Showing 87001 words to 90000 words out of 121250 words
tsokanarta,shi yasa take zama da hijabin.
Barin gaban madubin tayi ta tattara kayan ta fice dasu backyard na gidan,inda yake da famfo da wajen shanya ta zubesu ta fara wankewa,babu jimawa ta gama ta fara shanyansu daya bayan daya.
A nutse ya fito daga dakinsa yana rufe bakinsa saboda hammae data subuce masa,ya dubi kan dining yaga wayam babu komai,sai yasa hannu ya shafi cikinsa,don yunwa yakeji qwarai,gajiya ce ta hanashi fita yau da wuri yadda ya saba,ya yanke kawai ya kwanta yadan huta zuwa azahar ya fita din,ganin babu komai akan dining din saiya juya ya shige kitchen.
Can ma wayam,saiya taka a hankali ya bude qofar da zata sadaka da bayan gidan don ya samu fresh air kafin yayi tunanin abinda zaici.
Itace ta farko da idanunsa suka fara gani,tana ta shanyarta a nutse,gefe da gefen zaninta duka ya jiqe,hakan ya sanya yabi jikinta ya lafe,ya bayyana shatin santala santalan cinyoyinta,t.shirt din jikinta ta zauna mata itama ta fitar da duk wata sura tata.
A hankali yakai bayansa ya jingina da qofar daya bude din,yana goye hannayensa a qirjinsa,ba tare da yasan me yake aikatawa ba yaci gaba da binta da idanunsa duk inda ta motsa,wani irin abu me qarfi da baisan meye ba yana fusgarshi zuwa gareta.
Ζarar faduwar bucket daga hannunta shi ya taimaka masa ya dawo zuwa hayyacinsa,da sauri ya taka a hankali da baya ya koma cikin kitchen din,yana sauke ajiyar zuciya tare da jin dadi da bata ganshi ba,cak ya tsaya tsakiyar kitchen din,yama rasa wanne tunani yake,yasa hannunsa ya ranqwashi tsakiyar kansa,cikin zuciyarsa yana gayawa kansa me yake damunsa?,me yake aikatawa haka?,dogon tsaki yaja ya taka zuwa inda gas yake ya kunna ya dauki tukunya ya zuba ruwa,saidai kafin yakai ga zuba kayan hadin tea din ya lura da flask din tea dake wajen,yakai hannu ya daga sai yaji akwai a ciki,don haka ya dauki cup ya zuba ya jingina bayansa yana kurba a hankali.
A hankali ya dinga ganin motsinta na daxu cikin idanunsa,ba tare daya ankara ba zuciyarsa ta soma zayyano masa irin abubuwan da yake buqata tare da mace,kowanne tana haska masa shi cikin idanunsa,yana kaucewa da qarfin tsiya tare da qaryata kanshi da kanshi,ya dinga jan tsaki shi daya yana kokawa da tunanin.
Da hanzarinta batare da tsammanin akwai wani a kitchen din ba ta shigo,saita zabura zata koma da baya,daidai sanda suka hada idanu,saita tsaya cak na wasu sakanni,sanda taga ya dauke idanunsa ta fara shigowa ciki don ta wuce,zuciyarta na wani irin bugawa da yaqi daidaita.
Sake daga idanunsa yayi karo na biyu yana kallonta ta qasan idanu,kallon da idan duba daya kayi masa ba zaka zaci ita yake kallo ba,saika dauka a lumshe idanunsa suke,dab da zata giftashi tace
"Ina kwana" ya amsa qasan maqoshinsa.
Ji take kamar zata harde ta fadi,jikinta yana gaya mata akwai idanu a kanta,kamar ta zuqo qofar ficewa daga falon ta fice gaba daya,saidai kash!,dab da zata fita taji muryarsa a dake yana cewa
"Zo nan" haka kawai ya tsinci kansa da fadin hakan ba tare daya shirya ba,sai yaji baiso ta fice ne kawai,kamar tace masa zata qarasa daki ta dauka hijabi,to amma batasan me zaya fassara hakan ba,don haka ta sake juyowa ta dawo zuwa inda yake,dukka idanunsa na kanta da salon kallon qasa qasa mai kama da me bacci
"Hadamin breakfast" ya furta yana sake kurbar tea din hannunsa,ta zaci fita zayayi ya bata waje,sai taga ya matsa gefe kawai abinsa yana ci gaba da shan tea dinsa,daga qarshe ma sai yaja kujera yayi zamansa cikin kitchen din,sannu sannu kansa tsaye yaci gaba da binta da kallo duk motsin da zatayi.
