Showing 75001 words to 78000 words out of 121250 words

Chapter 26 - ALKIBLA complete

Start ads

24 Aug 2025

467

Middle Ads

Haidar*


Sosai yayi relax a bayan motar bayan ya aje hularsa a gefe yana furzar da iska daga bakinsa,yana jin yadda sanyin ac ke ratsashi tare da qara haifar masa da kasala da kuma tayar masa da gajiyarsa ta zirga zirgar wunin yau.


Zuciyarsa da qwaqwalwarsa tayi nisa wajen tuna abubuwan da suka faru yau wayarsa dake aje tare da hularsa ta dauki tsuwwa,dan qaramin tsaki yaja,ba kasafai ya fiya son kira ba,saidai yau yasha kiran har ya gode Allah,a hakama don yana kashewa ne baya amsa wani.


Ganin sunan me kiran yasa ba shiri yakai hannu ya dauka,labbansa suka motsa cikin ransa ya furta
"Rigimammiyar tsohuwa" saiya kara a kunnensa
"Badai har kunje gida ba?"
"Harma mun huta yanzu haka?"
"Ma sha Allah,sannunku da qoqari,Allah ya qara girma da nisan kwana me amfani"
"Amin ya rabbi...amin Aliyyu,Allah yayiwa rayuwa albarka"
"Amin hajja"
"Yauwa.....dama na kiraka ne na gaya maka,nabar amanar jikata a gidanka" fuska yadan yamutse yana son ya fahimci maganar tata,kamar kuwa tasan tunanin da yakeyi tace
"Matarka zahra....zaku taho tare idan ka gama abinda kake...."
"Amma hajja....bamuyi maganar ba....sannan ma kuma karatunta fa?"
"Kai da ita ku kukasan wani karatu.....,jan kunne na kiraka nayi maka,aronta na baka,bance kuma atabamin ita tun yanzu ba ehe" tun kafin takai ga kashe wayar shiya kashe,saiya jefata gefe yana dafe kansa,hajjan ta soma wuce tunaninsa,tunda harta fara masa manya manyan maganganu irin wannan,banda abinta ma shi da bashi ya nemi a barta ba su suka barta don raɗin kansu har tazo da wannan maganar,shikam wannan sabgar gada dayanta akwai qwara a cikinta.


Da ire iren wannan tunanin daya ci gaba dayi har suka isa gidan,ya fita yabar drivern yana kulle motar,yayi cikin gida,ma'aikatan dake harabar gidan suna masa sannu da dawowa.


A yanayi na gajiya yake nufar dakinsa yana observing na falon,komai fes kamar yadda yakeso,don babu abinda yafi tsana irin qazanta kaf rayuwarshi,shi yasa har yanzu ba abincin kowa yake ci ba,hakanan ba kowa yake bawa wankinsa ba.


Bandaki kawai ya wuce direct ya kunna water heater,saida ruwan ya tafasa ta kashe kanta sannan ya daidaita na zafi dana sanyi yadda zai masa dai dai da wankansa,kana ya shiga qasan ruwan ya soma sauka tun daga kansa yana tafiya da gajiya da kasalar data ma jikinsa qawanya,saiya rufe idanunsa yana tuna irin tarin baiwa da Allah ya masa,musamman a yau din,a hankali can qasan maqoshinsa ya dinga furta
"Alhamdulillah...Alhamdulillah".


Ya kusa minti talatin yana sakarwa jikinsa ruwan dumin sannan ya cuda sabulun wanka ya dauraye ya hada da alwala ya fito.


Sai daya tsane jikinsa da towel sannan ya nemi doguwar riga me gajeran hannu ya sakakkiya ya saka,ya feshe jikinsa da turaruka bayan ya taje kansa,sannan ya koma ya zauna saman kujerar dake dakin ya dauki wayarsa ya soma laluben 'yan gidansu,yanason yi musu ban gajiya,don wayar yakeson ya kashe gaba daya,don idan ya kwanta ya tabbatar salla ce kawai zata tasheshi,saboda yadda yake jin jikinsa.


