Showing 9001 words to 12000 words out of 121250 words

Chapter 4 - ALKIBLA complete

Start ads

24 Aug 2025

452

Middle Ads

daurin da za'a kasa ganeshi,ba gidan 'yan iska bane nan,hope kin haddace abinda nace?" Tuni hawaye ya soma ambaliya saman fuskarta saboda tsabar bacin rai,hakanne yasa ta kasa amsa mishi,har sai daya maimaita mata cikin tsawa
"Kinji ko bakiji ba?"
"Naji" ta amsa cikin muryar kuka
"Ku bacemin a wajen sakarkaru kawai!" Ya kuma fada cikin tsawar.


Tuni suka miqe har suna rige rigen barin wajen,sai da suka tabbatar sun bar inda zai iya jinsu suka fara bawa zahra dake kuka haquri,kasa amsa musu da komai tayi,ta kuma kasa zuwa tura watsapp da zuwa sassan umminta don tayata dora girkin da mafi yawancin lokutta nata girkin dana hajja take hadawa,duk da itama hajjan idan tayi sha'awar wani abun tana dafa abinta,sai kawai ta juya ta koma sassan hajjan da sassarfa kuka Na sake qwace mata,maganganunsa na dawo mata.


Me yake nufi kenan?yana mata kallon 'yar iska ne koko meye?,bin maxa take a makarantar kenan har suke biyota gidan ubanta yake nufi?ko ita ta kirayesu tace suzo,bayan batama san kosu waye sukazo din ba,fatanta daya Allah kada yasanya da nuraddeen dinta akayi hakan.


Saman kujera ta zube a falon tana qoqarin tsaida qwallarta duk da taqi tsaiwa,daidai lokacin hajja ta fito daga dakinta tana riqe da carbi,da alama zikirinta data saba takeyi.


"Ke lafiya?,kukan me kike bayan qalau kuka fita?" Hajjan ta jero mata tambayar tana tsaiwa kan zahran tana rungume da hannunta fuskarta cike da damuwa da fargaba.


Kasa bata amsa tayi saboda yadda zuciyarta ke suya,sai data dauki wasu mintuna kana cikin sheshsheqar kuka ta gaya mata abinda ya faru,sannan ta dora da cewa
"Ki masa magana hajja,ki shiga tsakanina dashi"
"Ya isa,amma karna qara jin kince haka saboda yayanki ya miki fada,kawai maganganun daya fada dinne basu dace ba,tunda an jima ana wannan case din,kuma duk sanda irin haka ta tashi ina masa bayani,dole su dinga haquri wata macen haka Allah ya halicceta da farinjini,kome qoqarinta na ganin ta kaucewa samari bata isa ba musamman idan tana kan ganiyarta,yanzu dai ki tsaida kukan nan haka,zaizo ya sameni har inda nake".


Da qyar hajja ta sha kanta,duk da tsaida kukan amma saitayi kwanciyarta saman doguwar kujera tana ta hadiyar zuciya gamida tuna maganganun daya gasa mata,ta jima zaune anan har akayi sallar magariba sannan ta shiga dakinta ta daura alwala ga bada farali,bata cire hijabin jikinta ba ta miqe da niyyar taje ta tura watsapp din da bata samu damar turawa dazu ba.


"Ga abincin dare fa an gama,ki tsaya kici sannan ki fita"
"Yanzu zan dawo hajja,ba dadewa zanyi ba" ta amsa mata tana ficewa,don tana son taga nuraddeen koda online ne,shurun yayi yawa,bataso kuma ta sake kiranshi da kanta.


Da sallama ta shiga babban falon sassan,kusan duka yaran gidan na zaune a falon,ba kums komai suke ba sai kallon tashar arewa 24,abinda ita sam bai ɗaɗata da qasa ba,sau tari tafi ganewa tayi charting da qawayenta a watsapp,don idan baquwar number ma tayi mata magana sau tari tana blocking dinta ne,don wayar tata a kowanne lokaci umminya na iya karba babu notice ta binciketa,hakanan yayanta ammar,idan ba watsapp ba kuwa sai tahau facebook ta karanta labarai kota kalli vedio,ko instagram ta kalli hotuna da gajerun labarai,duk da ba kasafai ta fiya hawa instagram dinta ba,saboda tattalin data dinta.


