Showing 27001 words to 30000 words out of 121250 words
zumudi zumudi cikin muryarsa,babu alamun bacin rai ko damuwa tattare da sautinsa,saidai bata jima ba hajjan ta shigo cikin jimami,inda ta takura mata sai data tattara ta zuwa dakinta,tace gwara su zauna tare har ta samu sassauci.
Saidai kuma abinda ya bata mamaki shine,a daren ranar saiga nasir ya kirata,kamar ba zata daga ba sai kuma ta daga,don tunda abun ya faru tsakanin jiya da yau bai kira ba sai yanzun,tana son taji da wacce kalma shi kuma zaiyi amfani?,me zaya fada?,zai kare kanshi ne kamar yadda nuradden ya kare?,ko kuwa zai tabbatarwa da kansa laifinsa?.
A yanayin sallamarsa kawai ta fahimci baisan mai afkuwa ta afku ba,da irin salon daya saba yi mata magana yayi mata,sai daya gama sannan a hankali tace
"Ango" dif yayi na wasu sakanni sannan yace
"Wanne irin wasa ne wannan zahra?,waye kuma angon?" Wani bacin rai ne ya taso mata,wato ita zaya ninke a baibai kenan?ya shirya saidai kawai taji an daura aurensa?,saita miqe ta zauna tana tuna irin kalaman daya jima yana amfani dasu a kanta,tana tuna yadda yake nuna kaffa kaffa da zallar kishi a kanta,tana tuna yadda koda yaushe yana tafe da kyaututuka domin ta,wanda koda taqi amsa zai tilastata ta karba din,zaice tukuicin soyayya kenan kyauta,ashe babban tukuici yana tafe
"Nasir....bude kunnenka da kyau!,idan zaluntata kasoyi to ubangiji yamin kariya da katanga dakai saboda ya bayyana min gaskiyar abinda kake boyewa,ka zalunceni nasir!,kaso ka yadaureni kaje kayi aurenka ba tare da na sani ba?,to na godewa Allah daya bayyanamin shirinka" cikin wata rudewa da dirircewa yake cewa
"Calm down fatima....ki tsaya kiji mana,wallahi Allah ba haka bane,yarinyar nan auren hadi akayi mana da ita.....zabin hajiya da alhaji ce....."
"Watanni nawa?,kwanaki nawa?,amma kullum nuna min kake bata da muhimmanci a wajenka?,hakanan maganar itama bamai muhimmanci bace?,ka gayamin cewa ka gamsar da hajiya ta aminta da naka zabin,amma abun mamaki saiga sauti farinciki daga maqogwaronka kana sanarwa da duniya daurin aurenka,a hakan zakace baka ita akayi?,ahaka kakeso na yarda dakai,bayan an ganemin babu wani damuwa ko kadan tattare dakai?"
"To naji,amma fatima....ina sonki ki yarda dani.....kuma in sha Allah zan aureki a matsayin matata ta biy....."
"Allah ya tsareni da hada hanya da mayaudari....har abada ni dakai nasir na barka kenan,kaje....ina roqon ubangiji yayimin sakayyar abinda kayimin,Allah ya isarmin" daga haka ta kife layin ta sake sakin kuka.
Kuka tayi mai yawan gaske,wanda kafin tayi controlling kanta fa sassauta kukan nasir ya hada mata massages da kiraye kiraye babu adadi har ta kasa irga yawansu,sai kawai ta kashe wayar baki daya ta cusata qasan filo.
A ranar ta balla layin shima kamar yadda ta yiwa nuraddeen,hakanan ta kawar da duk wani abu da tasan zai tuna mata dashi,ta baiwa kanta qwarin gwiwar ci gaba da rayuwa,da kuma fuskantarta,tana mai burin haduwa da kyawawan sakamako a nan gaba
_saidai ina!,kowanne babi na rayuwa tafe yake da qaddararsa,saidai kuma DUKKAN TSANANI YANA TARE DA SAUQI!_
Duk da ta cinyewa ranta komai amma hakan bai hana rama bayyana a jikinta ba,saboda ita damuwa tana da tasirin bayyana gangar jiki koda an danneta a ruhi,hakan yasa ta faɗa sosai kafin komawarta makaranta.
