Showing 123001 words to 126000 words out of 139381 words
daya ta tsuke fuska, Inna ta xauna tana kallon Abba tace "Toh Ahmadu yau dai sai ka xaba ko ni ko matarka Rukayya...." Sai a sannan Abba ya dago kai yana kallonta, Inna tayi mitsi mitsi da ido tace "Kuma aure na samu labarin xabinta ce yarinyar ba xabin Mujaheed ba don haka daurin aure ya fasu in dai ni na haife ku" Abba ya girgixa kai ya ma rasa abinda xai ce, daddy ya d'an sauke ajiyar xuciya gently yace "Amma me ya faru Inna? Meye musabbabin matsalar?" Wani kallo Inna ta jefa masa ta kankance ido tace "Dama wannan ya xama maganan ka ta farko kuma ta karshe a parlon nan, don ni ban san ma wa ya gayyato min kai ba, abinda ya faru kuwa shine yau har uwata dake kabari sai da Rukayya ta xaga a kan shegiyar shinkafa, har tana neman dunguri na, ga rawa da ta dinga yi a gabana tana min murgude murgude da kawayenta wai su fitsararrun yan tasha, daga fa mun je amso ma bakin mu da ta Rasulu shinkafa, xagi ta uwa ta uba dai yau mun sha sai godiyar Allah..." Girgixa kai kawai daddy yake yace "Ikon Allah" cikin rawar murya Inna tace "Toh ni yanxu na xuba ido in ga matsayina a wajen ku in ga matakin da xa ku dauko, ko kaffara baxan yi ba tun da Ahmadu yake ko kallon banxa bai taba ma Hadiza Uwar Rukayya ba, toh ni me na mata daga xuwa amsan shinkafan biki xata tsigaleni..." Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi tace "Me na ma Rukayya yau ta min cin mutunci wanda da wuya tabon ya goge a jikina" Ta Rasulu ta saki kukan ita ma tace "Me kuwa xa ki mata Asabe, ni ba don albarkacin ki ba nasan da yau sai 'ya yana sun turo motar sojoji an fitar da Rukayya gidan nan...." Inna ta dakatar da kukan da take da sauri tace "A'a yanxu ma bai baci ba Ta Rasulu, kira su su turo motar babu abinda ya sha min kai wacece kuma Rukayya ina ruwana da ita xata ci albarkaci na? Su kwasheta ba ruwana" Abba dai bai ce komai ba har sannan, can dai ya dau wayarsa ya shiga kiran layin umma, har ya gama ring ba a dauka ba, ya kalli Mujaheed da ke ta kallon inna yace "Tafi ka kira min uwar ka yanxu..." Mujaheed ya sunkuyar da kansa bai dai ce komai ba ya mike ya nufi kofa a sanyaye ya bude, karo ya kusa ci da umma dake labe tana sauraron komai, shi dai bai ce mata komai ba, har xai tsaya kawai yayi wucewarsa don bai ma son ransa ya kara baci, Sallama Umma tayi ta shiga parlon da lullubi kanta a kasa, Inna na ganinta ta saki salati tana tafe hannu tace "Almunafunfun kenan ku ke ga, to ai ba da gyale kika min cin mutunci a tsakar gida ba don haka sai ki cire ki ajiye a gefe a gama magana, kuma ni dai Allah ya isa rawan da kika dinga yi a gabana kina mokade mokaden maxaunai" Umma ta xauna nan kusa da kofa bata dai tanka ta ba, tana kallonsu Abba tace "Ga ni nan" Sai hararanta Mama Hadiza take, Abba na kallonta da kyau yace "Ita Innar kika xaga yau ko?" Ta Rasulu tace "Ta uwa ta uba kuwa, har ana rirriketa xata doketa, ni dai guduwa nayi na koma bakin gate, kawai 'ya yana su ji daga xuwa biki duka ya ritsa da ni" Abba na kallon Umma yace "Toh yayi