Showing 42001 words to 45000 words out of 116763 words

Chapter 15 - SHAHAAB COMPLT

Start ads

10 Aug 2025

807

Middle Ads

jin lips dinsa yana ta6a Nata, hakan ne yasa tashiga wani irin yanayi Wanda bata ta6a tsintar kanta aciki ba, cikin salon shagwa6a da narkewa yace "kema kina sona?"

Gabanta ne yafadi, numfashinta yana fita da sauri da sauri, idan tace bata sonsa tabbas tayi qarya, ahankali ta bude Dan qaramin bakinta tace "Nima Ina sonk...."kasa jurewa yayi, Bai Bari ta qarasa ba yahade bakinsu waje daya.

Wani irin qarfi taji yazo mata, Nan take tafara kokarin hanashi abinda yake, Amma ruqon Dayayi mata yasa takasa qwacewa, tanajin yanda yake tsotsar bakinta ahankali kamar yasamu sweet.

Jikinta ne yafara rawa, bata sababa, bata ta6a aikata hakan ba, wannan ne dalilin dayasa take jin komai Sabo agareta, bata iya yimasa komai ba, tana jinsa yana shan bakinta son ransa, saida yagama kissing din Dan Kansa, sannan ya zare bakinsa ahankali, har yanzu hannunsa yana riqeda fuskarta, cikin qasa qasa da murya yace "ki kula min da kanki maama,karki kula kowanne saurayi Dan Allah, Ina dawowa daga qasar waje zanzo inyi magana da Abban ki"

Daga masa Kai tayi cikin mutuwar jiki, batareda tace komai ba ta bude motar tafuto sannan tarufe, akan idon malam Manu maqocinsu, Wanda tun shigar ta cikin motar ya ganta, haka Kuma yaga futowar ta (=?F? @&?=?3?)

Kai tsaye gida ta shige tana tafiya hannunta yana kan lips dinta Wanda yaji tsotsa, tunani take Dama wannan ne kiss din?.
Kai tsaye d'akin Hajja ta wuce, tanajin Hajja tana cewa "mesunan qawa fira tayi dadi yau kin dade awajan Walida"

Bata amsa mataba ta qarasa shigewa daki tareda fadawa kan gado, wani irin yanayi takeji ajikinta Wanda tarasa gane Kansa

A 6angaren Shahaab kuwa daqyar ya'iya komawa kano, Alokacin shadaya da kwata na dare, hannunsa akan mararsa yashiga gidan da akayi musu masauqi,yadade acikin motar yana kar6ar caji kafin yabude motar yafuto, duk yanda yake jin azaba daga ciki, Bai Bari Ramadan yagane halin dayake ciki ba (=??)

Kai tsaye toilet yashige domin tsaftace jikinsa.


******

Yau kwana biyu kenan da tafiyar Shahaab Australia, tana lura da Abban ta tun washe Garin ranar da Shahaab yazo wajan ta take ganin yanayin sa ya sauya, komai yana yinsa ne a sanyaye, yau ma zaune suke a tsakar gida gaba dayansu, Hajja tana dura kunun Aya, jabir yana zaune kusa da Ummah, Abba kuwa yana Gefe ya zubawa Aisha ido itada qawarta Walida yana kallon su, tun shekaran jiya da malam Manu ya shaida masa cewa yaga Aisha tashiga motar wani, sun dauki lokaci acikin motar, sannan tafuto, shikkenan yashiga damuwa, yarasa waye yake son rushe wa yarsa tarbiyar daya bata tsawon shekaru, a yanda yakeji yanzu, zai iya yi mata dukan lahani idan ya tambayeta motar ubanwa tashiga taqi fada masa gaskiya

Walida ta kalli Aisha tace "tabdi, wallahi na manta ban taho da biro naba, Kuma sonake yau kisake koyamin lesson plan dinnan Dan inyi sauri in qarasa, jibi muke son komawa makaranta hutu yaqare Kuma"

Hajja tace "ai kun samu ma kundan huta, Amma da ace lokacin azumi Kuna zuwa Aida jikinku Yagaya muku"

