Showing 75001 words to 78000 words out of 116763 words

Chapter 26 - SHAHAAB COMPLT

Start ads

10 Aug 2025

804

Middle Ads

din za'a cewa a barshi da Aisha su zanta?>??
Kuma acikin daki su biyu?>??

Hannun Aishan takama suka wuce Dakin Hajja,yanda taji qamshin turaren yarinyar ya sauya akan Wanda tafita dashi, shine ya tabbatar mata da cewa Mahmud ba ido yazuba mata ba, Amma taji dadi tunda taga Hajja bata fahimci komai ba, Gara ayi magana guda daya gobe Dasafe, abawa Mahmud yarinyar Nan tun kafin azo ayi abun kunya.


Suna zuwa daki Aisha tahaye gadon Hajja ta kwanta tareda Lumshe idonta, sukan sabuwar hira suka dasa, yanayin yanda ya rungume tane yafado mata Arai,tasake tuna yanda ya furta mata cewa yana sonta ,wani irin yanayi take jinta aciki, cikin zuciyar ta tace"nima Ina sonka..."

Tun tana tunanin sa, har batasan bacci ya dauketa ba, Sai cikin dare ta farka taji su mama sunata zance itada Hajja, mamaki ya kamata, lalle an dade ba'a hadu ba, ita Kam juyi tasake yi taci gaba da baccinta.


A 6angaren Shahaab kuwa daqyar yasamu ya runtsa, Sai juyi yake yana murqususu shi kadai, yadade rabonsa da mace, yana fuskantar matsala ta kowacce jijiya ta jikinsa, yasan duk lokacin daya kama munirat a hannu, bazai mata da sauqi ba, saboda an dade ba'a hadu ba.(=?H?)
Haka ya daure, yaci gaba da yakice tunanin Aishan daga ransa, Bai yarda tunanin Nata yajanyo masa wanka ba, saboda agidan surukai da kunya katashi da asuba aji kana wanka.=??


Su mama kuwa saida sukai sallar asuba sannan suka kwanta, Alokacin Kuma Aisha bata koma bacci ba, azkar takeyi har gari yayi haske,kowa yana bacci duk basu tashi ba,tafuto tad'auki tsintsinya tafara share gidan, yana jin qaran shara yafarka, wayarsa yaduba yaga bakwai da rabi na safe, tunda suka dawo daga masallaci da asuba shida Abba ya kwanta Sai bacci yasake daukansa saboda gajiya, wayar ya ajiye yatashi yayi miqa tareda salati, sannan ahankali yazo bakin kofar Dakin ya tsaya, yadan daga labulen kadan yaga waye yake shara, karyaje yafuto Kuma yaga Ummah.

Ahankali yadan leqa,saiya ga Aisha ce, ajiyar zuciya yasauke yanda ta sunkuya tana sharar hakanne yabashi damar hango tsayaiyun boobs dinta, wani irin abu yaji ya tsirga masa tundaga Kansa har qafafunsa,ya hadiye wani irin yawu,lokaci daya yanayin sa yafara sauya wa, hannunsa yatura cikin aljihun jallabiyar jikinsa, Gara sutafi daga gidannan, inba hakaba idan sukace zasu sake wasu kwanakin to yanada tabbacin wataran bazai iya Hana hannunsa ta6a wadannan abubuwan ba.(=?2?=?H? )

Domin yaci gaba da kallon su sosai, saiya daga labulen yafuto ya tsaya abakin kofar Dakin, yaharde hannunsa a qirjinsa yana kallon ta, yadade a tsaye yana kallon ta, sannan yayi gyaran murya, cikin sauri ta d'ago kanta ta kalleshi, hannunsa yatura cikin aljihun jallabiyar jikinsa sannan yatako ahankali zuwa kusa da'ita yace"ina kwana?"