Dan zama cikinsu tayi aka dan taba cafta,don ta tadda ya musty da adam,wadanda dukkaninsu gwanayen raha ne da barkwanci,ba zaka ce ciki daya suka fito da yaa haidar ba,shi kadai kusan ya fita zakka a cikinsu
"Ina yaa zahra ne?" Zahran ta tambaya unaisa dake wani assigment,duk kuma rabin hankalinta nakan tv
"Tana ciki ita da ya hafsa"
"Abba babba fa?"
"Ya fita masallaci bai dawo ba"
"Ok" ta fada tana miqewa,kanta tsaye ta nufi dakinsu hafsat din.


Su uku ta samu a dakin,yasira 'yar mommy hafsa da kuma zahra din.


Zahrar na zaune saman dressing chair dake gaban mirrow din dakin,sanye da purple din hijabi mai hannu,ma'abociyar sanya hijabi ce,zaiyi wuya ka sameta babu hijab,duk wanda ya santa a haka ya santa,yasira na qasan dakin zaune tana cin abinci,hafsa na zaune saman katifa,hannun zahran riqe da wasu takaddu,fuskarta cike da fara'a,da alama cikin farinciki take,jifa jifa suna taba hira dasu yasiran zahra tayi sallama.


Dukkansu suka amsa mata zahra na sauke qafarta data dora daya saman daya tana gyara takardunta dake riqe a hannunta
"Yanzu nakeson gama cin abinci naje na amso tsarabata" yasira ta fada tana dauke hannunta daga kwanon abincin,murmushi zahra tayi wanda ya bayyana jerarrun haqoranta tana jifan yasira da harara
"Wai wuni guda don Allah ina kika je?"
"Au basu gaya miki ba?,wallahi shirye shiryen bikin huda muketa yi,mommy tace naje ayi dani,tunda hudan nata naci da mitar naqi cewa komai" idanu xahra ta fidda
"Wayyo,kada dai kice babu ni za'ayi sabgar?,saura sati nawa?"
"Sati biyar ya rage" saita narke fuska kamar zata sanya kuka,harga Allah taji babu dadi,don taso ace tana nan za'ayi bikin,don suna shiri da huda sosai
"Sati daya da komawata school kenan fa?,kai ya rabb,ka rabani da wannan boarding din" dariya dukka suka saka mata,saboda kullum bata rasa abun qorafi dangane da makarantar,amma sun sani dole tayi haquri ta qarasa,tunda tazo tsakiya.


Neman wajen zama tayi bayan ta yiwa yasiran fatan alkhairi a bikin ta dubi xahra
"Takwara....zuwa nayi ki turan watsapp,nawa yayi expeir.....amma naga yau fuskarki kamar gonar auduga" caraf hafsa ta karbe
"Yo ba dole ba.....ta samu admission fa a kust wudil" cikin mamaki zahra ke duban hafsa,abu biyu ya bata mamaki,na farko ya haidar data tsayar a matsayin wanda zasuyi aure ita dashi ya sani ya kuma aminta cewa zatayi?,abu na biyu indai kuwa hakanne su me yasa harda shi cikin masu dokar ba zasu ɗara daga secondry ba?".


Kamar hafsa tasan me take tunani cikin salo na mita tace
"Kinga aikin dan adam ko?,mu nan ya tsaya an saka mana dokar aure muna candy amma shi xaibar matarsa ta soma jami'a,saiya wani fake da cewar zuwa sanda zata gama ko tayi nisa a karatun ta qara girma da shekaru.....zuwa sannan shine dai dai aurensu".


Maida dubanta tayi ga zahra dake murmushi kawai tana dubansu,tana kuma mamakin yadda suke sanyawa yayansu tsanani da yawa haka,duk da ta sani cewa shi dinma ba kanwar lasa bace,baida sauqi ta kowanne bangare,hakanan bauɗaɗɗen mutum ne me wuyar sha'ani,wanda idan baka fuskanceshi ba baka kuma karanci ALƘIBLArsa ba zaka ci wuyar zama dashi,amma kuma yana da dadin xama qwarai idan ka ganeshi ka kuma gane wayeshi,ka tsare doka da qa'odojinsa,ita din shaida ce,don bata tunanin soyayyarsu xatayi tsahon rai haka ba,bata taba tunanin zasu shaqu da zazzarfar soyayya a tsakaninsu haka ba,bata taba masa kallon qwararre kuma gwani a fannin soyayya ba saida suka fara son junansu,bata jin a duniya akwai wani namiji da yakai haidar dinta iya sanin makamai da matakan mallakar zuciyar mace,ya kuma tafi da dukkan tunani da imaninta lokaci qanqani.


