Showing 78001 words to 81000 words out of 121250 words

Chapter 27 - ALKIBLA complete

Start ads

24 Aug 2025

476

Middle Ads

da wani zancan dinner ta anjima,baya ga haka ma ina ita ina saka kanta inda Allah bai kaita ba,shi kansa uban gayyar bata ga fuska ko alama ba bare ma aje ga batun zuwa makeup,waya aiketa bare yaga ta dade?,Allah ya taimaketa take qaryan da zatayi ta qwaci kanta ba tare da dr nasreen din ta fuskanci komai ba yazo mata,saita karyar da murya
"Ayyah....zanso hakan,amma kinsan halinshi fa,banjin anjiman nan zai yarda naje"
"A'ah....ya zai min haka,amma da bai kyauta min ba oga haidar,kuma ai ya sani mr and mrs ne.....let me call jafar ya masa magana ya barki..." Tana qoqarin tsaidata tuni har ta katse wayar,saita bita da sauri saidai an shaida mata busy,hakan ya tabbatar mata harta kira din.


Wayar ta aje ta dora hannu saman ka
"Innalillahi" ta fada jimantawa kanta,saita damu gaba daya,ta kuma zauna zaman jiran jin abinda zai biyo baya.


Minti biyar minti goma ashirin talatin awa daya biyu uku shuru dr nasreen bata kira tace komai ba,hakan sai yasa hankalinta ya kwanta taci gaba da sabgarta cikin dakin.


Cikin awa ta hudu taji ana knocking a qofar falon,saita share saboda tana tsammanin yana cikin gidan,jin knocking din na sake daduwa saita aje wayarta ta miqe.


Shuru falon babu kowa,saman table dinma babu komai duka an kwashe,dauke idonta tayi ta isa qofar ta bude,macace a tsaye sanye da uniform na sojoji,fara ce 'yar tsamurmura mai qaramin jiki,gefanta wata ce sanye da kayan gida,saidai ita waccan din tana da garin jiki,cikin fara'a suka soma gaidata,ta amsa musu fuska a sake sannan suka fara mata bayani
"Oga ne ya aikomu,za'a shigar da kaya,sannan kuma idan kin shirya zamu kaiki" matsawa tayi suka fara shiga da kayan abincine dasu lemuka da drinks,saidai kuma bata gane idan ta shirya ba,don haka ta jawo wayarta saiga kiran dr nasreen
"Dear yace zakizo....amma fa ki hanzarta,wata takewa,daga ita saimu"
"Ok to" ta fada badon ranta yaso ba,dondai kawai bataso tayi wani abu dazai fallasa abinda ke tsakaninsu ne da haidar din,sannan bugu da qari idan ta fitan ko banza taga gari,ta huta da wannan zaman kurkukun data wuni yi.


Daya daga cikinsu ce ta bude mata bayan lafiyayyar motar ta shiga,sannan suma suka shiga suka tada motar suka fice,mai gadi yaja qofar ya rufe.


Babban gurine wanda kana kallonsa kasan ya tattara mata masu aji da wayewa,tana shiga masu karbar custumers suka tareta,ta tambaya inda dr din take suka mata jagora.


"Oyoyo....kinyi sauri amma" dr nasreen din ta fada cikin fara'ar nan tata,sai zahran itama tayi murmushi tana zama inda ta matsa matan suka shiga hira kafin azo kansu.


Dr nasreen din tace a fara yiwa,tana ta addu'ar Allah yasa lokaci ya qure kafin azo a kanta,don har ga Allah bata so,saidai addu'ar tata bata ci ba,nan da nan aka gama yiwa dr din akazo kanta
"Lite makeup pls sis" ta fadawa me yi mata kwalliya
"Ok" tace tana gyada kai.


