Showing 54001 words to 57000 words out of 139381 words
kai yace "Ina yini Hajiya" tace "Lafiya Alhmdllh, ya Hajiya Rukayyar, fatan an watse taro lafiya" yace "Alhmdllh" xaunawa tayi tana kallo su Maimoon da Imaan dake gasiheta tace "Wannan kamar kanwar khadijah da tayi aure Us koh?" Ta fadi haka tana nuna Maimoon, Mujaheed yace "Ehh kanwarta ce" tace "Maa sha Allah ga kamanni na gani, to ita wannan fa" Mujaheed ya kalli Imaan da ta nuna, da sauri yace "Yar uwarsu ce" tace "Allah sarki shi sa ban santa ba" Maimoon ta mike ta ajiye abun hannunta kusa da ita tace "Gashi Hajiya tace a kawo maki" Hajiyar tace "To maa sha Allah, nagode kwarai Allah ya basu xaman lafiya" Bude kofar parlon aka yi, wata yarinya ta shigo parlon cikin English wear bata ko kalli wa enda ke xaune parlon ba xata wuce sama Hajiya tace "Safeenah lafiya na ga ranki a bace" Jin sunan da Hajiyar ta kira Mujaheed ya daga kai yana kallon yarinyar, ita ba doguwa ba kuma ba gajera ba, farin ta har yayi yawa and she is beautiful, lkci daya ya dauke kansa, Maimoon da Imaan kuwa kamar sun samu TV imaan har da juyawa gaba daya tana facing dinta, rai bace Safeenar tace "Wai ki ji mum ashe birthday din ma wani local waje xa ayi, sai kinga yanda raina ya bace bayan duk shirin da nayi, wllh Saleema koluwa ce I don't know what's wrong with her, ni ko gaya masu na tafi ma ban yi ba" Mujaheed dai sai danna wayarsa yake, Hajiya tace "Atoh gaskiya basu kyauta ba, to why not baki ce masu a canxa hall din ba, ko ke ba sai ki biya kudin hall din ba" Tsaki Safeenah tayi tace "Ni duk raina ya baci wllh Mumy" xata wuce sama Hajiya tace "Toh ga doctor ku gaisa" Juyowa tayi tana kallon cikin parlon taga Mujaheed da ya ki dago kansa, ta fi second goma tana kallonsa, kafin ta karasa cikin parlon ta xauna hannun armchair da uwarta ke xaune cikin sanyayyen murya tace "Ina yini" sai a sannan ya daga kai yace "Lafiya lau, ya kike?" Tayi wani sanyayyen murmushi tace "Lafiya lau" Ta kalli su Imaan tace "Sannun ku" Imaan dai tace "Yauwa" Maimoon kuma ta gaisheta, Hajiya ta kwalo ma mai aiki kira ta fito da sauri, Tana kallonta tace "Pepper chicken da ku ka yi daxu xa ki kawo masu tun da ba ku gama lunch ba" Mujaheed yace "Daga gida muke yanxu Hajiya, we ate before leaving, so we are okay" tun da ya fara magana Safeenah ke kallonsa ko kiftawa babu har ya dasa aya, Hajiya tace "Wannan ae is more or less a dessert, daxu yara suka ce suna son pepper chicken, shine nasa su yi, kuma da yawa sosai suka yi don nasan baxa a cinye gaba daya yau ba sai dai a ba masu gadi da almajirai" Mujaheed ya d'an yi murmushi yace "Ni dai I am okay" Imaan tace "Ni dai xan ci" kallonta yyi da sauri, Hajiya tace "Yauwa, bar sa yayi ta fulako dama yayi kama da fulanawan, ke ma ai xa ki ci ko" Hajiya ta fadi tana kallon Maimoon, Murmushi kawai Maimoon tayi ta sunkuyar da kanta, mai aiki ta dawo rike da tray da plates uku a kai, ko wanne dauke da kaxa da aka yi garnishing sai kamshi da turiri yake, Mikewa Safeenah tayi ta dau plate daya ta karasa kusa da Mujaheed ta ajiye masa, hada ido