Kanta ta sunkuyar qasa,Babban mutum kamar wannan shine yake gaishe ta, Sai taji kunya ta kamata tace"lafiya kalau, dafatan kana lafiya"

Yace"um Gani nan de"

Kallan sa tayi da sauri, kafin tayi magana ya matso kusa da'ita, dan kwalin kanta ya janye qasa, lokaci daya dogon gashinta yafuto fili, cikin sauri tajujjuya ta kalli dakunan gidan, kar wani yafuto ya gansu, tana juyawa tana Kallan dakinsu Ummah hakanne yasa ta turo masa qeyarta, cikin sauri yasaka hannu yacire ribbon din kanta, dogon gashinta yabazu akan fuskarta, kallon sa tayi da sauri, kafin tayi magana yace"kinfi kyau ahaka"

Idonta ta furfuto dashi waje, tsoro takeji kar wani yafuto ya gansu Ahaka, cikin takunsa me aji yaqaraso wajan ta, yad'ora hannunsa akanta, yafara wasa da gashin kamar zaiyi mata kalba dashi, cikin jin dadi yace"kawo tsintsiyar na tayaki sharar...."jin takun mutum ne yasa ya tsaya cak!
Shibe cigaba da wasa da gashin ba, shibe saki gashin ba, gyaran murya Abba yayi, cikin sauri suka juya, wata irin kunya ta kama Aisha, Shahaab kuwa cikin sauri yasaki gashin Nata tareda komawa Gefe yana Dan shafa sumar Kansa, Amma ko kadan yaqi kallon Idon Abba, Dan kwalinta ta maida kanta ta tsugunna Tace"Abba Ina kwana"

Ataqaice yace"lafiya"

Cikin sauri tashige daki, Shikuwa Shahaab Kansa yana qasa,yace"barka da futowa"

Abba yayi murmushi, a ransa yana mamakin yanda Shahaab baya iya 6oye soyaiyar dayake wa Aisha, yanzu inda tabashi tsintsinyar sharar zaiyi kenan?>??
Kansa ya Girgiza tareda bashi hannu yace"yalla6ai ya gajiya?"

Shahaab bai bashi hannun ba, ganin yanda yake jin kunya yasa abban yakama hannunsa sukayi hanyar waje, yana fada masa akwai yan'uwan mahaifinsa, yakamata suje su gaisa dasu.

Aisha kuwa saida taji fitarsu sannan tafuto tana qarasa sharar, hararar inda suka tsaya itada Shahaab tayi, cikin ranta tace"bashida kunya, gashinan yaja Abba yaganmu"

Saida tagama sharar, sannan taje ta tambayi Ummah abinda za'a dora, Sai umman tafuto suka fara harhada abun Karin kummallon tare,har zuwa lokacin Hajja da mama,Sunata bacci, basu tashi ba.

Sai wajan karfe goma su mama suka tashi, basu zauna Zaman cin abinci ba Sai wajan shadaya na safe, Alokacin harsu Abba sun dawo shida Shahaab, yakaishi yaga dangi, yaga iyayensa, sun kuma yi maganar neman auren Aisha da Shahaab yakeyi, anan suka tabbatar masa zasuzo har gida Sai ayi maganar agaban Hajja, Bayan sun dawo gida wanka yayi, ya maida kayansa na jiya, Amma baisaka babbar rigar ba, ta cikin kawai yabari Sai hularsa daya dora, Sai hakan yaqara yimasa kyau yakoma tamkar saurayi, anan tsakar gida sukaci abinci shida Abba, Aisha tana cikin daki bata futo wajan su ba, Shahaab Kansa na qasa yana danna wayarsa,Mama ta kalli Hajja tace"to Aysha ai sai kuyi shiri mutafi ko?"

Cikin sauri Hajja tace"ina zamuje?"

Mama tace"Abuja mana, kina tunanin zan Barku kuci gaba da rayuwa anan ne?"

Hajja Tace"A a, banfada miki ba, dade Ina cewa duk lokacin Dana ganki to wajanki zan koma kodan in rabu da jarabar mesunanki ,Amma Kuma yanzu tunda akwai alaqa, akwai dalili, bazan biki ba, zan jinkirta idan aka daura auren takwarar ki, sainabi Yan kaiwa amarya mutaho tare, kude turo motoci masu yawa, Dan inada jama'ah, kinga jummai ma nasan itama zatayi gayya,tunda ta dalilin ta ne har Allah ya hadani dake koba haka ba"(=??)