Aisha tasaka hannunta cikin jakar makarantar ta tana cewa "Bari inbaki nawa Biron, saikiyi dashi Amma Sabo ne, Baiyi laushi sosai ba"

Walida tace "Bani"

Zuciya daya Aisha tadauko Biron da Shahaab yabata, ta miqawa Walida Biro, Walida tana ganin wannan biro tazaro idonta waje, cikin tsananin razana tace "la'ila....waye yabaki wannan Biron? Wallahi irinna babanmu ne sak, Shima gwamna ne yaraba musu shi Kuma yace mana biro ne Mai mutuqar kyau da tsada, dubu Dari biyar ake saida shi" (=?F? @&?)


Hajja ce tazaro idonta waje (=?3?)
Abba kuwa Aisha ya zubawa ido yana jira yaji daga gidan ubanwa tasamu Biron, Ummah da jabir ma idonsu yana kan Aisha, yayinda kan Aisha yasara, tarasa asama take ko'a qasa, gabanta yahau luguden faduwa.






(tofa Al'amari ya lalace yau =??>?y?)





Littafin Shahaab na kudi ne, ki biya naira 300 kacal ki karanta abinki Hankali kwance, idan kika karanta batareda kin biyaba, keda mahaliccinki,.

08033300034
Amnah El Yaqoub
'

Page 21

Kafin Aisha tayi magana Hajja tace"kekuwa Walida da masifar qarya kike, yanzu inbanda qarya, wanne irin biro ne za'a ce dubu Dari biyar saikace kudin qaramin gida?"

Aisha da idonta ya furfuto ta juya ta kalli Hajja, jitake kamar babu nauyi ajikinta, Sai takeji kamar tana tashi sama ne saboda tsabar rashin nauyi, har zuwa yanzu idon Abba yana kanta, duk wani motsi datayi, idonsa yana kanta

Walida kuwa kallon Hajja tayi tace" Hajja.... Wallahi Allah da gaske nake, nasan Abbana bazai mana qarya ba, lokacin ma agaban mu yabawa Alhaji Ali yace aje a saida Biron zai sayi fili da kudin"

Hajja ta kalli Aisha datayi tsumu-tsumi tana zare ido tace"mesunan qawa a'ina kika siyo Biron?"

Cikin faduwar gaba tace "Hajja ni Bani akayi, Kuma Wanda yabani bashida kudin da Walida take fada bare harya'iya siyoshi"

Abba daya zubawa Walida ido yana kallon ta yace"tashi kije gida Walida, qawar Taki zatazo ta sameki"

Babu musu Walida tatashi tana cewa Aisha "to wallahi ki binciki Wanda yabaki karkije na sata ne, idan kinzo saimu qarasa rubutun"
Daga Nan tasakai tafice daga gidan

Abba ya kalli Aisha fuska babu Fara'ah yace "bani Biron"

Babu musu ta dauki biro tabashi, Kai tsaye yatafi gidan Alhaji Ali domin jin gaskiyar magana,ko kadan bai yarda da maganar da Aisha tafada akan Biron ba, Ummah datake tsoron yiwa Aisha fada Hajja Tahau kanta da masifa tace "Allah yarufa asiri"

Aikuwa cikin sauri Hajja tace "Amin, aiya dade da rufawa"

Cikin sauri Aisha tatashi ta shige dakin Hajja, gaba daya fuskarta ta sauya tunani take da kokonto akan maganar da Walida tafada mata, Ina Shahaab zai samu kudi har nera dubu Dari biyar?
Lokaci daya ranar da sukaje mall itada fati yafado mata Arai, da fad'an da masu mall din suke mata, Kuma lokaci daya suka dawo suna bata hakuri saboda wani body guard datagani da baqin glass yazo yayi magana dasu, ta tuna lokacin dasuke cewa Babban customer dinsu ne yazo Kuma bayason hayaniya.

