Showing 66001 words to 69000 words out of 139381 words
bata gaya min ba, she told me everything" Ta xaro ido kawai ta katse wayar ta fashe da kukan takaici, duk kiran da ya dinga yi kin dagawa tayi daga karshe ta shige daki ta kwanta kan gado bata fasa kuka ba. Bayan Isha jin ana knocking Ammi ta sa Hijab ta nufi kofar ta bude, Abba ta gani tsaye da Mujaheed ta ba su hanya tace "Ina yini Alhaji?" Ya shiga parlon Mujaheed na biye da shi ya xauna yace "Lafiya lau Aisha, ya mai jikin?" Xaunawa tayi ita ma tace "Da sauki Alhmdllh tana daki" Mujaheed bai yarda ya kalleta ba yace "Ina yini" tace "Lafiya" Abba yace "Ko bacci take?" Ammi ta mike tace "Anya kuwa...." Mujaheed dake tsaye dama bai xauna ba yace "Bari in dubata" Har xata dakatar da shi sai ta ji kunyar Abba, ta dai bi sa da hararan gefen ido don ko kadan bata so tafiyarsa dakin ba, murda kofar bedroom din yyi ya shiga ciki, tana xaune gaban mirror daga ita sai towel tana shafa lotion a duk jikinta, duk tunaninta Ammi ce ta bude kofar don bata ko kalli direction din kofar ba, jin shiru ta daga kai tana kallon kofar ta madubi, tsaye yake yana kallonta, suna hada ido yayi saurin dauke kansa, ta xaro ido tana gyara daurin towel din tace "Yayaaa" Mikewa tsaye tayi ta juyo tana kallonsa kafin tace komai calmly yace "Abba na jiran ki a parlor" bai jira cewarta ba ya fita dakin ta bi sa da kallo tana turo baki, Mujaheed na duban Abba yace "Tana xuwa abba" Abba yace "Ohk" Hijab ta sa har kasa ta fito parlon, ta gaida abba da murmushi fuskarta yace "Ya jikin mamana" tace "Abba ai na ji sauki" yace "Toh Alhmdllh, Allah kara lafiya" tace "Ameen" Abba yace "Ga watermelon nan you take much of it kin ji" a hankali tace "Toh nagode Abba, but...." Sai kuma tayi shiru, yace "But what?" Ta boye fuskarta tace "Abba ina son cin suya" Abba yace "Toh Mujaheed xai siyo maki yanxu" Mujaheed ya kalleta ta gefen ido irin kallon harara, Tana murmushi tace "Toh nagode Abba" daga haka Abba yyi ma Ammi sallama Mujaheed ma yyi mata suka fita. Abba yace "Idan mun fito part din inna sai ka tafi ka siyo mata, there is still time ai" Mujaheed yyi kasa da murya yace "Abba yanxu tare xa mu gun innan?" Yace "Of course, ban san urgent kiran da take min ba, it might even be something that isn't worth the call" Mujaheed yyi yar dariya yace "Dama xaka ga it's nothing that important...." Abba yyi murmushi yace "But we still have to listen, gudun matsala" Suna shiga parlon Inna ta shafe addu'ar da take kan darduma tace "Har ka iso kenan Bukar, to shi kuma wannan jelan da ya biyo ka fa?" Dariya Abba yyi ya xauna yace "Aa mun shiga duba mamana ne shine muka karaso nan din tare" tace "Atoh na gansa wani sandan sandan kamar basamude a bayanka" Mujaheed dai sae hararanta yake k'asa k'asa, tayi kasa da murya tace "Kana ji na Ahmadu?" Abba yace "Ina jin ki" tace "Kaga kujeran can da Mujaheed ya xauna?" Kai ya gyada mata yace "Na gani" tace "To wllh tllh a kai Bulasawa ya xauna" da mamaki Abba yace "Bulasawa kuma?" Tace "Eh, amma d'an sa ba shi din ba" Abba yace "Tohhhh.... a ina ya san ki?" Ta