Showing 39001 words to 42000 words out of 121250 words

Chapter 14 - ALKIBLA complete

Start ads

24 Aug 2025

464

Middle Ads

qoqarinta na nuna mata cewa ta daina din kamar yadda tace,ya amsa a dake kamar yadda dabi'arsa take,bata damu ba ta dubi hajja
"Hajja...zanje na karbo dinkin nan,na samu guda daya"
"To...ba matsala....amma haidar ya saukemin ke,naga fita zakayi ko?" Tayi maganar tana dubanshi,ya amsa da eh ba tare daya daga kanshi daga matsa wayar da yakeyi ba
"Yauwa,ka sauketa da Allah,inaso ta dawo da wuri ta kitsemin kan nan nawa" ta fada masa sanda yake takawa yana barin falon,wani irin sak zahran tayi,ta buda baki zatayi magana yadda hajja ke kallonta yasa ta wayance
"Hajja santsin gashinki fa yasa kitso bai zama fa"
"Hakanan za'amin,bana son zama da tsefaffan kai"
Kai ta gyada kawai sannan tabi bayansa itama ta fice,hajja ta samu waje ta zauna,cikin ranta tana raya cewa yawan samun kusancinsu kamar haka me yiwuwa *SABANIN ALKIBLA* da rashin fahimtar dake tsakaninsu zai ragu ko yaya.


Sanda ta iskeshi a ma'ajiyar motoci har ya kunna motar,ta bude gidan baya ta zauna,a nutse ya waiwayo ya mata wani kallo daya sanyata tilas ta fito daga bayan ta dawo gaba,don ga fahimci manufar kallon nasa sarai.


Luff tayi cikin motar,wani irin qamshi mai taushi da sanyawa zukata nutsuwa ke tashi cikin motar,ga sanyin ac daya karade motar,shi kansa wani qamshi yake busowa kamar an zuba iskar wani abu,yayin da wani slow music ke tashi qasa qasa yadda bazai takura me sauraro ba.


Basuyi nisa ba wayarshi ta kama ringing,cikin wani sauti mai dadi,wayar ya janyo ya kara a kunnensa da hannu daya,yayin da daya hannun yaci gaba da tuqi dashi
"Ya akayi?" Ya fada da sauti mara amo
"Ok....ba damuwa....ganinan" ya fada yana aje wayar ba tare daya damu da kasheta ba,sannan ya sanya signal ya fada wani titin.


Da sauri zahra ta dubeshi,don ba titin da zatayi ba kenan,kwata kwata sun kauce hanya
"Ya haidar b....." Hannunsa ya daga mata alamun ta dakata ba tare daya waiwayo ya dubeta,a hankali ya gangara gefan titin,sannan yace
"Sauka" still idanunsa na kallon gaban motar,da mamaki ta kalleshi,ta kalli titin da suke kai,indai tace anan zata samu abun hawa zataci wahala koda kuwa ace ba bikin sallah ake ba,saboda titin ya baude sosai da hanyarta,saita kau da kanta daga duban data masa,shuru ya ratsa motar na sakan goma,sannan ya tasheta yaci gaba da tafiyarsa hankali kwance.


Basuyi nisa ba suka tsaya qofar wani gini,wanda baiyi kama da gida ba,yafi kama da qawatacciyar ma'aikata,parking yayi da kyau,sannan ya buda murfin motar yayi ficewarsa,ta bishi da kallo har aka bude masa qofar ya shiga.


Ajiyar zuciya ta saki ranta na baci sanda ta kalli agogon hannunta taga ta kwashi minti talatin zaune a motar babu shi babu dalilinsa,Saita fara neman abinda zata rage zaman kadaicin dashi,tunda ta baro wayarta a gida,a tunanin yanzu yanzu zataje ta dawo.


Aljihun gabar motarsa ta bude,duk da zuciyarta na gargadarta da aikata hakan,tana budewa wani dan qaramin littafi mai adon zaiba ya fado,yana da Ι—an nauyi kadan,saita daukeshi daga qasa,har zata maida sai taji ya dauki hankalinta,don haka ta tsaya ta bude.