Abban tsakiya ya fara kira,sannan abba yusuf,abbansa ne daga qarshe sai ya kira ummi,tata number bata shiga ba,don haka ya kira umma sa'annan ya kira mamanshi.


Tana hannun nurain a sannan,da hanzari ya nufi dakin maman yakai mata,don yasan zaiji babu dadi idan yayi gigin daga kiran ya haidar din,tunda yasan bashi yake nema ba.


A ladabce ya gaidata ya mata sannu da hanya,ta amsa masa sannan addu'a ta biyo baya,cikin farincikin dake ratsawa har cikin zuciyarsa yake amsa mata,sai kuma tayi kiran sunanshi
"Don Allah ka kula musu da amanar yarinya da aka bar maka,kada kayi wani abu da xai zamana ka watsamin qasa a ido,ka kuma barar da tarbiyyar da muka baka,a qarshe kuma ka qaryata soyayyar da hajja ke maka"
"In sha Allah mama zan kula....in sha Allah" daga haka sukayi sallama ya aje wayar yana sakin ajiyar zuciya yana shafa kanshi da hannunsa guda.


Tsahon wasu mintuna yana a haka ba tare da yasan me yake tunani ba,saiya miqe ya zura slippers dinsa ya fito falon.


Dining ya isa,ya zauna ya fara zuba black tea ya dumana cikinsa,sannan ya duba abubuwan da aka dafa din,ya zuba iya yadda zai iyaci ya koma saman kujerun falo ya zauna acan ya fara ci yana yi yana duba saqonnin da suka shigo masa waya yana maida amsa tsahon wani lokaci.


Dai dai lokacin da yunwa sosai ta dinga sakadar zahran,ta dinga juyi tana jin yadda ulcer dinta ta fara motsawa harta fara sanya mata ciwo tsakiyar cikinta,saita koma rub da ciki ta kwanta qwalla na sauko mata,ita koma meye ya faru hajja ce sila,ita ta jawo mata komai.


Qarfe hudu na dare ya farka kamar yadda ya saba tashi duk dare,wansa baya komawa daga sannan kuma sai bayan sallar asuba,a nutse ya miqe ya shiga bandaki ya dauro alwala,saiya janyo wayarsa zai duba lokaci,saboda dakin ba'a sanya mishi agogo ba tukunna,don gaba daya cikin kwanaki biyu aka zuba dukka furniture din gidan qarqashin jagorancin wani kamfani,duk da ya kashe kudo sosai shi kansa ya sani,amma yadda suka tsaran gidan da kaya masu kyau da inganci kadai ya isa ya gaya maka sunsan aikinsu.


SMS ya gani wanda da alama tun daren jiya ya shigo,dannawa yayi ya bude saqon,daga ummi ne,saiya zauna saman abun sallar tashi sannan yabude saqon ya fara dubawa.


A hankali ya sauke ajiyar zuciya,a rayuwa bayaga mahaifiyarsa da hajja itace mace ta uku da yake ganin kima da darajarta fiye da kowa,saiya sauke ajiyar zuciya yana tuna cewa akwai jininta cikin gidan,wanda karon farko sun kwana sun tashi qarqashin rufin gini guda,tana kuma amsa sunan matarsa.


Ko ba komai,ko yaya tana buqatar yayi mata kara a rayuwa,koda komai bazaije ko ina ba,koda komai taqaitacce ne,amma ta cancanci ya nuna mata wannan karar.


Maganganun mama ya tuna datayi masa su awanni kadan da suka shude,kowa muhimmanci yake bawa zancan,kowa kulawa yake bawa yarinyar why?,saiya aje wayar tasa ya tada sallarsa,yana sallamewa ana tayar da iqama,don haka ya dauki abun sallah a gurguje ya fice,duk da yaso tsaiwa ya tadata kafin ya wuce din.


