Showing 30001 words to 33000 words out of 116763 words

Chapter 11 - SHAHAAB COMPLT

Start ads

10 Aug 2025

795

Middle Ads

cewa kyakykyawar amarya, itace ta Fado masa, baisan Ina yarinyar ta kwaso kyau irin haka ba, saikace aljana, cikin murmushi yace "Amin mama, dafatan kinyi sallah lafiya"

"Alhamdulillah Shahaab, ya munirat? Tayi sallah lafiya?"

Cikin mamaki ya kalleta "kamarya? Batazo bane?"

Tace "a a, nida ba nice na haife ta ba, Yaya za'ayi tazo ta gaishe ni, Amma nasan idan mahaifiyar ta tana cikin gidannan bazai iyu a kwana atashi, taqi zuwa ta gaishe ta ba"

"mama kiyi hakuri, zanyi mata magana"

"a a, rabu da'ita, inda Sabo ai yaci ace nasaba da halin munirat, dama kaina ke jira, inaso kasiyomin ticket,gobe zanje marad'i ganin dangin babanka, idan zakaje Kuma saika siyo mana mutafi"

Cikin sauri yace "a a mama, kijeki, ni jigawa zanje"

Cikin mamaki tace "jigawa Kuma?"

Sai yanzu ne ya gane irin Shirman Dayayi, cikin sauri yasake cewa "Eh... Eh.... Ina nufin akan aikin gidan marayun Nan"

Ajiyar zuciya ta sauke tace "to Alhamdulillah, nayi tunanin wani abun ne yataso"

Ahankali yace "a a, Amma mama kwana nawa zakiyi kidawo? Kwana uku yayi?"

"haba Shahaab , har yanzu de kana Nan da halinka bakason inje unguwa in zauna? Kwana biyar nakeso nayi, idan kajini shiru Kuma to sati daya zanyi"

Cikin ladabi yace "to shikkenan mama, Allah ya dawomin dake lafiya,saimu fita goben Nima gobe nakeson wucewa"

Tace "Allah yakaimu, tashi muje nabaka abinci"
Babu musu yatashi suka nufi dinning

Bayan yagama cin abinci fita yayi daga gidan, baije part dinsu ba Sai Bayan ya dawo da daddare, baiyi wa munirat maganar mama ba, yasan Bayan fitarsa zataje su gaisa, abinda bai saniba kuwa shine mama ko idon munirat bata Gani ba, washe gari karfe goma suka shirya shida mama suka tafi, Bai fadawa munirat inda zaije ba, yadai fada mata cewa sunyi tafiya shida mama, mama tayi tunanin Dasafe kafin su tafi munirat zatazo, shiru shiru bata zoba harta fidda rai, haka motoci guda biyu suka rakasu Airport, mama ta wuce Niger, shikuma yawuce Jigawa.


Wannan Karon ma a hotel ya sauka, tunda yamma yake shirin tafiya wajan ta, Amma idan ya tuna maganar Ramadan cewa akwai Wanda suka sanshi agarin, Sai yaji wani irin taqaici,yanason yaganta dawuri kodan yasata agaba yadinga kallonta harya gaji, shi Kansa yarasa meyasa yake murna da zumudin zuwa wajan ta.
Da daddare wata shigar yasake kamar ta jiya, manyan Kaya yasaka harda babbar riga, saide jiya shigar fararen Kaya yayi, yau Kuma light blue ne, shi Kansa daya kalli Kansa a madubi saida ya jinjinawa Hajja data iya auren kyakykyawan babansa Dan Nijar har Allah yasa Shima ya'iyo kamar baban nasa, saikuma yayiwa Allah godia bisa ni'imomin Dayayi masa, turare yafara fesawa kamar wani sabon ango, sannan yasaka face mask,yafuto a gurguje yashiga motarsa, rabonsa da driving harya manta, Sai yake jin wani irin nishadi a ransa, yana tafiya ahankali yana Sauraron yanda gidan Radio suke labarai na gaishe gaishen sallah, Ahaka harya qarasa cikin Garin, yau Garin yaga Yacika da mutane Kuma ga manyan motoci Nan alamun duk wasu wanda basa zama agarin ma sunzo gida bikin sallah, a'inda suka tsaya rannan shida Ramadan yauma anan yayi parking, face mask dinsa ya danja qasa, sannan yad'auki wayarsa yafara Kiran number ta, saida yaji tashiga sannan cikin ransa yace "yanzu da wayar akashe take Yaya zanyi? Ahankali yasake cewa" Sai inje gidan inyi sallama idan mungaisa dasu infada musu wajan yar qarama nazo"(>?-?)