Gaba daya duk sai ta rude ta daburce,sabida wani irin tasiri da idanunsa ke mata cikin jikinta,jikinta duka rawa yake,gani take kaman ba ya zakinsu ba,tun da can idan ya tsareka da idanunsa saika gwammace ya dakeka akan kallonsa mai nauyi,wani irin kwarjini ne cikin idanunsa,batasan me yasa ya tsareta haka da kallo ba,don haka duk aikin da zatayi saita dinga yinsa kwan gaba kwan baya.
Ta bangaren haidar kuwa haka kawai ya samu kansa da nazarinta,tun daga halitta zuwa yanayin aiki,shi kansa baisan nazarin na meye ba,amma ya kasa dainawa ko hana kanshi,har zuwa lokacin data sanya hannu zata sauke prying pan,wanda sam ta manta da ya kamata tasa wani tsumma ko safar hannu ta kitchen dake rataye kafin ta sauke din,sai ta saka hannun nata kawai kai tsaye.
Cikin tsananin jin zafi ta saki prying pan din tana sakin qara,abinda ke ciki ya tarwatse,radadi da zugi ya soma ratsata,ta fara yarfe hannunta.
Cikin sauri ya iso wajen kamar qiftawar idanu,yasa qafarsa da sauri ya ture frying pan din wanda saura kadan ta sanya qafarta still,hannun nata ya kama da sauri yana dubawa,tuni qwalla ta fara cika mata idanu saboda zafi,tuni yatsun sunyi ja,sai yajata suka isa bakin famfo ya kunna ya tara hannun a qasan ruwan dake zuba,a hankali sanyin ruwan ya fara ratsata,radadin ya tafi,saita lumshe idanu tana sakin ajiyar zuciya,dai dai lokacin da yake kallon fuskarta da lamsassun idanunta ke a rufe har yanzu.
Abinda bata so yawan kusancinsu,duk sanda yayi kusa da ita sosai haka takanji wani nauyi daga gangar jikinta har zuciyarta,sai taji kamar ya cika wajen da kwarjininsa da haibarsa,bugun zuciyarta yakan dadu,jiki da zuciyarta yayi wani laushi,ba zata iya fayyace me takeji game dashi ba,saidai ta sani cewa ya rage jin haushi da tsanarsa tun ranar bikin qara musu girma,maimakon haushinsa sai bugun zuciya da jin nauyinsa daya maye gurbi,haka kawai taji wani rauni na mamayarta,hakan ya baiwa qwalla damar ratsowa ta gefen idanunta.
A lokacin yana tsaye yana qarewa fuskarta kallo,yaga wasu abubuwa sama fuskarta da suke kama da nashi,wanda ko qannensa da suka fito ciki daya basuyi tarayya wajen kamanceceniya a su ba,a baya sanda take qarama idan aka fadi akwai kamannin,yana kallon mai fadar ne a matsayin me matsalar gani da kyau,amma a yanzu a dai dai wannan lokacin ya yarda kai tsaye babu musu.
Yatsunsa biyu ya saka a hankali ya dauke qwallar dake fitowa din
"Raguwa....kuka kikewa ciwon?,haka kikewa hajja?" Yaji ba zato ya fada,ita kanta sai data bude idanunta da gashin idanun suka jiqe da hawaye ta dubeshi mamaki fal qasan ranta,suna hada idanu ya janye idonsa kamar bashi ne yayi maganar ba,saiya saka hannu ya kashe famfon,ya jawo hannun saitin bakinsa ya soma karanta mata fatiha babu adadi yana tofa mata,daga ita har shi babu wani me cewa komai,sai hada idanu da sukanyi lokaci zuwa lokaci.