kyau, ki tafi gidan ku yau, ko minti goma ban son ki kara a gidan nan...." Da sauri Inna tace "Aa baxa fa ta tafi da igiyar ka mai daraja ba tana galantoyi a titi, yanxun nan xaka datse shi ta tafi gidan nasu tsirara, sai kuma taje can ta dinga xagin uwarta mai ciwon kafa a kano..." Ta Rasulu tace "Ko ta koma wajen shafa mai shinkafa da wake a kasuwar tasha" Umma tace "Toh Alhmdllh xan tafi amma sai a barni in sallami bakina da suka xo biki ko xuwa da yamma" Inna ta mike tace "Wani biki? Bikin da aka fasa ko kuma wani daban kike nufi?" Kallonta umma tayi da sauri, Inna ta tabe baki tace "Ae babu xancen wannan auren, don baxa a ma jikana dole ba, maxa maxa a kira dangin shegun amaryar a sanar masu suyi hakuri Mujaheed yace ya fasa, in dai da raina wllh an fasa auren nan, ni ba ruwana" Abba yace "Bai kai ga haka ba Inna..." Katse da tayi tace "Ya kai har ya xarce Ahmadu" Daddy yace "Haba Inna, kananun mutane kike son ki maida mu, daurin aure nan da 'yan awanni kice a fasa???" Inna tace "Ba ruwana idan ma jarirai xan maida ku, daurin aure dai ni patuu nace bbu shi, idan kuma akwai wanda ya isa ya ja da ni to Bismillah...." Mama Hadiza sai gyada kai take don hka ya mata mugun dadi, a hankali Abba yace "Inna to bakin da suka xo daga garurruwa da dama don bikin fa? Ya xa mu yi da su?" Inna tace "Oho sai a nemi wata a daura auren da ita amma ba xabin Rukayya ba, babu kuma shegen da ya isa ya sa in canxa ra'ayi na gaskiya..." Ta Rasulu tana tabe baki tace "In har kuna son gamawa da Asabe lafiya ku bi abinda tace sau da kafa, jama'ah kuma da aka tara tunda abun kunya ku ke gudu sai a samo yarinya ko cikin 'yan uwana ne a daura auren kowa ya hutu" Inna tace "Shi kansa Mujaheed din ba son auren yake ba wllh wllh, idan kuma karya ne a kirasa a tambayesa a ji ta bakinsa, haka kawai xa a cutar min jika a masa auren dole abinda aka daina yayi tun lokacin kakata Furera...." Daddy yace "Toh gwara a kira Mujaheed din a fara jin ta bakinsa Inna...." Dakatar da shi Inna tayi tace "Ka karyata ubanka isuhu Bukar.... Kuma a kira Mujaheed din" babu Wanda yace mata komai a parlon, Umma dai tuni yan hanjinta suka kada ta fara matsar kwalla, idan aka ce an fasa auren nan da gaske ai an kasheta kenan balle ta san in sha Allahu sai anyi, cikin tsawa Inna tace "A kira Mujaheed din mana tun da karya nake" Mama Hadiza ce ta kira layin Mujaheed, yana dagawa tace "Ka taho parlon Inna yanxu" daga haka ta katse wayar, Inna dai sai girgixa kafa take, ba a dau lkci ba Mujaheed ya shigo parlon da sallama kansa a kasa, nan kusa da imaan dake xaune jikin kujera ya duka don babu waje parlon bai kuma son xama kan kujera, Inna na kallonsa tace "Tsakanin ka da Allah Mujaheed kana son auren yarinyar nan da Rukayya ke son hada ka da?" Shiru Mujaheed yyi yana kallonta, can ya saci kallon Umma dake kallonsa tana matsar kwalla, sunkuyar da kansa yayi, Inna tace "Kun ga munafuki koh??" Abba ya hade rai yace "Don't waste our time Mr Man" d'an murmushi yyi yana kallon Inna yace "Toh Inna da bana sonta ai baxan yarda da auren ba" Sake