suka yi yace "I said I am okay baxan ci ba" tace "Kaci ko kadan ne pls" Daga haka ta koma ta xauna, a hankali Imaan ta xamo kasa ta fara cin kazar, sai kallonta Mujaheed yake ta gefen ido, Maimoon ta dau tsoka daya daga kan kujerar tana ci a kunyace, Hajiya tace "To ya aikin doctor, Hajiya Rukayya tace min ka dawo Kaduna da aiki gaba daya yanxu koh?" Yace "Ehh" tace "To da kyau, Allah yayi albarka" yace "Ameen" idonsa na kan wayarsa amma da ya dago sai yaga kallonsa Safeenah take, Hajiya ta mike tace "Toh bari in d'an shiga ciki...." Mikewa yyi da sauri yace "Wucewa xa mu yi ai, xan je gun aiki" tace "Da wuri wuri haka, ka dai ki shan ko ruwa ne kuma ban ji ddi ba" yace "Am sorry bana jin cin komai ne yanxu" Tace "Toh ai sai ka jira kanninka su gama tukun na ko?" Yace "Bana son in makara xuwa gun aiki ne Hajiya" tace "Toh shikenan, bari a masu take away da shi" Imaan tace "Toh" wani kallo Mujaheed ya dinga mata, Hajiya ta kwalo ma mai aiki kira ta sanar da ita tayi masu takeaway din kajin, Imaan ta mike tace "Ina xan wanke hannu" Safeenah ta nuna mata hanyar dinning ko kitchen, tare suka tafi da Maimoon suka wanke hannu suka dawo, Hajiya ta basu dubu biyar Maimoon ta amsa da kyar, tuni Mujaheed ya fice gidan suka bi bayansa, Hajiya ta kalli Safeenah tace "Baxa ki raka su ba" bin bayan su tayi ita ma. Mujaheed har ya shiga mota sai ga ta tare da su Maimoon, tana kallonsa tace "I don't even know ur name" ba tare da ya kalleta ba yace "I am Mujaheed" tace "That's nyc, I am Safeenah" kai kawai ya gyada mata, Tace "Toh sai yaushe?" Yace "Watarana" yar siririyar dariya tayi tace "Do you mind sharing your digit with me pls?" Yace "Ohk" mika masa wayar hannunta tayi ya amsa ya sa mata lambarsa da bai fiye amfani da ba ya mika mata, tace "Thank you" yace "You are welcm" Daga haka ya tada motarsa ya wuce, haka ta bi motar da kallo har ya fita layin, da sauri ta koma ciki tana kallon uwarta tace "Wllh Mum naji ina son sa sosai" Uwar tace "Haba, to ai shine wanda na maki magana a kai kwanaki kika ce ke ba ruwan ki da hade hade in rabu da ke, uwarsa ce dama ta kawo shawarar ba ni ba tunda nasan kina da samari iri iri" ta marairace tace "Mum ai ban san haka yake ba, ni wllh mum ina son sa har raina" Hajiya tace "To ai shikenan, bari anjima sai in kira mahaifiyar tasa dama kwanaki duk ta dameni da kira a kan hakan bana daukan kiranta" Safeenah ta sauke ajiyar xuciya ta xauna tace "kaiii... Ya hadu wllh, his beards are damn cute, his lips so sexy with those catlike eye, gashi dogooo, I guess he have got six packs daga ganinsa yana workout, dama kuma ni bana son namiji fari pau, wllh Mum gayen ya hadu sosai, kuma naga sai wani basarwa yake yana shan kamshi, to ai irinsu nake so" Tun da Imaan taga irin kallon da Mujaheed ke mata bayan sun dau hanya ta kagu su isa gida ta fice daga motarsa tayi ta kanta, gashi dama so take suna komawa gida ta dau Atm card ta tafi supermarket siyo ma Sadeeq abinda ta masa alkawari jiya, a kofar gida Mujaheed yayi parking tana jin ya bude lock din motar ta bude ta fita da