23/10/2021, 08:47 - ππ»ππ»: 33
Karo na qarshe da suka hada idanun saiya saki hannun nata,yaja mata kujera ya mata nuni da idanu kan ta zauna a kai,a sanyaye kuma a hankali ta zauna din,saiya juya ya tsugunna yana tsince barin da tayi,ya gyara komai,kawai sai tagq yaci gaba da girkin
"Ya rabb..." Ta fada tana lumshe idanunta cike da zallar mamakin ya haidar din,dama zai iya amsar mata girki saboda kawai ta qone?,sauqin kaine ko ganin dama?,saboda dai su sun riga da sunsan halinsa,mai fada da kaushin hali shine tambarinsa a wajensu,bata gushe ba tana binsa da kallon mamaki har sanda ya kammala,yana juyowa suka hada ido,karon farko data ji wani abu me kama da kunya ya kamata,saboda kamata da yayi tana kallonsa,sai ya basar kawai yana riqe da plate din ya miqa mata daya,sauran kuma yayi hanyar fita dasu.
A daske a wajen take bin farantin da kallo,ya hada komai perfectly,duk da dama ta kusa gama komai din,amma shima yayi qoqari sosai,ba yunwa take ji ba,amma sai taji tana sha'awar taste dinshi,don haka ta sanya hannu ta diba takai bakinta.
Komai yayi daidai,kamar ita ta zuba seasoning din,a hankali tana ci tana ci sai gashi taci da dan yawa,ta ajjiye plate din tana duba hannunta,bai tashi ba har yanzu saidai alamun quna,hakan yayi mata dadi,tasan kuma sirrin fatihar daya dinga karanta mata ce.
Da kanshi ya dinga gayawa kansa akwai matsala,yana jin tsoron faruwar wani abu,yana ga ya kamata ya maidata gida tun baiyi abun kunya ba,abun kunyar daya tabbatar da cewa hajja saita masa tareren kaf dangi da 'yan uwa.
Bai taba yarda da zantukan abokansa ba sai yanzu,wani lokaci idan suna irin wadan nan hirarrakin da suka danganci aure,yana dauka shirmensu ne kawai da kuma batawa kai lokaci,har suna ganin ko lafiya ce baida ita?,saboda sun riga da sun saba,dai daiku ne cikin wanda zai zama soja,ya kuma kai mataki da matsayin da haidar din ke kai ba tare da yana mu'amala da mata ba ko kuma shaye shayen abubuwan maye,sai gashi shi din Allah ya tsarkake shi,ya kubutar dashi,ko sigari baya sha bare akai ga barasa da sauransu,game da mata kuwa bai ma tsaiwa ya musu wani dogon kallo,ko yayi dogon nazari a kansu da zaya dami rayuwarsa,hakan ya kawo masa sauqin al'amuransa sosai,ya kuma sake kauda masa duk wani abu game dasu,duk da yasha tsallake tarkunansu,saidai suma suna kama kansu saboda sunsan halinsa,bashi da sauqi sam.
Yana gama cin abincin yayi wanka ya fice,bai dawo ba sai gab da magariba,ganin an kusa kira saiya daura alwala kawai,da niyyar idan ya dawo yayi wanka,sannan ya leqa yaga hannun nata,ya kuma nema musu abinda zasuci,saidai yayi mamaki da yazo tafiya sallah yaga kwanuka kan dining,harta samu qarfin halin yin girki kenan.
Tana dakin taji dawowarsa,saidai bata sa sha'awar fitowa don ta gama duk abinda tasan zai maidata falon,ana kiran sallah ta shiga wanka,ta fito ta shirya cikin hight waisted skert ta shirt mai gajeran hannu wadda ta dace da skert din,ya fidda qugunta sosai tare da plate tummy dinta,gashinta ta taje sosai wanda ta tsefeshi saboda tana period,yawanci haka takeyi,saita tsefe idan zatayi wankan tsarki ta wankeshi sannan a maida mata kitso idan tana ra'ayi.
Kamar daga sama taji sallama a falonsu,saita aje comb din hannunta da take kwantar da gashin nata cikin sauri ta bude qofa ta nufi parlour din.
Dr nasreen ce a tsaye cikin ado kamar yadda take a dabi'ance,kowaccensu fuskarta qunshe da fara'a suka nufi juna cikin murna,don har zuciyarta zahra taji dadin zuwan dr nasreen din,ko banza ta debe mata kewa yau na wasu awanni.