Shafin farko ne kawai ke dauke da wasu kyawawan rubutu,wanda ajiki akayi magana mara tsaho kamar haka

_Abune mai matuqar ciwo ne a rayuwa rashin masoyi ko kuma wanda yake qaunarka,zaka yita tunawa cewa yayi maka nisa,kullum idan rana ta fito ta fadi ya maka nisan da babu masaniyar ranar da zaka taddoshi,sannu a hankali saika soma manta yanayin murya dariya ko murmushinsa,kome yawan damuwarka ba zata taba dawo maka da shi ba,amma sai zuciyarka ta kasa gasgata hakan,kayita hasashe da fatan zai dawo gareka_


Yaa zahra ce ta fado mata a rai,tasan tabbas kalamanta ne,da ita yake,hakanan sai taji jikinta yayi sanyi,kalamai ne marasa yawa amma masu ratsa zuciya,saita samu kanta da sake maimaita rubutun.


Tana tsaka da maimaita rubutun taji tsaiwar mutum a kanta saitin window din da take,aliyyu ne tsaye,harde da hannayensa a qirji yana dubanta,kwarjininsa da tsoro yasa ta diririce,ta soma qoqarin maida littafin inda yake,sai taga kawai ya miqo mata hannu,ba musu ta sanya masa littafin a hannun nasa a sanyaye,sai kuma taga ya bude murfin sit dinta,da idanu ya mata alamun ta fito,a sanyaye ta fito cike da tsoron me zai mata,tana tsaye ya zagaya ya shiga nashi sit din,ya sanya hannu ya rufe daya murfin bayan ya rufe nasa,sannan ya kunna motar yaja yana barin wajen,zahran ta bishi da kallon mamaki har sai daya fice daga layin.


Ginin daya fito daga ciki tabi da kallo,haushi da takaici na cikata,koma me ya mata hajjan ce ta jawo mata,inda ta qyaleta ina ruwan biri da gada?,ta hau napep asirinta a rufe ya kaita ya dawo da ita,yanzu gashi nan ya jawo mata bankada tana zaman zamanta,haka ta dinga takawa da qafafunta har ta isa titi,saidai acan ma sai data dan sha wuya kafin ta samu abun hawa,kasancewar garin kano kan cika ya tumbatsa da baqi a duk yayin da ake shagulgulan bikin sallah,hakan yakan sabbaba cinkoso da rashin samun abun hawa akan kari.


Ranta a bace ta isa shagon,abinda yadan sanyaya mata raima taje ta taras ya gama mata duka dinkunan,tana amsa tayo gida,saidai batayi niyyar gayawa hajja ba sam bare tace wani abu da zai sake dagula mata lissafi.

*********** **** ********

*_BANKAƊA_*
_abun Ι“oye!_


A hankali take takowa daga cikin gidan zuwa qofar gida sanye da doguwar riga marron mai sulbi,duk da ba kwalliya tayi ba amma tayi mata kyau sosai,hakanan jikinta na fidda wani qamshi mai aji da tsayawa a rai.


Abdulrashid ke kiranta,wanda tasan da zuwansa dama,tunda jiyo yazo harta zuba mishi bincin salla da sukeyi,wanda a tsarin gidan kwana uku akeyi ana abincin sallah,ran salla washegari da wata washegarin,ya shaida mata gobe zaiyi tafiya,an kirashi wani aiki me muhimmanci,amma kafin ya wuce zai biyo suyi sallama.


A tsaye ta sameshi ya bata baya,goye da jakar matafiya,ya waiwayo fuskarsa fadade da fara'a yana amsa sallamarta
"Wai har ka gama shirin?" Agogonsa ya duba
"Wallahi,ni suke ma jira abokan tafiyar fa,bazan iya tafiya bane saina zo na ganki".


Murmushi tayi,sosai takejin dadin yadda yake bata kulawa
"To ai gani" ta amsa masa tana murmushi,kafin ya bata amsa wayarsa ta sake tsuwwa,ya cirota daga aljihunsa ya daga
"Ok....gani,ganinan ai nace" maida wayar yayi yana cewa
"Fatima,tafiya zanyi saina dawo,banajin zan wuce sati daya kacal"
"To Allah ya tsare hanya....am na manta,bari na shiga na dauko ma saqo minti daya" tuni ya soma tattakawa
"Jirana ake fatima afwan....amma da mun dauki hanya zan kiraki in sha Allah,daga nan har zuwa 12 na dare ki jirani" kai ta gyada
"To shikenan,Allah ya tsare hanya,ya dawo daku lafiya"
"Amin na gode" ya fada yana takawa da sassarfa,ita kuma ta juya zuwa cikin gida.....