"Allah ya kyauta" zahra ta fada cike da mamaki da ganin cewa ya raina ma zahran wayo kawai,wato kallon yarinya da bata isa ma aure yake mata ba kenan?,abinda a qalla dukkansu ta basu shekara biyu wasu ma uku,tana mamakin wanne irin so take masa haka?,tana kuma jinjina mata yadda ta iya juriya da tafiyar da halayyarsa,sam ita ko zancansa ma batason yi,don haka ta dora mata wayar saman cinyarta kawai tace ta tura mata,ta kuma amshi takardun hannunta tana dubawa gami da kautar da wannan hirar.


Kusan awarta guda a dakin sannan ta karbi wayar ta musu sallama ta fito,tana fitowa mama na fitowa daga kitchen dauke da fulasan abincin mai gidan,qarasawa tayi wajen mama ta russuna cikin girmamawa tana gaidata
"Lafia lau inna wuro 'yan makaranta,ashe kin dawo?" Kaita gyada
"Eh na shigo daxun ai mommy tace min baki nan"
"Ban ko jima da shigowa ba,matar auwalu ce a akwance a asibiti ba lpy,kuma kwata kwata ban samu zuwa dubata din ba sai jiya"
"Ayyah anty laraba,Allah ya sawwaqe"
"Amin amin"
"Abba ya shigo kuwa?,ban samu gaisawa dasu ba duka wannan karon ba wanda na samu a gida"
"Eh ai kuwa duk suna tare yau zasuci abincin dare tare,muje saiku gaisa" maman ta fada ta fara yin gaba,zahran ta bita ta amshi kwanukan daga hannunta ta riqe,maman tayi gaba ita kuma ta bita a baya.


Tun kafin su shiga take jiyo muryoyinsu cikin raha da barkwanci,hira irin ta 'yan uwantaka,'yan uwan da kansu ke hade suke kuma ƙaunar junansu.


Cikin qanqanin lokaci Idanunta suka tara hawaye,ba abinda ya fado mata sai mahaifinta,da tuni yanzu haka yana cikinsu anayi dashi,duk da cewa suma din sun riqeta tamkar su suka haifeta,kamar yadda itama ta daukesun a haka,amma duk da wannan babu wanda zai cike maka gurbin mahaifa a yayin daka rasa daya daga cikinsu.


Sallama tayi bayan mama tayi tata,dukka suka amsa,kowa kuma ya soma nuna murnar ganinta,yayin da nauyi da kunyarsu duka ta kamata,ta qarasa tsakiyarsu ta aje kwanukan,sannan ta matsa gefe a nutse tana gaidasu daya bayan daya cikin girmamawa,kowanne na amsawa cikin nuna kulawa,suna kuma mata tambayoyi kan karatu da sauransu.


Kusan a qalla minti biyar kafin ta tashi tana cewa
"Abba saida safe,saida safenku abba"
"To Allah ya bamu alkhairi" suka fada kusan a tare,ta juya a hankali cikin nutsuwa ta fice.


Har ta nufi sassan hajja sai kuma taga ya kamata ta sake zuwa taga mahaifiyarta,don haka saita sauya akala xuwa nasu sassan.


Da sallama ta shiga kamar yadda dabi'arta take tana saka kai cikin falon,sai kuma ta soma rage fara'a da walwalar kan fuskarta ganinsa zaune darashe darashe tsakiyar falon nasu yana cin abinci hankalinsa a kwance shida qaninta rafeeq,ta gefan idanu ta saci kallonsu tana qarasowa cikin falon,ranta cike fal da mamakin shaquwa da sabon dake tsakaninsa da umminta,kusan kaf fadin gidan bata taba taba ganin inda yake zama ya sake haka yaci abinci ba bayaga wajen hajja sai wajen ummi,duk da cewa dama can tun tasowarta ta budi ido da ganinsa a sassan nasu da kuma kalar wannan alaqar tsakaninsa da ummin nata,saidai kuma bayan rasuwar mahaifinsun wata sabuwar kulawa yake sake bawa ummin da duka qannenta.


