Showing 102001 words to 105000 words out of 121250 words

Chapter 35 - ALKIBLA complete

Start ads

24 Aug 2025

459

Middle Ads

su biyu ne daga ita sai hajjan.


Da yake anguwar tasu babu laifi basa rasa nepa,tv ce a kunne take aiki,saidai dukka hankalin zahra yana kan wayar hannunta,charting take,kuma tana jin dadin xaman sosai.


Wayar hajja dake gefanta taji ta dauki burari,ta waiwaya ta kalli wayar da yake tana dab da ita kan hannun kujerar da take kai,number ce babu suna,yanzun hajja ta tashi bata jima ba ta shiga toilet,saita miqa hannunta daya ta jawo wayar ta daga ta kara a kunnenta,yayin da daya hannun take ci gaba da danne dannenta dashi a tata wayar
"Hajjan bata kusa,amma idan ta iso xa'a gaya mata" shuru taji anyi,duk da cewa da alamu bawai rashin network bane,tunda ga hayaniya irin daga dan nesa da inda me wayar yakeyin wayar nan tana shigo mata tana ji,saita dan maida hankalinta kan kiran,ta daga wayar ta duba taga ana kan layi,ta sake maidawa kunnenta tana fadin
"Hello....ance hajjan bata kusa,idan ta fito za'a gaya mata" jin still dai an sake yin shuru sai ta daga wayar daga kunneta hadi da jan tsaki,ta kashe kiran,ta maida wayar gefanta ta aje taci gaba da chart dinta.


Tana shirin shiga wani grp nasu na 'yan makarantar kachako unity girls,group ne na 'yan set dinsu da suka gama makaranta a shekarar,saiga saqo daga saman watsapp dinta ya shigo da baquwar number,bata fasa shiga grp din ba,sai data shiga ta gama uzurinta ta fito sannan ta duba saqon,saqone da bai wuce layi daya ba,amma saiya tsaya mata a rai,ta dinga nanatashi ita kadai
*_KINYI NESA DA IDANUNA DA RAYUWATA,AMMA KINA KUSA DA RUHI DA ZUCIYATA_*

sake shiga profile din tayi ko zata ga suna,babu suna babu dp,ta bincike contact dinta tsaf babu me irin number,zargin da yazo kanta yasa tayi saurin daukar wayar hajja ta bude,ta loda numbers din ta danna dial ko zataga suna ya fito a number amma babu,tabbacin zarginta ba haka yake ba kenan,ba haidar bane,to waye?.


Jin takun tahowar hajjan yasa ta maida mata wayar ta ajjiye,don ta lura yanzu wani gani gani take mata akan wayarta,saidai ta ganta hajjan
"Me akemin da waya ne?,bana son fa satar lamba ahto....idan mutum naso yayimin magana da kaina na dauka na bashi" shuru zahra ta mata,sai da taga ba zatayi shuru ba sannan tace
"Ni ai duka wayarki hajja babu lambar da xan sata fa,babu,ni kawai ko bandakin zaki shiga ki dinga shiga da abarki ma huta" baki ta tabe
"Oho dai,banda rashin gaskiya daga jin tahowata sai a maida waya da sauri a aje,kinga kuwa ai babu gaskiya ne" ta qarasa maganar tana zama,sai kawai zahran tayi kwanciyarta ba tare data sake amsa mata ba,tana ci gaba da maimaita saqon,jikinta yana bata daga inda saqon ya fito,amma zuciyarta ta gaza gasgata hakan,har sai data gaji da kallon saqon,kamar shi xai bata amsar tambayarta,ta sauka daga watsapp dinma gaba daya,saita dora wayar saman qirjinta ta lumshe idanunta tana tuna wasu abubuwa da suka zame mata farilla kullum sai tayi bitarsu a kwanyarta,haka nan tunasu suke sanyata nishadi suke kuma debe mata kewa.


****** ****** *******

*_BAYAN WASU KWANAKI_*


Yamma ce lis,wanda tun safiyar ranar ake fama da hadowar hadari da kuma washewarsa,saidai zuwa yammacin hadarin ya hadu sosai a sama,yana bada iska mai sanyi hadi da qamshin qasa,wanda hakan ke alamta cewa ruwan sama na tafe kowanne lokaci daga sannan


Ita da umaima da ilham ne a falon hajjan,ilham na mata manyan kitso a kanta saboda wankeshi da tayi,ya kuma isheta hakanan babu kitso,tana mata kitson suna hira jefi jefi,suna kuma kallon tashar arewa 24,gidan yauma babu mutane sosai,duk sun tafi sunan faccalar hafsat data haihu,da yake macace me kirki,kusan kowa ya santa a gidan,sauran yaran kuwa kowa yana makaranta.