Saida wayar takusa katsewa sannan yaji an dauka, ahankali kamar Wanda yake rad'a yace
"inajiranki a kofar gida"

"waye?"

Shine abinda tace, cikeda tsananin mamaki

Kai tsaye yace "SHAHAAB"

gabantane yafadi harsaida tasa hannu akan qirjinta, idan bata manta ba mutumin dayazo da Azumi yakawo musu kayan abinci har yace mata shi Yaron Mahmud Wakili ne, shine Shahaab, toba rannan yazo ba? Meya dawo yi wajan ta?

Kafin tagama tunani taji yace "I'm waiting for you"
Sannan ya katse wayar, ahankali ta dauki dogon hijab dinta Wanda yazo mata har qasa,haka tafuto daga d'akin kamar kazarda qwai ya fashewa, Ummah na banda ki danhaka ta kalli Hajja tace "Hajja inada baqo a kofar gida, zanje wajan sa daga Nan natafi gidansu Walida, yanzu zan dawo"

Hajja zuciyar ta daya tayi tunanin Inusa ne, Kai tsaye batare da tantama ba tace"ki gaishe ta"

Tana futowa qofar gida ta hango motarsa, Kai tsaye wajan ta nufa, tana zuwa ta Qwanqwasa masa glass din motar, ahankali ya sauke glass din, yana ganinta gabansa yafadi, cikin zuciyar sa yace "yasalam!"

Sannan yabude motar yafuto, ganin wajan babu mutane sosai yasa yakama hannunta yajata ta dayan site din, samun Kansa yayi da bude mata motar, sannan yasaki hannunta ya kalleta tareda nuna mata cikin motar yace "Bismillah"

Kallan sa tayi,tana mamakin yanda Babban mutum dashi Amma yake bude mata mota, yakamata ace tatakawa mutumin Nan birgi akan yanda yake riqe mata hannu kamar wata matarsa, kallansa tayi wata zuciyar tana hanata shiga, Amma ganin shi din Babban mutum ne, a shekaru ma zai iyayin na Abban ta, Saitayi Bismillah tashiga, rufewa yayi, sannan ya zagaya yashiga shima ya zauna tareda rufo motar, juyowa yayi yana fuskantar ta,Kallan ta yafara kamar zai had'iyeta, fuskarta babu kwalliya Amma saiyaga tamasa kyau sosai, cikin ransa yace "yar qarama Kyakykyawa".

Aisha kuwa jitayi motar wani irin sanyi, ga qamshi yana tashi, ahankali ta kama yatsun hannunta tana wasa dasu, kanta yana qasa, ko kadan takasa kallansa,wani irin kwarjini yayi mata musanman yau data ganshi cikin manyan Kaya, tana ganinsa ta Qasan idonta yanda ya zuba mata Ido kamar yanason Gano wani abu a fuskarta, Itakam tana zaune ne, Amma azahiri gabanta faduwa yake, saboda bata taba shiga mota mekyau irin wannan ba tunda take a rayuwar ta, acikin motar ma Kuma da wani namiji, ganin har yanzu yakasa yimata magana yasa tace "Ina wuni"

Saitaji yayi shiru,ahankali tad'an d'ago kanta ta kalleshi tace "Ina wuni"

Cikin sauri ya dawo hayyacinsa, ajiyar zuciya yasaki sannan ya gyara zamansa, ya kalleta cikin qasa-qasa da murya yace "Lafiya"

Daga Nan babu Wanda yasake magana, kusan minti takwas shiru, taga babu abinda yace, Sai aikin kallonta kawai yake,ahankali ta motsa d'an qaramin lips dinta tace "zan'iya tafiya?"
(tab! yaufa Ana zance anan=?
?>?#?=??)
Amnah El Yaqoub
'
Page 21&22






Cikin sigar rad'a yace mata "meyasa?"