Fadawa tayi kan gado tana Girgiza kanta, tasake tuna lokacin datake cikin adedeta ance mata Mahmud Wakili yazo shi aka sauka acikin gidajen data Gani,gabanta ne yake faduwa, meyake shirin faruwa ne?To Amma Kuma ai yace mata shi Yaron Mahmud Wakili ne bare tayi tunanin ko qarya yake mata, tasan cewa Shahaab bazai ta6a yimata qarya ba, Shahaab bazai fada mata abinda bashine ba, yanada Hankali, Kuma yanada nutsuwa, sannan babba ne yanada shekaru, bazai yi mata qarya ba, lokaci daya kanta ya d'aure, tarasa waye zai bata amsa, wayar Hajja ta d'auka cikin sauri har hannayenta na karkarwa tafara Kiran layinsa, saide Kuma wayar tasa akashe(>?&? @&?)

Tana daga d'akin tajiyo Abba ya dawo, kujera yar tsugunno yaja ya zauna agaban Hajja dasu Ummah, sannan yace "naje na kaiwa Alhaji Ali Biron, yace zai Kai a siyar dashi,zan jira shi inji Yaya ake ciki"

Hajja tace "nifa mamuda itama Walidan data fadi maganar kallon mahaukaciya nake mata, tsakani da Allah tayaya me sunan qawa zata samo wani biro har dubu Dari biyar?to kaima tun kafin infara yima kallon mahaukaci kawai kayi shiru"

Abba yace "Hajja kenan,bakisan abinda yarinyar Nan take qullawa bane"

Jin abinda Abba yace yasa gaban Aisha faduwa, kode Abba yasan tana kula Shahaab?

Kafin Hajja tayi magana suka jiyo sallama daga kofar gida, jabir ne yatashi yafita, Sai gashi ya dawo yace "Abba Ana sallama dakai"

Kallan jabir yayi yace "nikuma? Suwaye?"

Jabir yace "wasu baqi ne, Amma Naga tare suke da Bulama"

Abba yace "baqi tareda Bulaman Gari? to Bari naje,"

Yafadi hakan tareda nufar kofar gida.
Yana zuwa yaga baqi su hudu, tareda bulaman Garin,hannu ya basu suka gaisa, daya daga cikin baqin ya kalleshi yace "kaine mamuda?"

Abba yace "eh nine,meyake faruwa?"

Yace "karka damu babu komai, munzo ne daga National Hajj commission,ma'aikatar aikin Hajji, muna farincikin sanar dakai sunanka yafuto acikin jerin Wanda zasuje Umara cikin wannan satin, sannan danka yasamu gurbin karatu a qasar Australia, zamu wuce daku dutse domin yimuku international passport"

Abba yayi shiruu kamar baiji abinda suka fada daidai ba, cikin tsananin mamaki yace"ranka yadade Saudia de Dana Sani?Kai inaga de kuskuren adreshi kuka samu"

Daya daga cikinsu yace"Muma Umarni ne muka Kar6a daga sama,kashiga kasanar agida muje mucika umarnin da'aka bamu"

Cikin mutuwar jiki Abba yajuya cikin gida tunani fal ransa, dama mutum yana samun karatu ne batareda yanema ba?jabir din dasuke fafutuka yasamu ko legal Ringim ne yatafi yayi diploma shine yanzu yasamu gurbin karatu a qasar waje? Tayaya? Yanzu a wannan zamanin har akwai mutumin dazai biyama Saudia ne batare da yasankaba? Kuma sunce umarni aka basu daga sama, hakan na nufin koma wanene yasaka su to wani Babban ne a qasar, Kuma yayi bincike sosai akansa tunda gashi har yasan yanada d'a namiji

Yana qarasawa cikin gidan yafadawa Ummah da Hajja abinda yake faruwa, Hajja tace "to mamuda, dayake Saudia de Kiran Allah ne bazan hanaka zuwa ba, Amma abun da mamaki ace an dauki nauyin karatun jabir, kaikuma anbi Yama Umara, to waye ne wannan?"

