Showing 39001 words to 42000 words out of 116763 words

Chapter 14 - SHAHAAB COMPLT

Start ads

10 Aug 2025

798

Middle Ads

a wuce dasu folice station, bazai iyu munada Babban customer, haka kawai saboda masu shigowa yin photo susa hankalin customer mu yatashi ba, a tafi dasu kawai"

Jin wannan furucin ne yasa Fatima ta Fashe da Kuka tana basu haquri


Tunda suka shigo Mall din shida Ramadan da sauran guard dinsa, baiji motsin kowa ba, dama Kuma hakan yakeso, shiyasa ma tun kafin yazo yaturo musu saqo ta Email cewa zaizo shopping mall din, yanaso abashi awa biyu yagama abinda zaiyi, idan yafita, Sai subar sauran mutane su shigo,yarinyar da yayiwa waliyi jiya, ita yazo ya siyawa gift yanaso yabata.

Kukan Fatima dakuma hayaniyar datake tashi tsakanin Auwal da sauran security shine yad'auki hankalin sa, ransa ne ya6aci, kwata kwata baison hayaniya arayuwarsa, cikin 6acin rai ya kalli Ramadan tareda nufar inda yake jin hayaniyar tana tashi, sannan yace "muje"

Jijjiga Kai Ramadan yayi sannan suka nufi wajan, guard din dake bayansa cikin sauri suka rufa masa baya.
Shan kwanar da zaiyi, Idonsa ya sauka akan Aisha(=?F? @&?)
Wata irin faduwar gaba ce ta ziyarceshi, Jiyayi Kansa yayi wata irin sarawa cikin sauri ya damqe hannun Ramadan yaja shi sukayi wata irin kwana suka dawo baya,duk da sunbar layin dasu Aisha suke gabansa bai daina faduwa ba, menene zai faru data ganshi? Mezai ce mata? Hakan yana nufin da yanzu asirinsa ya tonu kenan tasan cewa da Mahmud Wakili take mu'amula batare data saniba....., meya yakawota kano?

6oye fuskar sa yafara yi a Bayan Ramadan kamar wani 6arawo(=??)

Daga Ramadan har sauran body guard Kallan Shahaab suke da mutuqar mamaki, zare ido suka fara suna dube dube atunaninsu wani abun cutar wa Shahaab din yagani.

Cikin tsananin mamaki Ramadan yace "Shahaab lafiya? Meyasame ka?"

Yana 6oye a Bayan Ramadan din cikin fada yace "dalla malam Kamin shiru, duk ba kaine kajamin ba?"
Mutara zuwa gobe =?O? Ramadan yace "kamarya?, mekake nufi ninaja?"


"Tura musu mutum daya kace su sallami yaran can injini, sannan subata haquri"

Ramadan da mamaki yagama kasheshi, yace "okay" sannan yajuya ya kalli daya daga cikin guard dinsu yace "kace a sallami yaran can, sannan abasu haquri inji Mahmud Wakili"

Cikin sauri yanufi wajan da su Aisha suke, yana zuwa yayiwa daya cikin security din dasuke fada da Auwal magana.

Ramadan yadan leqo yaga abinda Shahaab yake gudu, anan yayi tozali da wata kyakykyawar yarinya, shagala yayi da Kallan yarinyar, fada dakuma tashin Hankali yasa Dan qaramin da kwalin abayar data yafa akanta yasa yayi qasa, dogon gashinta yafuto fili muraran, Shahaab daya d'an leqo da Kansa ta Qasan Ramadan Shima ya leqo yana ganin ta, ransa ne yayi baqiqqirin ganin dogon gashinta awaje, ribbon din daya daura mata shine akanta, haushin mazan wajan yafara ji dasuke tsaya tareda ita, yanzu haka kowama kallon gashinta yake, yasake Kallan Auwal da'ake fada dashi, cikin tsananin kishi yace "ko wanne yaro ne Kuma wancen?"

Ramadan ya juyo ya kalleshi, yaga fuskar Nan tasa tayi kicin kicin hankalinsa kacokam yana kan wancen yarinyar.