sauri, fitowa yayi shi ma bai kai ga bin ta ba tayi tuntunbe bakin gate sai ga ta a kasa, d'agata yyi ta fashe da wani matsanancin kuka tana cewa "Wayyo yaya kafana ya gurde wllh" maidata gun motar yayi fuska daure ya daga kanta yace "Waye kika fita wajensa shekaranjiya da daddare" k'in cewa komai tayi sai kukan da take tana kiran daddy a tsorace, ya wani hade rai cikin tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba?" Still taki cewa komai xuciyar ta Sai bugawa yake, murda kunnenta yyi da karfi yace "Are you daft" ta kara rushewa da kuka tace "Don Allah kayi hakuri" yace "Waye shi" cikin kuka tace "Nima ban san shi ba yaya" Ji yake kamar ya sauke mata mari ya dinga mata wani kallo xuciyarsa na tafarfasa, he is just trying hard to control his temper, strictly yace "Toh daga yau Imaan, I mean daga yau.... na sake ganin ki da wani a tsaye wllh sai na kusa sumar dake a gidan nan I promise you that, ba ciwon jiki ko Asthma ba, idan ma jini ke xuba ko ina na jikin ki wllh sai nayi abinda na maki alkawari, ke har guda nawa kike xaki ke tsayawa da namiji jikin mota? How old are you??" Kuka kawai take tana kallonsa duk jikinta na rawa don ta dade bata gansa cikin yanayin nan ba, ya mata tsawa yace "Baxa ki bani amsa ba sai na gaura maki mari?" Cikin rawar murya tace "Ba na kusa 18 ba...." Rankwashi ya kai mata ta dafa wajen tana kiran inna a rikice, yace "In sake ganin ki da wani a waje, sai kin raina kanki wllh" daga haka ya saketa ya rufe motarsa, ta wuce ciki da sauri bata xame ko ina ba sai part din inna, xubewa tayi kan kujera tana rusa kuka, Inna ta fito daki da gudu tace "Na shiga uku me ya same ku a hanya, ko hatsari ku ka yi??" Imaan ta mike xaune cikin kuka tace "Yaya ne ya rankwashe ni kuma ya ja min kunne ni ban masa komai ba innaa" Inna ta xauna kan kujera tayi tagumi a hankali tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, Wannan yaro dai ya isheni a gidan nan wllh, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, A kan wani dalilin kuma ya cuce ki, me kika masa?" Xata yi magana sai ga shi ya shigo, kin cewa komai tayi sai shessheka take hawaye na bin kuncinta, inna tayi mitsi mitsi da ido tace "Mujaheed kana manta cewar akwai hisabi koh, kana mance akwai lahira koh, ni ina jiye maka kada wataran ka karasa gawar da ba taka ba a gidan nan, idan abu ya sami yarinyar nan gaskiya xan rufe ido in mance ni na haifi Ahmadu in maka tijara kotu ta raba mu Mujaheed," Yace "Toh yanxu ma ki tashi a tafi kotun mana, duk ke ke karanta mata tsayawa da samari tun bata kai ko ina ba a titi, idan aure take so ae sai ta sanar da Abbanta ayi mata ba ta dinga tsayuwa da maxaje ba tare da saninsa ba, ita har nawa take, ni nasan wlh Abbanta bai sani ba, halan Ummi bata bata labarin abinda na mata kwanaki ba" Inna ta saki baki tana kallon imaan dake shessheka a hankali, can tace "Amma gaskiya ke munafuka ce Imaan, samm baki da hali, banda munafurci ya xa ayi kiyi sabon saurayi amma kiyi ta nuku nuku kina boye min?? me xai bani da Allah bai ban ba, shi kuma gantalallen bai san kakarki na