Ummah tace "Hajja koma wanene ba qaramin masoyinmu bane, wataqila lokacin da zamuji dadi ne yazo, Allah yasaka masa da alkhairi, yasa ladan abunda yayi yadinga binsa har qabarinsa"

Abba ya jijjiga Kai yace "hakane, Amin ya Allah"

Cikin sauri Aisha tafuto daga daki tace "Abba Allah yasanya alkhairi"

Baice da'ita uffan ba, Sai kallon jabir da yayi yace "Kai taso muje"

Cikin sauri jabir yatashi suka fita, Kai tsaye dutse sukaje kamar yanda mutanan suka fada, anyi musu passport duka su biyun,Wanda sukaje gida suka Dauko su sune suka kar6i passport din, sannan suka dubi Abba, daya daga cikinsu yace "Zaku iya komawa gida, yanzu zamu Kai passport din Abuja, za'a yi muku visa"

Abba de da yaga abun nasu da gaske ne, saiya tsugunna yafara yimusu godia, cikin sauri suka tarbeshi yatashi tsaye, sannan sukace babu komai, Abba har hawaye yake yana qara yimusu godia, daqyar suka samu yayi shiru, sannan sukai sallama dasu

Basu koma gida ba Sai dare, agida ma magana daya aketa maimaita wa, mata Sai sallama suke yi a gidan anayiwa Hajja Allah yasanya alkhairi mamuda zai tafi Umara, Abba yarasa Ina Yan gari suka samu labari, Amma daya tuna da Bulama saiya Dena tunani akan hakan.


(Shahaab littafin kudi ne, ki biya naira 300 kacal ki karanta abinki, duk wadda ta karanta batare data biyani haqqina ba nabarta itada mahaliccinta,
0164549488
Amina muhammad
GTbank)

******

Cikin dare hadari yahadu sosai, Nan da Nan aka tsinke da ruwan sama, acikin wannan ruwa Aisha tatashi tafuto tayi alwala, kafin Takoma daki duk ta jiqe, Dakin Takoma ta kunna wayar Hajja ta shimfida sallaya, sannan ta kashe hasken wayar tacire kayan jikinta, ta dauki wani kayan tafara sakawa, cikin rashin Sani tad'an bigi breast dinta,cikin sauri ta runtse idonta saboda zafin dataji, tarasa meyasa wani lokacin suke mata ciwo, sannan Kuma kullum cikin qaruwa suke, hijabi tasaka sannan tatada sallah, Bayan ta idar haka ta dinga addu'ah Allah ya dawo da Shahaab lafiya domin ya wanketa akan wannan biro, yazo yafada musu Bahaka bane, sannan tayi wa Allah godia akan abun farincikin daya samu Abban ta da jabir, tayi musu addu'oi sosai, sannan ta kwanta awajan tana istigfari, batasan lokacin da bacci ya dauketa ba, saiji tayi Hajja tana tashin ta sallar asuba.

Tunda suka tashi da safe ta gaida Abban ta taga ya amsa mata daqyar, jikinta yayi sanyi, haka Takoma Dakin Hajja ta kwanta batareda kowa ya lura da yanayin datake ciki ba, da yamma Alhaji Ali yazo gidan yayi sallama da Abba, Abba na fita suka gaisa da Alhaji Ali, anan Alhaji Alin yaqara tayashi murna saboda samun labarin Dayayi Abba yasamu kujerar umara, sannan yaqara da cewa "Mamuda ga wannan kudin, jiya nakira wayar ka akashe, dama inaso in fadama ne Wanda yake siyan Biron baya Nan, Sai yaransa nasamu, sukuma sunce bazasu siyeshi haka ba saboda babu kwalin Biron, danhaka zasu iya siya dubu Dari hudu da hamsin, ga kudin Naka"

Jikin Abba ne yafara rawa ganin wannan uban kudi, ,qafafunsa suka fara karkarwa yana neman faduwa, ahankali yasaka hannu ya kar6i kudin sannan yace "nagode Alhaji Ali, zanzo gidanka anjima"

Alhaji Ali yayi godia yajuya yatafi, Abba kuwa duhu duhu yake Gani daqyar yakai Kansa gida,yana zuwa ya zauna akan tabarmar da Hajja da Ummah dakuma jabir suke zaune, ya ajiye kudi agaban Hajja, tsorata sukai da yawan kudin, cikin 6arin jiki Hajja tace" mamuda Ina kasamu wannan uban kudin?"

