Showing 6001 words to 9000 words out of 116763 words

Chapter 3 - SHAHAAB COMPLT

Start ads

10 Aug 2025

787

Middle Ads

meyasa batason munirat Kai tsaye tafuto tafada masa cewa matarsa kudinsa tagani shiyasa ta aure shi, sannan akwai alqawarin dasukai itada qawarta cewa zasu hada yayansu aure, Kuma yasani muddin Aysha ta bayyana Tofa saiya auri yarta inde mace ta Haifa, idan Kuma ba mace ta Haifa ba shikkenan.

Tun daga lokacin idan tasashi yayi wani kokari akai Dan agano qawarta, Sai yayi mursisi da batun, saboda bayason maganar hadin auren Nan datake yi kokadan.

Akwai lokacin data dameshi akan maganar, Amma Shahaab yaqi yayi mata binciken, tayi zuciya tafice tabar gidan a hanya kidnappers suka saceta (=??)

Saida yasha wahala kasancewar sa sannane yasa hukumar tsaro ta qasar tabashi hadin Kai har saida aka kamota daga hannunsu, tundaga lokacin ya zubawa gidansa tsaro, sojoji ne suke gadin mama, banda Yan sanda dasuke Gefe suma suna nasu aikin.

To dayaga de mama da gaske take, shine yabada sanarwa a kafafen sadarwa dakuma yanar gizo, ganin yanzu harkar yanar gizo kowa yanayin ta, shiyasa yayi tunanin za'a iya samun labarin qawar ta mama, abinda bai saniba shine Hajja A'i Kam vivo gareta itama screen din duk ya Fashe, wannan gidan ta abincin dazasuci sukeyi, bata yanar gizo ba(9&?)

To ganin haka yasa hankalin mama ya kwanta, Amma idan ta tuna qawarta, ranar haukace masa take, tun yana bata haquri harya dawo Shima yazama kamar ta, ya dinga zigata, to saita sauko su zauna lafiya.

Tsawon wannan shekarun munirat ko 6atan wata bata taba yiba, data fahimci hankalin mama dakuma shi Kansa Shahaab din yana kan haihuwa, saita shiga damuwa, akan yanda suke nuna son haihuwar, danhaka Sai take jinyar qarya, dasu amai, mama da Shahaab hankalin su yatashi, suce taje Asbiti taga likita ko ciki ne, saita kar6i maqudan kudade awajansa daga baya Sai tace ai ba ciki bane, tayi haka yakai sau uku, mama kuwa tariga tagane kawai kudin yarinyar takeso, bawai Shahaab din ne da haihuwar suka Dame taba

Tarasa Yaya zatayi, aure tsawon shekara Tara babu ciki, but ita hakan bai dameta ba saboda tana cikin daula, ko neman magani batayi, shikuma duk lokacin daya shirya yatafi Saudia Tofa addu'arsa daya ce akan Allah yabashi haihuwa, ita kuwa mama burinta guda biyu ne, nafarko taga qawarta, na biyu Kuma taga Shahaab ya haihu.

Duk juma'ah Ana bada abincin sadaka a gidan, kunu, abinci, dakuma bread tareda nera Dari biyar, wannan Kuma aikin mama ne, tana bada sadakar ne saboda Allah yakaiwa mijinta dakuma ahlinsa ladan.
Ta bangaren Shahaab kuwa lokaci zuwa lokaci yana yin tasa sadakar, Amma yafiyi lokacin zuwan azumi, yana sauke farashin kayan da kamfanonin sa suke sarrafawa domin talakawa su iya siya.

Back to story =?L?
******

Jigawa

Aisha ce take sallah, Hajja na gefenta tana Jan carbi, ta kalleta tace "mesunan qawa kiji tsoron Allah, wannan ba sallah kikeba, sallah batafi minti goma ba an idar"

Aisha batace mata komai ba, Sai abincin ta data Dauko tafara ci,batare data cire hijabin jikintaba, qwaine guda daya akan abincin Nata Wanda qawarta Walida tabata, Hajja taleqa kwanon abincin Aishan tace "Menene wannan nake Gani aciki?"