da rai bane da bai taba cewa xai shigo gaisheni ba? Ko uwar ki ce tace ki boye min ban sani ba" Mujaheed ya dinga kallonta da mamaki, rai bace inna tace "Toh ni dai ba ruwana, dama ana boye abun arxiki irin wannan Ashe, me na maki da xaki boye min sabon saurayin ki Imaan?"Juyawa Mujaheed yyi ya fice daga parlon, Imaan ta kyabe baki tana share idonta tace "Shi fa bai san ko waye ba xai wani dinga ce wa saurayina, ni dai wllh inna ku ce masa ba ruwansa da ni a gidan nan" inna tace "Atoh dama meye hadin ki da shi, kawai ni dai nasan ubansa wan ubanki ne kuma duk ni na haifesu, to bayan wannan bbu abinda ya hada ki da Mujaheed ba dangin iya balle na baba, ke dai kawai ki rabu da shi ya ji da wawancin sa kiyi ta kan ki, banda fitina ma ina ruwansa da lamarin rayuwarki, idan ma saurayin kika yi baki isa ba ne, ko idan kin rasa mijin aure astaghfirullah shi xai aure ki ne?? kar ki sake saurarensa duk saurayi ya kira ki shirya ki fesa turare ki tafi, wa xai xauna biye ta Ahmadu da Bukar ga d'an su ma ya dauko hanya, bokon jaraba kawai ni wllh kina gama sakandari aurar da ke xance ayi mijin yaji da lalurorin ki d'a na ya huta haka shi ma" imaan ta mata wani kallo ta mike tana goge guntun hawayenta ta fice a parlon. Da yammacin ranan daddy ya gama shirin komawa Abuja ya tafi yi ma Inna sallama, ta gama goge gogen da ta ke ta dawo ta xauna tace "Tafiyar na nan yau din kenan" yace "Ehh, jirgi xan bi kada jirgin ya tashi ba ni" inna tace "Toh Allah ya tsare, amma xaka tafi kuma ya xancen da ku ka min kai da Ahmadu jiya?" Daddy yace "Na me fa?" Inna tace "Tafiyar yaran nan su je gaida Hansatu mana" Daddy yace "Ehh Barrister yace xuwa satin da xa a shiga sai su tafi" inna tace "Ehh gwara su je, duk da dai uwarta axxaluma ce amma ina mata fatan Allah ya ji kanta na kuma yafe mata, amma gaskiya shari'ar mu sai a lahira, don ta cutar da ni...." Daddy yace "Haba inna, bayan kuma kin ce kin yafe" a fusace inna tace "Toh ai Allah ba axxalumin bawansa bane, don na yafe ai a duniya nake nufi ba a can ba, kai baka san komai ba wllh, kaga irin abinda uwarta tayi min ne, kishi dama hauka ne, ni dai kawai albarkacin marigayin uban ku yasa nake barin ayi xumunci da 'ya yan da ta mutu ta bari ma, kuma duk yaran ba xuwa gaida ni suke ba" Daddy yace "Ke fa kika ce kin yafe xuwan, kowa ya xauna inda yake" Inna tace "Toh idan bance haka ba ya kake so ince, kai so kake su xo su sa ma kai da d'an uwanka ido, yanxu da ake nisa nisa ba ya fi ba, babu wanda yasan halin da wani ke ciki, sai ku dinga wata magana kai da Ahmadu don ba ku aka cuta ba, yanxu kishiyoyin da bani da hakkinsu ba gashi duk sun mace sun bar 'ya ya duk a gantale ba, to me xa su xo su min bayan ga nawa 'ya yan... Ku uku wllh kun isheni xaman duniya ita ma Hadiza tace ta kusa dawowa kasar nan gaba daya, to me xai dameni, a hada masu goma ta arxiki aje dai a gaishesu, har shi wancan katon Balan dake Abuja su karasa su gaida shi, ba komai Allah ya ba mu lada su kuma aniyarsu ta bi su" Daddy yace "Bari in je inna, Mujaheed xai kawo maki sako anjima" tace "Toh