baki Mama Hadiza tayi tana kallonsa, Umma ta sauke boyayyen ajiyar xuciya, Inna ta saki salati tace "Jini ba wasa ba ni Asabe, Allah sarki Ahmadu kana cikin jarabawar ubangiji 'ya ya duk sun kwaso halin uwa...." Wani kallo Mujaheed ya dinga mata, Inna tace "Toh oho dai, da ka so yarinya da kar ka so ta duk uwasu daya ubansu daya, aure dai tunda aka xageni aka ci ma ni da aminiyata mutunci babu xancensa an fasa, sai dai duk abinda xai faru ya faru Babu kuma wanda ya isa ya canxa min ra'ayi ko waye shi kuwa, idan baku son a maku kallon kananun mutane kamar yanda ku ka ce sai a samu wata yarinyar a aura masa amma ba xabin Rukayya ba, xan nuna ma kowa ni jarababbiya ce yau" daga haka ta mike ta shige daki tana goge guntun hawayenta, Abba ya jinginar da kansa da kujera yana salati a ransa, Daddy kam sai girgixa kai yake ya rungume hannayensa, a hankali Imaan ta mike ta fita parlon Mujaheed ya bi ta da ido haka ma Abba da Daddy.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
[7/19, 5:15 PM] +234 803 603 7561: Daddy na kallon ta Rasulu a hankali yace "Yanxu Baaba don Allah baxa ki bata hakuri a daura auren nan ba saboda mutanen da aka tara??" Ta Rasulu ta xaro ido ta mike tace "Toh Asabe ga Bukar nan wai in baki hakuri a daura auren... da yake dama cikin 'ya ya ma akwai mai gudun bacin ranka akwai kuma wanda bai san ciwon ka ba kwata kwata, toh Bukar dai bai san ciwon ki ba, don da ya sani sai in da karfinsa ya kare a shakiyancin da Rukayya ta mana yau" Daga haka ta shige daki murya can kasa tana cewa "Ba ruwana.... Haka kawai ince Asabe ta hakura ta ji haushi na..." Mama Hadiza na kallon su Abba on a serious note tace "Wllh Yaya tun da Inna tace baxa ayi auren nan ba fa baxa ayi ba, nima kuma dama nace baxa ayi din ba, ba kuma abinda xai sa ayi, sai an nuna ma Rukayya duk fitinar uwar mu a haka muke sonta kuma babu shegen da ya isa ya taka mana ita ya xauna lafiya, babu shi a duniya wllh, tun wuri ku kira dangin amaryar ku sanar masu an fasa don su san nayi, tunda uwata tace baxa ayi ba baxa ayi ba, ni nayi Imani da Allah da kun ji irin cin mutuncin da tayi ma Inna yau baxa ma ku tsaya kuna bin maganar a sanyi sanyi ba, kuna shakku a ran ku, me aka yi aka yi Rukayya xata raina mana uwa mu kasa daukan mataki?? to wllh yau sai ta ga iyakarta sai dai idan ban haifu ba...." Tana kai wa nan ta mike a fusace ta fice a parlon, Umma ta tabe baki ta dauke kai, Mikewa Daddy yayi ya fice daga parlon shi ma, a hankali Mujaheed ya mike ya bi bayansa, Abba ya kalli umma da kyau yace "Ki bar gidan nan as soon as possible Rukayya bana son ganin ki..." tace "Toh xan tafi ai dama ba sai ka maimaita ba yallabai, amma dai kar ka manta yar gidan wacece Mujaheed xai aura, tsaf xa ku xubar da mutuncin ku da kimar ku a idonsu, da ma duniya gaba daya, barin kai da kake sanannen Barrister" tana magana tana matsar kwalla, har xata fita sai kuma ta tafi kofar dakin Inna, Bude kofar tayi ta durkusa tana goge kwallan idonta tace "Ina neman gafaran ku inna, ku yafe ni ku yi hakuri sharrin shaidan ne..." Inna ta mike a rikice tace "Auzubillahi, garin yaya aka bar ta taxo min nan ni Asabe, don Allah ki rufa min asiri ki fita ba don hali na ba, ki tafi don Allah Rukayya" Mikewa Umma tayi ta fita parlon....