"Bakiga mutane bane da zaki shigo ki samu waje kizauna kanki tsaye baki gaidasu ba?" Ummintata ta jefa mata tambayar da tafi kama da akwai wata a qasa kenan,a sanyaye tace
"Aina gaisheshi tun dazun?"
"Ok,shi yasa yanzu ba zaki qara ba kenan?" Kaita girgiza kawai dolenta a sanyaye tace
"Ina wuni?"sai daya sha qamshi sannan yace
"Riqe abarki kawai,tunda sai kinyi jayayya da na gaba dake sannan zakiyi abinda aka saki" wani ɓacin rai ne taji ya riqe mata wuya,cikin ranta tace
"Wato ko dakin mamarka munafiki ya rigaka shiga sai kaga sauyin fuska,yanzu gashi babu gaira ba dalili daga zuwa ganin mamarta zai hadasu,bayan shi babu wanda ya hadashi da tashi mamar.


Miqewa tayi kawai tace
"Zuwa nayi yi miki saida safe"
"Allah ya bamu alkhairi" ta amsa mata ciki ciki,jikinta ya bata akwai abinda ke faruwa,akwai abinda ta yiwa ummin,saidai kanta ya kasa kawo komai,tubda ita dai tasan awanni kadan duka duka da dawowarta gia,don haka sawunta a likkafa ta fita a sashen.


A falo ta sami hajja ita da mariya da halima yaran wajen umma matar abba abu suna kallo,dubanta hajja tayi
"Kin dawo kenan?"
"Eh wlh....yunwa bari na samo abinci" tayi gaba da sauri zuwa cikin kitchen
"Ahto tun dazu nace ki tsaya kici ai" hajja ta fada tana gyara kashingidarta,ita dai zahra tuni tayi kitchen,ta samu faranti ta zuba abincin,sannan ta dawo falon ta zauna sosai saman carfet.


Kafin tayi lomar farko ta soma da bude data dinta sannan ta aje wayar gefanta ta soma cin abincin tana kallon wayar tare da jiran saqonnin su gama shigowa,duk da wasu sun yayyanke,wasu kuma waiting suke nuna mata,don haka basu jima ba suka gama shigowa tsaf,sai tasa hannun hagunta ta dauki wayar,daya hannun kuma tana diban abinci dashi.


Duk yawan saƙonnin dake kan wayar bata bi ta kansu ba,sunan data sanyawa nuraddeen taje ta lalubo ta shiga inbox din tana qoqarin duba last seen dinshi ko kuma yana online.


Ga mamakinta saita ganshi online,dole tayi mamaki,don bata taba ganinsa online ba ba tare da ta tarda saqonshi ba koda kuwa na sallama ne.


Ba jinkiri ta rubuta slm ta tura mishi,yayi mata tick guda biyu alamun yaje,saita tsaya ta zubawa sallamar data tura din idanu kamar ba ita ta rubuta ba,tana jiran taga ta sauya launi zuwa blue,saidai kafin hakan ta faru ta lura daya sauka.


Goshinta ta dafe,sam sai takeji banbarakwai,wannan karon kamar nuradden din ya canza,tunda sam basu saba haka ba dashi,zama tayi sosai ta tura masa saqon cewa tayi fushi dashi,daga haka ta kashe data gaba daya ta maida hankalinta ga abincin,tana son ta gama ta wuce daki kawai ta kwanta gaba daya.


Da wayar da kwanon ta miqe gaba daya a hannunta,hajja ta dubeta
"Yau babu hirar dare kenan?" Fuskarta tadan yamutsa
"Wai so nake nadan huta,tun dazu nasoyin bacci ban samu dama ba" kai hajjan ta gyada
"Ya kamata.....yau banji duriyar nuraddeen ba?" Sai data dubi wayar hannunta sannan ta maida dubanta kan hajjan
"Nima yau na rasa me ya riqeshi haka,kwata kwata bamuyi waya ba"
"Ai yau da gobe sai Allah" bata ce komai ba ta juya ta wuce kitchen ta aje farantin sannan ta wuce dakinta,tasan me yiwuwa su salma nacan na jiranta zaman hirar dare yadda suka saba,idan kuwa basu jita ba zasu biyota ne sassan hajja ayi a nan yadda sukanyi mafi yawancin lokutta,ita kuwa yau sam bata jin wani karsashi.