Wannan karon hajja da kanta tayi mata tayin zama a gida ta qara koda sati daya ne ta qara murmurewa kafin sannan amma tace a'ah,saboda jarabawar qarshe ta wa'ec da neco da suka fara jiyo qamshinta,gwra ta tattara hankalinta ta samu sakamako me kyau,don yadda qaddararta ta fara zuwa mata a hagunce ya sanyaya mata jiki.
Da yammacin ranar ana ya gobe zasu tafin haidar ya iso gidan,tana falon hajja tana goge sauran kayanta da zata wuce dasu yayi sallama falon ya shigo.
Kai ta daga ta dubeshi na sakan daya kana ta amsa tana maida kanya ga gugar,har yanzu yana nan da gayunshi kwarjini izza da isa,saima cika da 'yar qiba da kuma murjewa daya sakeyi,hakan ya qara masa kyau sosai,kusan watansa biyu baya nan,sai yau ya dawo.
A sanyaye ta gaidashi,sannan ta tattare gugarta ta wuce ciki tabar falon,duk da haka sai data fara biyawa ta dakin hajja ta gaya mata isowarshi sannan ta fito ta koma dakinta ta barta tana ta murna da zumudin dawowar jikan nata,wanda babu yashi cikin jikokin nata,kasancewarsa jika na farko a wajenta,mai kuma yawan kula da ita da damuwarta,tamkar shita haifa ba mahaifinsa ba.
Wannan karon ma ta fito zata sha ruwa a kitchen taji hajjan na gaya masa abinda ya faru da ita,itakam bataso harga Allah hajjan na gaya masa
"Allah ya sawwaqe" kawai taji yace,qwafa taja a ranta tana cewa maganin hajjan da take gaya masan,aiba matsalar data shafeshi bace dama.
Basu jima da komawa ba lokacin visiting yayi,wanda su shine na qarshe d za'a musu saboda jarrabawa da zasu fara gab da lokacin ziyarar ko kuma bayan lokacin,sun wuni cikin farinciki,kamar yadda aka sani cewa rana ce ta farinciki ga kowanne dan makarantar kwana,wannan karon 'yan gidansu da iyalan abban gwammaja da wuri suka koma,don haka ta dawo hostel abinta.
Gab da zata isa gadonta ta hangi ladifa hamza zaune riqe da takarda cikin hannunta,gefanta kuma maryam mustapha ce riqe da hannun ladifar dake digar hawaye.
Ba laifi suna zaman mutunci sosai dasu,kasancewar zahran mai faran faran da jama'a yasa take da yawan jama'a,banda yanzun da walwalarta taja baya ba kamar da ba,don ko da take shugabar dalibai kusan iya mu'amalarta yasa dalibai ke sonta,musamman juniors da bata yadda a zaluncesu ba don suna qasa dasu,hakanan suma basu isa su raina na sama dasu ba dole su basu girma.
"Allah dai yasa lafiya ladifa"
Maryam ce ta buda hannun ladifan ta ciro takardar ta miqawa zahra,ba bata lokaci zahran ta bude ta soma karantawa.
A hankali ta koma gefansu itama ta zauna tana fidda murmushi mai ciwo,wanda iyakarsa saman labbanta,ta ninke takardar sannan tace
"Ashe bani kadai bace ba?,bani daya keda irin wannan matsalar ba,gayamin ya kuke dashi" muryarta da sautin kuka take bata labarin yadda yake nuna mata soyayya,amma sai gashi tashi guda ya yaudareta,yayi aurensa ba tare ma data sani ba,sannan kuma saboda tsabar qwarewa yaci gaba da soyayya da ita,sai a yanzu data kusa tonashi ya bayyana mata yayi aure a sanda suke tare,ya tsallaketa ya auri wata,bayan ta kori kowa a kansa,bata sauraron kowa saishi,wannan wanne irin yaudara ce?,wanne irin cin amana ce?.