Cikin qalilan din mintuna saiga zahran kamar an sauyata da wata ne,bakin dr nasreen yaqi rufuwa,cewa take
"Kefa kada ki bada 'yan maza yau,wallahi kada kisa oga haidar yayi abun kunya gaba mutane,kinganki kuwa?" Murmushi kawai tayi bayan ta kalli fuskar tata a mudubi itama,tana sake dubawa nasreen din ta aje mata wata leda gabanta
"Ga kayanmu da xamu saka.....tunda ba'a gayyacemu biki ba da dear yacemin sun hadu dasu hajja tace masa kinzo na tanadar mana don mu saka iri daya...."
"Kai kai,duka dai dr?"
"Haba babu komai,mu saka sai suyi mana dauri,don naga tex din dear yace suna hanya" tayi maganar tana ware zaninta.


Wani irin lace ne mai azabar kyau da daukar idanu butter colour,dinkin da aka masa yayi masifar dacewa dashi,hakanan zahran kamar don ita aka dinka shi,kamar yadda ya zaunawa dr nasreen din sosai itama,sai duka kallo ya koma kansu sanda aka gamawa nasreen dauri aka fara yiwa zahra nata.
23/10/2021, 08:46 - πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»: 29
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_

_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_

_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-β€˜dai_
_______________________________



Dai dai sanda aka gama kira ya shigo wayar dr nasreen,ta dauka da hanzari
"An gama dear....gamu nan" saita sauke wayar tana duban zahra
"Ke....oganki ya matsu....yanata mita,muje" duk yadda zahra taso dr nasreen ta barta ta biya kudin kwalliyar qememe taqiya,haka ta biya sannan suka dauka kayansu suka fito.


Yaja saki gami da kallon agogon hannunsa yafi a qirga,idan banda kada jafar yaga kamar ya watsa masa qasa a idanu baiga abinda xai dakatar dashi xaman jira ba,shi totally ma bai shirya zuwa wajen dinner din ba gaba daya,hakanan yakejin baison yadda matansu ke karakaina a tsakiyarsu,sai yakega sam hakan bai dace ba.


Karo na qarshe daya kalla agogonsa,ya yanke ma ransa indai basu fito ba zaiyi tafiyarsa ne,saidai shi jafar din da ya daurewa qaryar zuwan qarqashi ya daukosu,ya daga kai da niyyar duban bakin qofar,saiya hangi fitowarsu sun jero a tare,dauke idanusa yayi daga kan dr nasreen ya maida kanta,murmushi ne kwance saman fuskarta,har fararen haqoranta na bayyana,da alama wata magana dr nasreen din ta fada data bata dariya.


Janye idanunsa yayi ya maida daya side din,har cikin zuciyarsa yaji inda ya maida din baiyi masa ba,ya sake canza waje,nan ma yaji baiyi masa ba,saiya dauke idonsa ya kuma maidawa inda suke tahowar.


Zuwa yanzu sun iso dab da motocin,kana iya ganin fuskokinsu tarwai ta hasken fararen qawayen da suka haske wajen,haka kawai ya samu kansa da xubawa fuskarta idanu,wane sashe na ranshi yaji yana baci ba tare da yasan dalili ba,saiya dauke idanunsa daga wajen,yama rufesu gaba daya sanda take qoqarin bude gidan baya ta shigo.


A tunaninta yana gaba,sai data shiga ta zauna ta maida murfin ta rufe sannan ta lura dashi,duba daya tayi masa ta kauda kai,kamar mai bacci,saidai kuma yanajin komai,fuskarsa kamar ko yaushe a hade dai,tabe baki tayi cikin ra ta tana mita,tana kallo motarsu dr nasreen ta wuce gaban tasu kadan,sai suma suka tsaya,dai dai sannan wayarsa dake aje tsakiyarsu ta dauki kuwwa.


Bai buda idanun nasa badai still ya laluba hannunsa ya dauka ya kara a kunne,murya can qasa taji yace
"Kuje kawai" sai kuma yayi shuru yana saurare na sakannin da basu wuce biyar ba sannan ya kuma magana
"Banjin zamu iya zuwa" still dai wayar tashi tana kunnensa na wasu sakanni,da alama akwai abinda ake gaya masa,saiya sauke wayar,ya bude idanunshin kana ya shiga ya rubuta gajeran sms ya tura sannan ya maida wayar inda take,shi kuma ya gyara zamanshi,kamar wanda dama can ya shiryawa zaman cikin motar ne.