Mama tayi dariya tace"to uwar gayya,har yanzu de kina Nan da jama'arki kamar baya,to aini banice meturo muku motoci ba, kin ganshi Nan, kifada masa"

Hajja ta juya ta kalli Shahaab tace"Kai Shahaabu, kanajina nida uwarka aiko?"

Murmushi yayi yace"Hajja hanya fa babu tsaro yanzu, za'a iya saceku acikin daji,kigama lissafin mutanan ki tsaf, saiki fadawa amaryar,duk yanda kukayi da'ita saita fadamin ta waya, inyaso saikubi jirgi, Amma kude bazaku dawo ba idan kunje, saboda haka kuyi sallama da kowa kafin kutafin"

Abba ya Girgiza Kansa yace"haba yalla6ai, a a baza'a yi hakaba, zamu dorama nauyi yalla6ai"

Batare daya hada ido da abban ba yace"Babu damuwa,koba Dan Aisha ba, dole zaku bimu kodan amintar mama da Hajja"

Ummah ce tafashe da Kuka tace"mungode Allah yasaka da alkhairi, Allah yaji qan mahaifin ka"

Gaba dayansu suka amsa da "Amin"

Hajja Tace"A a to tunda jirgi zamubi, bazanyi gayya ba, tun Ana abu na Hankali karkuma a koma na rashin Hankali, saboda haka duk Wanda yake min mutunci dashi za'ayi tafiyar Nan, lalla6a jummai zanyi inyi shiruuuu, tanamin abu komin qanqantar sa zan cireta daga list..."(=??=?2?)

Dariya suka saki gaba dayansu, mama tace"ni bakima kiramin ita mun gaisa ba"

Kafin Hajja tayi magana yan'uwan mijin Hajja suka shigo gidan susu uku, Hajja Tace"A a malam baqori kune a gidan? Sannunku da zuwa"

Ummah ce tasake shinfida musu wata tabarmar suka zauna, Bayan sunyi gaishe gaishe dakuma bayanin juna, anan aka tsaida lokacin biki sati uku masu zuwa, shi Shahaab asan ransa ma a saka sati biyu, saboda shi kadai yasan meyake ji, jiyake kamar ya hadiye Aishan kowama ya huta, Amma Hajja ta daddage tace saide a saka sati uku, kafin Nan sungama kintsawa.

Mama ce tad'auki kudin komai tabayar kamar yanda al'adar Garin take,daga Nan Kuma Shahaab yayiwa securities dinsa waya suzo su tafi, daga Nan shida Abba suka raka tsofaffin gida.

mama da Hajja suna zaune arumfa suna qulla Goro, Wanda za'a rabawa mutane, nasaka ranar Aisha,mama ta kalli Hajja tace"oh bakiga idon Shahaab ba da'aka saka sati ukun Nan, inajin da Kuka zai saki"

Hajja tayi dariya tace"naganshi,Dan qaniyarsa ai gata nake masa, a wannan lokacin nefa zan Dan samu Tasha magungunan Sanyi,muda muke neman haihuwa ai dole mu nemi maganin Sanyi, Shima idan kun koma akwai maganin dazan baki kitafi dashi saiki bashi yadinga Sha,idan akwai sanyin ma to zai rabu dashi insha Allah"

Mama yace"aikuwa zan bashi, zan dinga zaunar dashi Ina bashi yanasha,har komai ma bashi zanyi, ai ba ita kadai yakamata Tasha maganin matan ba, Shima saiya Sha irin Wanda yadace"

Haka suka dinga zancen su har mamakinsu Ummah takeyi, ko gajiya basayi da zance.
karfe biyu daidai sukayi shirin tafiya,Aisha tana daki tanaso ta ganshi Amma Kuma tana kunyar futowa, mama da Hajja sukayi gaba, Abba ya kalli Ummah yace"kira masa ita suyi sallama"

Daga Nan Shima yafice daga gidan, Ummah ta kalli Shahaab dayake tafiya kamar bayaso Dama Kuma Shima abinda yake ransa kenan, jira yake ko Yaya ne yadan kalleta kafin yatafi, Ummah tace"bari Akira ta"

Babu musu kuwa yaja ya tsaya, a gabansa tashiga d'akin Hajja sannan tafuto itama tafice daga gidan, yana tsaye tafuto daga daki tana Sanye cikin hijab, Kallan ta yayi yace"Maa-mah, banda yawo, banaso kina fita kowa yana kallon ki kinji ko?"