Cikin gatse tace "gishiri"

Hajja tata6e baki, Sannna taja bakinta tayi shiru tana kallon yanda gumi yake jiqa mata fuska, har gashin gaban goshin ta ya kwanta yayi luf-luf dashi, Amma Dan masifa Taki tacire hijabin jikin Nata, bacci ma wani lokacin da hijabi takeyi, tarasa Ina mesunan qawa tad'auki wannan dabi'ah

Wani yaro ne yayi sallama yashigo gidan yace "Hajja A'i abani kunun Aya na nera Dari"

Tace "idan Sadiya ce ta aikoka kakoma kace mata akwai kudin rannan ma"

Yaron yajuya yatafi, baifi minti biyar ba Sai gashi ya dawo, yace "Wai tace babu,bakya Binta bashi"

"au haka tace?, to shikkenan taje na rataya awuyanta, kawo Darin abaka"

Kudin yabata, Aisha tamiqe ta bude Dan qaramin fridge din Hajja tabashi kunun ayar, yatafi

Jabir ne yashigo gidan, Bai nufi wajan Ummah ba Kai tsaye rumfar dasu Hajja suke zaune yaje, ya kalleta yace "Hajja Dan Allah kisiyar min da wayar ki dubu uku"

Tace "kawo dubu biyar de saina baka"

Dariya yayi yace "wayarda batafi dubu uku ba?"

"aikuwa bazan siyar ba saide dubu biyar"

Aisha ta Kalle su tace "kawai kabata dubu ukun in taga Dama ta kar6a kokuma tabarshi"

Hajja ta yatsina fuska tace "yo Ina yaga dubu ukun ma?"

"Arziqi Aina Allah ne, Shima wataran zaiyi"

Hajja najin wannan furucin na Aisha saita Fashe da Kuka, da gudu umma tafuto daga daki tana tambaya "Hajja meyafaru kike kuka? Keda waye?"

Cikin kuka tace "nida mesunan qawa ne, nariga nadade da sanin me sunan qawa d'auka ta take a matsayin sa'arta, tunda taga ta girma tafara nono shikkenan ban'isa inyi magana ba acikin gidannan, saide in fad'a itama tafad'a,inda ace nasan haka halin yarinyar Nan yake tun farko daban Bari ansaka mata sunan qawata ba, saboda Bahaka halin qawata yake ba, saide in uwarta ce take Koya mata rashin kunya"(=??)

Ummah tanajin haka tafara hawaye, duk lokacin da fadan Aisha da Hajja zai tashi, to akanta take hucewa, Kuma ita bata Isa tahana Aisha zuwa wajan Hajja ba, Kota hanata ma Sai taje, Kuma ko tayi zuciya taqi zuwa inda Hajja take to Hajjan da kanta take zuwa sutafi

Ganin Ummah na kuka Sai hankalin Aisha yatashi, menene laifin Ummah anan daza'a ce itace take Koya mata rashin kunya, cikin 6acin rai ta kalli Hajja sannan tace "niba abinda Ummah ta take koyamin, gaba daya halin me sunana nabiyo, haka kawai antashi ansaka min sunan matarda banma santaba, qila ma tamutu" (=?F? @&?)

Abbansu ne yashigo gidan dawowarsa kenan daga rumfarsu inda yake aikin facin tayar mota Kota machine, kukan Hajja ne yaqaru, cikin kuka ta kalli Aisha tace "ta Allah ba Taki ba, insha Allahu qawata tana nan da ranta, Kuma tana bayyana zan tattara kayana intafi inbar miki gidan ubanki"

Abba ne ya kalli Aisha yace "ke rufemin baki anan, marar kunya kawai"
Sannan ya kalli Hajja yace "Hajja Dan Allah kiyi hakuri Kidena kukan Nan, mesunan qawarki batada Hankali yarinya ce Kidena biye mata Kuna sa'insa Dan Allah"