Saboda ita bai jima a masallacin ba,ana idar da sallar yayi addu'o'insa da basu wuce minti goma ba yafita a masallacin.


Sai da ya tsaya ya kunna dukka fitilun falon sannan ya dinga takawa a hankali ya nufi inda dakunan baccin nasu yake.


A hankali ya dora hannunsa kan handle din qofar sannan ya tura ta a hankali,dunɗum dakin yake babu haske,hakan ya sanya baka iya ganin komai a dakin,saiya sanya qafarsa ciki,ya miqa hannunsa side din da makunnin qwan lantarkin dakin yake ya kunna,take haske ya gauraye ko ina tarwai.


Tsakiyar katifar ya hangota cikin kwanciyar rub da ciki,gashin kanta mai tsayi da santsi na asalin fulani data gada daga wajen umminta yayi ɗai ɗai saman filon saboda ciwon qirjin daya matsata ta cire ribbom din data daure gashin.


A hankali ba tare daya shurya ba idanunsa suka sauka kan sumar tata da kallo,wanda duk da gida daya suka taso zai iya cewa bai taba ganinta ba sai yau,saboda tunda can zahran ma'abociyar zama da dankwali ce ko hula,cikin biyu baka rasata da daya,ummi ta riga data sabar mata da hakan,koda za'a kamata da kowanne laifi ayi mata hukunci banda na zama babu dankwali,baya ga haka ma duk sunsan halinsa,kada ki sake ya sameki babu dankwali akanki.


Doguwar rigar baccin jiya ce a jikinta,saisai ta tattare dukka qaurinta a waje yake,da yake armless ce kana iya ganin dantsen hannunta wanda hannun nata guda daya ta sanyashi qasan fuskarta,dayan kuma tayi baya dashi,ya lanqwashe sosai,duk yadda akayi bacci ya dauketa a hakanne bata shirya ba,saiya janye idanunsa da sauri,yayi one step back da niyyar ficewa,saidai ya a matsayinsa na soja ya tabbatar yadda ta kwanta din idan ta tashi xata iya wahala,don haka saiya sake turo qofar ya dawo cikin dakin,ya taka a hankali har zuwa bakin katifar.


Har yakai hannunsa zai tattare mata gashin kanta,saiya janye hannun da sauri ya maidasu baya kamar wanda aka sawa shocking,tsahon second biyar sannan ya sake kai hannunsa.


Cak ya dagata da niyyar ya juyata gaba daya ya canza mata position na kwanciya,ya manta cewa bacci take,cikin baccin taji kamar tana tashi sama,hakan ya sanyata razana ba kadan ba,take kuma baccin ya yanke,saidai kafin takai ga bude idanunta qwaqwalwarta ta aike mata da saqon dagata akayi,cikin tsananin razana ta dunqule cikin jikinsa gaba daya tana sakin qara,qarar data gigitashi,saboda bai taba kawowa ranshi zata iya farkawa ba,gigitashin da tayi da qarar data qwalla da yadda ta dinga qoqarin zillewa daga hannunsa,don har ga Allah ta manta a duniyar da take,bakuma ta gane waye ba yasa gaba daya suka zube saman katifar ita dashi,don idan ya saketa ta fadi ita kadai duk da saman katifa ne yasan dole taji zafi......
23/10/2021, 08:46 - 👍🏻👍🏻: 28

