Showing 63001 words to 66000 words out of 139381 words

Chapter 22 - IMAAN

Start ads

20 Aug 2025

669

Middle Ads

masa, Anty ta wuce ta bar sa wajen tsaye, da kyar ya ja kafafuwansa ya wuce dakinsa. Ammi ta hada ma imaan ruwan xafi a bayinta ta fito tace "Ga ruwan ki shiga, saura ki salance ruwan" Tashi Imaan tayi ta wuce dakin nata. Wanka Mujaheed yayi ya shirya jin lkcn Asr yyi yayi alwala ya fita gidan, yana dawowa masallaci dama part din inna ya nufa don Allah yasan yana tsoron haduwarsa da mahaifiyar tasa Inna ta fito daga daki jin an bude kofar parlor ganinsa tace "oyaa Alale, fitar min parlor kada in tara maka jama'ah, uban me ka xo min??" Mujaheed yayi dariya yace "Haba dai mai gidan kuma kike kora yau inna?" A fusace tace "Yana kabari, tun raina bai baci ba Mujaheed ka fita" Mujaheed yace "Abba ne fa yace kada mu tafi dake Inna" ta buda baki tana kallonsa tace "Kai haba?" Yace "Xan maki karya ne" xauna wa tayi tace "Ikon Allah, shi Ahmadun yace ku tafi ku bar ni kenan, to ya ma kansa kuwa, shine har da shi a bani hakuri da masu gadi a tsakar gida daxu, har hawaye fa sai da na xubar" Mujaheed yyi murmushi ya kwanta kan kujera, Inna tace "Toh ae shikenan, ya jikin Imaan din?" Yace "Da sauki" inna tace "Kuma da gasken bata da lafiya Mujaheed? Naga kamar don kar aje kauyen da ita yasa ta langwabe fa" Mujaheed yace "Ni dai akwai abinci?" Tace "Gashi can wanda Aisha ta kawo min ne daxu, bai wuce shinkafa da miya ba, Idan kuma biskit xa ka ci ga su can iri iri a daki wanda aka kawo ma Imaan, Kazan ma daxu na dumama na karasa cinyewa..." Mikewa xaune Mujaheed yyi yana kallonta na kusan second goma, can yace "Wa ya kawo mata?" shiru Inna tayi kanta a kasa, can ta saci kallonsa suna hada ido tace "Yo wa gareta banda Bukar??" tana fadin haka ta mike ta shige daki.... Imaan ta fi minti biyu tsaye bakin kofar bedroom din Ammi ta kasa shiga don bata san me xata ce mata ba, bude kofar dakin aka yi ta ja baya da sauri, Ammi ta dinga kallonta tace "Meye haka kike yi a bakin kofa ta?" Ta fara kame kame ba tare da ta kalli Ammi ba, Ammi tace "Imaan" daga kai tayi ta kalleta kamar xata yi kuka, Ammi tayi kasa da murya tace "Tell me what you want" tana jan fingers dinta a hankali tace "Ammi dama... Dama Sadeeq ne yace min yana waje ya xo gaisheni" Ammi ta dinga kallonta tace "Waye Sadeeq" ta sunkuyar da kai tace "Abokin ya Muhsin" Ammi ta yi shiru, can tace "Toh kar ki dade" Ta d'an yi murmushi tace "Toh nagode Ammi" daga haka ta saka Hijab dinta ta fito don tun da aka yi la'asar Sadeeq ke waje amma ta rasa yanda xata sanar ma Ammi ta fita, sosai hankalinta ya kwanta ganin ba motar Mujaheed a parking space, kamar mai tausayin kasa ta fita kofar gida, Tsaye ta ga Sadeeq jikin motarsa ya rungume hannunsa, as usual sanye da spec dinsa, dogon hancinsa da cute millionaires belt dinsa shine first abinda xaka fara noticing a fuskarsa daga nisa, Ta sunkuyar da kanta har ta isa inda yake tsaye, kallonta yake daga cikin glass din idonsa ko kiftawa babu, murya can kasa tace "Ina yini?" Yyi murmushin da ya bayyan dimples dinsa ya cire glass dinsa yace "Lafiya lau Imaan ya jikin?" A hankali tace "Na ji sauki" yace "Sure??" Ta gyada masa kai, yace "Toh Allah ya kara lafiya, hope kin sha dosage na afternoon, I mean ur drugs?" Ta gyada masa kai tace "Na sha" yace "Good, ya mama fa?" Tace "She's inside" ya langwabar da kai yace "Yaushe xan xo gaisheta pls" ta xaro ido tace "A'a xan ce kana gaisheta" cikin sanyin murya yace "Ke dai baki son yan