Showing 15001 words to 18000 words out of 121250 words

Chapter 6 - ALKIBLA complete

Start ads

24 Aug 2025

450

Middle Ads

tsammani yayi fatali da sauran wanda suka bari cikin faranti,hafsat ce ta ajeshi daga gefanta,nufinsu idan sun cinye wancan saisu qara,take ya fantsama har saman takalmin nasa dai.


Dif falon yayi kowa tamkar anyi ruwan sama an dauke,sam basusan yana gidan ba da basu tarki yin dan malele ba,dukkansu sunsan halinsa,ya tsaneshi wai kayan qazanta ne,tsantsaminsa yake kuma ba tun yau ba haka yake.


Mari kawai ya kaiwa hafsat da farantin dake gefanta,wani huci yabi ta gefan fuskarta,duk da cewa ta samu ta kauce amma sai daya dan sameta
"Uban waye yayi wannan abun!" Ya tambaya cikin bacin rai yana nuna farantin da yayi nasa waje,kasa amsa masa sukayi saboda basu da amsar bashin
"Ok....baku da bakin magana ko?,i wil deal with u!" Ya fada yana gyara tsaiwarshi,kowacce saida cikinta ya duri ruwa,har inna wuro dake kitchen,gashi mama ta fita ta qofar baya bare taji abinda ke faruwa tayi masa magana.


Sallamar xahra ce ta ratsa falon cikin sanyin nan nata,sanye da hijabinta har qasa mai hannu da madauri,hannunta riqe da jaka,fuskarta wadace da murmushi da kuma alamun jin kunya take duban haidar dake tsaye,sam bata ankara da abinda ke wakana ba saidata taka dan malelen daya fantsama saman door mat,ta kuma tsinci muryar haidar din yana basu umarnin dukkansu su wuce zuwa farfajiyar gidan.


Ko ba'a gaya mata ba ta fuskanci akwai matsala,tasan kuma halin kayanta,don haka ta qaraso gabanshi tana qunshe dariyarta bayan ta gama satar kallonsu suna roqonta da idanunsu da suka raina fata kan ta nema musu afuwa.


Qasa qasa tayi masa magana ba tare da sunji me tace ba,idanu yadan xuba mata shima na 'yan sakanni,kallon dake narkar mata da zuciya ya kuma sake sanya mata tsananin qaunarsa a zuciyarta,wani sanyi ya mamaye ilahirin jikinta,saita dan lumshe ido kadan tana kauda kanta cikin murmushi,takawa yayi a hankali ya nufi qofa ya fice daga falon.


Wani irin ihu suka saki gaba dayansu,ta musu nuni da yatsa zuwa qofa da sauri,sai kowacce ta saka tafin hannunta tana toshe bakinta gami da raba idanu,suna tsoron kada ya jisu kashinsu ya sake bushewa karo na biyu,ihun ne ya jawo hankalin innawuro ta dauko farantin da sauri ta fito
"Wallahi anyi babu ke sister!" Salma ta fada da sauri tana dariya sanda innawuro ta fito,idanunta dukka a waje tace
"Aina godewa Allah da akayi babu ni din,ina kitchen ina muku jaje da addu'ar Allah ya rangwanta muku izayar da zaku sha yau"
"Dalla banza,ba wannan ba,ke kinga wani scene da akayi yanzu tsakanin ya zaki da yaa zahra?,gaskene da ake cewa soyayya ke sawa me qarfi ya sunkuya saman gwiwoyinsa" bata tsaya ba sai data kwashe mata yadda akayi,zahra nakai mata duka tana
"Banason sharri fa,banson haka"
"Allah ya zahra ki bamu sirrin,dama akwai sanda ya zaki zai russuna haka?"murmushi kawai ta koma binsu dashi da taga abun nasu bana qare bane.


Saida suka gama zolayarsu son ransu sannan ta gaya musu abinda ya shigo da ita
"Gida zan wuce,mama naketa nema in yiwa sallama,ta dauka na daga tafiyar,to kuma dazun abba ya dawo,yace yana son ganina,duk da umma ma tace sunyi waya ta gaya mata"
"Kai yaa zahra har tafiya?"cewar inna wuro data aje farantin tsakiyarsu
"Haba ina laifi,ku kun tabamin kara nema kunxo kamar haka?" Murmushi inna wuro tayi
"Nidai ayimin uzuri ba maxauniya bace"
"Eh amma ai kuna samun hutu ko?"
"Zanzo ki kwantar da hankalinki" ta tari numfashin zahran tana dariya
"Allah yasa da gaske ne" ta fadi itama tana miqewa
"Bari na shiga na fito" zahran ta fada tana yin gaba,yayin da su kuma sukaci gaba da shan dan malelensu suna tattauna abinda ya farun yanzun,da sa'ar da sukaci yau basu sha purnishment wajensa ba,Allah ya cecesu.