Baice da'ita komai ba, ya kalli jabir yace"kiramin yayarka"

Jabir yaje Dakin Hajja yace "qawar Hajja kizo inji Abba"

Haka kawai taji faduwar gaba ta ziyarceta, cikin sanyin jiki tafuto ta zauna akusa da Hajja, ahankali tace "Abba Gani"

Abba yajuya ya kalli Hajja yace "to Hajja gatanan, wannan kudi da kike Gani kudin biro ne, saboda haka ta bude baki tafada mana waye yabata Biron? Saboda ni kwata kwata ban yarda da yarinyar Nan ba"

Yajuya yasake kallon Aisha da kanta yake qasa, idonta Yacika taf da hawaye, sannan yace "AISHA...., fadamin waye yabaki wannan Biron? Sannan Ina kike zuwa da daddare?"

Cikin sauri Hajja tace "bangane Aisha haka Kai tsaye ba mamuda, sunan qawar tawa kake kira haka? Ashe zaka iya kirana Kai tsaye Nima? To Bari kaji idan baka yarda da wannan yarinyar ba mamuda Nina yarda da'ita,tayaya za'ace biro qwaya daya jal nera dubu Dari hudu da hamsin? To shi Biron baya qarewa ne?"(>??)

Abba yace"Hajja wannan biro haka kudinsa yake, kuma qarya take tasan inda taje ta Nemo shi, saboda ban yarda da ita ba, ta bude baki ta fadamin gaskiya kokuma yanzun Nan inyi mata dan'iskan duka wallahi"

Hawaye ne ya zubo daga idonta, ahankali tafara shashshekar kuka, cikin wata irin murya tace "Abba Dan Allah kayi hakuri"

Cikin 6acin rai Abba yace "ta tabbata kenan abinda malam Manu ya fadamin gaskiya ne ko? Irin tarbiyar Dana baki kenan ko?"

Hajja ta kalli Aisha tafara tafa hannu tana salati, tace "Nina Rasa abun damuwa anan mamuda, waime kake nufi da wannan maganar taka ne? Memakon kayi murna yarinya tafara samo mana kudi Amma Naga Kai tuhumar ta ma kake, ni idan hakane ai jummai rufata tayi, inusa ba mijin aure bane, duk Wanda yabawa mesunan qawa wannan biro ai shine mijin aure "(=?D?=??=?F? @&?)

Ummah ta zubawa Aisha ido tana kallonta, Sarai tasan akwai abinda take 6oye musu, yanayin ta kawai zaka kalla kasan batada gaskiya,tsoronta daya kartaje wani marar tsoron Allah yayi amfani da rashin wayon 'yartata yana amfani da'ita awani waje, saboda babu Wanda zaiga qirar Aisha yaji bai kwadaitu akanta ba,share Hawayen idonta tayi,cikin muryar kuka Ummah tace"waye yabaki Biron? Sannan Ina kike fita da daddare?"

Cikin kuka tace" Ummah ni gidansu Walida nake zuwa"

Abba yasa hannu yad'auki wayar hajja dake ajiye agefe, number Walida yadubo yakira Walida yasa ta a amsa kuwwa yanda kowa zaiji abinda take fada, Walida tana daukan waya Abba yace "Walida mamuda ne"

Cikin ladabi ta gaishe shi, Shima ya amsa mata, sannan yayi mata ta manya yace "meyasa bazaki yiwa qawar ki fada bane ta dinga zuwa gidanku da rana, Amma kullum saide tazo da daddare, mu kinga munyi mata fada, taqi jin maganar mu"

Walida bata gane shan cikinta Abba yake ba, tayi murmushi tace "Abba da daddare Kuma? Ai Aisha bata zuwa da daddare, sau daya tata6a zuwa wajena da daddare Kuma Shima narakota har gida, ka tambayi su Hajja zasu fadama ma nazo gidan"

Abba yace "eh anyi haka fa, na manta wallahi, toki gaida mutanan gidan" daga Nan yakashe waya.