Sai data cikata da kayan ciye ciye sannan ta dubeta cikin mamakin me yasa har yanzu bata zauna ba
"Zauna mana kinata tsaye haka?" Murmushi tayi ta girgiza kai
"Ai banga ta zama ba,dear tana waje fa a tsaye" ido zahra ta fitar
"Kai!,ya shigo mana,me yasa kuma zai tsaya a waje" kai ta girgiza tana qwalalo ido
"Ah wai....ai bazai shigo ba,yasan fa waye mai gidan nan,wannan boss din naki akwai ban tsoro,yasan halinsa sarai....,ki fara shaida masa dai yana da baqo ko?" Saita dan daburce,tana nufin ta shiga dakinsa kenan ta masa magana,tunda ta tabbatar yana dakin tunda ya dawo gidan,dakin da tunda tazo bata taba gigin shigarsa ba,batason tace wani abu da zata dago kome ke tsakaninsu,don haka cikin fara'ar yaqe tace
"Yanzu kuwa zan sanar mishi,ai ba'a bar masoyi a waje ba" tayi qarfin halin tsokanarta,sai ta sake fadada fara'arta tana cewa
"Kema kya fada,shi yasa na kasa zama ai".
Inda zai yiwu zata faki idanun nasreen ne taje ta sanyo hijabi,to amma yin hakan zai sanya ta saka mata ayar tambaya,dole qanwar naqi tayi qundunbala takuma yi shahadar quda ta durfafi dakin.
Fitowarsa daga wanka kenan daure da towel iya qugunsa,yana tsaye gaban mudubi yana sharce ruwan jikinsa,duk da cewa daga wanka ya fito kuma a tube yake amma ac ke kwarara cikin dakin,kamar baya jin yawan da tayi.
A hankali ta bude qofar dakin ta saka kai,ta daga idanunta a hankali tana wulgasu cikin dakin,saiko suka sauka a kansa yana taje kansa da wani cumb,idanunsa cikin madubin yana kallota,ko kadan bata tsammaci samunshi a yanayin data ganshi ba,yanayin qira da duk wata siffa ta jikinsa ta fito muraren,mai tsayayyen jiki da siffa dake nuna qarfi da mazantaka,da kuma alamun ya horu sosai kan aikinsa,kana ganinsa kasan yana daga qarfe.
Sosai idanunta suka nuna razana muraran,da hanzari ta juya a sukwane ta durfafi qofa,taku uku qwarara ya cimmata,ya sanya hannu ya cafkota tare da birkitota gaba daya,sai gata tayi kyakkyawan masauki cikin faffadan qirjinsa,damshin ruwan dake jikinsa ya ratsa fatar hannunta da wuyanta,tsigar jikinta ta zuba,saiya matseta yana fadin
"Nutsu mana,ina zaki koma a haka kamar wadda wani mugun abu ya biyo,ba baqi mukayi ba?" Ya fada a dake,kasa furta komai tayi sai jikinta dake rawa,saiya yasa hannu ya janyeta daga jikinsa yana ladabtar da ita da kaifaffan kallonshi.
A nutse yake qare mata kallo tun daga yatsun qafarta har zuwa kanta dake gyare cike da baqa qirin din suma,fuska a hade yake dubanta
"Uhummm....,me yasa ko yaushe kike firgita kanki?,tell me,meke baki tsoro a jikina?" Gam ta rintse idanunta,don har ga Allah ba zata iya kallonshi a yadda yake tsaye a gabanta ba,don ita a wajenta bashi da maraba da tsirara,gashi hanya takeso ta samu ta tsere,saiya kada yatsanshi saman fuskarta
"Niba dodo bane?....kinji ni?" Kai ta gyada,sotake kawai ya bata waje ta fita,amma a maimakon haka ma sai taji yana saka lock na jikin qofar yana rufe qofar,saita bude idanunta da sauri,sai kuma ta sake kauda kai,cikin rawar murya tace
"Pls....zanje wajenta....jira take" baiko bi ta kanta ba yayi gaba abinsa,ya bude ma'ajiyar kayansa ya dauko wanda ya dace da ra'ayinsa,ya dawo gaban mudubin yaci gaba da shiryawa,tilas taci gaba da tsaiwa tana jiran tsammani,saidai kuma ta bashi bayane tana duban qofa,hakan ya bashi damar qare mata kallo,lokaci lokaci,yana dubanta yana shiryawa.