Su Aisha basu San menene yafaru ba Sai Gani tayi wannan securities din duk sun sunkuyar da kansu qasa suna fuskantar ta, har rige-rigen bata haquri suke, haushi da Kuma mamakin su ya kamata, yanzu yanzu suka gama cewa zasu kaisu folice station Amma Kuma suna bata haquri yanzu, kamar wasu masu Fama da aljannu, taqaici da 6acin ran da aka bata ne yasa tayi jifa da turaren data dauka, tajuya tafice cikin fishi, ice-cream dinma tafasa Sha,har suka fice daga mall din Ramadan bai daina kallonta ba, yarinyar tahadu ta ko'ina, babu wani namiji me lafiya dazai ganta yakasa yabawa.

Shahaab kuwa yana ganin yanda tafice cikin fishi yace"to 'Yan masifar sunzo"

Ramadan yajuyo yasake Kallan Shahaab daya 6uya abayansa Sai magana yake shi kadai, Kallan rashin fahimta yayi masa sannan yace "meyake faruwa ne?"


Wata irin ajiyar zuciya yasauke tareda Lumshe ido yabude, sannan yace "MAAMA"

Ramadan daya dauki haske cikin sauri ya zaro Idonsa yace "what...?"

Shahaab bai iya bashi amsa ba Sai Kansa daya daga masa kawai

Suna shiga mota Auwal yafara lallashin fati saboda kukan datake yi, saida tayi shiru sannan yaqara Bawa Aishan ma haquri, Bai qyalesu ba saida ya tabbatar sun Dan saki ransu, sannan sukai sallama suka shiga gida, Bayan sunyi shirin kwanciya Aisha banda tsinewa masu mall dinnan babu abinda take yi,ta nayi itama fati tana tayata, daqyar suka samu bacci ya dauke su


(Shahaab littafin kudine, idan kika karanta batareda kin biya ba, nabarki keda mahaliccinki, nide ban yafe a)

******

Tunda suka dawo masaukinsu Shahaab yayi shiru yana tunani shi kadai, Babban abinda yafi 6ata masa rai shine yanda ya ganta dawani yaro.
Ramadan ya kalleshi yace "Wai Dama haka yarinyar Nan take?, Shahaab Anya kuwa bahaushiya ce?"

Kansa ya jijjiga masa alamun hakane, ajiyar zuciya ya sauke yace "gaskiya tanada kyau sosai, amma Kuma yarinya ce sosai ya'akai Takeda kyan diri haka?"

Cikin masifa Shahaab yace "bansaniba, meya Hana kabita ka tambayeta?"

Murmushi Ramadan yayi, Bayan yagano kishi ne yake cin abokin nasa, ajiyar zuciya yasauke sannan yace "menene abun 6acin rai Kuma a magana ta?"

Cikin fishi yace "to kazo gabana Sai wani yabon ta kake, kaiba matarka ba, ba komai ba, ni abinda yafi 6atamin rai ma shine Yaron Dana gansu tare, bansan Yaya zanyi in tambayeta Shiba, zatace min Yaya akai nasan taje mall, idan nace Ina tareda ogana tace Amma nakasa yimata magana Ina Gani security suka ka masu, Ramadan duk kaine kajamin wannan abun, inda kabarni naje mata a Mahmud Wakili na, daduk haka bata faru ba, daga Kai har mama kira kuke idan zanyi mu'amula da mace tona 6oye mata kaina, na6oye mata koni waye, ta hakane zansan mesona tsakani da Allah, Ramadan ni banga amfani 6oyewa MAAMA kaina ba, saboda yarinya ce qarama, batada wani ilmi akan Zaman takewar rayuwa, yanda yarinyar ta yarda Dani idan saceta zanyi da tuni na saceta, na lura batasan komai ba akan soyaiya Sai abinda aka Koya mata,nafada mata banda aure, ta yarda, nafada mata nidan maiduguri ne, tayarda, nafada mata ni Yaron Mahmud Wakili ne, tayarda, duk wani abu Dana fada mata yarda take saboda tasan bazanyi mata qarya ba,nafada mata inason haihuwa idan nayi aure da bakinta tace zata fara azumin sitta shawwal tayi min addu'ah ko Allah zai ban haihuwa, yanzu Mena aikata haka? Inda nafada mata gaskiya tunda farko dazan iya futowa a ko'ina ne in kare ta amatsayina na Mahmud Wakili"