Kukan Aisha ne yake tashi awajan, sosai take kuka harda Jan zuciya. Abba ya kalleta yace "muna jinki, wajan wa kike zuwa?"

Cikin kuka tace "SHAHAAB"

Hajja tanajin haka tafara tafa hannu,Nan da Nan hawaye yafara sauka akan kumatunta, cikin mamaki tace "mesunan qawa?,to kode shine yabaki ribbon din Dana Gani a kanki kikace Walida ce tabaki?"
Babu musu ta daga kanta alamun hakane,
Cikin 6acin rai Abba yatashi ya wanketa da Mari yace "waye SHAHAAB?"

Zafin Marin ne yasa tasaka hannu ta dafe kuncinta, muryarta na rawa cikin kuka tace "shi.... Shin.. Shine yake zuwa yake kirana awaya Sai naje, Abba Allah Ina sonsa nide"

Wani Marin Abba yasake mata, cikin 6acin rai da takaici yace "shine kike binsa har cikin mota yana hure miki kunne ko? Ai kinsan da maganar inusa, wato irin mayaudaran samarin Nan ne yake zuwa wajan ki yana hure miki kunne harni Zaki kalla kina cewa ke kina sonsa ko? Idan na qara ji kince kina sonsa saina kakkarya ki a gidannan, Kuma daga yau babu ke babu shi,inusan damuka Sani shi zamu baki"

Cikin kuka tace "Allah banason inusa, nide Shahaab nakeso"

Jin abinda tace yasa Abba yayo kanta zai rufe ta da duka, cikin sauri Hajja tajanyota jikinta,
Hawaye ne suka sulalo daga idanun Ummah,koma waye wannan Shahaab haqiqa yariga yagama hurewa yarsu kunne, tunda gashi har mahaifin ta yana fada itama tana fada.

Hajja tasaka salati tana sake rushewa da Kuka, cikin kukan tace "wannan masifa Dame tayi kama? Mesunan qawa Ina kika samo wani Shahaab Kuma? Yaushe Zaki bi saurayi har cikin mota? Kifadamin su waye iyayensa inje inji Dame suke taqama da dansu zaizo wajanki batareda ubanki yasani ba?"

Cikin kuka tace "Hajja ni bansan iyayensa ba, Kuma nide Allah Shahaab nakeso"

Hajja tace "to inajin de aljani ne, Danni banta6a jin irin wannan sunan ba, saide a jinsin aljannu, ninasan ba zakiyi haka da niyya ba mesunan qawa, Gamo kikai da aljan"

Abba yace "babu wani aljani Hajja, Sai iskanci dayake damunta, Kuma ni bazata 6atamin suna ba, bazata janyomin abun kunya agida ba...."

Jin furucin Abba yasa Hajja tasake rushewa da Kuka tace"mummunan bakinka ba'a kan mesunan qawa ba, inda zatayi ciki da tuni tayi, jinake can unguwar gabar Yara suna Nan sunkai su talatin kowacce cikin shege ne da'ita, ita kanta Malamar asbitin dasuke zuwa wajanta take zubar musu cikin itama cikin shegen ne da'ita, Bayan Wanda ta haife, Amma ninasan Mesunan qawa inde tabiyo halin takwararta to ba zatayi cikin shege ba"

Ummah ta kalli Hajja da sauri, yaushe akayi ciki agarin har mutum talatin? (=??>??)
Tagama lura cewa soyaiyar Aisha tasa kwata kwata Hajja bata ganin laifin yarinyar,ko kadan bazata iya tsawatar mata ba,Abba yace "tunda kince kina sonsa, tona tabbatar kona miki katangar qarfe tsakanin keda shi watarana bazan San lokacin dazaki tsallake kije wajan sa ba, danhaka ki shirya, zanje in samu jummai infada mata ta shirya takaiki can kano, daga Nan kuwuce Abuja akai ki gidan Mahmud Wakili aiki, tunda da naji tausayin ki nace ba zakije ba Gara ki zauna agaban mu abaki inusa, to

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login