Dab da magariba suka gama kitson,kowacce ta soma miqewa,wasu nayin sassansu,wasu kuma na haramar daura alwalar sallar magariba,ita da take fashin salla saita wuce dakinsu hafsat,tayi kwanciyarta saman carfet bayan ta dauko wayarta da tayi full charge ta kunna data,suna da matsalar network na mtn wani lokaci,amma a lokaci irin wannan akan dan samu qarfin network,bayan ta kunna saita aje wayar gefanta ta miqa hannu tana sake dauko filo ta qara saman kanta yadda zataji dadin kwanciya sosai.


Kamar kowanne lokaci inbox na nuraddeen ta fara dubawa,last seen dinshi 5minutes ago,amma ga mamakinta bata tarda saqonsa koda na sallama ba,abun ya fara daure mata kai game da lamarin halin ko.in kula dinsa,gashi ba wani isashen lokaci ne da ita ba bare ta bibiyi komai taji inda matsalar take,nan da jibi zuwa gata zata koma inda ta fito.


Gaba daya sai taji bata sha'awar hira da kowa,madadin ta kashe data din ta sauka saita shiga wajen status ta fara bin status din mutane tana kalla,wani ya bata dariya ta murmusa,wani ya bata haushi,wani kuma tayi tsokaci akai ta turawa wanda ya dora status din.


Katsam!sunan nuraddeen ya bayyana bayan ta gama kallon status din wata qawarta ga islamiyyarsu da take zuwa duk sanda akayi hutun makaranta zuwa sanda zasu koma.


Wani irin zabura tayi ta miqe ta zauna daram tana raba idanu,zuciyarta na wani irin bugu,tabi wayar tata data subuce daga hannunta saboda miqewar da tayi da hanxari da kallo.


Kamar me tsoron wayar haka ta miqa hannu ta sake dauko wayar a karo na biyu,bugun zuciyarta na sake tsananta,addu'a take cikin ranta Allah yasa idanunta gixo suke mata,Allah yasa saqe saqe ne na zuciyarta.


Saidai dukka fatanta bai zama gaskiya ba,don sauran hotunan har sun bude kansu da kansu.


Cikin rawar jiki ta fara komawa da baya ta fara daga hoton farko,nuraddeen ne shida wata budurwa,wanda kallo daya kafin kakai ga karanta rubutun dake qasan hoton xai gaya maka tabbas ango da amarya ne cikin yanayin hotunan nan da ake kira da free wedding pictures,rubutune a qasa kamar haka

*SAVE THE DATE 22/07 IN SHA ALLAH*


Wani kakkarwa hannayenta suke kamar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi tana ci gaba da buda hotunan ba tare data iya tsaiwa ta duba rubutun dake qasan kowanne hoto ba,abunda ta iya dubawa shine lokacin da aka dora,6minutes ago,kenan shi ya dora da hannunsa da kansa,tunda sanda ya sauka da sanda ya dora tazarar minti daya ce.


Hafsa ce ta shigo tana dariya abunta riqe da hijabi tana qoqarin sawa,da alama daga waje ta baro abunda ya bata dariyar,sam bata lura da yanayin da innawuro ke ciki ba sai dataji tana kiran sunanta da wata iriyar shaqaqqiyar murya tana yafitota da hannu.


Qarasowa tayi tana dubanta,ba wanda ya iya magana cikinsu sai wayar da zahra ta miqa mata cikin rawar murya tana cewa
"Dubamin don Allah.....dai dai idanuna suke ganemin?" Hannu tasa ta karbi wayar,hoto daya tak ta kalla saita koma saman qafafunta ta zauna itama tana ci gaba da kallon hotonan cikin matuqar mamaki da sanyin jiki,kalamanta a sanyaye qwarai tace
"Nura ne zahra,nuraddeen dinki fa" rasa abu na gaba daya kamata tayi tayi,sai kawai tasa dukka tafin hannunta biyu ta rufe fuskarta dasu kamar wadda bata da muradin ganin duk wani haske dake cikin duniya,tana jin kamar ana yamutsa qwaqwalwarta,daidai sanda salma ta shigo,da sauri hafsat tace
"Yauwa,zo kigani don Allah,zoki tayani gani" da hanzari salman ta qaraso tana amsar wayar daga hannun hafsat.