gidanku su san ni koh?" xata yi magana aka bude gate, Inna ce tsaye bakin gate din tana kallon mai gadi tace "Kai iliya kake ko ilu, Kasan kan waya kuwa? Hadiza xa a kira min duk ba kowa gidan sai mai laluran can kuma nasan tana can tana bacci yanxu haka, yaran duk sun tafi kauye sai gobe xa su dawo" Imaan tayi stiff inda take bayan gabanta yayi mugun faduwa jin muryar inna, Mai gadin ya mike da sauri ya amshi wayar yace "Toh Hajiya...." Buda baki inna tayi tana kallonsa tace "Eh lallai baka da da'a, banda barbada kace ma matan gidan Hajiya nima kace min Hajiya, to bari kaji ko wa enda suka dauke ka aiki ma inna suke ce min balle kai, bar gani na haka xuciya mai kyau da rikon gaskiya da amana yasa ka gan ni har yanxu da kyau na, amma wllh da kyar idan ban girmi wanda ya haifi kakanka ba ma" yayi kasa da kai yana murmushi sosai yace "Yi hakuri Baaba tuba nake" inna tace "Kaji min yaro dai" Imaan dai ta kasa tsaye waje daya tayi backing din inna xuciyarta sai bugawa yake, murya can kasa Sadeeq yace "Ur grandmum?" ta gyada masa kai a hankali, kamar ance inna ta daga kai ta gan su, sake baki tayi ta kalli mai gadin tace "Kai wancan ba Imaan bace nake gani a tsaye?" Yace "Ita ce Baaba" Sadeeq yace "Let me go and greet her tunda ta gan mu" imaan dai kasa cewa komai tayi, ta ji kamar ta fashe da kuka, ae kuma shikenan.... Sadeeq na isa gun Inna dake ta kallonsa ya risina ya gaidata da ladabi, tace "Kai ne sabon saurayin nata?" Murmushi Sadeeq yyi ya kasa cewa komai, Inna tace "Ikon Allah, Kai ni fa na haifi ubanta Bukar, jikata ce fa, ita kenan Allah ya ba Bukar fa, a hannuna fa aka haifeta wllh, yanxu d'an nan da ban fito na gan ku ba shikenan, kai a garin ku haka ake yi?? ko bata ce maka kakarta na da rai bane, ita tunda bata da hankalin cewa ka shigo ka gaisheni kai baxa ka yi tunani ka shigo ba, dubi fa yanda ta ji kunya ta kasa juyowa kamar warce ruwa ya cinye" Sadeeq dai sai murmushi yake yace "Dama ai xan shiga in gaida ki kaka, kiyi hakuri" inna tace "Ni dai ba ruwana a dinga abu saboda Allah, tunda dai na kama ka mu je ciki" Yana murmushi ya bi bayanta suka shiga compound din ta rufe gate, tana nuna masa bangaren su Mujaheed tace "Kaga wancan katon ginin?" Yace "Na gani kaka" tace "Toh na wan ubanta ne, barrister suke ce masa, a India yayi karatun lauyancin sa, matansa biyu sai 'ya ya bakwai, Mujaheed shine d'an sa na fari, ina tsaye bakin kofar asibiti aka haifesa, yana nan xaka gansa wani lafcece dogo, da yake ada yana daga wannan karafunan turawan, to da kyar dai Ahmadu ya raba sa da su, nima na dinga rokon Allah har ya daina, a gabana fa ya girma, tun yaye yake wajena iyayen suka bar min, yana gama sakandari dama babansa ya biya masa kudin karatun likita a turai, ai ko in gaya maka babu irin fitsarar da bai koyo a can ba gaskiya, ni dai lkcn da ya dawo ma tsoron sa nake ga wani uban gashi da ya tara, buduwar da xai aura ma yar hayi ce, to sai kaninsa Yusuf, xaka gansa shi kuma wani lagwai lagwai kamar ya karye malam, da ma muka samu ya d'an yi kauri yanxu, sai kaga yanda aka haifesa d'an fiyot, to sauran kuma duk mata ne" Murmushi kawai Sadeeq ke yi yana bin inna, inna ta nuna masa part din su Imaan tace "Toh kaga wannan bangaren na su Imaan ne, Ubanta a can Habuja wajen neman abincinsa yake, ita kadai Allah ya basa a duniya, to dai ya fi babu d'an agwai da bak'in da, uwarta na nan wata bafillatana sai kirki, toh ni kuma kaga akurkin da suka gina min nake rayuwa ciki" ta fadi haka tana nuna masa nata part din.




