kallon daddy, daddy yace "Kiran ka tayi kenan" Kai ya gyada masa, Daddy ya girgixa kai bai ce komai ba, nan Mujaheed ya fada masa duk yanda suka yi da ita, daddy murmushi kawai yake yace "Dama xan je yanxu in sameta" Mujaheed yace "Amma kuma xan fita da ita xuwa can gidan ta gani, xaka sameta yanxu ko sai mun dawo?" Daddy yace "Toh shikenan ku tafi kawai, anjima xan je idan kun dawo, Ku tafi tare da imaan din..." Mujaheed yace "Toh" Daddy ya kira Imaan dake dakinta, fitowa tayi parlor, ganin Mujaheed ta xaro ido ta koma da sauri ta dauko Hijab dinta tasa, shi dai Mujaheed dauke kansa kawai yyi, Bayan ta sake fitowa daddy yace "Ki shirya xa ku fita tare da Inna yanxu" a hankali tace "Toh" daga haka ta juya ta koma daki, Mujaheed ya mike yace "Toh sai mun dawo Abba" Daddy yace "Toh Allah ya tsare, thank you son" murmushi kawai yyi ya fita parlon. Back seat ya bude ma Inna ta shiga tana cewa "Allah dai ya shiryi Bukar, Ni dai inaga bakin cikin 'yar kazar da xa a ban in ci a can yake min, to ni kuwa wani irin nama ne ban ci ba a rayuwar nan, ni wllh ya ma fara bani tsoro, sam ba haka yake ba da, yasan wahalan da nayi da shi yana karami kuwa, kamar fa baxai yi rai ba mayu suka kama min shi, kasan lkcn yana da kyau tsantsaa ga shiga rai yanda dai kaga wannan figaggiyar yar tasa da ya haifa, haka nayi ta wahala in gaya maka Mujaheed, Ni ce can nice nan cikin kishiyoyi gantalallu lkcn Ahmadu na da shekara hudu shi kuma ba shi da aiki sai shegen kiriniya yyi ta kwaso min kayan bola...." Rufe motar Mujaheed yyi bayan ta shiga ya juya suka yi ido hudu da imaan dake tahowa sanye da hijab dinta har kasa hannunta rike da wayarta.... Ya dauke kai ya xaga ya bude driver seat ya shiga, Imaan ta bude back seat xata shiga ya juya ya jefa mata wani mugun kallo yace "Do I look like ur driver?" Turo baki tayi bata shiga ba kuma bata ce komai ba, Inna tace "Oh oh Allah, kaga jaraba ko Mujaheed, yanxu wa ya gayyatota nan, ba Uban cewa yayi kar ta bi ni ba, meye kuma ta wani xo mana nan salalo salalo" Imaan ta hade rai tana kallonta, Inna tace "Ni dai ba ruwana, ki shiga gaba ki xauna tunda ubanki ba son tarayyar mu yake ba, ni ki daina ma xuwa min sashina nunawa yake a fakaice wai ina koya maki bakin hali" Imaan taji kamar ta juya ta koma bangarensu amma sanin Daddy na parlor kuma kafin ta fito ta ce masa ita baxata bi su ba yayi insisting sai taje, tasan tana komawa yanxu fada xai mata yace