Showing 15001 words to 18000 words out of 116763 words

Chapter 6 - SHAHAAB COMPLT

Start ads

10 Aug 2025

796

Middle Ads

da cikin Gari suke so.
sunji dadin yanda aka kar6esu,Kuma abun yazo musu da sauqi kasancewar filin na Gwamnatin Jihar ne,Bayan sungama akayi musu photo Sannna suka koma masauqinsu

Suna zuwa Shahaab ya daura towel yashiga wanka, Bai dade da futowa ba aka kira sallar magrib, shida Ramadan suka tafi masallaci Bayan sun dawo suka Sha Fruit da sauran abubuwan buda baki

Bayan sun dawo daga sallar tarawih sun dade suna kallon labarai shida Ramadan, saida matar Ramadan din ta kirashi awaya Sannna yayi masa sallama yatafi dakinsa, shi kuwa da mama kawai yayi waya, yafada mata yanda sukai, taji dadi sosai, munirat kuwa wayarta akashe, tunda yayi try bata shigaba saiya haqura ya kwanta.

Washe gari sukaje sukaga wajan, aka auna yanda abubuwan zasu kasance, suka tsara yanda aikin zai dinga gudana, dakuma mutanen da aka damqa aikin a hannun su

Awajan suka wuni Sai gab da shan ruwa suka koma hotel, washe gari aka fara tono, manyan motoci suna kawo bulo, wasu yashi, wasu siminti, saida yaga aikin yafara kankama Sannna suka tafi, da magrib suna shan ruwa Shahaab duk tunanin matarsa ya isheshi, duk rashin dadinta yana rage zafi da'ita a hakan, cikin kwana ukun Nan da sukayi shi yasan yanda yakeji, wata irin sha'awa yake ji kamar zaici babu, sauqin sa daya yataho da qananun wandunansa masu kamar pant, yana sakawa, Amma badan hakaba ya tabbatar wataran idan yafita Sai yaji kunya,saide yadinga tafiya yana bude qafa saboda tsaro(=??)
Saboda haka Gara suyi abinda yarage musu kawai yakoma gida, yajuya ya kalli Ramadan yace "yakamata mu raba kayan azumin Nan Ramadan, yau ankai azumi na goma kenan,sonake gobe mu wuce gida"

Ramadan yace "Dasafe zamu raba kayan ne?"

Girgiza Kai yayi "da nayi niyyar mu raba da safe da yamma saimu tafi gida, to nariga nasai mana tickets Dasafe jirgin mu zai tashi"

Cikin sauri Ramadan yatashi zaune yace "Wai kana nufin yanzu daga shan ruwa zamu fara daukar kwalin taliya da macaroni muda yakamata ace mun huta?"

Murmushi yayi yace "ba Lada muke nema ba? Yazakayi?"

Kamar zaiyi kuka yace "to yanzu Yaya zamuyi?"

"kira mun Wanda kayan yake hannunsu kagani" cewar Shahaab

Babu musu Ramadan yakira su, yasaka wayar a hands-free sannan ya ajiye ta a tsakanin su

Cikin aji Shahaab yace "yawwa kana Jina, muna sone muwuce gida gobe insha Allah, so kayan Nan za'a rabashi yanzu, Wanda basu qare ba saiku qarasa gobe, Ramadan zai kar6i account number ku, insha Allah Zakuga saqona"

Cikin ladabi Yaron yace "to yalla6ai, yanzu Yaya za'ayi Rabon kenan?"

Shahaab yace "akai trella daya yankin Hadejia da gumel, dayar Kuma abarta anan yankin dutse,ku dauki Rabin trella ku raba a wasu qauyukan saiku saka mana Rabin acikin mota, direban yazo Nan Tahir guest palace ya daukemu muje mufara rabawa"

Cikin biyaiya yace "to wanne qauyukan zamuje yalla6ai?"