Jikin Ramadan ne yayi Sanyi,kafadarsa yadan bubbuga yace "kayi hakuri Shahaab...,Amma shawarar damuka baka nida mama itace mafita,inda bakayi hakan ba, zaka San halaiyar yarinyar ne kamar haka? Ni banga laifin taba dakake cewa baka sonta, wannan yarinyar babu inda bazaka shiga da'ita ba, asalima yarinya ce qarama Sai abinda ka dorata akai zatayi, Amma tunda baka sonta, kadena zuwa inda take, kanisanceta, idan Kai kasan zuciyar ka, ita bakasan Tata ba, zata Iya sonka, qarshe karabu da'ita, hakan bai kamata ba, karabu da yarinyar mutane kawai "

Cikin tsananin kishi Shahaab yace"Nina Rasa gane inda kanufa Ramadan, saika dinga nunamin kamar so kake narabu da yarinyar kaikuma kaje ka aure ta"

Dariya ce ta kama Ramadan, Amma saiya danne, yace "Aure kuwa da gudu"

Shahaab yayi masa wani irin kallo, cikin zuciyar sa yace zan dauki mataki, dole zan kawo qarshan komai, haka suka kwana babu wanda yasake magana, kowa da abunda yake saqawa acikin ransa, shikam Ramadan ransa fes yayi bacci, ko banza yasan ya tunzura Shahaab, dama da niyya yafadi hakan danya ga gudun ruwan abokin nasa.

******

Washe gari tunda safe, Aisha tatafi gida, tana zuwa Hajja ta tareta cikin murna, tsarabar Lemo da bread din data kawo musu suka rarraba har jummai saida aka kaiwa, cikin sauri ta shige dakin Hajja ta dauki wayarta tafara duddubawa ko Shahaab Yakirata, saide bataga komai ba, tunani tafara me zata siyo masa idan yazo tabashi Shima a matsayin tsarabar kano? Wani tunani tayi, cikin sauri Takoma Dakin Umman ta, asusunta dayake Qasan gado tafasa,dubu biyar biyar din daya bata sau biyu, dakuma dubu biyunta na albashin ta, tahada dubu goma Sha biyu, tasaka hijab dinta ta cewa Ummah da Hajja "natafi gidansu Walida yanzu zan dawo"

Hajja tace "dole kije Kam kwana biyu Baku hadu ba, itama rannan tazo nace mata ai kin tafi kano"

Aisha batace komai ba tafice, tana fita kofar gida bata nufi gidansu Walida ba Kai tsaye wata hanya ta d'auka, saida taci tafiya sosai, sannan taje wani Babban shago, tabawa me shagon kudin tace "gashi abani agogo da links"

Cikin sauri ya d'ago ya kalleta yace "to wanne Kala kikeso?"

Tace "Nima bansaniba ba, kawai kabani me kyau"

Murmushi yayi yace "to Wanda zai saka fari ne ko baqi?"

Tace "fari ne"

Cikin farinciki yabata agogon da links din tuwan toka yace "to wannan zaifi kyau"

Kar6a tayi sannan tafice, acikin hijabinta ta 6oye su, sannan Takoma gida tasaka su acikin kayanta


******

Da yamma yaga Shahaab sai shiri yake, manyan Kaya ne ajikinsa na wani yadi Mai mutuqar kyau, cikin mamaki ya sake Kallan sa yace "fita zamuyi ne? Naga Kanata shiri"

Cikin sauri yajuyo ya kalli Ramadan din sannan yace "fita zanyi de"

Daria ce ta kama Ramadan, yayi murmushi yace "to naji, Ina zakaje?"

Kai tsaye yace "jigawa"

"Amma Shahaab kasan fa jirgin safiya zamubi mutafi Abuja, yanzu karfe hudu, idan katafi yaushe zakaje harka dawo?"