Kai zahra ke gyadawa sannan ta basu nata labarin,shuru koqacce tayi,a hankali maryam tace
"Bansan me samarin yanzu suka koma ba,sam.basu da wata ALƘIBLA ko manufa a rayuwarsu,ya kamata muma 'yammata muyi karatun ta nutsu,mu daina basu yarda amanna da dukka soyayyarmu,da wahala ka tara yammata goma baka samu takwas a cikinsu suna da tabon yaudarar namiji ba,yaudara taban haushi,imma yaqi aurenki haka kawai saboda ranshi ya raya masa haka,ko kuma ya gujeki saboda ya nemi ki bashi kanki kinqi" kai zahra take gyadawa kawai,duk sanda ta tuna nuraddeen da nasir sai taji ranta ya sosu,abu daya data sani shine,a koda yaushe daka cuci mutum gwara shi ya cuceka,kuma sakayya yanzu tun a duniya Allah yake yinta.
*_IBRAHEEM_*
Bayan dawowarsu hutu babu jimawa suka zana jarrabawar fita daga makaranta,cikin iko da taimakon ubangiji,duk da irin qalubalen da suka dinga kawo mata tarnaqi amma hakan bai dakushe karsashi da karatunta ba.
Ranar da suka kammala aka kuma hada taro na yayewa da kuma sallamarsu,ranar ta zama ta musamman kuma me dimbin tarihi a wajen zahran.
Ranar da sai da tayi kuka na farinciki,saboda tarin kyaututtuka da kuma yabo data samu,kyaututtukan da wasu ma bata zacesu ba.
Kyauta ta qarshe data samu itace wadda daliban makarantar suka hada mata,saboda yadda sukaji dadin shugabancinta,da yadda ta tsaya tsayin daka akansu wajen kwatanta adalci da gaskiya.
Tana rungume da kyautar suka sake hada ido dashi,wannan shine kusan karo na biyar,duk sanda ta hau step din ta amsa kyauta tazo saukowa saita tsinci idanunshi a kanta,qaramin tsaki taja tana jin haushi har cikin ranta,ita sam ta tsani dabi'ar kallo,bama kuma kamar yanzun data yanke tsammani wa maza,tayi musu kudin goro.
Dukkaninsu suna tsaye gaban motocin gidansu,wanda kaso mafi yawa na 'yan gidan nasu sunzo mata,ciki harda hajja,bata da wasu kaya masu yawa da zata koma dasu,don kusan duk ta kyautar dasu,kamar su katifarta botiki house wear dinta da sauran tarkacenta ciki harda jakar goyo ga wadanda basu da qarfi,yau jinta take kamar wadda aka 'yanta daga kurkuku,kana kallon fuskarta zaka shaida hakan.
Cikin yaran da sukayi sabo dasu suke kuma mata kallon yayarsu ta qaraso tana cewa
"Anty fatima.....ance anason magana dake" ta fada tana nuno wata mota,daga kai tayi ta kalli motar,babu kowa kusa da ita,hakan yasa ta tambaya waye?
"Wai mamar qawarki ce"
"Mamar qawata?" Ta maimaita cikin mamaki,kafin tasan amsar da zata bada hajja tace
"Yi maza kije ki dawo kuzo mu wuce kada muyi rana a hanya" saita waiwaya ta cewa salma tazo ta rakata,suka jera tare har zuwa jikin motar.
Suna tsaiwa aka bude murfin motar aka fito,kallo daya tayi masa ta shaidashi,saurayin dazu ne,wanda yaketa faman binta da kallo,sanye cikin shadda dinkin zamani,kanshi babu hula,kallo daya zaka masa kasa cewa wayayyen mutum ne,wanda ilimin zamani ya rasashi,da murmushi yake dubanta
"Ayimin afuwa,nayi qarya da maman qawarki ko?,naga alamun idan ba hakan nayi ba babu lallai na samu ganinki,mai yiwuwa ma nayi asarar dama ta" itadai batace komai ba sai dubanshi da take,gami da son jin ba'asin kiranta,ganin kamar yana bata musu lokaci yasa ta tambayeshi kai tsaye
"Allah dai yasa lafiya,ko yarinyar tayi batan kan wadda kasa a kira ma?,don mi bansanka ba" murmushi ya saki yana dubanta
"Ni na sanki,tun ba yau ba,saidai kuma yau din idanuna suka fara ganinki" bata fahimci zancansa ba,kuma taga alamar kamar yana son maida zancan wasa ya kuma bata mata lokaci,don haka tace
"Zaifi kyau ka fadi saqonka,don na bar iyayena na jira" gyara tsaiwarsa yayi
"A'ah,aiko ba za'ayi haka ba,ya zamu barsu mama na jiranmu?,inaga kawai ki bani lambar wayarki sai muyi magana"
"Baka da abin cewa,don haka sai anjima" ta fada tana yin gaba.