Kaman jira yake ta gama gyara kwanciyarta saiga kiranshi ya shigo,murmushi ta sake cikin zumudi ta daga kiran
"Kimin afuwa ranki ya dade tuba nake" cikin shagwabar nan tata tace
"Aini tuni nayi fushi ma"
"Kimin rai,karkisa cikin daren nan na kamo hanya"
"Na yi maka" ta fada murmushi na qwace mata,yayin dashi kuma ya saki ajiyar zuciya yana cewa
"Kinsan duk duniya ke daya ce fushinta ke daga min hankali,gwara ran kowa ya baci,hankalin kowa ya tashi indai naki yana a kwance"


Farr tayi da idanunta cikin jin dadin yadda take da girma da matsayi cikin zuciyarsa,kullum kwanan duniya sake nuna mata matsayinta yake a wajensa,hakan yana mata dadi qwarai,tana jinta cewa itama takai mace,ba kamar yadda ko yaushe ya haidar ke nuna musu suna mata bane.


"Baby ina zuwa,minti biyu,mama tayi kirana zan kiraki"
"Kace ina gaisheta" ta fadi,bata ji amsarsa ba amma taji qit wayar ta katse,saita sauke wayar daga kunnenta tana murmushi,soyayyarsu da nuraddeen koda yaushe ta dabance a zuciyarta,gyara kwanciyarta tayi ta bude inbox nashi tana bitar saqonninshi da ita,fuskarta wadace da murmushi,ta jima a haka sannan taji hayaniyar 'yammatan gidan,tasan zuwan zasuyi su dasa hira,wala'alla ma idan nuraddeen ya kirata su hanata dagawa,don haka ta cusa wayar qasan filo ta runtse idonta ta gyara kwanciyarta kamar me bacci,tana jinsu suka shigo suka qaraci nacin tashinta suka haqura suka shiga hirarsu.


Tun tana jinsu sama sama har har bacci ya kwasheta.


Bata tashi farkawa ba sai da aka kirayi sallar asuba.


Misalin sha daya da rabi na safe ta gama dukkan abinda zatayi,tana gaban madubi tana qarasa kwalliyar fuskarta,bayan ta shirya kanta cikin wasu riga da skert na atamfa da suka yi mata cif a jikinta,abu na qarshe datayi gaban mudubin shine feshe jikinta da turare,ta kalli kanta ta tabbatar komai yayi,saita sakarwa kanta murmushi,saboda ita kanta tasan tayi kyau.


Hankalinta ta maida kan wayarta dake gefanta,tun daxun take trying number nuraddeen,tana son gaya mishi xata fita,don kada yace zayazo kuma bata nan,gwadawa ta sakeyi tana fatan ta sameshi,tun jiya da yace zaya kira bai biyo din ba,amma ta masa uzuri,mai yiwuwa basu gama magana da maman nashi da wuri bane.


Cikin sa'a wannan karon ta sameshi,sai daf da zata tsinke aka daga,muryarshi can qasa kamar mai bacci suka soma gaisawa
"Zan je gidan abban gwammaja ne nace bari na gaya maka kada kazo gida baka sameni ba"
"Ok,babu matsala,na tarad dake acan kawai"taji dadin hakan don tana da muradin ganinsa,amma saita boye murnar tata da cewa
"Ok fine,yayi" daga haka sukayi sallama ta aje wayar tana sakin murmushi tare da sake duban kanta sosai,nufar ma'ajiyar sarqoqinta tayita cire dan kunnen kunnenta ta saka sarqar da dan kunne harda abun hannu,wanda ada batayi niyyar sanyawa ba,data sake duban kanta sai taga kwalliyar ta sake qawatuwa fiye da daxun.


"Kince karna bata mana lokaci,kuma naga kamar kedin xaki bata mana" ta jiyo mitar salma daga can falon hajja
"Ina zuwa" ta fada da sauri tana daukar mayafinta dake saman katifa ta yafashi saman kafadunta,ta maqala hand bag dinta a hannu ta zura takalmi ta fito.


"Wannan mayafin fa salma?" Zahra ta fada tana duban salma
"Hmmmm...kin manta yaa zaki yana nan,baki nan ranar daya kora mana warning kan saka irin wadan nan mayafan,wai bama ganin zahransa,ita bata ishemu darasi ba" baki zahra ta tabe,zata ce

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login