Suna daga zaune suka jiyo qarar shigowar mota harabar gidan,ilham ta kalli umaima
"Kai....yau wani cikinsu abba ya dawo gida da wuri,mun shigesu yau munyi fashin makaranta....wallahi mu nema wajen buya" harara zahra ta aike musu tana cewa
"Ko kun buya saina gaya musu,ba yadda banyi daku ba ai kuka qi ji,haka ma hajja,gwara ma ku xauna suxo su ganku yafi muku sauqi" tana rufe baki hancinta ya soma shaqar mata qamshinsa,saita saki ajiyar zuciya,tana mamakin yadda ta damu da lamarinsa haka da yawa,tasan cewa ba shi din bane,kawai kamar ta saka lamarin a ranta ne da yawa shi yasa take jin hakan,don haka tayi shuru tana duban bakin qofar dakin hajja tana kallon yadda iska ke daga labulen falon.


Kamar a mafarki taga tsaiwar mutum bakin qofar falon,gabanta yayi wani faduwa data jima bataji irinta ba,ta daga kanta a hankali daga kan takalman da idanunta ke iya gani zuwa sama fuskar mutumin dake tsaye.


Haidar ne,cikin unifoarm na sojoji da suka bayyana zallar kwarjini da kamalarshi,cikakken unifoarm ne a jikinsa,saidai babu hula a a kanshi,kamar yadda ta lura ba kasafai ya fiya son sanya hular ba.


Idanunsu ne suka sarqe cikin na juna,kowannensu ya shiga kallon dan uwanshi,zuciyoyinsu na wani irin rawa tamkar an kusanta mayen qarfe da qarfe,a hankali ya soma takowa cikin falon,idanunsa cikin nata,wani irin abu mai qarfi yana jansa,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa,tamkar me sanda haka yaci gaba da takowar har ya iso dab da su
"Ya haidar sannu da xuwa" muryoyin ilham da umaima suka karade kunnuwansu,saiya cira idanuwansa a hankali zuwa kan yaran,sam baigansu ba,bai kula dasu cikin falon ba sai yanzu,saiya gyada kai,muryarsa da wani irin laushi ya amsa da
"Yauwa,sannunku" ya qarashe zancan idanunsa na sauka kan lallausan gashin zahran da ilham takai kitso na qarshe ta kalmashe mata jelar,a hankali cikin wani irin sanyi da laushi zahran ta miqa hannu ta jawo dan kwalinta daya zame tunda aka fara kitson ta lullube kan nata,idanunta har yanzu suna qasa,ta gaza sake hado ido dashi,sai zuciyarta dake wani irin bugu,duk sai suka miqe,ilham ta dauke man kitson da comb suka nufi qofa ita da umaiman.


Kansu gama ficewa hajja ta fito,tayi turus cikin mamaki tana dubansa
"Kai kuma yaushe ka shigo?" Fuskarta na washewa da fara'a
"Yanzun nan,ko minti daya banyi ba" sakin labulen data riqe tayi,ta soma takowa ciki
"Lale marhabin,wannan irin tafiya haka babu sanarwa babu labari?,tun muna ta zuba idanun ganinka har mun haqura mun janye" dan qaramin murmushi ya saki na gefan baki yana gyara tsaiwarsa,har yanzu idanunsa yana kanta,ita ke daukar hankalinsa tunda ya sanya qafafunsa cikin falon,wani irin kyau da haske yaga ta qara masa,sai yake ganin kamar an canza masa ita,bai sani ba,tsabar kewar data addabi ruhinsa zuciyarsa dama gangar jikinsa ce,ko kuma dai hakane da gasken ta sauya,yaci gaba da dubanta ta gefan ido sanda take miqewa daga qasa zuwa kujera,saboda wani irin weak da jikinta yayi cikin qanqanin lokaci
"Barka da dawowa" ta fada kanta na kallon yatsunta data sawa lalle jiya da daddare,saboda ta gaji da yadda sukayi fari,har faratan hannunta.