A qalla sun kusa minti goma a tsaye anata kira yaqi dagawa,yayin da zaman ya ginshi zahra,ji take kamar ta fita a motar ta bashi waje,don batasan ma'anar zaman ba,shi bai bada umarni a tafi ba,shi bai maidasu gida ba,a haka ta hangi fitowar jafar ya doso motarsu.


Knocking din glass din side din haidar yayi,saiya sauke glass din yana dubansa,hannayensa ya hade waje daya yana murmushi
"Am sorry boss,we apologize you.....madam ma tace a baka haquri a madadinta" bakinsa ya bude zaiyi magana jafar din yayi saurin tararsa
"I know....i know...ka share kawai,yau ne fa,just some few hours an gama an wuce wajen" bai sake cewa komai din ba,saiya dage glass din kawai,jafar din ya koma motarshi,shi kuma ya bawa drivern umarnin jansu,zahra na gefe tana gulma ita da zuciyarta
"Me shegen baqar zuciya...kome akayi masa oho,ni dama ya fasa zuwan ai gaba ta kaini,mtsewewww" tsakinta na qarshe ya fito fili ba tare data sani ba,saiya waiwaya ya dubeta,suna hada ido kowa yayi saurin janye qwayar idanunsa,ta tsammaci zaice wani abu ko zai tanka,saidai babu abinda yace,haka suka ci gaba da zaman kurame har suka isa wajen taron.


Kowacce na fitowa daga mota ta nufi 'yar uwarta,tun kafin ta qaraso taga nasreen na danne dariyarta,saida tazo gab da ita qasa qasa tace
"Allah ya somu,da tuni muna gida yanzun,ashe kishin 'yan maza ne ya motsa,to da heavy makeup akayi miki kenan zuciya zai hadiya?,wannan kwalliyar da ba wani abu aka qara miki ba sosai,abar da aka yita sama sama,lallai sai yanzu na sake gane aliyyu,yana da abun ban mamaki" jin zancan zahra tayi wani banbarakwai,dama abinda ya tsaidasu kenan?,lallai nasreen batasan waye ya haidar din ba,ba wani kishi,kishi a ina?,zallar iya mugunta ce kawai irin tashi data motsa,amma a sarari sai kawai tabi dr da murmushi.


To tunda suka je mazan nasu basu wani zauna ba,sunata fama da jama'a,saidai duk da hakan zahra na ankare dashi,har yanzu ba wata dariya saman fuskarshi,sai wani murmushi mai kama da anyi masa dole,ta tabe baki yafi sau nawa duk sanda taga yana murmushin gefan baki
"Kai...Allah kayi mana magani" haka take fada cikin zuciyarta.


Cikin hakanne ta lura da wata qabila cikin kakin soja,da alama ita sojan ce,tana ta bibiyar aliyyun a gindi a gindi,duk inda ya sanya qafarsa,saidai babu alama ko daya data nuna yasan Allah yayi ruwanta a wajen,haka kawai ta dinga jin qunci da rashin dadin xaman wajen,har zuwa sanda dr tace
"Tabdi....wato dai tawa ba zata haqura ba.....zahra....see dis woman" ta fada tana nunata da yatsa,sanda aliyyun ke tsaye yana amsar wani award da qananun sojoji suka bashi da certificate of honour.


Murmushi zahran tayi,cikin salo na basaja
"Manta da ita dr.....ina da labarinta,ni dashi gaba daya mun rufe babinta"
"Good....." Ta fada tana jinjina ma zahran πŸ‘πŸΌ.


Cikin lokaci kadan bayan an gama ciye ciye wajen ya soma hargitsewa,kowa na hoto da familynshi,walau matarsa kawai ko kuma da yaransu,wanda yara daya zuwa biyu dama aka bayar da damar zuwa dasu.


Dai dai sannan jafar yazo ya janye nasreen dinsa,saiya zamana inda take din ita kadai ce zaune,hakan ya bata damar nutsuwa tana bin kowanne abu dake faruwa a wajen da kallo a nutse,gefe daya tana jin yadda qirjinta keson ya dawo da ciwon da yake mata data samu dazun ya lafa,wala'alla kodon tun tea din safe bata sake kai komai bakinta bane.