"gidansu Walida nakeso naje Dama, inaso ta rakani shago"

"what will you buy?"

Kai tsaye tace "biro"

Mamaki ne ya kamashi, gata de yar qarama, Kuma tatashi acikin qauye, Amma tana danjin Dan qaramin turancin dayake mata, samun Kansa yayi da cewa "muje na rakaki?"

Cikin sauri ta kalleshi, tab, Ina zata Iya tafiya dashi acikin Garin Nan, ai kowa kallon dazai mata daban, ahankali ta girgiza masa kanta alamun a a, sannan tasa hannu zata bude motar tafita, cikin sauri yamiqo hannunsa yad'ora akan Nata hannun da nufin hanata fita daga motar, juyowa tayi ta kalleshi har kusancin nasu yayi kusanci tana iya jiyo daddadan qamshin turaren dake tashi ajikinsa, ganin kamar tana tsorace dashi ne yasa ahankali cikin sigar lallashi yace "kina jin tsoro nane?"

Girgiza masa Kai tayi, ahankali yasake cewa "to meyasa kike son ficewa daga motar?"

Ahankali tace "toka matsa mana"

Wani irin murmushi yasaki, sannan yadauke hannunsa dake kan Nata hannun, sosai yayi mamakin furucin ta, ita yanzu tsoro take kartaje yayi mata wani abu, Sai maganar Tata tabashi dariya saboda shi yar qaramar yarinya yake ganin ta, babu yanda za'ayi yayi mata wani abu makamancin Wanda take tunani, yana jin nishadi atare dashine idan yana tareda ita, Sai yake ganin ta kamar wata 'yarsa, inda ace a gidansa take bayajin akwai yarinyar dazata nuna mata gata, to Amma Yaya zaiyi? Allah bai bashi haihuwar ba.

Cikin murmushi yace "Na matsa, shikkenan?"

Kallan sa tayi, taga yanda dimples dinsa suka futo, Sai taga yayi mata kyau, ahankali tace "to intafi?"

"meyasa kike son tafiya ne? Kinsan tundaga Ina nazo wajanki? To tundaga maiduguri"

Zaro idonta tayi,(=?3?)cikin mamaki tajuyo tana fuskantar sa batama San tayi hakan ba,tace "maiduguri? Tome kazoyi Nan Garin?"

Sosai yaji dadin yanda tafara sakewa dashi, cikin farinciki yace "wajanki nazo"

Tace "wajena Kuma?,to meyasa?"

Yace "wancen Karon nazo natafi, ban tambayeki sunanki ba, shine nazo kifada min yanzu"

Cikin tsananin mamaki tace "sunana kawai? Saboda sunana kayi wannan doguwar tafiyar? aikuwa da matarka taji dalilin zuwanka wajena, dasai tayi fishi dakai"

Cikin mamaki yace "waye yace miki inada mata?"

Tace "aikai babba ne, nasan kanada mata, da Yara"

Jikinsa ne yayi Sanyi, haka kawai saiya samu Kansa da fada mata gaskiya "banida Yara"

Cikin tausayawa tace "to Allah yakawo masu Albarka, insha Allah watarana matarka zata haihu"

"Wai waye yace miki inada aure ne? Ni banda aure, very soon de nakeson yin auren"

Sai Bayan yafada mata hakan, Sai yake tambayar Kansa menene ma abun 6oye 6oye? Meyasa zai 6oye mata yanada mata? To Amma yanzu idan ya dawo yasake ce mata yanada aure zata raina shi, zata dinga ganinsa kamar qaramin yaro me magana biyu, danhaka kawai saiya share zancen.

Aisha tad'an kalleshi tace "insha Allah zan fara azumin sitta shawwal, inyi ma addu'ah idan kayi aure Allah yabaka 'Ya'ya masu Albarka"

Cikin tsananin mamaki ya kalleta, zatayi azumi tayi masa addu'ah akan Yara? Abun mamaki, munirat bata ta6a fada masa hakan ba, gashi de itace wadda zata Haifa masa yaran, Amma ko kadan haihuwar bata gabanta, ganin kallon dayake mata ne yasa tace "lafiya?"