Ga tsammaninta salma na biye da ita,amma tana waiwayawa saita taras acan ta barota,dan tsaiwa tayi har salman ta iskota,cikin hade rai tace
"Ki tabbatar da cewa ba number wayata kika bashi ba" dariya salman tayi
"To meye amfaninta idan ba'a bashi ba,kika san inda rana zata fadi?,kika sani ma ko shine mijin da kiketa jira Allah ya kawoshi yanzu,indai hakane ai kinga yazo a dai dai,za'ayi aurenmu kamar yadda aka tsara" baki zahran ta tabe
"Ke kuma daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaqi?,to ba girin girin ba tayi mai dai" dariya ta sakeyi
"Zatayi mai lunqui ma kuwa in sha Allah,don shi yace kinyi masa,hakan kuma da kikayi babu komai,don tun ganin farko daya miki yace yaga alamun me ajice dama" tsaki kawai zahran taja,don ita sam abun ya fara barin kanta,tana ga hutu take buqata da kuma samun space sosai da zata hutawa zuciya da qwaqwalwarta.........
23/10/2021, 08:40 - 👍🏻👍🏻: 11
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ƘAWA DA KECE RAINI_💄💅🏽
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau'in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki gaba daya ZAHIRINKI DA BAƊININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
*kayayyakinmu sune kamar haka*
FACE AND BODY SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500
*Ku dubamu a handle namu na Facebook da Instagram*
Ummu Dufail
*ko ta number wayarmu kamar haka*
07067943479
*_muna turawa kowacce jaha dake fadin nigeria da yardar Allah_*
*_INGANCI DA RAHUSA SHINE TAKENMU_*🤞🏾🤞🏾🤞🏾
_____________________________
Tunda ta koma gida ibrahim ya samu nayi,kiran safe daban rana daban dare daban,har sai da duk wanda yake tare da ita yasan da xaman ibrahim din,tun tana sharewa itama har ta soma dagawa dole tana saurarensa.
Ibrahim din irin samarin nan ne 'yan hira,ya iya labarai kala daban daban,sau tari koda ba zatayi magana ba zaice babu komai,yau shi zai mata hira,zata tsaya tana saurarensa yanata bata labarai kala kala,saidai kawai tayi murmushi idan wani abun ya bata dariya,haka zasu kwashe kusan awa guda,saidai tace ta gaji.
Ya gaya mata wasu daga cikin abubuwan da suka shafeshi,sunansa da aikinsa da unguwarsu,saidai ita din banda sunanta bata gaya masa komai a kanta ba,don gaba daya komai ya fice mata akai,bata jin wani karsashi akan lamarin sam,shima kuma saita lura bai fiya tambayarta personal abubuwan da suka shafi rayuwarta ba.
Cikin haka maganar auren yammatan ta taso,an soma da kawo kudin hafsat da yasira,naira dubu hamsin hamsin kowaccensu,aka saka rana kamar yadda aka tsara za'a tsaida rana guda daya.
A daren ranar su abba suka kirata,kira na farko tsakaninsu tunda aka fara zancan aurensun.
Tunda ta shiga falon taga zaki a ciki sai taji kamar ta koma,batason ana tattauna personal issues dinta a gabanshi ko kadan,harta shiga ta zauna ta gaida abba babban dashi bai daga kai ya dubeta ba,itama tafison hakan,da da hali ma fiddashi zatayi daga falon.
Cikin nuna kulawa abban yace
"Mamana....nayi magana da hajja,ta shaida min akwai wanda yanzu kuke tare dashi ibrahim ko?" Kai ta gyada idanunta suna kallon qasa
"Eh abba"
"To ma sha Allah,yanzu abinda za'ayi shine,ki shaida masa cewa muna son ganinsa,ya kamata kuma ya turo magabantansa,tunda maganar auren 'yan uwanki ya taso,sai a hada gaba daya"kanta a qasa tace
"To abba".