Kallan sa yayi yace "akwai tafiyar dazanyi zuwa Australia goben da yamma idan mun koma Abuja Dasafe, tafiyar zata daukeni wasu Yan kwanaki masu yawa, dole zanje inyi sallama da Maama, ko zan tafi ne batare data Sani ba?"

Ramadan yayi murmushi yace "a a, Amma Dan Allah katafi Dani danna sake ganin ta" (=??)

Cikin daure fuska yace "zanyi sallama da yarinya kana cewa zakaje, idan kaje a'ina zaka zauna? Ka zauna anan kawai, zan saka face mask inje dakaina indawo"

Yana gama fadar haka yafice daga d'akin, Ramadan yasaki murmushi cikin ransa yace "Allah yakai damo ga harawa...."

Idar da sallar magrib dinta kenan, tafada duniyar tunaninsa, sotake ta kirashi, Amma Kuma tasan idan ta ta6awa Hajja katin waya to zata gane, Kuma ta dinga yimata mita kenan,kamar almara taji wayar tana qara,tana dubawa taga number shice, cikin sauri ta d'auka sannan tashige Dakin Hajja, cikin wata irin murya wadda zaka tabbatar yayi kewarta yace "Maaaamah"

Wani irin yarrrr taji ajikinta, ahankali tace "na'am"

Kai tsaye yace "Ina kofar gida"

Cikin murna tace "da gaske?"

Yace "sosai, kifuto yanzu"

Tace "to" sannan takashe wayar

Daki ta wuce tadauko abunda ta siyo masa dazu, sannan tafuto tana Sanye da hijabi dogo, Ummah ta kalla tace "Ummah zanje wajan Walida"

Kafin Ummah tayi magana Hajja tace "keni narasa gane wannan zarya da kike a gidansu Walida, kusan kullum Sai kinje inji de lafiya?"

Dan qaramin bakinta ta turo gaba tace "littafi zan kar6o fa"

Ummah tace "kuma kullum bakida aiki Sai zuwa da daddare? Kishiga hankalin kifa"

Hajja tace "Allah ya kyauta, toki tabbatar kina kar6owa Zaki dawo"

Cikin murna tace "to Hajja"
Sannan tafice daga gidan cikin murna, wannan motar bada ita yake zuwaba, Amma kasancewar tasan anan yake ajiye motarsa, saita nufi wajan, tana zuwa bata jira yafuto yabude mata ba, tazagaya ta bude tashiga, sannan tarufe, Kallan sa tayi cikin farinciki tace "Dama wallahi sonake naganka, na Dade inason muyi waya inbaka labari"

Cikin mamakin farincikinta yace "meyasa baki kirani ba to?"

Cikin shagwa6a tace "to ai idan na kiraka Hajja zata gane, Kuma zata San nata6a mata katin waya"

Cikin ransa yace Kati Kuma? A fili saiyace "Dama ba wayarki bace?"

Girgiza kanta tayi tace "wayar Hajja ce"

"wace Hajja?" ya tambayeta

Tace "kaka tace, Amma Kuma wayar a hannu na take wuni, inayin game da'ita, yanzu Kuma Dana dawo Naga duk ta gogesu daga wayarta" ta qarasa maganar idonta na cikowa da qwalla

Cikin sigar rad'a yace mata "menene na kukan Kuma? Kincika shagwa6a Maama, Kidena yin game, kici gaba da karatu yafi"

Murmushi tayi tace "kasan me? Inaso inyi karatu inzama likita, indinga aiki a Asbiti, inkai babana Saudia, nikuma saina tafi tareda Ummah na da Hajja"

Wani irin daci yaji acikin ransa, saboda idan akwai abinda yatsana to shine matarsa tayi aiki, baya fatan ma ace yarage ta tawani Fannin bare har tayi tunanin yin aiki domin samun kudi, matsayin matarsa yawuce tayi aiki abata kudi, saide ta dauki kudin tabawa ma'aikata, wata zuciyar tace dashi to ita matarka ce? Acan Qasan maqoshinsa yace "yes"

saboda kada ta gane yanayin dayake ciki na rashin son karatu,Sai yayi Murmushi yace "nikuma fa? Bazaki kaini ba?"