Jan zuciya tayi tace "ai tashen balaga takeji,Kuma wallahi Mamuda bazan haqura ba saika Nemo min qawata kokuma kaje ka siyomin ruwan Roba"

Jabir da dariya ta kamashi saiya silale yabar gidan, Abba kuwa shiru yayi yana tunani, toshi yanzu Ina zaije neman wannan qawar ta Hajja? Shida ba aljani ba tayaya zai dinga yawo gari gari yana neman Aysha Yakubu sagagi, toma Aysha Yakubu nawane a Nigeria?>??
Har gara ruwan ma, danhaka ya kalleta yace "kiyi hakuri to, zan siyo miki ruwan, wanne iri kike so?"

Babu kunya tace "Faro" (>?#?)

Yace "to kiyi hakuri yanzu zanje nasiyo miki" daga Nan yajuya yafita daga gidan, itama ta dakawa Aisha Harara, Sannna tashige cikin dakinta.



SHAHAAB littafin kudi ne, Naira 300 kacal babu yawa,kibiya kafin free page su qare, zaki turo 300 ta wannan account din


0164549488
Amina muhammad
GTbank


Zaki turomin shedar biya ta Number ta 08033300034
(Romance)


Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook =?G? https://www.facebook.com/amnahel


5&6


Baifi minti talatin ba ya dawo hannunsa d'aukeda baqar leda, yana zuwa yawuce Dakin Hajja yakai mata ruwan, budewa tayi taga faro ne guda biyu, tasaka hannu ta bude dayan tafara Sha, Sai da yaga fishin dake kan fuskarta yadan Kauce, sannan yatashi yafuto daga d'akin.

Aisha yasake yiwa fada sannan yashige dakinsa


******
ABUJA

Atamfofi ne a gabanta da shaddodi masu shegen kyau, d'ad'd'agasu takeyi tana magana cikin Isa "kayan sunyi kyau, Kuma sun kawo min su daidai kamar yanda nayi oder"

Ta kalli daya daga cikin ma'aikatanta tace "jeki kiramin munirat"

Cikin ladabi ta amsa sannan tajuya, Bayan wasu mintuna tadawo tace "Hajiya tace gatanan zuwa"

Jijjiga kanta tayi cikin ranta tana fadin lalle munirat ta'isa,intura aikiranta Amma saboda ta nunamin ita yar zamani ce batazata biyo yarinyar sutaho tare ba, saita nunamin itama tanada iko saboda tana auren Shahaab

Saida aka dauki kusan minti talatin sannan taqara so part din na mama,aqasan kafet din ta zauna tareda fadin "Gani mama"

Saida takusa minti goma, ta tabbatar ta6ata mata lokaci kamar yanda Itama tayimata, sannan tatura mata kayan tace "ga kayanki Nan, kidauki kikai wajan dinki"

Cikin ladabi ta d'auka tareda yimata godia, Sannna Takoma part dinta

Tana zuwa dakinta ta zubar da kayan tafada kan gadonta tareda fashewa da Kuka, ita kenan suturar dazata saka ma batada ikon dazata siyo da kanta taza6i irin Wanda take so saide sirika tasiyo takawo mata?

Yaya zatayi da wannan tsohuwar ne? Bata Rasa komai a gidan mijinta ba, wannan matar ita kad'ai ce ta tsaye mata, tarasa Yaya zatayi da'ita, wayarta ta janyo takira qawarta Mery, saide jin wayar Tata akashe yasa takira mamanta, cikin kuka ta zayyane mata komai, daga qarshe mahaifiyar Tata shawara tabata akan hanyoyin dazata dinga samun kudi ta hannun Shahaab, saita dinga siyar kalar kayan Dayayi mata, jin wannan shawarar ne yad'an sanyaya mata ranta.