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_

_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_

_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_

_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_

_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._

_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_

_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_

_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_

_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_

_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _

_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_

_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._

_RANO NET..!!!!_
________________________________




Gaba daya ya danne fiye da rabin jikinta,da sauri cikin cool voice dinsa yake fadin
"Calm down....calm down" saidai ina kunnuwanta ma basu iya jin me yake fada ba,burinta kawai tama ture koma wanene,ganin ta kasa gane me yake fadi,saiya sa hannunsa guda daya ya kama habarta ya riqe,cikin daga murya ya sake fadin
"Wakeup mana...nine fa,ke....ke!" Sai a sannan ta dauki muryarsa,gabanta yayi wani mummunan faduwa,saita tsaya cak da ihun data soma,yayin daya tsaya shi kuma yana kallon fuskarta na wasu sakanni,ganin ta tsaya yasa ya zare jikinsa a hankali ya miqe tsaye,har yanzu bata bude idanun nata ba,saidai ta mirgina daya side din ta yadda zata juya masa baya,tana jin yadda bugun zuciyarta ya dadu,hakanan qirjinta ya qara riqewa,tana fidda numfashi a hankali
"Ki tashi kiyi sallah" ya furta yana ficewa daga dakin.


Sai data tabbatar ya fita sannan ta miqe a hankali ta zauna,jikinta tabi da kallo,wani haushi ya kamata,yanzu a haka ya shigo ya ganta?,mema ya kawoshi dakinta?,sai taja tsaki ta miqe a hankali saboda yadda ciwon qirjin nata ke dada qaruwa,a dudduqe ta nufi bandaki.


Hancinta ta ringa budawa tana jin yadda qamshin turarensa ya kama jikinta adan shigarsa dakin,babu niyyar wanka a tare da ita,amma tasan cewa dole ta rabu da rigar,idan ba haka ba ba zata daina jin qamshin turaren ba,hakan yasa ta fidda rigar ta hada ruwan wanka tashiga.


Yana fidda kayan jikinsa zuwa na motsa jiki yana jan tsaki kadan kadan,tunanin yaqi barin ransa,me yasa bai qyaleta ta fadin ba?,da ba zata qara irin wannan kwanciyar ba,me yasa ma ya damu saiya gyara mata kwanciyar?,haka nan ya gama shiryawa cikin riga armless da wando iya gwiwa,wanda hakan ya sake fidda qirar jikinsa ta qaqqarfan namiji,da sassarfa ya fita daga dakin,yabi ta falo ya bude wata qaramar qofa data sadashi da dakin motsa jikin.


Babban daki na gym wanda ya hada duk wani nau'in qarafa da na'urori,kai tsaye ya haye saman daya daga cikin kayan motsa jikin,yanayi yana sauraren labaran duniya daga babbar tv din dake manne a dakin,daga wancan channel din idan sun gama ya juya zuwa wata,a haka sai daya shafe kusan awa daya da rabi sannan ya sauko ya ciro daya daga cikin towel dake rataye a dakin ya soma goge gumin jikinsa yana zama kan wata cushion chair dake dakin,sai daya huce sosai sannan ya dauki ruwa ya soma sha,yana duba wayarsa da bai jima da kunnata ba.


Minti goma sha biyar a haka sannan ya fito daga dakin,zuwa sannan ya tadda falon fes dashi,daidai lokacin kukunsa dake dauke da warmers guda biyu a hannunsa da alamu girkin safe yake hadawa ya fito daga kitchen,cikin matuqar girmamawa ya zube yana gaidashi,ya amsa mishi yana yin gaba,sai kuma ya dakata ya dawo da baya yana dan wani nazari,yana ganin ya kamata ya dakatar da williams da Andrew,ya cansu da mata,duk da cewa shi din yafi jin dadin aikin mazan
"Williams" ya kirashi
"Yes sir" ya fada da sauri yana aje kwanukan hannunsa saman table din,sannan ya garzayo da sauri ya zube a gaban haidar din
"Inason na dan baka hutu na wata daya,ba don ka yimin wani abu ba,bayan wata dayan zanyi magana dakai saika dawo,ka jirani na shirya idan na fito zan baka abinda zaka riqe na wata gudan kai da andrew" sosai hankalin William ya tashi,don kowa fadi yake yayi sa'ar gidan aiki,ya kuma yi sa'ar uban gida mai kyauta da tausayi
"Sir....ina fata dai ba wata matsala bace?" Hannunsa ya kada
"Eh....kada ka damu,zaka dawo bayan wani lokaci"
"To na gode mai gida" ya fada cikin nuna girmamawa,yanajin dadi daya kasance ba wani abu ya aikata ba da zai rabashi da gidan,daga haka aliyyun ya wuce shi kuma ya kama wajen dining din yaci gaba da gyarawa.