Ko kadan ba tare da wani jin nauyi ba,kamar ma ya manta da hajja dake wajen ya zuba mata mayun idanunsa
"Barkanki......mun sameku lafiya?" Yadda ya amsa din ya tilastata daga idanuwanta ta kalleshi,taci sa'a kuwa sun hada ido,saiya jefa mata wani kallo data ji ya girma kanta,tayi saurin dauke qwayar idanunta,sai kuma tayi rashin sa'a suka fada kan hajja,ashe su take kallo,hajjan kuwa data gwanance wajen iya fuskewa dauke idanunta tayi kamar ba'ayi hakan ba,saita miqe ma data jiyo ringing din wayarta tana cewa
"Yauwa....ina zuwa,Allah yasa nusaiba ce".


Fitarta sai falon ya zamana daga ita sai shi,gyaran murya yayi kamar wanda ya qware,ta fuskanci so yake ta sake kallon qwayar idanunsa,wanda ta karanci al'amura masu dama a ciki,bata jin xata iya bari cikin lokaci kadan ta fadi qasa warwas,kota bari ya gane lagonta,ita din ba yau ta fara soyayya ba,tuntuni ta gama karantar kanta tsaf,ta kuma karanci inda zuciyarta tasa gaba,saidai karatun ya bata tsoro qwarai,saboda banbance babancen soyayyarshi data mata wani irin kamu ta ruwan sanyi da sauran soyayyar data yiyyi a baya,wanda yawancinsu sun mata kamu ne ta farat daya,bata taba zata ko kawowa cewa soyayyar da zata dinga shiga jikinka tana dafa ka a hankali tafi illa fiye da wadda zata kamaka farat daya ba.


Batasan ya akayi ba,tana tsaka da wannan tunanin ta shaqi qamshinsa sosai,wanda hakan yake gaya mata mamallakin wannan qamshin yana dab da ita fa,saita daga kanta da hanzari,yana tsaye a kanta ya kafeta da ido dai kamar maye,ya ciro hannunsa guda daya amma sai yayi saurin dunquleshi ya kuma janyeshi baya saboda jin motsin fitowa hajja,sannu a hankali shima ya janye jikinsa
"Zan shiga na sanarwa mama dawowata" ya fadi yana juyawa a hankali,saidai fiye da rabin hankalinsa yana kanta,so yake yaji kalaman bakinta,hakanan bai gaji da ganinta ba,yana son yajita cikin jikinsa,yaji dumin lallausan jikinta da yayi kewarsa kamar yayi hauka,baisan haka aikin yake ba,baisan harda kanshi zai nanawa hauka ba,inda ya sani,da bai fara aikin ba bare ya tafi da tabonsa,ya hanashi sukuni,rashin sukunin da saura qiris ya janyo masa damuwa kan aikin da yaje yi din.


Wata ajiyar zuciya me nauyi ta sauke,ta manta da wanzuwar hajja sam a wajen,sai suka hada idanu da ita,sake fuskewa tayi kamar bata fahimta komai ba,saidai can qarqashin ranta tana jin wani farinciki yana mamayarta,lallai ba shakka Allah shine abun godiya,ta gama karantar komai,tafiyar haidar din aiki ya zame musu kamar wani haske,kuma mataimaki wajen cikar aikinta,ba shakka lokaci yayi,lokaci yayi da za'a kawo qarshen komai kowa ya huta,zatayi qoqari tayi dukkan abinda ya dace,amma zata bashi sati daya kacal taga shin xaiyi wani motsi daya dace shima?.
"Tashi kije ki sama masa wani abun da zaici kafin ya kintsa,tunda yau tazarce kukayi mana saboda tsabar ganda da qyuya,kinsan kuwa shi din ba ci xaiyi ba" karon farko.....lokaci na farko da taji ranta babu damuwa babu takura saboda hajja tace ta sama masa abinci....lokaci na farko da taji tana marmarin shiga kitchen,tun daga qasan ruhinta zuwa zuciyarta,taji a ranta cewa she's ready a dai dai wannan lokacin tayi dukkan girkin daya dace,don haka ba bata lokaci ta yiwa kitchen din tsinke.


Haka kawai ta samu kanta da zurfafa tunaninta kadan ta maidashi can baya,tana tuna kalolin abincin da yafi muradin ci,wanda a wancan lokacin matuqar su sukayi ya dinga gwalewa da kushesa kenan,wataran ma yaqi ci,har sai mama tayi masa fada sannan,ta saki murmushi tana tsaka da aikin,sanda ta tuna wani lokaci da hajja tasa ta diba masa abincin data yiwa abdulyasar,ranar kamar zaiyi me saboda tsabar hade gira,hatta hajjan tasha muzurai,akaci sa'a tayi magana,dama neman mai tankashi yake,yahau fada sosai,har sai dasu hafsat suka dinga kwasarsa suna gulmarsa a boye
"Hmmm...hala yau allurar sojoji ce ta motsa?"
"Allah sarki....duniya labari" ta fada a sarari ita kadai.