Murmushi yayi yace "aika fini sanin yanayin garin, ku kukasan yanda zakuyi, but mude mungaji,kafadawa direban qauyukan dazai kaimu, Amma qauyukan dasuke kusa, Wanda muna gamawa zai dawo damu hotel"

Nan da Nan Yaron yace "yalla6ai akwai,
Dan masara, da Chai-Chai, Abaya, Baranda, dakuma Chamo, da.... "

Cikin sauri Shahaab yatareshi yace"kai Kai kai kaga ya'isa haka, kafada masa yakaimu chai-chai, idan mungama dasu saiya kaimu inane kace na qarshen?"

Cikin sauri yace "CHAMO yalla6ai"

Cikin yatsina fuska yace "to yakaimu chai-chai da chamo, nagode" daga haka yayi masa godia suka kashe wayar

Kallan sa Ramadan yayi yace "wanne irin Rabon kayan abinci ne wannan da daddare kamar munafukai?, yaushe zamu tafi mufara to?"

Murmushi yayi yace "sahabban manzon Allah (S.a.w.) haka suke yi, suna ajiyewa talakawan su kayan abincin aqofar gida, duk Wanda yafuto Dasafe anan zai Gani, idan muka idar da sallar tarawih Sai mutafi, kafin Nan direban yazo, idan mun samu mutum aqofar gidansa saimu bashi, idan baya Nan saimu ajiye masa aqofar gidansa"

Suna wannan maganar aka kira sallah, futowa sukai suka tafi masallaci, tun kafin su idar direban yazo yake jiran su, suna futowa daga masallaci suka wuce, Ramadan ya kalli Shahaab ya kwashe da dariya

Kallan sa yayi yace "lafiya?"

Ramdan yace "kawai shigarka ce tabani dariya, yau babu suit, Kaci wani jallabiya kamar balarabe"

Murmushi yayi suna shiga motar Shahaab yace "aini dadin hakan nakeji, Jina nake wani iri, babu masu tsaro, babu sojoji, babu Yan sanda, sainake ganina kamar kowa"

Ramdan yace "gaskiya hakane ai Naga alama jihar akwai Zaman lafiya kowa yana harkar sa babu wani tashin Hankali"

Suna tattaunawa har suka Isa chai-chai, Shahaab Kam kallon mutane yake kamar yaga sabun halitta, idan yaga wani gidan Sai yaji kamar yayi kuka, Ahaka harsu ka sauka, aka hadasu Dame unguwar Garin, ya gayya to musu wasu mutanan, Shahaab da qura tafara tashi saiya nemi face-maks dinsa yasaka, shida Kansa yace "duk mutum daya abashi taliya katan biyar, macaroni katan hudu"

Nan da Nan masu unguwa suka fara rabawa mutane abincin gida gida, Shima yad'auki wani Ana kaiwa dashi, Ramadan ma haka, basu suka bar Garin ba Sai daya saura, Ramadan ya kalli Shahaab yace "Abokina bakasan wani abu ba, nifa Garin Nan ya birgeni, gashi dare yayi Amma muna tafiya cikin kwanciyar Hankali babu kidnappers, babu masu fashi, babu 6arayi, Dan Allah kagani"

Kafin Shahaab yayi magana
Direban ya jiyo ya Kalle su yace "yalla6ai zamuje can chamo din?"

Agogon hannunsa ya kalla yace "muje"

Babu musu yaqara gudun motar suka dauki hanya, Sai qarfe daya da wani abu suka qarasa cikin Garin chamo, Garin yayi shiru babu motsin mutane, Shahaab ya kalli gidajen Garin yana qare musu kallo, baisan meyasa ba, Bai kuma San dalili ba haka Nan yaji gabansa yana wata irin faduwa, Bai kawo komai a ransa ba haka ya share, suka tsaya a tsakiyar Garin, duk suka futo daga cikin motar, motar datake binsu da Kayan itama ta faka

Samarin dasuka zo da motar kayan suka Kalle shi "yanzu yalla6ai ya za'ayi? Garin nanfa sun kwanta wallahi, zaku tafi gida ne mu saimu kwana Dasafe muraba musu kokuma akwai shawara?"