Dariya tayi, tace"kaima saimu tafi dakai to,kabani wayarka nayi game kaji"

Cikin ransa yace"kodan yarinya ce? Yanzu inashi Ina wani game a wayarsa? Kallan ta yayi a fili yace "banda game"

Cikin sauri tace "to cartoon"
Murmushi yayi yace "Shima babu"

Bakinta ta turo gaba tace "to photuna"

Daukan wayar yayi batareda tunanin komai ba yabata, saboda yasan shide babu pictures dinsa aciki, haka babu wata shaida dazata Gani ta tabbatar mata cewa shine Mahmud Wakili.

Kallan pictures takeyi dayawa na takardu ne Wanda batasan kona menene ba, wajan videos tashiga, anan taci Karo da video na wata mata da'akayi mata operation, cikin sauri tabashi wayar tareda fashewa da Kuka, cikin kuka tace "Dama haka ake ciro yaro? Bazan iya aikin asbitin Nan ba, nafasa, saide indinga saida Kati"

Dariya ce ta kamashi, cikin dariyar yace "da kudin katin Zaki kaimu Saudia kenan?"

Batace Masa komai ba Sai kuka datake, wayar yakashe gaba daya, sannan ya gyara zamansa yajuyo yana fuskan tarta, yarasa Yaya zaiyi mata, tacika shagwa6a dayawa, yanzu tayaya zai fara lallashin ta?
Ahankali yad'ora tafukan hannunsa a fuskarta yariqe fuskar Tata dakyau sannan yace "kiyi shiru, bafa haka akeba, kawai hadawa akayi, yi hakuri kinji?"

Kanta ta daga masa, hawaye ya silalo daga idonta, ahankali yasaka hannunsa guda daya ya share mata Hawayen, duk yanda yaso daqin ta6a dogon hancin ta, kasawa yayi, hannunsa yad'ora akan Karan hancinta yafara shafawa ahankali, rufe idonta tayi, hakan saiya qara yiwa fuskar Tata kyau, gashin idonta daya hadu da dan'uwansa yajiqe saiya kwanta yayi luf,cikin wata irin murya Mai Kama da rad'a yace "ogana zai turani qasar waje maama, Dan Allah karki kula kowa kafin nadawo kinji..."

Cikin sauri ta bude idonta, sannan ta janye hannunsa daga fuskarta tace "yaushe zaka dawo?"

Yace "zan'iya yin wata daya, mezaki Bani Wanda zan dinga tunawa dake?"

Cikin sauri tad'auko agogo da links din data siyo masa, ta ajiye akan cinyarsa tace
"gashi"

Mamaki yakama Shahaab, ya kalli abinda ta ajiye masa akan cinya yace"na menene wannan?"

Ahankali tace "siyo Maka nayi, kaima kasaka a hannun ka, tsarabar kano ce, kasan naje kano, tona siyowa su Hajja bread da Lemo, shine kaima nasiyo ma"

Mamaki ne yahana Shahaab magana, ya zuba mata ido yana kallon ta, yanaso ya tambayeta wanne yaro ne ya gansu akano Amma yarasa ta wacce hanya zai tambayeta? Sake Kallan agogon yayi, sannan yasaka hannu yacire agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya ajiye shi agefe, links dinma ya ciresu, sannan ya maida kallon sa gareta yace "to dauki kisaka min"

Kallan sa tayi tace "ai ban'iya sakawa ba"

Ahankali cikin qasa da murya yace "dauki saina gwada miki"

Babu musu ta dora hannunta acinyarsa tad'auki agogon, sannan ta dora tafin hannun ta akan nasa, wanne irin laushi taji hannun nasa nayi, agogon ta dora akan hannunsa Wanda gashi Yacika shi sosai, shagala yayi da kallon ta, dogon hancinta yake Gani dakuma yanda take qoqarin daura masa agogon, cikin shaqaqqiyar murya yace "wannan dayan zaki saka acikin wannan qofar, shikkenan"

Kallan sa tayi jin yanayin muryarsa tad'an sauya, sannan ta Girgiza masa Kai, tayi abinda yace, tana dauke hannunta yad'ora bakinsa akan agogon yayin kissing dinsa, sannan ya kalleta yace "nagode, saura link's din"

Babu musu Shima ta d'auka tasaka masa da temakon sa, suma saida yayi kissing dinsu, Aisha de tana ganin ikon Allah, sannan taga ya juyo yace mata "Ina kika samu kudi kika siyomin wadannan abubuwan?"