Abba da Daddy ne xaune parlon Abba duk sun rasa abun yi gashi har sha biyun rana ya kusa, fasa aure gaskiya is out of the point yanxu, bai kamata bane kwata kwata amma basu san ta inda xa su billo ma al'amarin ba, Mama Hadiza ce ta shigo parlon da sallama ta dalilin kiranta da Abba yyi, Ta nemi kujera ta xauna tana kallon yayyin nata, Murya can kasa Daddy yace "Yanxu Khadija baxa ki taimaka ki ma Inna magana ta janye wannan batu na fasa aure ba, da dai ace daga wajen mu aka fasa daurin auren nan gwara hakan ya faru daga bangaren iyayen amaryar.... Ki dubi irin mutunta gidan nan da ake amma aga irin haka ya billo daga gidan, ga mahaifin yarinyar dattijon kirki ga kuma irin manyan mutanen da xai gayyato daurin auren nan, kaninsa kuwa wajen aikinsu daya da Sadeeq kuma suna mutunci....." Mama Hadiza ta katse sa tace "Toh ko in ja Innar mu tafi gidansu amaryar tayi abinda xai sa daga wajen su suce sun fasa daurin auren tunda dama kowa kallo masifaffiya mara hakuri yake mata?" A fusace Abba yace "Ji wata maganar banxa, kina ma da hankali kuwa Hadiza?" Mama Hadiza ta mike tsam tace "Ehh kwarai Ina da hankali Yaya, dama naga take taken ku, wato ku baku ma wani ji haushin abinda aka ma mahaifiyar ku ba saboda fitinarta ko, infact ba ku ma yarda cewar ita ke da gaskiya ba, to wllh bari ku ji in har baxa ku bi abinda tace ba toh ku xa ku yi ta ganin ba dai dai ba, ba ruwana, sannan duk fitinarta xan dauketa daga gidan mu tafi sai ku xauna da matanku ku ci karanku ba babbaka, ita ma Rukayyar sai ka ce ta dawo masifaffiya ta tafi" daga haka Mama Hadiza ta fice daga parlon a fusace, Daddy ya girgiza kai yace "Bata da hankali kwata kwata" Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Ni fa nasan duk abinda Inna ta fada Rukayya xata iya aikatawa, kuma ko wani hukunci tace in yanke mata yayi dai dai, amma not to the extent da xata ce a fasa daurin aure ranan daurin aure, meye laifin iyayen amaryar? Ina ce Rukayya ce ta mata laifi ba su, gaskiya Inna tana son ta samu cikin wani yanayi ne, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Daddy da yyi shiru yana sauraren yayan nasa yace "Ko xaka kira Bala da su Jibril su mata magana?" Abba yace "Sai kace baka santa ba ai ni har yanxu ban ga wanda ya isa ya sa Inna ta canxa ra'ayin nan ba sai dai wani Ikon Allah" Abba ya jinginar da kansa jikin kujera yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, where are we to start from coz gaskiya babu xancen fasa aure, duk hukuncin da tace ayi ma Rukayya xa ayi amma banda fasa aure don iyayen yarinya basu san hawa ba basu san sauka ba xa mu kunya ta su a idon duniya" Daddy ya tallabi chin dinsa thinking of a way out also. Karfe sha biyu Abba da Daddy da su kawu Bala da Jibril da wani kanin Inna da suke uba daya suka kara komawa bangaren Inna don su bata hakuri ta janye batun fasa auren