Agogonsa ya kalla yace "no, kawai muraba musu, kowa idan yatashi saiya Gani da asuba"

Nan da Nan suka fara rabawa, babu motsin kowa saina su, wasu suna saukewa daga cikin motar, wasu Kuma suna rabawa, Ramadan ya tsugunna yadauka yanufi wani gidan yana tunani a ransa gaskiya sahabai sunyi kokari, Kuma suna neman aljannarsu da gaske

Shahaab ma dauka yayi yanufi wani gidan can daban, ya ajiye a kofar gidan, sannan ya dawo yasake dauka yakai qofar gidan Jummai qawar Hajja, sannan yasake dawowa ya dauka yakai gidan Alhaji Audu Wanda hukumar efcc ta qwacewa gidan mansa, dawowa yayi yarungumi taliya guda hudu ya jibge a kofar gidansu Aisha, Sannna yakoma zai Dauko sauran

Cikin baccinta taji wani irin fitsari, cikin sauri ta tashi tad'auki buta da gudu tashige bandaki Dan kwalinta a hannu,ta tsugunna tana fitsari tana daura dankwali, mamaki take wanne irin fitsari ne wannan kodan ta dirki ruwa da yawa Bayan tadawo daga masallaci sallar tarawih dazu.

Jitayi kamar an ajiye wani abu aqofar gida, mamaki ya kamata, saida tayi tsarki Sannan tafuto daga bandakin, cikin sand'a ta nufi hanyar kofar gida tana so ta leqa taga qaran menene wannan, tana zuwa bakin kyauren nasu Sai taji takun mutum, gabanta ne yafadi to kode 6arayi ne?

Matsawa ta sake yi, ta sunkuya taleqa ta cikin wata yar qaramar 6ula inda kyauren yafara cire wa, mutum tagani ya tsaya a kofar gidan, Amma bataga fuskarsa ba, Adede lokacin shikuma Shahaab ya ajiye sauran macaronin daya Dauko, yana ajiyewa kwalin macaronin ya bugi kyauren, jikake garam Sai a fuskar Aisha (=??)
Cikin azaba tace "wayyo goshina"

Mamaki yakama Shahaab, mutum, Kuma muryar mace acikin wannan Daren? Fitilar wayarsa ya kunna, sannan yasaka Hannunsa yatura kyauren cikin mamaki yaganshi yabude alamun basuda Sakata a gidan, yana budewa Idonsa ya sauka akan dogon gashinta Wanda yarufe mata fuska, dankwalin Nata na hannunta, yayinda hannunta guda daya yake kan goshinta tana mulmula wajan data bige, gabansa ne yafadi, wannan kwa mutum ce? Wanne irin gashi ne wannan?

Hannunta tad'auke daga kan goshinta ta d'ago fuskarta ta Kalle shi tace "waye?"

Baisan metake fad'a ba,gaba d'aya hankalin sa, tunanin sa, dakuma Idonsa yanakan kyakykyawar fuskarta yana qare mata kallo, hannunta ya kalla yaganshi fari tas, yasake kallon hannun ko zaiga alamun shafe-shafe, Nan ma yaga babu, ya kalli Dan qaramin bakinta Mai launin pink, mamaki yasake kamashi, tayaya? wannan kyakykyawar yarinyar acikin wannan qauyen?

Ganin tana magana yayi shiru yasa ta meqa hannu dede fuskarsa ta had'a hannayenta suka bata sautin d'as d'as, cikin sauri ya dawo hayyacinsa ya kalleta, cikin masifa tace "waye ya aikoka da wannan kayan?"

Yayi mamaki yar qarama da'ita Amma ta'iya masifa da wani Dan qaramin bakinta kamar gidan tsuntsu, abun mamaki Wai shi ake tambaya waye? Lalle Allah daya gari bambam,dama akwai mutanan da zasuce wai basusan waye MAHMUD WAKILI ba?

Baisan meyasa ba, baisan Yaya akai ba, lokaci daya ya tsinci Kansa dabin shawarar mama da Ramadan, maimakon yafada mata waye shi, saiyace "sunana SHAHAAB"

Cikin 6acin rai tace "to koma de waye, Mahmud Wakili ne kaima yaturo ka Rabon kayan abinci kamar yanda yaraba a wasu jihohin ko?"