Daga masa Kai tayi sannan tace"insha Allah, Allah yakaiku lafiya"

Yace"Amin,saiki fara shirin tar6ata nanda sati uku, ni banso ma akasa lokacin har haka ba, kefa?"

Cikin kunya tace"jinake ma wata uku za'a saka"

Girgiza Kansa yayi, ya matso kusa da'ita yayi kissing goshinta yace"ki kulamin da kanki, banda kula maza, Sai munyi waya"

Tace"to insha Allah"

Daga Nan yafuto daga gidan cikin sauri, saida yagama sallama da mutanan dasuka zazzo Yan Garin yayi musu ihsani , sannan yashiga motar suka tafi, har lokacin Hajja da mama labari suke, saida mota taja, sannan suka juyo cikin gida, tundaga Nan Kuma mutane suke zuwa gidan Ana yiwa Hajja Allah yasanya alkhairi, jikar ta takusa aure.

(littafin kudi ne, idan kika karanta min baki biyaba nabarki da Allah)

******


Wannan Karon kawai Airport suka wuce sukabi jirgi shida mama, suna sauka a Abuja Kai tsaye gida suka wuce shida mama, munirat tana part dinta batasan sun dawo ba, zama yayi akan kujera cikeda gajiya, mama ta wuce wajan ma'aikatan gidan tana sanar dasu auren me gidansu nanda sati uku, yana zaune Idonsa a Lumshe aka masa waya, daukar wayar yayi tareda sallama"ranka yadade mungama tracking din number Nan daka turo mana,angama bincike akan number, yanzu haka yarinyar tana hannun mu, Amma tafada mana ba'ita kadai bace, itada qawarta ne, zamu turo Maka pictures dinsu da sauran information din damuka dauka awajansu ta Email dinka, sauran bayanin Kuma sai abinda kace"

Cikin sauri yace"babu damuwa,Sai munyi waya"

Kai tsaye Email din yaduba

Yana ganin fuskar su yarasa Ina yasan su, mama data dawo falon tayi magana taji shiru, tasake yimasa magana taji shiru, mamaki ya kamata, yazuba wa waya ido yana kallo kome yake kallo? Hannu tasa ta ta6oshi, cikin sauri ya kalleta, tace"tunanin me kakeyi haka?"

Wayar yabata yace"mama wannan sune Wanda suka hada wannan vedion da aka turo muku keda munirat, Amma Kuma narasa Ina nasan fuskokinsu, kamar de qawayen munirat ne"

Mama ta kar6i wayar, tana ganinsu tace"sune mana, qawayen tane, ai wani lokacin idan sunzo Ina ganinsu, tosu menene amfanin hada wannan shirmen? Menene ribarsu nayin hakan?shiyasa banaso munirat ta dinga mu'amula da qawayen banza irin wannan, yanzu banda raini yaza'ai suyiwa mijin qawar su haka?"

Cikin damuwa yace"shine abinda nagani Nima"

Tace"kaje ka sameta kuyi maganar, Amma su din karka yi musu komai, kabar su Suda mahaliccinsu, idan sunyi hakan ne da wata manufar ai gashinan Allah yatoni asirinsu, kodan mutuncin dasuke yi Suda matarka, karabu dasu, Amma kasa a qwace wayoyin su a duba sosai idan akwai irin vedion agogeshi, wannan 6ata suna ne, ita Kuma saika fada mata tasan irin mu'amular dazata dinga yi dasu"

Cikin gamsuwa da bayanin Nata yace"to mama"

Daga Nan yatashi yanufi part dinsu, yana tunanin tayaya zai iya yiwa munirat din maganar aurensa da Aisha?