******



Zaune yake a Babban office din companyn sa na takalma dake lagos, Sai wasu mutane guda biyar dasuke fuskantar sa, cup din tea ne a gabansa Sai turiri yake da alama yanzu aka had'ashi

Wata takarda ce agaban su Mai d'aukeda zanen taswira ta wani qaune dake jihar oyo, daya daga cikin su ne yake tsaye, gaban wata babbar TV dake manne abangon office din, yana Sanye cikin suit kamar yanda gaba dayansu itace Sanye ajikinsu, saide Shahaab yacire jacket dinsa yasakata a jikin kujerar dayake zaune, yad'ora Kansa a jikin kujerar ya kishingida kujerar Sai juyawa dashi take, Hankalinsa gaba daya yana kan matashin dake yin bayanin wajan daki-daki, wani ruwa matashin ya nuna yace "kwata kwata bangaren da zamu Gina company bashida ruwa, Amma a opposite dinsa akwai ruwa sosai Wanda yake wucewa, saide akwai titi a tsakani, sannan kamar yanda muka tattauna da gwamnan jihar, yabamu tabbacin cewa inde zamu ninkawa masu gonakin wajan kudin gonarsu to zasu siyar mana da gonakin, saboda Nan ne yafi da cewa da Gina company shinkafa, dazaran mungama zamu yi gada, wadda motocin zasu dinga bi ta wannan kan gadar, mukuma saimuja ruwan ta qarqashin gadar, wannan shine zanan wajan dakuma yanda yake, ga Kuma yanda tsarin ginin company zai kasance Bayan an kammala ginawa "

Ajiyar zuciya Shahaab yasaki, yace" duk Wanda zamu sayi gonarsu dake wannan dajin, ba ninki biyu na kudin gonarsu zamu basu ba, zamu basu ninki uku insha Allah "

Tafi sauran mutanan sukayi, saikuma daya daga cikin su yace"amma akwai yar qaramar matsala fa oga, nafarko daji muka yanka zamu fara wannan aiki, Amma munyi bincike mungano ginin yayi daji dayawa, yakamata ace wajen ya kasance na jama'ah dayawa ta yanda muma zamu amfanesu, suma Kuma su amfane mu, hakan zaisa kamfanin mu yazama kamar wata kasuwa ce ta daban da kowa zaiyi burin zuwa wajan, duk Wanda yazo wajan, dole zaiso jin farashin shinkafar mu, daga Nan mukuma zamuyi kokarin janyo shi jikin mu harya zama Babban customer awajan mu "

Kallan su Shahaab yayi yace" why not mu qirqiri gari awajan?"

Wani ne daban yace"tayaya?"

Shahaab yace" tunda wajan daji ne, saimu qirqiri gidaje,kamar guda Dari biyu, daidai Zaman mutum daya zuwa biyu, Sai mu rabawa mutane mabuqata, Wanda muka tabbatar basuda gidan kansu saina haya, kaga saisu dawo Nan suci gaba da rayuwar su"

Nan da Nan sukayi na'am da shawarar tasa.

Sign yayi akan takardar dazasu bada kwangilar aikin gidajen, saboda yanaso aikin ya kammala cikin Dan qanqanin lokaci, ba kowa yake son mallaka wa kamfanin ba face munirat, yasan cewa zatayi farinciki sosai, bayason ita kanta tasan da aikin, saide kawai ya gabatar da'ita a matsayin mamallakiyar kamfanin.



******


Da azahar suna zaune atsakar gida cikin yar qaramar rumfarsu, Almajiri ne yayi sallama gidan, yakawo mata jarkokin da aka siya kunun Aya a kofar gida tace"dan malam koma kasake dubamin akwai wasu jarkokin,ba dukane ba"

Almajiri yace "babu jarka Sai guda daya,Kuma Haladu me p.o.s ne yaturata cikin shagonsa yatafi masallaci"

Cikin jin haushi tace "ai shikkenan, qyaleshi, Sai yaje ya kaiwa uwarsa ta dinga d'ura kalanzir aciki, dama sana'ar tace" (=??)
Ummah da Abba sukai murmushi, sude basu Tanka mata ba, suna tsoron tahuce akansu

Tashi tayi tashiga Dan qaramin kitchen dinsu na ginin qasa, tafara zuba abinci, Wanda Aisha tagama girkawa yanzu, Alokacin itama Aishan tazo zata sakawa Abba nasa abincin acikin kula, Hajja ta kalleta tace "yanaga kinata raragefe, zoki dauki abinda Zaki dauka mana, keda gidan ubanki?"