Mamaki ya kamashi, Yaya akai tasan sunansa Amma batasan waye Shiba? Bai iya bata amsa ba Sai kansa daya daga mata kawai

Hannu tasa ta gyara dogon gashinta yakoma baya, Cikin jin dadi tace "Alhamdulillah, dama na Dade inaso na ganshi, ka dauki tsiyarsa ka maida masa, Bama so, kafin yabamu abinci Dama can muna rayuwa, shine matsiyaci Mai Kama kudin talakawan Allah yana riqewa,Kuma dayake kama mutane yana qwace musu Kaya Shima ai abun atuhumeshi ne, tunda bamusan daga Ina yasamu kudin dayake facaka dashi ba, qila ma kudin talakawan ne, saboda haka bamaso, Kuma kakoma kafada masa muddin nahadu dashi to haduwar mu bazatai kyaub......"

kafin ta qarasa ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu.( ' Bai saba ganiba, Bai taba ganin Wanda ya tunkareshi fuska da fuska yafada masa baqar magana haka ba, asalima kowa girmamashi yake Ana ganin qimarsa, babu Wanda yake masa rashin kunya saide lallashi, inda ace yana candy yayi aure ya tabbatar da tuni ya haifi kamar wannan yarinyar, cikin 6acin rai da daure fuska ya matso da fuskarsa dab da Tata har sunajin hucin numfashin juna, yace"ke!!!, marar kunyar yarinya, yar qanqanuwa dake kin'iya masifa, idan naqaraji kin zagi ogana saina kakkarya qasusuwanki na zubar anan wajan, maza dauke wannan kayan kikai ciki "








Mutara zuwa gobe =?O?


SHAHAAB littafin kudi ne, babu tsada nera 300 ne kacal, Yar'uwa kibiya tun kafin free page yaqare.


Zaki tura 300 ta wannan account din

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaki tura shedar biyan kudi ta wannan number

08033300034









Mrs Usman ce
' (Romance)


Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook=?G? https://www.facebook.com/amnahel



11&12

Tsoro ne yakamata, idonta yayi tsilli-tsilli tana Kallan sa,duk da bata sanshi ba,yanda taga ransa ya6aci tsaf zai iya aikata abinda yafada,wani tsoron ne yasake shigarta, gashi cikin dare ne kartaje haka kawai yakasheta a banza awofi, bare taga yanda yake da kyau, bata Sani Bama ko aljani ne, to sune akace suna shigar mutane su shigo cikin su, gabanta ne yafara faduwa ganin yanda ya matso kusa da'ita kamar zai shige mata jiki


Batare datace masa komai ba ta sunkuya,dogon gashinta ne ya dawo fuskarta sakamakon sunkuyawar da tayi,yasake rufe mata fuska, kwalin taliyar ta d'auka tayi ciki.

Kallan ta yayi yaga yanda uban hips dinta yake juyawa,girgiza Kansa yayi, yafara magana cikin zuciyar sa, inaga fa yarinyar Nan ba mutum bace, yar qaramar yarinya da'ita Amma ta mallaki abubuwan more rayuwa, Kuma inba aljana bace tayaya yanda yakewa mutane kwarjini Amma ita baiyi mataba Sai rashin kunya take zuba masa? Kaiii Gara yayi sauri yabar gidan, idanma aljanar ce to aniyarta tabita,cikin sauri yafuto daga gidan, Aisha kuwa tana ajiye kwalin taliyar tashige cikin Dakin Hajja da sauri gabanta yana faduwa, runtse idonta tayi, Amma shi take Gani a'idon zuciyarta yanda ya matso kusa da'ita ya nuna ta da hannu, yake zare mata ido, dak! dak!! Haka gabanta yake faduwa, Allah yasa ba Gamo tayi ba, Allah yasa ba aljani ne yabude mata idoba.