Bata dauki wani lokaci mai tsaho ba,kasancewar abincin dai dai cikin daya zuwa mutum biyu tayishi,ta shirya komai bisa wani tsari me birgewa,tana gyara kitchen din hajja ta shigo,ta kalli yadda ta tsara komai saita kyabe baki
"Ashe dai ashe dai,yanzu dukka zakin aka yiwa wannan?" Waiwayowa zahran tayi tana duban kwanukan data shirya da hannunta,sam batasan ma tayi abunda hajjan ta gani din ba sai data magantu,komai a tsare,duk wanda ya kalla saiya burgeshi bare ya bude ciki,flask din hajja ne sababbi,wanda jikoki da 'ya'yanta ke siyo mata da wanda ake bata kyautarsu dake ajiyewa bata amfani dasu suta dauko ta bare ta zuba masa abincin a ciki
"Ya gama ci kuyi lissafin kudin kwanukana,saikun bayani,ko naje har gida na fanshe a kitchen dinki" kunya taji ta kamata sosai,don bata kawo komai a kanta ba sai yanzu,sai ta yiwa hajjan tabarmar kunya,tahau zumbura baki tana cewa
"Wai komai mutum yayi shi bai iya ba,inafa zaman zamana kika ce sai na masa abinci....inda naqi tashi kuma nan ma qilu ta jawo bau,nayin kuma nan ma ban miki gwaninta ba....to inaga kawai a fasa kai abincin"
"Iyeee.....to uwata,ni meye nawa a ciki idan baicin bama,asarata ko taku keda shi?,ki tambaya kiji,mijina bai taba neman abinci ya rasa ba wajena har ya mutu,girki ma daya amsa sunansa ba irin nakun nan ba taba ka lashe....wanda kula da mijinma kamar an muku gori sai ance kuyi,yo ni meye nawa afasa kai masa.....kai....mustapha" tahau qwala kiran gangan da ganganci,don tasan mustapha baya falon,baya ma gidan gaba daya,tun safe abba yusuf ya aikeshi gyaran motarshi,ai kam a sukwane ta saki kwanon hannunta cikin sink ta isa gaban kwanukan
"Saiki bari na bayar da kaina nida nasha aiki,amma kya kira ya musty mai shegen ci da saiya kusa hadawa da flask din duka ya cinye ma?" Dariya sosai ta qwacewa hajja ba tare data shirya ba,sai kuma tadan maze bayan ta gama dariyarta
"Ya suke da mijinki wajen shegen ci,kijimin yarinya" itadai sai raba ido take,kada hajja tayi mata aika aika,bata sake tanka mata ba har ta gama abinda ya kawota kitchen din ta fice abinta ko a jikinta.


Gangar jikinsa ce kawai zaune waje daya da sunan hutu,amma gaba daya zuciyarsa da qwaqwalwarsa sun gaza samun hutun da yake buqata din,ga yunwa da yakeji amma ya kasa katabus,minti daya biyu saiya dubi qofar shigowa sashen nasa,haka kawai jikinsa ke bashi tana nan zuwa gareshi kowanne lokaci,saiya yunqura zai tashi ya aiwatar da abinda zuciyarsa ke gaya masa,sai kuma miskilanci ya maidashinya zaunar,yana sonne ya tabbatarwa kansa cewa aikinsa yayi kyau?,duk da ya fara ganin alamomi da suka sanya ya baiwa kansa mark,tare da shanshano qamshin nasara,mutum ne shi daya tashi kaf rayuwarsa cikin cimma nasara kan abunda yasa gaba,matuqar nasararsa ta kasance......to wannan shine mataki na qarshe da zai kawo qarshen komai.


Miqewa yayi a karo na qarshe,yana jin juriyarsa da haqurinsa sunkai qarshe,bazai iya ci gaba da zaman jira ba,saidai yana isa bakin qofa yaji an murda handle din an turo qofar,dai dai sanda wayarsa ta dauki ringing,saiya dakata daga bayan qofar,ya ciro wayar yana dubawa.