Ganin Abba yana Nan yasa Aisha bata ce mata komai ba, kawai ajiye kular tayi, Takoma Dakin Ummah tayi Zaman ta

Ko minti uku batayi ba saiga Hajja tabiyo ta Dakin, hannunta dauke da ruwan faro Wanda Abba yasiyo mata jiya, Tasha daya, dayan Kuma tabar wa mesunan qawa=??
Bata tayi tace "ga ruwanki na jiya, na jira kizo kwana da daddare naji shiru bakizo ba, shine na ajiye miki"

Kar6ar ruwan tayi tana cika tana batsewa, Hajja tata6e baki tace "yar Albarka me sunan qawa, ga niqan Aya ta can zoki tacemin ita, sonake na durashi a jarka yanzun Nan"

Murya can ciki tace "to"

Hajja tafuto daga d'akin Takoma Nata Dakin, shiru shiru tana jiran Taga Aisha tazo tayi mata aikin data sakata Amma taji shiru, daga murya tayi tace "mesunan qawa idan bazaki Dena dauremin fuska Ki futo ki tacemin ayar nanba toki dawomin da abata daki, kar akuyarki ta kunce tazo ta shanyemin kijanyomin nayi asarar ayata"

Ummah dake zaune awaje itada Abba, tace "kifuto kiyi abinda aka sakaki mana"

Futowa tayi tana mita qasa qasa, "asara tanawa Kuma, aikuwa itace tasai asara tunda batada qanqara Kuma basu kawo wuta ba, kullum mutum yana abu daya, idan baya gindin murhu to yana wajan Tatar kunun Aya, kwana biyu da mukai fadan ma ni harna huta"

Hajja datake jiyota tana mita tace "to mesunan qawa idan baki tacemin ba waye zai tacemin? Ko mamuda zansa ya tacemin ayar?, saboda wa nake sana'ar? Saboda auren ki ne"

Aisha batace mata komai ba,haka ta tatace mata kunun ayar tsaf, takai mata shi gabanta, Hajja tabata kujera tace "sannu me sunan qawa, zauna anan to"

Zama tayi cikin shagwa6a tace "Allah Hajja nikidena min zancen aure na"

Murmushi Hajja tayi tace "to shikkenan yawuce, yanzu de shawara Zaki Bani, sonake nasiyo tinkiya ko Rago, da Dan kudin Dana Tara na ciniki, idan Allah yasa jabir yasamu gurbin karatu, Sai a siyar da'ita abiya masa kudin makaranta, idan Kuma auren ki yariga karatun nasa tashi, Sai a siyar acika ayimiki kayan daki Mai kyau, Amma ke Yaya kika Gani? "

Ummah dake zaune wajan Abba tayi murmushi duk da bata ji amsar da Aishan ta bayar ba, cikin ranta tana mamakin shaquwar Hajja da Aisha


Da yammah Hajja tasa Abba yasiyo musu kifi, da kanta tashiga kitchen din nasu tana dafawa, saboda tasan cewa me sunan qawa yau taje makaranta Kuma tagaji, Aisha datake duba jarabawar Yara kasancewar sun kusa hutu sakamakon gabatowar watan azumi, tace "Hajja me kike dafa mana ne?"