Masu karatu
*ALƘIBLARSU!*πŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈπŸšΆπŸΎβ€β™€οΈ
23/10/2021, 08:40 - πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»: 15
*_ina 'yan uwa musulmai masu kishin addinin islama???_*

*_maza ku matso ga wani aikin lada ya samu_*

*_Ɗanku kuma dan uwanku kuma qaninku wato ABDURRAHMAN,yaro mai hazaqa gami da kwadayin haddace littafin Allah mai tsarki,ya bude YOUTUBE CHANNEL nashi na qashin kansa,ku tallafa masa ta hanyar shiga wannan shudin rubutun ku danna masa subscribe,ba abunda xai rageku dashi saima samun dimbin lada dalilin KARFAFA MASA GWIWA,MUN GODE πŸ™πŸ½πŸ™πŸ½πŸ™πŸ½_*
πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½

https://youtu.be/WWIGq5Jbtb0




Tana komawa cikin gida shirin kwanciya tayi saboda a gajiye take yau din,duk da tana son zuwa susha hira da hafsat wadda tazo dazun,zata kuma kwana har uku,saboda me gidan nata wata tafiya ta kamashi,da qyar kuwa ya haidar ya barta saida yaji daga bakin mijin nata,sun yiyyi baqi yau din sosai,bata zauna ba hakan yasa ta gaji da yawa.


Sai data kwanta sannan ta kira hafsat tace karta jirata,tayi kwanciyarta gobe da sassafe zata shigo ta tasheta
"Ba komai wuron hajja,Allah ya kaimu"
"Aha" tace tana datse kiran.


Tana sane da maganar da sukayi da abdulyassar din kan ta jirashi zai kirata,tasan kuma tsaf bacci zai iya daukarta,don haka sai kawai taja laptop dinta 'yar qarama da abban gwammaja ya siya mata ta kunna,ta zabo daya daga cikin fina finan ciki ta kunna ta soma kalla.


Tun tana cijewa tana kallon har idanunta sukayi nauyi,batasan sadda bacci ya dauketa ba.


Sanda ta farka da sauri ta jawo waya tana dubawa,a zatonta zata samu miscal din abdulyasar din,babu miscal babu kuma saqo,ta kalli agogo,sha biyu na dare har da rabi,kenan ya saba lokacin da yace zaiyi kiran nata?,hakanan sai taji idanunta ya bushe,baccin yayi nasa guri,saita miqe ta shiga bandaki ta daura alwala,ta dawo ta tada salla.


Ta kusa kaiwa qarfe biyu saura na dare tana zaune saman abun sallahn,har bacci ya sake dibanta taji qarar wayartata,saita miqa hannu ta dauko wayar,idanunta ya sauka kan agogon qarfe biyu da rabi na dare,ga mamakinta lawal ne abokin abdulyassar yake kiran,sosai hakan ya bata mamaki,wata mummunar faduwar gaba ta ziyarceta har batasan sanda ta daga wayar ba.


Muryar lawal dince ta bayyana cikin tsantsar tashin hankali yake fadin
"Zahra....abdul ya mutu,abdul ya rasu,qarfe sha biyu na dare yayi hatsari a hanyarsa ta tafiya,Allah yayi masa cikawa a take" dif wuta ta dauke mata,saita daina jin abinda lawal din yake fada,sai wata qara dake ratsa kunnenta kamar an buga qarfe da qarfe,ita dai batasan mintinan data shafe a haka ba,batasan kuma sanda lawal ya katse nashi kiran ba,batasan yadda akai ta kai kanta dakin hajja ba,sai ganinta tayi ta fada saman hajjan tana wani irin numfashi.


A matuqar firgice hajjan ta miqe ta zauna,don dama bata jima da gama sallar dare ba ta koma ta kwanta
"Zahra'u....zahra'u!....mene ne?,innalillahi wa inna ilaihi raji'un,yi kuka....kiyi kuka zahra'u,barshi ya fito" ta fada taba danne mata qirji,ganin yadda yake sama da qasa numfashinta kuma na wahalar shaqa,cikin ikon Allah ta fusgo numfashin da qarfi sai kuma ta saki wani qaqqarfan kuka ta fada jikin hajja gaba daya ta qanqameta
"Innalillahi" hajja keta maimaitawa,cikin ikon Allah itama zahran saita kama,tsayin wasu mintuna masu tsaho sannan ta iya magana cikin sheshsheqar kuka
"Hajja.....abudul....yassar ya.....mutu,yayi hatsari baya.....n nyabar wajena,ya rasu hajja!" Ta qarashe cikin gunjin kuka.