Cikin rashin damuwa tace "kudin daka Bani ne, nahada da Wanda nake Tarawa saboda qanina yatafi makaranta, shine nasiyo ma dasu"

Jiyayi wani irin shock ya kamashi, kudin da take Tarawa saboda qaninta yatafi makaranta? Hakan yana nufin shita sadaukarwa da kudin kenan saboda tayi masa kyauta yaji dadi,wacce irin yarda yarinyar Nan tabashi? Dama ashe akwai yarinyar dazai samu yanzu ta dinga bashi irin wannan kulawar? Ashe akwai yarinyar datake sonsa da gaskiya? Hakan yana nufin mama da Ramadan sunyi gaskiya kenan, yakamata zuwa yanzu ace yafada mata abinda yake ransa, ga Ramadan ma dayake kusa yana cewa tsaf zai iya aurenta, cikin sanyin jiki yamatso dab da ita, ahankali yad'ora Kansa akan cinyoyinta

Zaro ido tayi cikeda faduwar gaba, menene haka Shahaab yake mata? Hannu tasa tafara janye masa Kansa, Amma sai yaqi bata damar hakan,saina hips dinta daya riqe yajin kamar su dauwama Ahaka, dagewa tayi ta janye Kansa, cikin sauri yakama hannayenta yariqe da hannunsa biyu, Kallan qwayar idonta yayi sannan yace "maama kinason aure yanzu?"

Mamakin tambayar tasa tayi, saida tad'an juya idonta sannan tace "inaso Amma banason kishiya"

Gabansa ne yafadi, cikin sauri yace "meyasa?"

"saboda Hajja ita kadai ce, Ummah nama ita kadai ce, Nima nikadai zan zauna da mijina, banason hada komai nawa da wata, yaje can Dakin, yazo Nan dakin, nifa ko tunawa nayi anayin kishiya raina 6aci yake, Ina Gani a cewa wata mijina shine mijinta, idan yayi wani abu a Dakin amarya, yaje Dakin uwar gida yafada mata"

Cikin sauri Shahaab yace "koda mijin baida surutu?"

Itama cikin sauri tace "koda kurma ne, idan zan kirashi to inde yana gaban matarsa bazai dauka ba, nifa banason damuwa ko kadan musanman akan kishiya,namiji yaje wajan kishiya ta, Nima yazo wajena"(=?H?)

"yazo wajan ki yamiki mei?"(=?3?)
Yafadi maganar yana zaro Idonsa

Sai a lokacin tatuna dawa take magana, cikin wata irin masifaffiyar kunya tayi sauri ta 6oye fuskarta da tafukan hannunta

Murmushi yayi, sosai maganar Tata tabashi dariya, yar qanqanuwa da'ita har tasan kishi, idanu yazuba mata yana sake qare mata kallo, ahankali yamiqa hannayensa yakama fuskarta, Kallan sa tayi taga yanayin Idonsa yana sauya wa, ahankali tadora hannunta akan nasa hannayen daya riqe fuskar ta tana so ta janye masa hannayensa,Kansa ya Girgiza mata, yayinda yake sake matso da fuskar sa dab da Tata, gabansa ne yake faduwa, zuciyarsa na sake zigashi akan yafada mata abinda yake ransa,dogon hancinsa yad'ora akan Nata hancin, yahade goshinsu waje daya, lips dinsa yana gogor Nata, ahankali cikin muryar rad'a yace "maamaaaah....,maama Ina sonki"

Yanda yafadi maganar cikin wata irin murya, dakuma yanda take

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login