Cikin tsokana Hajja tace "Kifi ne qwaya biyu nake dafawa bawani abun kasawa a faranti bane"

Itama Aisha tace "Alhamdulillah tosaikici daya kibani daya"



******



Zaune yake akan wasu lafiyayyun kujeru masu laushi a balcony din falon Mama, Wando ne ajikinsa three quarter, da wata Riga yar qarama wadda ta kama jikinsa, kana hango yanda faffadan qirjinsa zuwa jikinsa yayi wani layi layi, dantsan hannunsa yafuto sosai, coffee ne a gabansa Amma yakasa Sha ya zubawa sojojin dake shawagi a harabar gidan ido, azahiri su yake kallo, Amma badini tunanin rashin haihuwar sane yake damunsa, yayi tunani sosai, amma yarasa mafita, maganar Babban abokinsa Ramadan Wanda yaje Italy yake shirin dawowa jibi, itace take masa yawo acikin qwaqwalwar sa, (Yakamata ka qara aure Shahaab, mutum baya cire rai da Rahmar Allah,tsawon shekaru kaji shiru daga bangaren munirat why not kasake auren wata yarinyar ka gwada kagani ko zaka dace? Wani lokacin idan ta cikin gida ta dade bata haihu ba Ana auran ta biyun idan tasamu ciki zakaga itama dayar Allah yabata idan da rabo, sannan karka kuskura ka nunawa yarinyar dazaka aura kanada kudi, tahakanne zaka samawa yayanka uwa tagari....)

Ajiyar zuciya yasaki, Sannna yafara magana cikin zuciyar sa "matarda zan aura, kowa de matarda zan aura, mama kullum maganar ta, matarda zan aura, Ramadan kullum maganar sa Matarda zan aura, tayaya zan'iya yin shigar talakawa saboda neman aure?, inde tana sona menene hadinta da kudi na? Dama a yanzu akwai yarinyar dazata iya auran wani Bayan ya nuna mata bashida kudi? Tayaya mama da Ramadan suke tunanin wata zata Iya sonsa badon abun hannunsa ba? Zata so shi koba kudi? Wacece? A'ina take? Idan yayi hakan Anya yayiwa munirat adalci kuwa?)

Mama tada Jima a tsaye tana kallon sa, duk yanda akai yana cikin damuwa, duk da tasan Dama ba magana ce ta dameshi ba, Kuma tasan cewa Shiba neman aure yake ba bare tace yana tunanin budurwa, to tunanin me zaiyi? Ta tambayi kanta

Kafadarsa ta dafa tace "kode ansamo min sabuwar suruka ne, Ana Nan Ana tunanin ta?"

Murmushi yayi, dimples dinsa suka futo duka biyun, hannunta data maida cikin sumar Kansa ta Yan asalin Nijar yad'ora nasa hannun akan Nata, ya d'ago Kansa yana Kallan ta yace "idan akwai kece mutum ta farko dazan fara sanarwa mama"





SHAHAAB littafin kudi ne, ki biya naira 300 kacal ki karanta abinki Hankali kwance kafin free page yaqare, siyan nagari maida kudi gida=؃?
Zaki tura 300 ta wannan account din

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaki tura shedar biya ta wannan number 08033300034

Amnah El Yaqoub
' [13/09, 20:50] +234 803 697 8511: (Romance)


Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook=?G? https://www.facebook.com/amnahel




7&8



Munirat datazo part din maman domin yin dinner, ta tsinkayi zancen dasuke shida mama, gabanta ne yafadi, ahankali tajuya zuwa part dinsu, kwata kwata saitaji abincin ma ya isheta, ko inda take saka qafarta bata Gani, daqyar takai kanta d'akinta.

Numfashin tane yake sama sama kamar Wanda zai dauke.
Ahankali taji hawaye sun zubo mata, tarasa meta tsarewaa tsohuwar Nan datake so taga Bayan auren ta, tayi biyaiyar, a banza, tayi kissar a banza, daga ganin mutum a zaune Zaki d'ago masa da maganar aure? Idan bashida ra'ayin auren ma ta tabbatar wannan matar saita saka shi yayi, tana son Shahaab tana kishin sa, bazata taba jurar ganinsa da wata yarinyar ba, hakan bazai taba iyuwa ba, Mahmud natane ita kadai.

Lokaci daya taji tatsani mama, duk mutumin dazaisa dansa yaqara aure, a yimata kishiya tabbas wannan mutumin Babban maqiyinta ne.


Ahankali mama ta sunkuya tayi kissing goshinsa, sannan tace "Allah ya nuna mana,

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login