Wani ashar salman ta dura,da yake itadin batakai haqurin hafsat ba,ta lalubi waje ta zauna tana cewa
"Meke shurin faruwa kenan zahra?laaa,kinga ana goge hotunan daga status.....sunyi disappearing gaba daya"ta fada tana kallon hafsat tare da nuna mata wayar
"Tabbas gogesu akayi,don ba'afi minti goma da dorasu ba,bajci ace har lokacin saukarsu yayi ba,me nuraddeen ke nufi?" Tambayar da bata da amsarta data cilla mata ita ta sanyata sakin wani irin kuka me ciwo,kukan daya daga hankalinsu gaba daya,lokacinne yasira itama ta sako kai,cikin yanayi na tsoro ta isa wajensu tana tambayarsu abinda ke faruwa,basu kai ga bata amsa ba kira ya shigo wayar zahran,duk da bata duba tasan me kiran,salma cikin fushi tace
"Bari na daga naji dan gidan marasa mutuncin me zaice?"kai hafsa da yasira wadda batasan ma ainihin meke faruwa ba suka daga mata,ta daga wayar ta sakata a handfree tayi shuru ba tare data ce komai ba,muryar nuradden ta bayyana
"Dear.....don Allah karki hukunci da abinda bakisan ainihin menene ba,ki bani dama inyi miki bayani pls"
"Ai karka damu,saqone ka bayar ya kuma iske inda kakeso ya iske,yo meye kuma wani abun damuwa a ciki?,kaci gaba da shagalinka kawai,amma ka sani,indai da haqqin zahra a wuyanka Allah saiya mata sakayya"
"Ki tsaya kiji don Allah,wacece?,hafsat ce ko yusra?"
"Ban sani ba dan gaba da rainin hankali,karka sake kiran wannan number" qit daga haka ta katse wayar,wanda kafin ta kuma cewa komai wani kiran ya sake biyo baya,haka suka sanya wayar gaba kowa ya rasa abun tabukawa,yanata faman kira ba qaqqautawa kamar yadda zahra ke kuka itama babu qaqqautawa,yasira ce ta karbi wayar daga qarshe bayan sun zayyana mata abinda ke faruwa ta kasheta gaba daya,har cikin zuciyarta tana jin wani irin suya da bacin rai,wannan wacce iriyar yaudara ce haka kai tsaye ta rashin mutunci da cin fuska,yana sane ma yayi posting hotunan a status dinsa?,abinda yafi tsaya musu a rai kenan.


Su hudun gaba daya suka hadu suna bata baki,harda nadiya data shigo daga qarshe gami da maimaita zancan cike da mamaki,don dukkansu bama su ba kusan kowa yasan da zaman nuraddeen a matsayin wanda zahra inna wuro ta tsaids zata aura,abun yazo musu matuqa a ba zata.


Ita kadai tasan yanayin data tsinci kanta da zuciyarta a ciki,wani yanayi da tun tasowarta bata taba jin irinsa ba saiyau,jin lamarin take kamar a mafarki,wai ita?,nuradden?,wanne irin abu haka tayi masa dafa cancanci irin wannan yaudarar mai ciwo?,har yana da bakin cewa ta saurareshi?,ta jima cikin wannan rudun,daga qarshe taji babu abinda take da buqata illa kadaicewa tayi kukanta ita kadai ko hakan zai sa ta samu gurbin da zata zuqi numfashi yakai har zuciya da hunhunta,tana jin kamar numfashinta zai katse ne.


Yanayin yadda suka shigarwa hajja zahran na kuka lullube da fuskarta ya sanyata miqewa da sauri cikin firgita tana tambayar
"Kai...meye haka?,lafiya?" Itakam zahra bata iya tsaiwa ba saita wuce kawai zuwa daki,waje ta laluba ta kwanta gami da sake rushewa da sabon kuka.


Bayan minti biyu tajiyo muryar hajja na rafka salati da salallami,da alama sun gama gaya mata komai,sai kawai taja filo ta rufe kanta tana sake fashewa da wani irin kuka,tanajin sanyi na ratsa gabbanta,kafin kace meye wannan zazzabi ya rafketa.