daga hannu da sauri tace "A'a ni bai san ni ba, a titi muka hadu yau kuma muka fahimci juna kwarai da gaske..." daga Abba har Mujaheed kallonta suka tsaya yi without blinking, can Mujaheed ya girgixa kai planning to get up and leave the parlor yaji tace "Ashe wai saurayin 'yar ka ce Imaan, amma algungumar bata ta6a sanar da ni ko da wasa ba, a wajen na gansu tsaye jikin santalelen motarsa, in gaya maka taji kunya tsamo tsamo da ta gan ni, ni dai ban kulata ba bakina a leko na taso keyarsa muka shigo cikin gida, d'an wajen Amadi Bulasawa mai gidajen man fetur sun fi dubu a arewa fa Ahmadu" dakatawa Mujaheed yyi da sauri ya juya yana kallonta, Abba na gyada kai yace "Tohh da kyau hakan" Inna tace "Kai fa kasan da kyau yaro, wato idan Allah yyi auren har kasan waje fa sai an fitar da ita an juye duk gurbatattun jinin jikinta dake ja mata lalura a sauya mata sabo, sannan kasussukan jikinta su ma duk sai an ce xa a sauya su ta rabu da ciwace ciwace na har abada, kasan fa bbu abinda turawan nan basa iyawa in dai da naira, to ga naira dai faca faca ta samu, ae ni bayan fitarsa sai da nayi ya ma ake kiran sujjadar nan na godiya ga Allah?? To ni dai nayi wllh kuma na dade goshina a kasa" Dariya kawai Abba yake yana kallon mahaifiyar tasa, Mujaheed dae sai juya counter din hannunsa yake, inna ta marairaice tace "Ahmadu ka rufa min asiri ba abun dariya bane wannan, sannan yaron fa duk ya damu wai xai turo magabatan sa nan ba da dadewa ba ayi xancen aure, kasan su kuma manyan mutane basa son kwalo kwalo kada a bari wannan yaron ya kubce ma jikata in shiga uku gaskiya" Juyawa Mujaheed yyi ya dinga kallonta, Abba yace "Haba maganar aure kuma Inna, ko secondary fa bata gama ba" Inna ta wani tsuke fuska cikin d'aga murya tace "Allah ya tsine ma sakandarin, sakandarin banxa ga abun arxiki kana xancen sakandari, ko a gidansa wllh xai bari ta karasa, baka gansa ba dogo yanda kaga wannan mutumin dake kusa da kai a xaune, shi ma da kyar idan baya daga karafunan nan na turawa don kirjinsa duk a tale, kana ganinsa kaga d'an boko don gilashi ne ma a idonsa, toh irin wannan ne baxai bari ta karasa sakandarin jaraban ba idan anyi aure, gaskiya Ahmadu ku maida hankalin ku sosai a kan maganar nan da nake gaya maka, wllh kullu yaumin fargabana mijin da Imaan xata aura tunda ga yanda Allah ya halitto ta, mai rufin asiri kadai baxai iya da lalurorinta ba sai hamshakin mai kudi, da yau ace Bukar ya tara yara kamar yanda ka tara to fa da imaan bata kai labari ba don nasan ba xai tara uban kudin da xai dinga kashewa kan ciwonta ba, to astagfirullah kaga amfanin haihuwan kadan ba da yawa ba, to yanxu dai ga yaro matashi kyakkyawa d'an masu kudi ya fito, bari ma kaga abinda ya ban Ahmadu"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment grouAbba na kallon Daddy yace "Kada kayi ma Imaan magana tukun, I want to confirm who the guy is from Yusuf, Mujaheed yace baxai rasa sanin sa ba" Daddy yace "Toh shikenan, amma I will so deal with her, ita har nawa take xata fara kula samari can you imagine?" Abba yace "Nace kar kace mata komai