A hanya tana tafe tana tunani,hakanan sam maganar ibrahim bata kwanta mata a rai ba,amma babu yadda zatayi,ba zataso ace duka sa'anninta kowa babu shi ba saura ita kadai a gidan.
Tana shiga daki saiga kiranshi,ta dauka tana zaman gefan katifa suka fara magana,kafin takai ga gaya masa nata saqon yace
"Baby....ya kamata ace mun soma ganin juna fa,yin waya a iya waya kawai abun ya isa,ya kamata mu canza tsari....a ina zan ganki?"
"A gidanmu.....akwai maganar dama da nakeso muyi dakai" cikin 'yar dariya dariya mai kama da murmushi yace
"Ah haba.....ai yanzu an daina wannan yayin,haduwa a gida kamar zamanin da,mudai samu wani waje haka,wanda zamu sake sosai,mu mori soyayyarmu da lokacinmu,inda babu abinda zai dinga razanamu" sosai mamaki ya kama zahra,amma saita danne mamakin nata tace
"Razana kuma kamar wasu marasa gaskiya?" Ta fada sound din muryarta yana sauyawa
"Eh mana,kinsan ita soyayya tana buqatar kebewa da nutsuwa" tsaf ta fahimta inda ya dosa,kuma bata taba tsammatar hakan daga gareshi ba,don haka ta kaurara muryarta sosai
"Ina jin baka shiryawa ganina na ba,a qa'idar gidanmu duk wanda keson ganinmu zai samemu cikin gidanmu ne,idan ka shirya zuwa saina gaya maka saqon gaba daya" daga haka ta katse wayar,ta koma da baya ta kwanta tana nazarin kalamansa,ba shakka ya bata mamaki,saidai kuma ba zata yanke masa hukunci haka da wuri ba,tunda wannan shine karon farko da hakan ta faru.
Ga mamakinta zancan ya wuce,sai gashi bai haqura dayi mata maganar inda zasu hadun ba,harda bata list na sunayen guraren shaqatawa yace ta zabi duk wanda takeso a ciki.
Yanzu ya daina bata mamaki saima tsoro,randa ta gaji da jin zancan ta buda baki cikin bacin rai tace masa
"Ibrahim,wannan maganar da kake yawan gayamin itace take tabbatar min da cewa ba sona kake ba!" Cikin dirircewa yace
"Hana baby....ki daina fadar haka,waye yace miki bana sonki,kinsan yadda nake jinki a zuciyata kuwa?"
"Ban gani a qasa ba,idan ka damu dani....idan har sona kake da gaskiya ka tako kazo ka riskeni gaban mahaifana mana,baka dinga neman kebewa dani a wani waje da babu idon naka ko nawa ba!" ta fada da zafinta
"Shikenan,is ok" shima ya fada cikin sanyin murya ganin yadda ta dauki zafi
"Allah ya baki haquri,yanzu ki gayamin saqon da kika ce tun rannan an baki"
"Ance na gaya maka cewa ka fito"
"Na fito ina?" Ya fada da wani irin sauti
"Aure mana" ta fada itama kai tsaye tana sauraren amsar da zata fito ta gaba daga bakinsa,don tuni ta gama hasashen amsarsa ta qarshe
"Ok...ok...am really sorry,sai yanzu na fahimta" sai kuma yayi cool da muryarsa sosai
"To ai baby shi yasa nakeson mudan hadun,mu fahimta juna kafin akai ga batun aure,tunda kinsan shi batun aure ba qaramar magana bace,zamane na dindindin,kinga dole saimun fahimci juna face to face tukunna" shuru tayi kawai,wani abu mai tauri yana tokare mata wuya,abun akwai zallar rainin hankali da ban mamaki,ada kullum shine bashi da zance saina aurensu,amma a yanzu tazo da batun yana neman noqewa.
Tun daga ranar saiya zamana bashi da zance saina gini yakeson ya fara,mota yakeson ya canza,yanzu kasuwa babu ciniki komai ya zamana sai a slow,gininsa ko linter baikai ba,ga hada lefe da sauransu,kullum cikin qorafin ya fada