Ajiyar zuciya yasauke yace "no, babu komai, kawai... Kawai... de inajin dadin kasancewar ki atare Dani yanzu"
Yafadi hakan yana Lumshe Idonsa.

Yanda yafadi maganar yake Lumshe ido Sai hakan yasa taji wani iri ajikinta, cikin kunya tasa tafukan hannunta tarufe fuskarta cikeda kunya.

Murmushi yayi, cikin dabara yace "Ina Alhajinku megidan Mai?"

Cikin sanyin jiki tace "yana Nan, yazo sallah ma"

Kansa ya Jinjina, tunda yaji batayi masa maganar gidan man ba, yasan har yanzu basu saki gidan man nasaba, Amma yayi mamaki sosai, tunda shine yabada umarni zuwa wannan lokacin ai ya kamata ace anbashi gidan mansa.

Yace "aikuwa nayi wa ogana maganar gidan mansa, insha Allah zaiyi magana, nasan zasu saki gidan man"

Tace "hmm, kaifa bakasan halin wannan ogan Naka bane, nafada maka bashida mutunci, uhmm... Inama zan ganshi, wallahi dasai yagane kurensa" (=?F? @&?)

Runtse Idonsa yayi, cikin zuciyar sa yace "to masifar Tata tazo"

Kafin yabude baki yace wani abu tace "Bari natafi, zanje Walida ta rakani siyan biro, nagode da ziyara"

Ahankali yace "sunanki"

Cikin murmushi tace "A'ISHA"

yace "what!?"

Cikin mamaki tace "meyafaru?"

Cikin farinciki yace "sunan mamana gareki,kiyi hakuri bazan iya fadar sunanki ba, Amma zan dinga kiranki da Maaama"

Murmushi tayi tace "nagode"

Baice mata komai ba, yasaka hannunsa cikin babbar rigarsa yadauko dubu biyar din daya ware tun hotel, yace "gashi,kudinbarka da sallanki ne, duk da ba'a nunamin kwalliyarba"

Rufe fuskarta tayi cikin kunya, tace "a a ka barshi nagode"

Tace "banason musu, ki Kar6a, kisai chocolate, biro Kuma kibari karki siyo, zan kawo miki next time, karki kashe wayarki, zan kira ki idan nakoma masaukina, oya kar6i kitafi"

Hannu biyu tasa ta karba, sannan tace "to nagode" sannan cikin sauri tafice daga cikin motar.

Lumshe Idonsa yayi yana jin wani irin nishadi ta ko'ina.


******

Gidansu Walida taje, saide bata dade da zuwa ba tace gida zata tafi, kasancewar duk firar da walidan take mata bata jinta, sotake tasamu waje ta ke6e ita kadai tayi nazari akan wannan bawan Allah.

Har gida Walida ta rakota, su Hajja basuyi tunanin komai ba, saboda dama gidansu walidan tace zataje, saida suka gaisa dasu Ummah sannan Walida ta musu sallama tatafi gida.

Kai tsaye d'akin umman ta tatafi, kamar jira Yan nefa suke, tana shiga Dakin suka kawo wuta, kwanciya tayi akan gadon Ummah sannan ta duba kudin daya bata yauma dubu biyar ne, Nan take tafada duniyar tunani, shikam wannan wacce irin sana'ah yake dazai dinga yimata kyautar dubu biyar har sau biyu?, lalle in hakane Mahmud Wakili ba qaramin mutum bane, tunda gashi de Yaronsa ne yake yin kyautar dubu biyar, Amma kudin ai yayi yawa, mutumin Nan Dama fad'a ne yafara hadani dashi, idan nasake zagin ogansa Mahmud Wakili muka sake wani fadan daga baya yace nabiyashi kudinsa fa?
Idan ma bamuyi fada ba Yaya za'ayi na tunkari iyayena da wannan uban kudin? Cikin sanyin jiki tasauko daga gadon tasaka kudin acikin asusunta, sannan Takoma Dakin Hajja tasaka mata wayar ta acaji.

Yana tafiya a hanya Ramadan yakira shi, harzaiqi d'auka, saikuma yafasa yad'auki wayar, daga dayan bangaren Ramadan yace "oga jiya naje gida bansamu ganinka ba, yau Kuma nakoma madam tace min kunyi tafiya kaida mama, lafiya dai ko?"