tukun, ni nasan abinda xan yi" Daddy bai iya yace komai ba, don gaba daya ransa ya gama baci, suna isa part dinsa ya shiga, Abba kuma ya karasa nasa part din. Direct bedroom din Mujaheed Abba ya tafi ya bude kofar, Mujaheed na xaune tare da Umma a dakin ya sunkuyar da kai yana saurarenta, Umma na ganin Abba tayi shiru daga abinda take cewa, Abba yace "Ka sameni parlor Muhd" a hankali Mujaheed yace "Toh Abba" daga haka ya rufe kofar, Umma tace "Wai me ke faruwa, jiya naga mood dinsa gaba daya sai a hankali, halan tsohuwarsu ce ta tada wani fitinar?" Murmushi Mujaheed yyi yace "Ehh.." Umma ta buda ido sosai tace "Wai me take so?" Kamar Mujaheed baxai ce komai ba sai kuma yace "So take ayi ma Imaan aure" Umma ta xauna da kyau da mamaki tace "Aure kuma? imaan din saurayi gareta da xa a mata aure? Ko tana da yaron da xata hada ta da shi ne?" Mujaheed ya d'an yi shiru sannan yace "Ban sani ba Umma" Umma ta hade rai tace "Baka sani ba duk kusancin ka da inna, ko dai gaya min ne baxa ka yi ba??" Ya girgixa kai yace "Umma ni bata gaya min komai a kai ba" Tuni mood din Umma ya canxa, Mujaheed dai kallonta kawai yake, Tabe baki tayi tace "To ma gani ai, yanxu dai xaka yi transfer din ne ko Safeenar xaka ma?" A hankali yace "Anjima xan maki Umma" ta mike tace "Toh ina jira" daga haka ta nufi kofa ta fice dakin, Dafe kansa yyi na kusan minti daya, can dai ya tashi ya tafi parlon Abba. Abba na kallonsa yace "Mun gama magana da Yusuf yanxu a waya yace bai san yaron ba, so what I want you to do now is ka samo min number sa a wajen Imaan, but ita kanta bana son ta san ka dau number yaron, do it wisely" Shiru Mujaheed yyi, Abba yace "Yea just get his digit by any means without her knowledge" Yace "Toh Abba" Abba yace "I want it before the end of today" yace "I will do that in sha Allah" Abba yace "Xaka iya tafiya if u have anything doing" mikewa yyi ya fita, Umma ya gani sanye da Hijab ta rike purse ta nufi kofa, ko lura da shi bata yi ba har ta fita, ya bi ta da kallo sannan ya wuce sama . Imaan na xaune kitchen tana kallon Ammi dake kwashe girkin da tayi a warmer, Ammi tace "Kafin Magrib idan ban dawo ba sai ki kai mata" Imaan dai bata ce komai ba, bayan Ammi ta gama tana kallonta ta marairaice tace "Ammi amma me yasa baxan bi ki ba plss" Ammi tace "Nace ki bari lahadi idan kin dawo islamiyya kije, yanxu akwai mutane da yawa a gidan you will be uncomfortable" a hankali tace "Toh Ammi" Ammi ta fita kitchen din ta mike ta bi bayanta, Hijab Ammi ta sa ta shiga parlor gun daddy tace "Yallabai xan je xa mu amshi lefen Halima" Daddy yace "Ohk xan je cikin gari dama, let me drop you" Imaan ta turo baki ganin ita kadai xa a bari gida, kamar xata yi kuka tace "Daddy in raka ka?" Wani kallo da ya tsorata ta ya maka mata yace "You are stupid" sunkuyar da kanta tayi ta juya ta wuce daki, Ammi ta hade rai tace "Ni ban gane haushinta da kake ji ba tun daxu, ka kuma ki gaya min me ke faruwa" Yace "Madam dauko min makulli a daki and stop questioning me" daga haka ya fita parlon, tabe baki tayi ta tafi ta dauko masa makullin, dakin