*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group._23. Imaan














Am bringing this to the notice of my fans, idan xaku biya book din *Imaan* in dai ba digit din nan 👉🏻 07087865788 wato lambata kuka yi ma magana ba to Wllh ba ni kuka biya ma kudi ba, lambata guda daya ne kacal kuma gashi can a sama na rubuta, sannan ni bana amfani da wani kati idan ba Airtel ba, don haka duk wanda ya biya ta wani lamba daban wllh ya karanta hakkina without paying coz every page sai na sa number na da account number amma sai ku tsallake ku tafi kuna biya a gun wa enda ban sani ba ban san da su ba, ni kadai nake harkata a bangaren rubutu bni da wani xae ce ku tura masa xai turo min, talk to me directly through my WhatsApp digit 👉🏻 07087865788, su kuma masu siyar min da littafi har da hada document Billah na bar su da Allah, we shall surely meet in the hereafter in dai hakkina ne in sha Allah. Sannan masu *forwarding* ma su ci gaba there is power in the tongue_





Dariya Sadeeq yayi yace "Haba wannan ai ba laifi kaka" ta tabe baki tace "Mu je dai tukun" suna isa bakin kofa tace "To dai ka gani..." yana murmushi ya shafa kansa yace "Wannan ai ya fi duk sauran kyau kaka, ga shi ba hayaniya ba komai" Inna ta kara tabe baki ta bude kofar tace "Toh Allah ya masu albarka da suka gina min ai dai yafi babu" bin bayan ta yayi cikin parlon dake ta kamshin turaren wuta ta bude fridge ta dauko masa malt biyu da ruwan gora ta ajiye masa yace "Nagode sosai kaka" xaunawa tayi tana washe baki tace "Madallah, to ya sunan jik'an nawa?" Yyi kasa da kai yace "Sunana Abubukar Sadeeq" Inna ta gwalo ido ta saki wani kabbara da ya sa ya dago da sauri yana kallonta, tace "Yo ai sunan mahaifinta kenan Bukar, wllh shi ya haifeta, ai ko baka gansa ba mutumin kirki mai dattako da sanin ya kamata, sam yaron bai son 6acin raina, yo Ashe ma d'a na ne kai, to ka sha kurumin ka in dai wannan yarinya Imaan ce to wllh ka sameta ka gama ko taki ko ta so in dai ina numfashi kai ne mijin ba ruwana, don gaskiya ka kwanta min sosai, naga kana da hankali da nutsuwa" murmushi kawai Sadeeq yake, yace "Toh kaka idan ita bata ra'ayi fa?" Inna ta xaro ido tace "Wannan kuma ita ta jiyo ni dai ba ruwana, sunan ubanta fa gare ka kuma duk masu sunan an sansu da rikon aure, dubi fa yanda ubanta ya rike uwarta duk da rashin haifa masa yara da yawa da bata yi ba, to ni ko ina xan yarda ka kubce mata, A'a baxai sa6u ba wai bindiga a ruwa" Sadeeq yace "Toh nagode kaka naji dadi sosai" Tace "A'a ba xancen godiya, sunan d'a na fa gareka, ni dai ko yau kace xaka turo magabatanka kofa a wangale yake, to me xa mu ci da ita?? duk da dai ko sati ba ayi da aurar da yar uwarta ba amma idan ma iyayen nata sunce baxa su iya ba ni xan mata