Ba'a rufa awa guda ba hajjan ta shigo dakin
"Takwara.....kukan kike har yanzu?" Ta fadi tana qarasawa inda take kwancen,ta saka hannu ta yaye abun rufar tana kamo hannunta
"La'ilaha ilallahu,ke tashi,kwanciya kikayi xaki kashe kanki,kinji yadda jikinki ya rine da zazzabi?" Cikin daren dukka hankalin hajjan ya tashi,wanda hakan yasa hankalin yaranta su abba babba suma ya tashin,ta matsa lallai lallai saida su shamsu suka dau mota suka kaita asibiti,wanda basu dawo ba sai wajen sha biyu da rabi na dare saboda yadda zazzabin ya mata mugun kamu ya sanya suka dan riqeta sai daya sauka jikinta yadan daidaita.


Washegari duka tana kwance a daki,ko falo baga fito ba bare taga hasken rana,tana kwance tana bitar duka rayuwarsu ita da nuraddeen,bataga ta inda ta gaza ba da xai gujeta,bata ga me ta masa da zai saka mata d a wannan ba.


Duk yadda hajja taso ta fito da ita ta xauna koda a falo ne amma taqi,hankalinta kaf nakan zahran,duk bayan wasu mintuna saita leqo dubata,dukka jama'ar gidan kowa ya shigo ya dubata babba da yaro,amma banda mutum biyu,ummanta dai tasan kara ce da kawaici ya hanata leqoww,don koda hajja ma ta aika mata cewa tayi ace tana gaidata kawai,data sake aikawa sai tace ai tasan tana wajenta babu komai,shi kuwa dayan dama bashi a lissafinta,tama manta dashi cikin jerin jama'ar gidan.


Hajja da kanta ta yiwa abban gwammaja waya sanda yace zaya aiko a maidasu makaranta ita da hasina ta shaida masa bata da lafiya,a barta koda zuwa satin sama ne idan ta sake murmurewa,ya mata sannu da jiki,ya kuma ce zaisa a shaida hukumar makarantar idan ankai hasinan.


Sai da akayi kwanaki biyar da komawa makarantar sannan ta soma jin qwarin jikinta,don ta tattara dukkan wasu lamura na nuraddeen tayi qoqarin yin watsi dasu,a yadda ta lissafa kwanaki uku kenan da daurin aurensa,yana can wala'alla shida amaryarsa cikin farinciki,yama manta da lamarinta,hakan ya sanya washegari da azahar tayi wanka da ruwa mai dumi sosai,tasha dukka magungunanta,ta shirya cikin atamfa riga da zani sannan ta fito falon.


"Yauwa,ko kefa?" Hajja data taras zaune cikin falon ta fada cikin farinciki,tana kallon yadda zahran tadan fada,hancinta da fuskarta suka qara qara tsaho.


Mirmushi tadan yiwa hajja,cikin qarfin hali ta tsokaneta
"Ashe kina tsoro kada na mutu na barki"
"Zaki fara ko?" Hajjan ta fada tana watsa mata daquwa,dai dai sanda inna gaje ta fito daga kitchen zuwa falon
"Aah,ma sha Allah uwar masu gida jiki yayi kyau"
"Eh wallahi inna gaje" ta fada tana dan murmushi
"Alhamdulillahi,mun godewa Allah,Allah ya qara lafiya"
"Amin inna,akwai abinci ne?" Zahran ta tambaya
"Eh yanzu aka gama na rana...bari a zuba miki" inna gaje ta fada tans komawa kitchen din,sai zahran ta bita a baya ta amso abincin ta dawo inda ta tashi ta zauna
"Wannan abincin kamar na wasan yara wuro?" Hajja ta fada tana duban plate din
"Ya isheni hajja" saita qyaleta,tayi bismillah ta fara ci,lokaci lokaci idanunta nakan tv dake aiki.


Sallamar abubakar ce ta karade falon,abubakar shine yaro na farko a sassansu,daga shi sai ita,sai sauran qannenta maza guda biyu,sulaiman da yusuf,sai mace daya ilham,akwai tazarar shekara kusan biyar tsakaninta da abubakar,hakan ya wanzar da girmamawa sosai tsakaninsu,don haka umminsu ta tarbiyyancesu da bawa na gaba dasu girma.