Yana shiga falon nasu yaga TV a kunne ta nayi, Kai tsaye dakinta yanufa, yanaso ya nuna mata kuskuren ta akan laifin data masa na saida filayen mama, sannan Kuma ya hanata mu'amula da wannan qawayen Nata, saboda karsu dinga Zua suna hure mata kunne har taqi yarda suyi Zaman lafiya itada Aisha, gefe guda Kuma ga wata irin masifaffiyar sha'awa da yakeji, yadade-yadade, abun yamasa yawa, yana buqatar mace,da tunanin maganar auren nasa yashiga Dakin Nata, saide abun mamakin yana tura qofar yaji ta abude, tana zaune akan gado tabawa qofar Dakin baya,dinkin dake jikintane yamasa kyau, shiyasa ya tsaya daga bayanta yajingina da jikin qofar Dakin yana qare mata kallo, wannan ne Karon farko da yaji tsoron yiwa matarsa magana saboda auren dayake shirin yi, munirat kuwa waya take, kwata kwata ba taji shigowar saba, tariga tasan cewa baya gidan shida mahaifiyar tasa, shiyasa Hankalinta kwance taci gaba da fadin"suna dawowa zan sanar daku, zan San yanda zanyi in sakawa securities din maganin bacci alemo susha, Kuna ganin wayata kuzo ku kashe ta"(=?F? @&?)

Cikin tsananin tsoro, mamaki, dakuma firgici, Shahaab yazaro Idonsa waje(=?3?)
waza'a kashe?
Gabansa ne yafara faduwa, magana zaiyi mata, Amma saitaci gaba da cewa"karku damu, nafada muku babu matsalar komai, zan turo muku photon gidan, da inda zaku shiga har cikin dakinta, nafada muku Kuna zuwa kawai ku kashe ta, na tsaneta!, na tsaneta!!, na tsaneta!!!, tashiga cikin rayuwa ta tayi min Kane-Kane, ta hanani Zaman lafiya da mijina, harni zata bude baki tana fadawa zai qara aure, lalle-lalle ku tabbatar kun aiwatar da abinda nasaku,tsohuwa ce bazata muku wahalar kisa ba, Kuna kashe ta kushigo Nan Nima ku yanke ni, yanda baza'a gane dasa hannu na aciki ba, itama yarinyar dazai aura zan dawo kanta, karku kira wayata zan dinga kiranku idan buqatar hakan tataso"

Ruf idon Shahaab suka rufe, kwata kwata saiya daina ganin komai, baisan lokacin da qafafun sa suka fara rawa ba, saiji yayi yafadi qasa jagwab, salati yake acikin zuciyar sa, banda hannunsa guda daya da yakeji yana masa rawa, dayan Kuma ba yayi, saikace Wanda cutar 6arin jiki takeso ta kamashi, cikin ikon Allah yana motsa hannunsa yana salati har yaji hannun nasa yadena rawa, Idonsa yabude ras!.

Tun lokacin daya fadi tajuyo ta kalleshi, idan qirjinta yayi dubu, to yau gaba dayansu saida suka fadi, yanda gabanta yake luguden faduwa harji tayi kamar wani abu yafada cikinta, lokaci daya jikinta yad'auki karkarwa.

Shikuwa Shahaab wani irin kallo yake mata na tsoro, kisa!? Kisan mutum Kuma mutum dinma ba kowa ba Sai mahaifiyar sa?

Lokaci daya Idonsa yayi jajir!
Cikin sauri yatashi yawuce dakinsa, yana zuwa ya zauna akan gado tare riqe Kansa dayake masa barazanar rabewa gida biyu, wani irin kuka ne yazo masa Wanda Rabon Dayayi wannan kukan harya manta, kuka yake sosai harda shashsheka, acikin wannan halin tashigo Dakin nasa ta sameshi, tana zuwa ta zuba gwiwarta aqasa tareda sakin wani irin kukan, tsawon lokaci suka dauka Ahaka, shi yana kuka itama tanayi, saida taga bashida niyyar ce mata komai sannan tasa hannu ta riqe qafafun sa tace"my Dear, Dan Allah kayi hakuri, wallahi nadena, natuba kayafemin, bada nufi nayi hakan ba, kayi hakuri bazan sake ba"

Taqarasa maganar tana dora kanta akan tafin qafafun sa, cikin sauri ya d'ago Kansa tareda goge Hawayen Idonsa, muryarsa adake, kamar bashine yayi kukaba yace"MUNIRAT, kitashi kitafi gidanku daga yau Bana buqatar ki acikin rayuwa ta"

Cikin sauri ta d'ago ta kalleshi, hannunta tahade waje daya tace"mahmud nikake Kora daga gidanka yau?idan nayi niyyar aikata kuskure ashe bazaka Jani a jikinka ka nunamin illar hakan ba?Saboda kasamu wadda tafini?"