gado da kambodi da dirowa, Ina ce suna kenan kayan auren dai?" Sadeeq couldn't help it but laugh, tace "Kai ba xancen dariya bane, ni wlh sai in sa a siyar da filina guda daya in mata kayan daki, dama ni tsinannen bokon nan da ake yi yanxu ba d'ad'a ni da kasa yyi ba" Sadeeq ya sakko kasa yace "Da xa a ban ixinin turo magabatan nawa ba da jimawa ba da naji dadi sosai kaka" Inna tace "Wannan ai ba wata matsala bace bari Ahmadu ya dawo tunda kaga shi uban nata na Habuja" yace "Toh naji dadi sosai kaka" Inna tace "Kai don Allah... ai kuma an xama daya godiya ta me kuma, in ji iyayen ka a nan garin suke su ma?" Yyi kasa dai kai yace "Ehh suna nan" Inna tace "Toh dan siyasa ne uban naka?" Yana murmushi ya girgixa kai yace "Aa d'an kasuwa ne, Alhaji Ahmad Bulasawa ne Abba na" Inna ta xaro ido tace "Bulasawa?? Bulasawa dai da na sani na garin nan?" Bai dago ba still yace "Ehh shi" Inna ta bude baki tana kallonsa da kyau, can tace "Ikon Allah, ashe d'an babban mutum ne gabana ni Asabe, waye bai san Bulasawa ba duk garin nan da ma duk kasashen arewa, ba ance gidansa na nan nan GRA ba?" Yayi murmushi yace "Ehh" inna ta rike ha6a tana kallonsa tace "Ehh lallai ga kamanni kawai hanci ka fisa wllh, amma matansa aka ce biyu, to wacece uwarka a ciki, ko uwargidan? Don dai Bulasawa bai wuce Ahmadu na ba" Yace "Ehh ita" Inna tace "Atoh Alhmdllh, Allah na gode maka, kai abu sharr... bari Ahmadu ya dawo ko cikin watan nan ma ni gaskiya sai ka turo su Bulasawan, wa xai xauna" shi dai bai ce komai ba, Inna tace "Kai.... Allah mai iko, amma xan so kada wannan abun arxikin ya dau lkci gaskiya, ai aure abun arxiki ne" a hankali yace "Toh Allah ya sa haka kaka" tace "In sha Allah ya ma sa, ai abun arxikin xa a hada" Mikewa tayi tace "Bari in debo maka dambun namar da na ajiye ma Mujaheed" Da sauri yace "A'a xan koma ne kaka" Tace "Da wuri haka? Ni dai ka tsaya ko a leda ne sai in kulle maka" bata jira cewarsa ba ta shiga daki ba a dau lkci ba ta fito da gaba daya dambun naman a leda ta juye, ya xaro ido yace "Kaka wannan ai yayi yawa" tace "A'a ba ruwana ka amsa, dama Mujaheed da Imaan na ajiye ma to gaskiya ba rabonsu bane ynxu" dariya yyi ya karba yace "Toh ngd kaka, Allah ya kara girma" tace "Don ma dai duk sun cinye min cin cin din, kuma nasan ba kowa ya aikata min haka ba sai Maimoon da Ummi, ita Imaan bata daukan abu ba a bata ba sam ba halinta bane, gashi yarinyar bata da fitina tun tana jaririyarta, ga rashin yarda da kowa, lkcn ma ni har fargaba nake kada a kawota wajena don idan ta fara tsala ihu duk sai ta tara min munafukan anguwa an shigo min ana tambayar lafiya, me ya sameta?? dama Mujaheed kadai ne bata yi ma kiwa ba lkcn da take tashan kiwan, idan kuwa ta makalkalesa a lkcn bbu mai