"Excuse me pls,zan dauki wannan kujeran.....hope babu matsala?" Taji ana fada daga gabanta,saita daga kai ta dubeshi,matashin saurayi danye shakaf,wanda da alama ko talatin bai cika ba,kai ta gyada masa tana dauke kanta ta maida filin wajen,karo na uku kenan da yake attempting din yi mata magana tana basarwa.


"Bakaga mutuniyar bane?taawaa" Saif dake tsaye kusa da haidar ya rada masa a kunne dariya na taso masa,baice masa ci kanka ba,saidai yana sane da yadda take binsa din,ya tsani matar sosai,saidai ta rufe ido ta kasa fahimtar hakan,yakanji wani lokaci kamar yayi mata dukan tsiya,saidai ba dabi'arsa bace,hasalima yana kallon duk wani namiji da zai daki diya mace a tsayin wawa mara tunani kuma lusarin namiji,wanda ya kamata a kama ayita duka sai an jigatashi,yadan waiga suna magana da wani suka hada ido da ita,ya daure fuskarsa,bayason naci ko kadan a rayuwarsa,dama daya ce ta rage masa da xaiyi amfani da ita ya koreta kwata kwata daga dukkan sha'aninsa,yanzu kuwa zaiyi amfani da damar,saiya soma takawa yana lalubar inda take zaune da idanunsa,yayin da taawaa taci gaba da binsa a baya,tana tsammanin zai fita ne daga jama'a ta bisa ta fake da yi masa Allah ya sanya alkhairi wanda ta tura masa saqonni ta email dinsa sms da WhatsApp dinsa sunfi guda nawa amma bai amsa ko guda daya ba


Can ya hangota sanda saurayin ya sake dawowa yana tambayarta zai kuma daukar kujera daya kamar daga gidansu tazo da ita ta raya cikin ranta,saidai banza tayi masa bata ko kalleshi ba bare ta kulashi,ganin hakan yasa ya dauka yayi gaba,Aliyyu ya bishi da idanu yana bibiyar inda zai zauna,saidai tuni ya bace cikin mutanen dake kai kawo a wajen,wani abu ya hadiye har ya isa inda take zaune.


Hannu kawai taga an miqo mata,ta daga kai don ganin waye,sai tayi arba dashi da kuma tawakkalt dake tsaye daga bayansa,duk da fuskarsa a dinke take tsaf,saidai wadda ke bayan nasa bata iya hangen hakan,cikin second ta karanci komai,saita daga nata hannun ta sanya cikin tafin hannunsa da yake miqo matan,saiya maida hannun nasa ya rufe,ya runtse hannun nata tsakiyar nasa,wanda hakan ya sanya tsigar jikin kowannensu zubawa,dumin da tafin hannunta ke dashi ya ratsa duk wata jijiya ta jikinsa cikin sakanni,saiya dagota yana cewa
"Am sorry.....na barki ke daya ko?" Yanayin yadda ya dagotan gaba daya kamar wadda ya fusgo cikin salo yasa babu yadda zata iya tsaiwa da qafarta dole saidai ta fado gaba,shine kuma tsaye a gabanta,don haka jikinsa ta fada gaba daya,saiya sanya hannayensa ya riqe qugunta,a hankali cikin salo na rada yace mata
"Just a plan....karki zurfafa da yawa".


Rasa abun cewa tayi saboda gaba daya a rude take,jikin ya Aliyyu?,ya haidar yau itace rungume cikinsa?,kuma unexpected?,sannan uwa uba yadda taga nan da nan idanun wasu sunyo kansu,da alamu dama tun dazun suna bibiyarsu ne
"Nasan da zaman kowanne....and i want expel them daga rayuwata".