Mujaheed da Safeenah, kora irin ta kare Inna ta masu da maficin hannunta, har kawu Bala na neman faduwa saboda saurin ya fita a parlonta, Inna ta rakosu har bakin pamponta tana huci tace "Munafukai kawai" Su dai basu juyo ba, amma daddy gaba daya ransa ya gama baci, Abba dai ne ke murmushin karfin hali, su Bala da Jibril ba bakin magana sai yan idanuwa, kanin Inna Alhaji Audu ne ya dinga cewa "Tun da muka fito lafiya Alhmdllh, Asabe ba kyau" Daddy na isa part dinsa ya shiga ko sallama bai masu ba, Imaan da Maryam na dinning xaune Imaan na bata labarin abinda ya faru parlon Inna kasa kasa, Mama Hadiza na daki tare da Ammi, Ammi ta fito jin an bude kofa ganin daddy ne tana kallonsa ta xauna saman kujera bata dai ce komai ba don Mama Hadiza fa na kan bakanta na cewa babu xancen daurin aure ranan har ta gama hada kayanta, Daddy ya jinginar da kansa da kujera yace "Inna na son bata sunan gidan nan ta kunyata mu a idon duniya ne kawai, ta mance cewa bayan Mujaheed akwai yan baya da xa su yi aure, ta mance gaba daya akwai Yan baya.... wani interpretation take son mutane suyi ma gidan nan, auren namiji ma ga abinda ya faru balle mace?? This is very serious...." Ammi dai ta kasa cewa komai sbda Mama Hadiza, Imaan ta taso ta dawo parlor don a rayuwarta na duniya bata son abinda xai 6ata ma Daddynta rai, Durkusawa tayi gefensa a hankali tace "Daddy ku yi hakuri" Daddy bai iya yace Komai ba.... Can Ya kalli agogon wrist dinsa yace "Ya Allah, just an hour remaining, Me xa mu ce ma mutanen nan fisabilillahi??" Ammi dai ba bakin magana, Mikewa Daddy yyi ya fita parlon, duk suka bi sa da kallo, Ammi ta sauke ajiyar xuciya, imaan ta mike a sanyaye ta wuce daki. Hijab dinta ta saka ta tafi part din Inna, suna xaune tare da ta Rasulu sun cika faranti da shinkafa jollof ga kaji kusan goma ana ta ci, turo baki tayi ta xauna tana kallon Inna a hankali tace "Inna don Allah ku yi hakuri ku bari ayi auren nan, kuna son a dinga ma su Abba kallon kananun mutane ne a garin nan?" Inna ta ajiye cinyar kazar dake hannunta tana kallonta baki bude tace "Shi Uban naki ne ya aiko ki in tafi in samesa yanxu?" Imaan tace "Ni ba wanda ya aiko ni" Inna na nuna mata kofa tace "Toh maxa kiyi ta kanki, tunda ba uwar ki aka xaga ba dama me xai dameki, gantalalliya ki ma je ki ji da lalurorin ki xa ki dinga tsoma baki a xancen manya kina yar yarinyar ki da ke...." A fusace Imaan ta mike ta fice a parlon, part dinsu ta koma ta shiga dakinta ta tadda Maryam a dakin, Maryam tace "Ina kika je?" Imaan ta xauna gefen gado tace "Wajen Inna mana, naje na mata magana ta xageni" Maryam tace "ke me ya kai ki, ni fa am happy gwara a fasa auren gaba daya... yarinyar da ta walakanta ni ranan farkon da muka hadu, I sooo hate her with passion" Imaan tace "Toh reputation din su Abba da Daddyna fa? Ae shine abun dubawan ba fasa auren ba" Maryam tace "It's just for sometimes dear, ke kina ga akwai wanda ya isa ya sa Inna ta canxa ra'ayin ta?" Shiru Imaan tayi, can a hankali tace "Na san me xan yi, I pray it works" Inna na bakin tap tana