Imaan ta leka ta ganta xaune gefen gado tace "Ki tashi kiyi sllh sai ki sa kallo ko a daki ne kiyi" daga haka ta rufe mata dakin, kusan tare suka Isa parking space da Mujaheed, kansa a kasa ya gaida Daddy, daddy ya amsa yace "Ya aikin?" Yace "Alhmdllh, xa ku fita ne Abba" Daddy yace "Ehh xan je cikin gari ne" Ammi ta hade rai ta bude front seat ta shiga, Mujaheed dai bai yarda ya kalleta ba dama, daddy yace "Toh sai na dawo" Mujaheed yace "Toh a dawo lafiya Abba" daga haka ya bar wajen yana d'an murmushi, dama tun safe yake tunanin yanda xai hadu da Imaan har ya dau lambar Sadeeq, kan farin kujera ya tafi ya xauna har Daddy ya fita gidan, bayan kusan minti biyar ya mike ya nufi part din nasu, murda kofar yyi a hankali ya shiga ciki yana kallon parlon ya ga bata ciki, ya jawo kofar ya rufe ya nufi bedroom dinta, tsaye yyi bakin kofar kafin ya murda gently ya tura kofar, bai ganta dakin ba ya d'an yi jim, running tap ya ji a bathroom ya gyada kai, ya tafi gaban madubi ya dau wayarta dake ajiye xai yi silencing wayar yaga ma a silent yake, ya xura a aljihu sannan ya karasa kofar bayin ya makale jikin bango, Imaan ta gama alwalan da take ta bude kofar bathroom din ta fito, ji tayi an cafketa ta baya, ta fasa wani ihu a raxane ya jawo ta jikinsa ya riketa gam, kafin ma ya kai ga cewa komai ta gane shine saboda scent dinsa, k'asa cewa komai tayi ta dinga numfashi a tsorace don tayi mugun tsorata, bayan few seconds numfashinta ya dawo dai dai, juyo da ita yyi yana kallonta yace "Anjima Abba xai kira ki, kin dai ji abinda nace maki daxu koh?" Kin cewa komai tayi, ya hade rai yace "Ba magana nake maki ba" tace "Naji mana" Saketa yyi ya nufi kofa, ta murguda baki tace "After all he is just a frnd, and he is...." juyowa yyi da sauri yana kallonta, tayi maza ta shige bathroom ta sa key.
Mujaheed ya koma inda yake xaune ya fiddo wayar nata a aljihu ya shiga call log, bai ga wasu calls ba sai na Daddy sai wani number da bata yi saving ba, ya dinga kallon Number kafin yyi dialing, katsewa aka yi sai gashi an kira, ya daga ya kai kunne yyi shiru, daga daya bangaren Sadeeq yayi sallama, Mujaheed ya cire wayar a kunnensa ya katse kiran ya ciro wayarsa ya kwashe number sannan ya danna ma number block ya goge log din kiran a wayar gaba daya. Imaan na idar da sllh ta debo chocolates ta xuba su kan gadon ta sannan ta kunna kallo ta kwanta tana shan chocolates tana yi, ta fi minti talatin tana kallo ta tuna Sadeeq ya kira ta tun daxu bata dauka ba, mikewa tayi xaune da sauri tana kallon gaban madubinta don nan ta ajiye wayar, da mamaki ta karasa wajen mirror din idonta a kan inda ta bar wayar ganin babu shi, lkci daya Mujaheed ya fado mata, ta xaro ido tana fatan ba shi ya dauka ba, duba dakin ta shiga yi amma ba alamar waya, kamar xata yi kuka ta dau Hijab ta sa ta fita, bata tsaya ko ina ba sai part din su, Babu kowa parlon gidan tsit don har sannan su maimoon basu dawo ba duk da ta ji alamar akwai mutane a kitchen, ta wuce sama cikin sanda tana waige waige, tana ta tsaye corridor tana kallon kofar dakinsa, karasawa