Sai wajan karfe hudu saura suka gama, har suka koma hotel kuwa jikinsa a sanyaye yake,maganganun yarinyar ne suke masa yawo a zuciya,saida yayi nafila sannan yayi sahur ya kwanta, da asuba kuwa tunda suka tashi basu koma bacci ba sukai shirin komawa Abuja

Da asuba Abbah yana tashin su Aisha sahur, saiyaci Karo da kwalin taliya guda daya, Wanda Aisha tashigo dashi, mamaki ya kamashi, jiyake kwali ne, Amma yana ta6awa yaji nauyi, Hajja tana futowa itama ta tsaya tana Kallan sa, fita yayi daga gidan saboda hayaniya da yaji tana tashi awaje, yana zuwa bakin kofar gida yaci Karo da sauran kayan,fita yayi daga gidan inda yaga mutane Ana tsatstsaye kowa yana fadar Albarkacin bakinsa, wannan yace yaji tsayawar motoci to yayi tunanin Yan fashi ne shiyasa yaqi futowa, wannan yace kaza wannan yace kaza, haka de, Abba yajuyo yashigo da sauran, anan yaga duk mutanan gidan sun tashi, Hajja ta Kalle shi tace "mamuda ashe Wai kaji ita Me sunan qawa taji lokacin da aka ajiye kayan tafuto fitsari lokacin, to Kuma Wai kafin taje bakin qofar har Wanda ya ajiye yatafi, bataga kowa ba, shine tashigo da guda daya taji tsoro kartaje ko aljannu ne" (=?2?)

Murmushi Abba yayi yace "ba aljannu bane Hajja, Ina Yaron Nan Dan kasuwar Nan? Me sunana?"

Hajja tace "waye Dan kasuwa Kuma?"

Yace "shugaban EFCC da'ake maganar sa a gidan redio yana raba kayan abinci gari-gari, ai shi nake nufi, to wai shine ya aiko wasu mutane suka raba mana muma"

Fashewa da Kuka Hajja tayi tana goge hawaye da gefen zaninta, cikin kuka tace "Allahu akbar, Allah yasaka masa da alkhairi, Allah yabiya masa buqatunsa na alkhairi, mamuda kaima bancire rai zakayi kudi ba, kaima Naka kudin yana Nan tafe" (=??)

Aisha ta harareta tajuya tad'auki buta da brush tayi bandaki, har Bayan gama sahur dinsu,zancen aketa maimaitawa, Garin chamo babu sunan Wanda yake yawo saina MAHMUD WAKILI =?L?

******

Bayan sun koma Abuja Kai tsaye office suka wuce, saida yarage wasu ayyukan sannan yatafi gida, Bai nufi part dinsu ba, saboda yasan Idonsa idon munirat to yau babu batun daga qafa awajansa, kwana ukun Nan Dayayi jiyake kamar yayi shekara uku ne batareda mace ba.

Sai Bayan Ansha ruwa yaga lafiya lafiya yakai azumin sa, sannan yatafi part din nasu, a wannan Daren munirat tagane kurenta, domin kuwa taji jiki yanda ya kamata
Saide abun mamakin shine kwata kwata baiji wani canji awajanta ba, tana nan kamar de yanda yatafi yabarta,ko kadan bai samu gamsuwa ba, shiyasa Bayan yahuta saiya sake nemanta Bayan wasu awannin, Amma idan yasake maimaita wa dinma duk hakan yakeji, yayi tunanin idan yayi dayawa hakan zaisa yaji shi zam-zam, to Amma sai yaji sa6anin haka.
A 6angaren munirat kuwa tayi tunanin yanda yadage yake abu daya tun farkon dare har tsakiyarsa yaji tayi masa dadi ne, saboda Shahaab irin mazan Nan ne Wanda suke shiru yayinda suka kasance da matansu, tun tana amarya takeso ta rikitashi ta karya wannan dabi'ar tasa taqin yin kukan dadi, Amma duk yanda takai da gyara haka zata jishi shiru, shi Dan sumbatun Nan ma ba yayi, bata saniba dadin tane baikai yayi kukan ba kokuma haka dabi'ar sa take, dataga sun kwashi shekaru masu tsawo Ahaka, kawai saita sallama, tabarshi a hakan dabi'ar sa take, shiyasa yanzu ma bata kawo komai acikin ranta ba, saide Bayan komai ya gama wakana ta isheshi da kukan kissa, shikuma Nan da Nan ya lalace wajan lallashin ta, ko kadan baison abinda zai 6ata ran munirat.