A hankali ta shirya cikin atamfa riga da skert da suka zauna sosai a jikinta,don bata da wata tufa data wuce atamfar,saboda tafi sonta sosai,gashinta ta gyara saita ware dankwalinta kawai ta yafa,tana jin yadda hanjin cikinta ke nade waje daya,dole tana buqatar abinci,sannan charging wayarta yayi low,tana da buqatar jona chargy,hakan ya sanyata dole fitowa falon.


Chargyn ta jona sannan ta nufi saman dining din,taja kujera daya ta zauna,ita kam gaba daya takaicin yadda namiji ke shiga kitchen godai godai da sunan kuku yayi girki take,namijin ma kafiri,dyk tsantsamin ya haidar din ya tashi a banza kenan take rayawa aranta,yanzun ma banda mahaukaciyar yunwar da take ji da kanta zata shiga kitchen din tadan dafa wani abu,sai ta janyo ruwan zafi ta hada tea kawai ta soma kurba,lokaci lokaci tana tunanin gida da abinda sukeyi yanzu,wani sashe na zuciyarta kuma tunanin makaranta takeyi.


Tunanin da take ne yasa bataji tahowarsa ba,sai qamshin turarensa daya cika mata hanci,hakanne ya ankarar da ita ta daga kanta,ashe tsaye yake a wajen yana buda kwanukan gami da duba abunda aka dafa din.


Sanye yake da wata fara qal din shirt cotton mai gajeran hannu,sai wando three quarter shima fari tas dashi,hakama slipper din qafarsa,duk wanda yasanshi ya sanshi dason farar tufa tun asali,saita ajjiye cup din hannunta tana fadin
"Ina kwana?" Ba yabo ba fallasa ya amsa,saidai bai dubeta ba,kana yaja kujera ya zauna ya fara kurban tea din shima.


Zata bar wajen yana duba uban saqonnin taya murna da suka cika mishi waya,yana amsa wasu wasu kuma ya wuce,don yawan saqonnin da 'yammatan sukayi mishi ma yasa sa yaga alamun mace bai budewa saiya wuce gaba
"Ki zauna ki rubuta duk abunda zaki iya buqata" ya fada a taqaice,saita amsa tana yin gaba,ta qarasa wajen wayarta zata dauka,dai dai sannan Williams ya buda qofar kitchen din zai fito,haidar dake cin chips ya kalli qofar ya maida idanunsa ga farantinsa,sannan yace masa ya koma ya fita ta baya,ya jirashi a waje zai sameshi a can,a ladabce ya amsa ya maida qofar ya rufe din.


Tana cire wayar saiga kira ya shigo,dr nasreen ce wadda tun a jiya sukayi musayar numbers na juna,sai taji taji dadin kiran nata,don haka ta wuce da a hannunta zuwa daki.


Sai data shiga ta samu waje ta zauna sannan ta daga
"Mrs dabo....an tashi lpy" murmushi zahra tayi,yanayin faran faran dinta kamar na hindatu,saidai nata maturely yake kamar yadda take nutsatstsiya tun daga fuska
"Lafiya lau amaryar jafar" dariya tadan saki
"Amarci ai mun bar muku,muda muka kwan biyu" sosai suka gaisa a sake kamar wasu tsaffin qawaye,sai tace da ita
"Ya shirye shiryen anjima kuma?,kin ganni a wajen gyaran kai,kantin wata babbar makeup artist ce,nace ko a nan za'a mana makeup na anjima iyi mana booking?,sai su biyo su daukemu daga nan mu wuce ko?" Idanu zahran ta waro waje,danqari!.....yo ita aita manta ma

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login