tayi ta murda kofar a hankali ta tura, ba kowa dakin sai kamshi me dadi dake tashi, ta karasa ciki da sauri tana kalle kallen dakin, wayarsa ta gani gefen gado amma bata ga nata ba, dauke wayar tayi ta boye cikin Hijab ta fita da sauri, da gudu ta karasa part dinsu ta shige parlor ta sa makulli tana turo baki, xaunawa tayi tana kallon wayar ta bude taga ba lock, gallery ta shiga ta ci karo da hotan Farida a WhatsApp images, ta shiga wajen, duk yawanci hotunan farida ne ta ajiye wayar ta kunna TV nan parlor ta kwanta kan kujera ta ci gaba da kallonta. Mujaheed na kallon agogon wrist dinsa yace "Aunty xan wuce aiki yanxu..." Aunty dake hada stew tace "Toh Allah ya kiyaye" fita yyi daga kitchen din ya wuce sama ya shiga dakinsa, makullin mota ya dauka ya kara feshe jikinsa da turare, ya juya xuwa saman gado xai dau waya yaga babu, da mamaki ya dinga kallon inda ya ajiye wayar, ya fito ya duba dakin Aunty ko ya mancesa a ciki ne yaga babu, fitowa yyi daga dakin yana sauka stairs yyi still a zuciyarsa yace Imaan, to yaushe ta shigo?? karasa sauka yyi ya fita parlon dai dai shigowar daddy compound din da mota, a hankali yace "Shit" Ya tsaya har Daddy ya fito daga motar, ganin leda a hannunsa ya karasa da sauri ya amsa yana masa sannu da dawowa, daddy yace "Thanks Muhammad, Barrister ya dawo?" Mujaheed yace "A'a bai dawo ba" a tare suka karasa apartment din Daddy dake amsa call da ya shigo wayarsa, Daddy yyi knocking, Imaan dake kwance ta mike xaune da sauri tana xaro ido tace "Waye wannan?" Daddy yace "Open the door" tashi tayi ta bude kofar, Daddy ya ci gaba da wayar da yake, ta wani xaro ido ganin Mujaheed ta juya da sauri ta koma ciki, Mujaheed ya saci kallon Daddy sannan ya shiga, Har ta dauke wayar nasa da ke ajiye kan kujera xata gudu ya fixgota, ba daman tayi ihu hakan yasa ta gatsa masa cixo a hannu da duk strength dinta, ba shiri ya saketa, da gudu ta nufi dakinta, sai a kan idon Daddy da ya shigo ya dinga kallonta da mamaki yace "Zo nan Imaan, whats wrong with you?" Kamar xata yi kuka tace "Daddy yaya ne" Mujaheed ya kasa daga kai ya ji kamar ya nutse a wajen, Yyi saurin ajiye ledan hannunsa yace "Abba xan wuce gun aiki" bai jira cewar daddy ba ya nufi kofa ya fita. Da Magrib imaan ta tafi kai ma inna abinci bayan ta sake boye wayar Mujaheed da kyau, duk kiran da aka dinga masa na Farida kawai ta daga, tun da ta fito compound dama gabanta ke faduwa, da sauri sauri ta karasa part din Inna, Yusuf ta gani xaune, ta wara ido ta ajiye abincin hannunta tace "Lahh ya Yusuf yaushe ku ka dawo?" Ya kalleta ya d'an yi murmushi yace "Daxu..." Inna tace "Baki ga da ya shigo ba daxu duk a kode wllh, ai yanxu ya washe a haka, Allah ya rufa ma ke da Mujaheed asiri ba ku je ba, baku da rabon wahala, amma wannan garin ae ba wajen xuwa bane tirr" Imaan ta duka kusa da shi tana dariya tace "Toh me ka kawo min ya Yusuf" ya shafa kansa bai ce komai ba, Inna tace "Yauwa ina maka xancen kirki kafin wannan mata ta shigo..." Ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "Ae ina ji" tace "Ko kai ya ka gani, wannan