Allah ya tsare, yayi maka albarka, ya kare ka duk inda xaka shiga" yace "Toh Ameen nagode" daga haka ya fita parlon, part dinsa ya tafi suka yi sallama da Ammi yace "Gobe dai Imaan ta tafi islamiyya, xuwa Wednesday nasan xa su yi tafiyar, before than Dr dinta xai kawo mata drugs dinta coz ya dawo" Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye hanya ya tsare, ko in taso ta?" Yace "A'a bar ta" daga haka ya nufi kofa ya fita, Yusuf ne ya kai sa airport. Mujaheed ya daga kai yana kallon Abbansa bayan ya gama maganar da yake, a hankali yace "Abba kaga ba a dde da transferring dina nan ba da har xan fara daukan leave gun aiki...." Abba yace "You are just lookin for excuses, na lura gaba daya baka son tafiyar Muhd" ya sunkuyar da kai yace "A'a ba haka bane Abba, kawai naga...." Abba ya dakatar da shi yace "Toh xan ma boss din naka magana" da sauri ya dago yana kallon Abba amma bai ce komai ba, Abba yace "Beside idan ku ka tafi Wednesday xuwa Friday ai kun dawo, nan nan sulejah dai" Mujaheed bai ce komai ba still, jin Abba ma yyi shiru yace "Toh Abba kasan yanayin jikin Imaan, har da ita xa mu je?" Abba yace "Toh ba ga ka ba, you just go with first aid box" Mujaheed yace "Toh shikenan" Abba yace "And ina son dama muyi wata magana Mujaheed" Mujaheed yace "Ina ji Abba" Abba yace "Its high time you think of settling down with a family Muhd, naga baka san shiru ba kai, idan na kyale ka a haka xa ayi ta tafiya, duk abokanka sun yi aure with kids, not even kid, to kai me kake jira son?" Ya shafa kai a hankali yace "Abba warce nake nema tana karatu ne, amma ta kusa karewa nan da 'yan watanni in sha Allah" Abba yace "Yar ina ce?" Ya d'an yi murmushi yace "Nan Kaduna, a hayi iyayenta suke amma tana gun yayarta a Unguwar sanusi" Abba yace "Toh maa sha Allah, hakan yayi kyau sosai, but I think it's better a fara magana tun yanxu...." Muryar Umma suka ji tace "Babu maganar da xa a fara Alhaji" duk suka daga kai suna kallonta ta karaso cikin parlon, bacin rai karara fuskarta tace "Yanxu ni xaka munafurta Mujaheed, haka muka yi da kai, to kasani wllh idan ina numfashi a doron kasa baxa ka auri yarinyar nan bar, idan kuma kana son ganin ba dai dai ba a lamarin ka kaci gaba da alaka da matsiyaciyar yarinyar, ina zamana ka dauko mun talauci a matsayin surka, to wllh kayi kadan gwara kayi ta xama ba auren ya fi, ga yarinya mai hankali mai natsuwa Safeenah yar wajen Hajiyan Marafa can na nema maka yarinyar kuma tayi mugun na'am da kai xaka toxarta ni ka maidani karamar mutum a idonsu???" Abba yace "Abinda nake son in fara fahimta a nan shine, la6e kike min Rukayya?" Umma ta tabe baki tace "Idan ma la6en nayi Allah ne yasan bani da hakkin kowa shi sa har ya bani ikon labewan in ji komai, Alhaji wato idan Kasan talauci to a kan yarinyar da iyayenta ya kare, can wani ghetto fa suke, to idan ba toxarta mu Mujaheed ke son yi a idon jama'a ba ina shi ina yarinyar nan, Kyan banxa kyan hofi, yo ina ma take da kyan ita ba wai fara ba, gaskiya kayi min iyaka da Mujaheed kada in nuna masa 6acin raina a gidan nan, sam