Cikin muryarsa Mai aji yace "Bana Nan naje Jigawa"

Mamaki yakama Ramadan, cikin jin dadi yace "masha Allah, kacemin kaje qauye kana kokarin hada kan takardu domin bude sabon account" (>?-?)

Murmushi yayi yace "ba account zan bude ba, cbn zan bude, Wai mekake tunani akai nane Ramadan? Kawai zuwa nayi inji sunanta, last time ban tambayeta menene sunan taba"

Ramadan yayi murmushi yace "ok nagane, to Yaya sunan qanwar tamu?"

"sunan mama gareta"

"Kai kai Kai, kace me Babban suna ce, to Abokina, Allah yabar zumunci tsakanin ka da Ummi"

Cikin sauri Shahaab yace "no, ba ummi ba MAA-MA"

Ramadan da mamaki yagama cikashi yayi murmushi yace "to d'an autan MAMA abokin MAAMA, yanzu de Sai yaushe zaka dawo?"

"gobe babu inda zanje, zan huta, Ina tunanin jibi zan dawo insha Allah"

"ok to shikkenan, Allah ya dawo dakai lafiya, saika dawo din"

Batare daya sake maganaba yakashe wayar yaci gaba da driving, acan bangaren Ramadan kuwa murna yake, ta tabbata de Shahaab yana son yarinyar Nan, oh daga zuwa saudaya harya zare jiki yakoma batare da kowa yasani ba, ko Yaya wannan zance nasu ya kasance Bayan Shiba magana yakeba? Ko yabude baki yayi mata magana? Dariya yasaki yace "Abokina kenan, Allah yakaimu lokacin musha biki"



(SHAHAAB LITTAFIN KUDI NE, IDAN KIKA KARANTA BATARE DA KIN BIYA BA NABARKI KEDA MAHALICCINKI, NIDE BAN YAFEBA)


******


Bayan yagama komai ya kwanta, yakira mama suka sake gaisawa, cikin kulawa tace "kakoma gida ne?"

Cikin sigar shagwa6a yace "um Um mama ban komaba, saina huta de"

Mamaki ne yakamata,tasan cewa Shahaab da munirat Sai Allah, kamar yanda Shima yake fada, Amma yau shine awani gari daban batare da munirat ba, Kuma yake fadar haka, ajiyar zuciya tasauke tace "munirat din tabiyoka ne?"

Yatsina fuska yayi yace "no, bamuyi waya Bama tunda nataso, zande kirata yanzu Bayan mungama wayar nan, kawai inajin dadin inda nake ne mama, babu hayaniya, babu takurawa, babu Wanda yasan Dani, Ina rayuwa ta yanda nakeso, saina huta zan koma"

Cikin tsoro mama tace "akwai Wanda zaice baisan kaba bane Shahaab? Banason damuwa, idan hutun kakeso ka shirya katafi wata qasar mana, canma ai babu Wanda yasanka, kakoma gida ka dauki matarka kutafi hutunku kamar yanda kuka saba"

Cikin shagwa6a yace "mama ki kwantar da hankalin ki, babu abinda zai sameni kinji?"

Tace "to shikkenan, idan kunyi wayar ka gaisheta"

Tace "to mama" sannan yakashe wayar

Kamar wanda aka sakawa cutar mantau, yana kashe wayar Yama manta da batun munirat kwata-kwata, cikin sauri yakira Aisha (=?F? @&?)

Tana zaune agefen gadon Hajja tayi shiru tana tunanin al'amarin Shahaab, tarasa meyasa yake zuwa wajanta? Yakamata ace ta tambayeshi meyasa yake zuwa inda take? Ko wani aikin ogansa yaturo shi Garin?

Wayar Hajja dake caji tad'auki qara, Hajja dake kwance atsakar gida ita dasu Ummah ta daga murya tace "me sunan qawa Bani wayar nan Ana kirana"

Bakinta ta turo gaba tace "ni ake kira"

Hajja tace "au to, ko inusa me shago ne?"