Batasan ya gama ba duk da qamshin turarensa mai laushi daya addabeta,har sai data ji yana bude qofar sannan ta ware idanunta a hankali,sannan ta tako ta nufi qofar,dab da shi ta tsaya ganin shima yana tsaye bai fita ba,cikin husky voice dinshi yace
"Ko yaya iyayenka suka yanke maka hukunci,duk boren da zakayi kada ka yarda ka nunama duniya....aikata hakan kamar kana gayawa duniya ne how valueless they are",sai ya fara takawa yana ficewa daga dakin.
Magana yayi mata me harshen damo,saidai ta fahimceshi sarai,don haka tabi bayansa itama tana gyara yanayin fuskarta.
Ta taras suna gaisawa da nasreen din,daga yanda suke gaisawa kawai ya isa ka gane tana ganin girmansa sosai,cikin 'yar dariya kasancewarta mai yawan barkwanci tace
"Ai cewa dear nayi yazo muje dubiya....Allah yasa qaruwa muka samu" dan murmushin gefan baki kawai yayi,saidai ya maida dubansa ga zahra,sannan yace
"Wata qila,gatanan kya tambayeta" saiya miqe yana ficewa daga falon.
Dan tabota nasreen tayi
"Kai qawata daga zuwa kiransa yanzu fisabilillahi shine aka shanyani?" Murmushi tayi
"Ayimin afuwa...." Tun kafin ta qarasa tace
"Anyi miki....tun kafin boss yayi aure munsha yin gulmarsa nida dear...mun gode Allah ma da gidansa ke shiguwa,saboda irinsu ko.....basu iya qonewa a love ba,ki gansu a waje kamar gaske,amma a gida...uhmmm" dariya sosai ta baiwa zahra,lallai batasan ya haidar ba da bata fadi haka ba,batajin irinsu so na shagaltar dasu haka,amma saita share zancen kawai suka shiga wata firar.
Tunda ya isa farfajiyar gidan yaga tare suke da major ya sake tamke girarsa sosai,duk da cewa akwai saif a wajen
"Yallabai....irin wannan shanyamu haka?" Major ya fada yana washe baki,wani kallo haidar ya masa sanda yake bawa jafar hannu suna gaisawa,sai da yazo kansa sannan ya amsa mishi
"Da kasan kana da abubuwan yi da yawa ma da baka zo ba,incase nan gaba kaga irin haka ka dinga tafiyarka kawai" saif dai na danne dannen waya yana boye dariyarsa,shi yasan qarshen alewa qasa,don major ya dage ne kawai saiya biyosu,amma yasan haidar din bazaiyi maraba da zuwanshi ba,jin amsar daya bashin sai yayi shiru baice komai ba.
Daga nan inda suke tsaye haidar din ya qwalawa mai gadi kira,ya bashi umarnin bude guest room sannan suka dunguma zuwa ciki.
Zuwan dama ya shafi ayyukansu ne,tattaunawa zasuyi ta musamman,don haka kai tsaye haidar ya shiga abinda ya tarasu,don shi sam bai farinciki da zuwan major,shima daya lura da hakan suna gama maganar data tarasun ya musu sallama,yace yana da wani uzuri,akwai inda zashi.
Yana fita saif ya qyalqyale da dariya yana kallon yadda haidar din ya hada girar sama da qasa
"Mai master....wannan wai duka kishin ne haka?,lallai fatima ta ciri tuta...wannan so ba qarami bane" dashi da saif din duka sunsan magana yake gaya masa a fakaice,saiya masa wani irin kallo ya bude baki
"Sosai,ko laifi ne hakan?....akan me ma zaku daukomin wannan kwarton ku shigomin dashi gidana....kai J,haka ka hadoshi da matarka a mota daya kuka taho?" Ya jefawa jafar tambayar,bai amsa mishi ba shima illa danne dariyarsa da yakeyi,sai haidar din ya jijjiga kai
"Next time zan gaya mata,duk sanda zaka dauki wani qato a motarka to saika sama mata abun hawa,koka bata motar tayi driving ku kuje ku hau ta haya....kai kuma" ya nuna saif
"Ka kiyayi haduwarmu wallahi" saiya miqe yana ficewa don sawa a amso musu drinks.