banbareta sai uwarta Aisha, ita ce ma ta makala masa yaya tun bata da wayo, in ko ba shi ya bata abinci ba dama abincin sai dai yyi ta galantoyi ba ci xata yi ba, in gaya maka lkcn Bukar na siyo mata wani runtumemen alawa idan ta saka a baki bata yrda ta ba kowa don rowa sai dai Mujaheed, shima din d'an dangwala masa xata yi a baki tana makale jikinsa, kai har goyata Mujaheed ya sha yi fa ta saki fitsari jikinsa sai dai ya canxa kaya, gaskiya ta takura ma Mujaheed ba kadan ba tana karama, shi sa in har yana gida uwar ta kawo ta bani da fargaba in kyalesu can su karata inyi ta kaina, to idan ban kyaleta ba ya xan mata tunda bata yarda da ni ta sa iyayenta su fara wani mugun tunani a kai na in shiga uku? A'a ba ruwana wllh" Murmushi kawai Sadeeq yake yana kallon inna, ta tabe baki tace "Toh gashi dai Imaan an girma kamar ba ayi ba, bari dai in bar ka haka naga kamar sauri kake, to sai yaushe kuma xaka sake shigowa??" yace "Ae ko da yaushe xan dinga shigowa gaida ki in sha Allah" Tace "Kai toh nagode yarona, Allah maka albarka, ya kare ka sharrin mahassada" ya mike ya ajiye mata dubu goma a gabanta yace "Ba yawa kaka a sa katin waya ayi xumunci" ta kauda kai da sauri tace "kai kai.... Ayi haka kuma Bukar??" Ya nufi kofa yana murmushi yace "Sai na kuma dawowa kaka" ta mike tana washe baki tace "Toh Allah maka albarka ka gaida min uwarka kaji?" Yace "In sha Allah xata ji" daga haka ya fita parlon just smiling, inna ta koma ta dau kudin tana kirgawa tana murmushi. Dama tunda inna ta shiga ciki da Sadeeq imaan ta wuce part din su ta fashe ma Ammi da kuka, Ammi ta mike tace "Lafiya?" Cikin kuka tace "Ko ba inna bace ta wani fito ta gan mu shine ta sa suka shiga ciki tare da shi, yanxu ban san dame dame xata fada masa ba, wayyo na shiga uku Ammi, nasan komai ma yau sai ta gaya masa" Ammi ta sake baki tana kallonta, ita kanta hango irin maganganun da inna xata juye ma Sadeeq yau ta dinga yi, can tace "Ae ko sai ki tashi ki tafi bangaren nata, idan ta ganki xata kama bakin ta" Imaan na girgixa kai tace "Ammi baxan iya ba, tun fa a gate ta fara basa labari" Ammi tayi jigum, can tace "Toh Allah ya kiyaye, ban san kuma me xan ce ba" daga haka ta bar parlon, Imaan ta dinga hawaye duk jikinta yyi sanyi babban damuwarta ma kada inna tace masa ai gashinta na nan bata son a gyara mata shi. Sadeeq na fita compound din yayi dialing number imaan yana murmushi, da sauri ta mike xaune tana kallon wayar, ta fashe da kuka a hankali ganin shi ne, da kyar ta daga kafin ya katse ta kai kunne, yace "Toh ai xaki fito mu yi sallama amma?" Tayi gathering courage tace "Me grandma dita ta gaya maka?" Yayi yar dariya yana wara ido yace "Ai babu abinda

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login