Daya daga cikin jami'ansu ne me suna Deborah,tana qarqashin jagorancinsa,saidai ita din likita ce,wadda sanda suka dawo yabar kulawar sojojin da suka dawo dasu marasa lafiya da masu rauni ana kula dasu a asibitinsu,itace kuma shugabar likitocin ya buqaci zamun duk wani bayani bayan ya tafi kan ci gaban da aka samu kan marasa lafiyan,babbar macace sosai,don tayi shekara a qalla arba'in da takwas,kaf cikin ma'aikatan mata ita kadai yakewa dariya,saboda yana ganin girmanta kamar yadda take ganin nashi.


Mummunar faduwar gaba hadi da bacin raine suka bijiro mata sanda taji ya ambaci sunan mace cikin wayarsa,hakanan yana wayar cikin sakin fuska,abinda ba zata iya tune yaushe ne lokaci na qarshe data jishi yana waya da wani koda namiji bane cikin walwala haka,wani abu ya taso ya tokare mata maqogaro,har yasa kunnuwanta suka toshe,ta daina ji ko gane maganar da yake,maganganun da hasashen da zuciyarta keta kawo mata su take fahimta,don haka tana dire kwandunan hannunta tayi hanyar fita ba tare data ko kalleshi ba.


Duk takunta daya idanunsa na biye da ita,sai hankalinsa ya rabu biyu,rabi naga wayar da yakeyi,rabi kuma na akanta,karon farko daya taba qarewa tafiyarta kallo,kamar wadda ke rangaji haka takunta suke a tsare,saidai yanayin halittarta ne hakan,batasan ma hakan na faruwa ba.


Ganin ta nufo qofar gadan gadan saiya taka a hankali ya qarasa rufe qofar,ya murza muqulli ya rufeta gaba daya,sannan ya jingina jikinsa da qofar,sai ya zaman shida ita suna fuskantar juna.


Zata iya cewa bataji ya yiwa wadda suke wayar sallama ba,yadai zame wayar daga kunnensa ya jefata gefanshi,tsintar kanta kawai tayi cikin jikinsa,ya mata wata kyakkyawar runguma da taso zabge duk wani baci da ranta yayi kan wayar da yayi yanzun.


Tuni jikinta ya soma mutuwa saboda qamshij da jikinsa ke fitarwa,da wani irin dumi dake fita daga jikinsa zuwa nata,amma duk da haka ta aje wannan gefe,ta soma turashi da yunqurin barin jikinsa,da sauri ya sake yi mata qawanya da hannayensa yana sake yi mata kyakkyawan mazauni cikin qirjinsa yana fadin
"Ke......relax mana,kada kiyi kishi....abokiyar aikina ce fa,nothing else" mamaki ne ya kamata sosai,ya akayi ya karanci haka daga idanuwanta kawai?,kamar me aiki da sihiri,ko kuma wanda ya karanci ilimin sanin halayyar dan adam.


Mintuna a qalla kusan biyar suna tsaye a haka,shuru ba tare da ya sake cewa komai ba,ita dinma haka,kowa na sauraren bugun zuciya da fitar numfashin dan uwansa,ita kanta batasan ke ya debeta taci gaba da zama cikin jikinsa ba,sai taga ya kamata tayi koda pretendin ne,kada ta zubda kanta
"Ka sakeni" ta fada tana tura hannayensa,da sauri ya hannunsa ya birkitota ta dawo tana fuskantarsa,a maimakon dazu data bashi baya,hannayensa duka biyun ya sanya ya kama qugunta ya ruqe yana qarewa fuskarta kallo,cikin wata murya mai laushi da sanyi,can qasan maqoshi wanda koda kana kusa dasu sai ka kasa kunnenka sannan zaka iya jin abinda suke fada yace
"Zahra...." Mamaki ya kusan kasheta a tsaye a wajen,dama yasan sunanta ne?,eh dole tace haka,saboda tsahon rayuwarsu cikin gidan bata taba jin ya ambaci sunanta ba ko a wasa,ji tayi duk duniya kamar yafi kowa iya ambaton sunanta,kamar ya fadi sunan nata ne da wani yaren daban ba hausa ba
"Ke kadai ce rayuwata bata da amfani cikin taki rayuwar ko?" Ji tayi tambayar ta mata nauyi sosai,bata kuma gama fahimtar abinda ya fada din
"Yes....kowa yayi kewata amma banda ke....kowa yana nemana amma banda ke,kyautawa kenan?" Lallai yau mamakin da haidar din yake bata ya wuce tunaninta,da zata iya zata so

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login