Runtse Idonsa yayi, cikin tsawa yace"munirat na tsaneki, nadauki yarda nabaki, na amince dake, nasoki fiyeda kowa abaya, banajin maganar mahaifiyata saboda soyaiyar danake miki, mama na itace komai nawa, itace mahaifina itace mahaifiyata, ban rageki dakomai ba amma kin dauki filayenta kinje kin siyar,banyi miki magana ba, kinsan ko saboda me? Saboda Ina sonki, qawayenki sun hada min vedio na banza da 6atanci nida yarinyar datake ganin darajar mahaifiyata kamar Tata mahaifiyar, sun turo miki, kin dauki gaba Dani, kin hanani haqqi na, now saboda maganar aure Harkina cewa kin tsani mama,aje akashe ta, akashe min mahaifiya ta munirat? Sakamakon dazaki nunamin kenan? Wannan shine tukwicin soyaiyar Dana nuna miki abaya? Yanda kikace kin tsaneta Nima na tsaneki munirat, kiyi hakuri bazan iya cigaba da zama da wadda bata qaunar mahaifiya taba, kifice daga gidannan, kifice daga unguwar Nan,kifice daga cikin rayuwa ta"

Gabanta ne yasake faduwa, dama yasan da maganar takardun data sace? Wata irin tsananin kunya ce tasake rufeta, taji kamar qasa ta tsage ta shige ciki, lokaci daya jikinta yayi Sanyi kalau, bata taba nadamar abinda take aikata masaba Sai yanzu, ta Kuma yi Imani tabbas Mahmud yana sonta, domin kuwa Mai sonta ne kawai zai'iya yin haquri da maganar filayen Nan batare Dayayi mata hukunci ba, ta kalleshi Tace"Mahmud...."

Kafin taci gaba da magana ya dakatar da'ita ta hanyar daga mata hannu(>??
Cikin tsananin firgici tasake cewa "Mahmud...."

Idonsa ya runtse, ko kadan baison sake ganin fuskarta, cikin 6acin rai yasake cewa"munirat, namiki saki na biyu kitashi kibar min gidana"

Zaro idonta tayi, mamakine yasa tasake cewa "mahmu...." kafin ta qarasa cewa Mahmud din, yasake cewa "munirat.....namiki...."

Cikin sauri tatashi tafice daga d'akin tana kuka mecin rai, ta tabbatar idan bata fitaba, yanda ransa yake a6ace, to idan Ana saki goma, yau zai iya yimata shi.

Ko Kallan dakinta bata Kuma yiba, ta warware Dan qaramin mayafin data daura akanta, ta nufi bakin get tana kuka me tsananin ciwo















(haba Shahaab.... =?-?=?-?=?-?)


(wayyo Anty Munirat >?y?>?y?>?y?)


Allah ka rabamu da sharrin zuciya >?2?




Shahaab littafin kudi ne, idan kika karanta baki biyaba nabarki keda Allah, nide ban yafe ba


300 kacal
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN tareda shedar biya ta wannan number 08033300034











Mrs Usman ce
'




Page 25





Kasancewar ta matar megidan yasa kokusa basuyi kuskuren hanata fita daga gidan ba, hankalin megadi yaqi kwanciya, ya hanzarta zuwa cikin gidan, yasamu mama tana dudduba kayan da Hajja ta hado mata tataho dashi a leda, cikin rawar jiki Yace"Hajiya...ga Hajiya qarama can tafita tana kuka, da alamun ba lafiya ba, shine nace Bari nazo na sanar dake"

Cikin sauri mama tatashi tace"subhanallahi, Bari inje part din nasu"

Tashi tayi tafice ta nufi part dinsu, zata Iya cewa rabonta data zo part din Shahaab harta manta, saboda bata zuwa gudun kar taga abin 6acin rai, ita Kuma bazata iya yin shiru

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login