Cikin wani irin expression saman fuskarta ta daga kai ta kalleshi,qwayar idanunsu suka hadu waje guda,saiya dage mata gira daya,duk da har yanzu fuskarsa a dinke take
"Yes" canza mata wajen tsaiwa yayi daga gaba zuwa gefan kafadarsa,ya zagaya hannunsa a bayanta,ya riqe side din kafadarta daya da hannunsa daya,ya soma takawa a hankali tare da ita,dole gangar jikinta ta bishi suka soma ratsa wajen,yayi da taawa ta bisu da idanu,sai taji ba zata iya bari ba,don haka ta rufa musu baya dai still tana biye dasu,duk da tayi nesa nesa dasu ba kamar dazun ba.


Gaisaw yaci gaba dayi da mutanensa,kusan duk wanda ya gansu tare saiya tsaya,duk wani taku da zasuyi jikinsu na gogar na juna,hakan ya dinga weakening dinsu gaba daya ba tare da kowa ya sani ba,wanda kafin wani lokaci zahra ta rasa duk wani qwari daga jikinta,kusan riqon da yayi mata shike riqe da gangar jikinta,wannan shine karon farko data fara raba jikinta da wani da namiji,kamar yadda shima yake karin farko a rayuwarsa.


Hakan da yayi ba qaramin kada da yawa daga mutanen da yakeson kadawar yayi ba,a hankali yaga fuskokin suna canzawa,wasu kuma suna zamewa daga wajen,ciki harda taawa din data rasa inda zata tsoma ranta,ganin har a lokacin tana cikin jikinsa,hakanan duk inda zai zagaya tana tare dashi.


Da gaske yake bazai saketa a yanzun ba,riqonshi a gareta wani abune na daban da bata saba dashi ba,so take ya saketa ko zata rage wani abun,duk inda ya dora hannunsa a jikinta tana jin saqon saukar hannun har cikin qasusuwanta,kamar wanda keda wani abu na musamman cikin tafin hannunsa
"Cikina" yaji ta furta kalmar a hankali,saiya waiwaya ya dubeta kadan,suna hada idanu saita lumshesu,sam ya zuwa yanzu batason kallon qwayar idanunsa
"Ok" ya fada bayan ya dauke idanunsa daga ka ta na wasu sakanni,a hankali yayi niyyar zameta,saita tafi talau saboda yadda da gaske qirjinta ya riqe da ciwo,bai zaci haka ba cikin zafin nama ya riqota ta dawo jikinsa
"Are you serious?"kanta ta daga masa a hankali sanda take kwance a qirjinsa tana sauke numfashi,idanunta a runtse gam,hancinta na cika da qamshin turarensa,dumin jikinsa na ratsa fuskarta,tana iya juyo bugun zuciyarsa sosai
"Ok....ok" ya fada a hankali yana dan duban fuskarta dake cikin qirjinsa yana tunanin yadda zaiyi mata zuwa mota.


"Bani hannunki" ya fada calmly cikin qarfin hali,saita miqa masa hannun ya sake matseshi cikin nasa a hankali yana jin yadda tsigar jikinsa ke tashi tun daga qwaqwalwarsa zuwa gangar jikinsa,wanda sam baisan yaushe ya samo irin wannan feeling din ba,sai suka fara takawa a nutse har zuwa bakin motar.


Ga mamakinta da kanshi ya bude mata motar ta shiga ya rufe,saiya kunna ac na motar bayan ya dage dukka glasses din sama,sannan ya rufe ya juya yana barin wajen.


Idanunta ta bude tana kallonshi ta cikin glass din motar,karon farko da yayi wani abu da za'a bashi suna da tallafi a gareta kenan,bata sani ba,kona ganin idanun mutane ne?,saita rintse idanunta tana jin yadda ciwon ke sake motsa mata,ta sauke ajiyar zuciya tana kwanciya sosai cikin kujerar tana sauke numfashin wahala,wanda batayi cikakken minti ashirin ba taji saukar wani abu,ko data bude idanunta sai taga ruwan sama ke sauka,dai dai lokacin data hangi tahowarsa cikin sassarfa da qaramar lema a hannunsa,taci gaba da kallonsa tana riqe da saman cikinta har ya iso gab da motar,saita maida idanunta ta lumshe kamar me bacci,can qasan zuciyarta tana ambaton sunan Allah.
23/10/2021, 08:46 - πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»: 30


End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login