******

Yau satin su daya da dawowa daga jigawa, Amma tunani d'aya yabi yadameshi, yana son ya yakice maganganun da yarinyar tafad'a masa Amma yakasa, 'Dan qaramin tsaki yasaki, yafi awa daya a kwance a gadon mama, so yake tadawo yaji duminta Amma taqi dawowa tana can tana kula da Abincin da ake rabawa sadaka,Lumshe Idonsa yayi yana jin dadin yanda sanyin esi yake ratsa jikinsa, ko kadan bayajin wahalar azumin, sake sakin wani tsakin yayi Bayan tunanin yarinyar yasake fad'o masa, alqur'ani yadauka yafara karanta wa ko zai kawarda tunanin a ransa.

Sai gab da shan ruwa mama tadawo, alqur'anin ya ajiye ya dawo ya kwanta akan cinyarta, Kallan sa kawai tayi takasa magana, wani lokacin idan yayi mata wani abun kamar qaramin yaro, babu yanda zatayi dashi tunda shi kadai gareta, dan haka ta share shi tad'auki remote takamo tashar Sunnah TV tana kalla, saida aka Sha ruwa sannan suka dawo falo, anan ya tarar da munirat tana hada fruit salat, suna zama kuwa ta ajiyewa kowa nasa, wannan Karon mama batayi halin Nata ba, kawai dauka tayi Tasha, kodan saboda azumi ne yasa kwana biyu tayi shiru oho.

Bayan ya dawo daga sallar tarawih ma wajan mama yawuce, har lokacin suna tareda munirat, Sai wajan karfe goma sukayi mata sallama suka tafi part dinsu.
Kai tsaye dakinsa yawuce yayi wanka sannan ya kwanta, so yake yayi bacci da wuri, to Amma saide me? Dan qaramin pink lips din yarinyar yake tunowa, yasake tuna yanda take tafiya da sauri zatakai kwalin taliya cikin gida gaba daya hips dinta wani irin juyawa yake, yatunada dogon gashinta Wanda yafara daukan hankalin sa.
Meyasa ta tsaneshi? Meyasa take hamdala ga Rabbi saboda yace mata shi Yaron Mahmud Wakili ne? Hakan yana nufin akwai abinda ya yi mata, Kuma take neman sa ido rufe Amma bata sameshi ba, laifin meyayi dahar take fada masa cewa Shima ya kamata atuhume shi? Meyasa ta tsaneshi har haka? Wata zuciyar tace dashi yakamata kasan dalili.

Gyara kwanciyar sa yayi ya dawo yana kallon p.o.p din 'Dakin, tabbas inason jin dalilan yarinyar,gashi tanada masifa Amma da alama tanada tsoro, tunda tsawa d'aya kawai yayi mata, yaga idonta yayi tsilli-tsilli kamar ace kyarat ta gudu,idan ita din marar kunyar gaske ce to tsayawa zatayi ta fuskance shi yafada, itama ta fada, ya tuna yanda take zare ido cikin tsoro, baisan lokacin da wani irin murmushi ya qwace masa ba, cikin zuciyar sa yasake cewa yar qarama...
Yasake sakin wani murmushin har dimples dinsa yana futowa, a fili yace "me qaramin baki kawai...."

Munirat data dade da shigowa Dakin tana fesa turaren sa,cikin iyayi tajuyo ta Kalle shi tace"My Dear ni d'in?" (=?3?=?J?)

Firgigit yayi ya dawo cikin hayyacinsa,yasaki wata nannauyar ajiyar zuciya, yaushe tashigo Dakin bai Sani ba?
cikin salon basarwa yace"yes"

Tareda miqa mata

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login