Ahankali tace "um" tareda daga wayar

Zama tayi agefen gado tanajin yanda yake magana kamar mace, ahankali tayi qasa da murya yanda su Hajja bazasu jitaba tace "Wai Kai meyasa kake magana ne kana shagwa6a kamar wani Dan auta"

"mama nah nikadai ta Haifa"

Cikin mamaki tace "shiyasa kake shagwa6a?"

Murmushi yayi cikin shagwa6a yace "ni banyi miki shagwa6a ba"

Tace "ba gashinan ka nayi ba"

Lumshe idonsa yayi, yana jin wani irin dadi cikin zuciyarsa, yace "mama na kawai nakewa shagwa6a saike"

"kaifa ba yaro bane" cewar Aisha

"shine awajanki"

Cikin mamaki tace "kamarya?"

Cikin basarwa yace "babu komai, yau nahanaki bacci, ki kwanta kihuta"

Babu musu tace "to Amma inaso in tambayeka, meyasa kake zuwa garinmu?"

Murmushi yayi yace "ki adana tambayoyin ki, idan nadawo saiki tambayeni,insha Allah zanbaki amsa"

Cikin nutsuwa tace "to nagode sosai"

"Okay" shine abinda yace, tareda kashe wayar gaba dayanta, ko kadan baiyi yunkurin Kiran munirat ba, itama Kuma bata nemeshi ba.


******

Yau kwanan su mama biyu da tafiya, tunda suka tafi munirat bata kira mama awaya ba, shide Shahaab Yakirata yau da safe, Amma bata dauka ba, Shima Kuma bai sake kira ba.
Da rana, masu aikin gidan suka shirya abinci kamar yanda suka sabayi idan mama tana gari, cikin takun qasaita tataho tana tafe tana danna wayarta, Kai tsaye part din maman taje, abincin da aka shirya a dinning ta bubbude, cikin masifa tace "bazan iyacin wannan abincin ba, waye yabada umarni ayi wannan girkin?"

Cikin sauri daya daga cikin masu aikin ta d'ago kanta tace "Anty Idan Hajiya Mama tana nan haka mukeyi, dama kowacce rana akwai irin abincin da muke sauya wa, shiyasa yauma muka yi hakan"

Cikin masifa tace "okay, to yau nice ba mama ba, kuma bazanci wannan ba, saiku dauke kuje kusan yanda zakuyi dashi, saboda tsabar samun waje Ina zaune acikin gidan ban'isa ku tambayeni menake so adafa min ba? Maza maza ku kwashe minsu daga gabana aje azubar adafa Sabo a kawomin"

Cikin sauri suka kwashe abincin basu bar ko drinks ba, suna shiga kitchen suka Rasa Yaya zasuyi da abincin, daya daga cikin su ce tace "Bari nafita dashi ta kofar baya saina bayar awaje"

Dukansu na'am sukai da shawarar Tata, saboda zubar da abincin kamar almubazzaranci ne, Bayan suma dasuke zaune a gidan saboda neman abincin ne yasa suka nemi aikin a gidan.

Bayan sun shirya mata abinda takeso, part dinta ta wuce, akan kujera ta zauna tafara Kiran qawayenta, takira wannan takira waccan, duk da taga Kiran Shahaab, batabi ta Kansa ba, asali ma dadi taji yanda sukayi tafiyar Nan shida mama, yanzu gida ya dawo hannunta, Sai abinda takeso za'ayi, tasan suntafi Niger, inda ace de wani Garin yatafi daban to dole zata damu, saboda tana tsoron karya hadu da wata yarinyar ta dauke masa Hankali, Amma yanzu tunda tare yake da mama, batada damuwa, batada haufi akan mijinta tasan ita kadai ce acikin zuciyar sa, daga ita babu qari.(tofa=?D?)

Da daddare inusa yakira Aisha a wayar Hajja,sunsha hirarsu cikin kulawa, saide rabi zancen duk shine yakeyi, idan yayi mata maganar Hajja nema zaiga Nan da Nan ta ware tanata masa surutu, daga Nan ya fahimci cewa dole zai sake cusa Kansa awajan Hajja duba da yanda Ita kanta Aishan ta dauki Kakar Tata.


******


Washe gari ya shirya yatafi Abuja, tun

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login