"Maraba da saddiqu.....saukar yaushe?" Hajja ta fada tana dariya
"Ko minti biyu banyi da shigowa gidan ba" ya fada rabin hankalinsa nakan zahra data aje cokalin hannunta tana qoqarin gaidashi
"Lafiya lau...." Ya amsa a taqaice ya dora da
"Me kike a gida,duk 'yan makaranta sun koma makaranta?" Kafin hajja takai ga bada amsa an sake sallama cikin falon,muryarsa ta cika wani irin sauti mai sanyi,saidai tana cike da wani kwarjini mai ratsa kunne.


"Sannu da zuwa yaya" abubakar saddiq ya fada cikin salo na girmamawa,fuskarsa washe da fara'a
"Malam.....kana lafiya?" Ya fada yana miqawa saddiq hannunsa dake daure da wani rantsatsen agogo ruwan zaiba,wanda ya dace da lafiyayyar fatarsa da hutu da kuma kwanciyar hankali ya ratsata.


Da sauri sadiq ya miqa masa nasa hannun sukayi musabaha,saiya soma qoqarin zama hannun kujera yana gaida hajja cikin girmamawa,don shi sam baya wasan jika da kaka da ita,ta amsa cikin kulawa,don shi dinma dan gaban goshinta ne,sakamakon sunan maigidanta da yaci,sannan ta dora da fadin
"Kamar tare kuke da sadiq?" Yana dan latsa wayar hannunsa yace
"Tun dazun na shigo,na shiga ciki ne nadan huta"
"Auto ma sha Allah,ya aikin,da fatan an samu abinda ake bida?"
"Alhmdlh" ya fada hade da ajiyar zuciya yana maida wayarsa aljihun lafiyayyen trouser din jikinsa,wanda kallo daya zaka masa kasan me tsada ne,hakanan mai kayan yasan takan kaya masu aji.


Ido suka hada da xahra,kamar zaiyi magana sai kuma ya janye idanunsa duka cikin sakan biyu,ya harde hannayensa a qirji yana duban hajja dakewa sadiq bayanin dalilin xamanta a gidan,cikin sauri tace
"Ina yini" can qasa ya amsa kamar yadda ya saba
"Wallahi yaron ya bani mamaki,a haka kamar na Allah ashe bana arziqi bane,yaudara ce kawai ta kawoshi,yau ne mafa kawai na samu kanta ta fito falo ta zauna" ta qarashe zancan cikin nuna jimamai qwarai kan fuskarta idanunta kuma saman fuskar haidar,wanda ya dauke kansa zuwa yanzu daga kansu kamar ma baisan me ake ba.


Ajiyar zuciya sadiq yayi
"To Allah ya kyauta ya rufa asiri,abinda ya faru ya riga daya faru,sai kiyi qoqarin komawa makaranta.....hajja bari naje mu gaisa da sauran mutanen gidan,ummi ce kawai tasan da shigowata,zuwa anjima zan dawo abani abinda aka ragemin"
"Ka taho dai da abinda ka kawomin" dariya ya saki kana ya juya ya fice daga falon.


"A kawo maka abinci ne?" Hajja ta tambayeshi,kai ya kada alamun a'ah,sannan a nutse ya furta
"Idan akwai fura kawai ta isa" sai ta waiwaya wajen zahra,wadda tana son barin falon,amma kuma tana son kallon programe din da ake yi a wani gidan tv,bata so ya wuceta don yayi mata
"Duba fridge wuro akwai damammiya....kayi sa'a kuwa nonon me kyau ne,wanda aka kawomin ne daga can gida adamawa" yunqurawa tayi ta miqe,ta isa fridge din ta ciro furar,saita miqawa hajjan tasa hannu biyu ta amsa silver da nonon ke ciki,wanda har tsatstsafa yake saboda tsabar sanyi ta miqa masa tana cewa
"Kanaji muna magana kan case din inna wuro baka ce komai ba?" Sai daya amsa furar ya bude yasa ludayin dake kai sannan ya daga shanyayyun idanunsa ya kalli hajjan
"Me zance......i dn't know what to say" duk da bata fahimta qarshen zancensa ba amma saita gyara zamanta
"Na zaci a matsayinka na babba zaka nema yaron kaji komai daga bakinsa....tunda a a zahirin gaskiya suna son junansu" kamar bazai amsa ba,don itakam zahra har tayi

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login