Sosai hankalin hajjan ya tashi,ta sake qara qarfin salatinta tana kuma maimatawa,wannan dare ya zamewa zahra dare mai tsaho duhu da kuma qunci,haka suka zauna ita kuka hajja lallashi,kafin gari yakai ga wayewa tuni idanunta suka suntuma suka kumbure,qwayar idanunta dukka sun shige ciki.


Suna idar da sallar asuba hajjan ta daga waya ta kira abba yusuf,saboda abba babba baya gari,cikin lokaci qanqani ya iso,bayan su gaisa ta shaida masa zancan rasuwar
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shima ya dinga maimaitawa
"Yanzu abinda za'ayi....inaga idan gari ya sake shaaa,ka bawa mustapha ko shamsu muqulli sukaita gidansu yaron,don hankalinta bazai taba kwanciya ba,ba zata zauna ba,in yaso idan ya dawo daga kaitan zuwa lokacin mu mun kintsa saiya miqa mu,idan mukaje saimu duka mu dawo tare,ku kuma ko zuwa yamma haka zuwa dare kwa leqa ku yiwa iyayensa maza ta'aziyya"
"To shikenan,Allah yayi masa rahama,yasa ya huta".


Da qyar hajja ta sanyata tayi wanka,ta shirya cikin doguwar riga da hijabi,duk wanda ya ganta saiya tausaya mata,saboda yadda gaba daya fuskarta ta sauya saboda kuka,ga wani irin ciwon kai daya saukar mata lokaci daya,har dan zazzabi zazzabi takeji.


Kafin su tafi saiga hafsat ta fito itama a shirye,hajja zatayi qorafin ta koma tace da ita
"Ba za'a barta ta tafi daga ita saisu umaima yara ba,na kirashi na gaya masa mutuwar,nace zan rakata yace babu damuwa"
"Khalas....shikenan" hajja ta fada sanda hafsat din ta shige motar,shamsu ya tayar da motar suka fice.


Ko a cikin motar ma dai kukan take yaqi tsaya mata,ta dora kanta saman kafadar hafsat tana shashsheqa
"Kiyi haquri zahra ki masa addu'a,a yanzu ita yafi buqata"
"Shikenan hafsa...shima ya tafi ya barni,hafsat nice mutum ta qarshe da yazo wajenta,nice mutum ta qarshe daya kira da wayarsa,ashe da yazo bankwana yazo yimin?,ashe ya tafi kenan?" Sosai ta karyarwa da hafsat zuciya,haka taci gaba da lallashinta har suka isa qofar gidan su abdulyasar da taimakon kwatance da lawal ya dinga musu.


Babu kowa qofar gidan sai daidaikin mutane,da alama an tafi kaishi makwancinsa na gaskiya,hafsat din ita ta riqe zahra har zuwa cikin gidan.


Cike gidan yake da mutane,wasu kuka wasu tagumi,hafsat ce mai qarfin halin gaidasu,sannan ta tambayi inda hajiyan abdulyassar din take,aka nuna musu wani falo dake cike da jama'a suka nufi can.


Kana kallonta zaka gane mamansa ce saboda suna kama,tana zaune saman kujera,sanye da ash din hijabi da carbi a hannunta tana ja.


Gabanta suka samu suka isa,zahran ta zube a gabanta hafsa ta zauna gefanta,hafsat ce ta fara yi mata ta'a ziyya sannan zahra cikin shaqewar murya,daga bisani hafsa tace
"Zahra ce hajiya" hafsan ta zaci zataga wani alamu na nuna kulawa ko sanayyar sanin sunan,babu wani alamu na ta gane abinda hafsan ke fada,tadai ce
"Allah sarki,mun gode Allah ya bada lada".


Zaman shuru ne yaci gaba da wanzuwa a falon,zahra na cikin hijabinta tana kuka,ganin yadda falon ke sake cika yasa hafsan ta sama musu wajen zama daga waje,abinda ta lura dashi har suka tashi hajiyan ma bata lura da tashin nasu ba,zataso tambayar zahran cewa anya sunsanta kuwa?,to amma yanayin da a yanzu take ciki ba lokaci bane na mata wannan tambayar ba.


Awa kusan guda kenan da zamansu a wajen zahra ga dubi hafsa
"Hafsa qishirwa nakeji,bazan kuma iya shan komaj cikin gidan nan ba"
"To muje waje mana mu samu wani shop ko lemo kisha" kai ta kada
"Ruwanma ya wadatar" ta fada tana miqewa da qyar
"Wash kaina" ta fada sanda ta miqe din
"Lafiya?" Hafsa ta tambayeta,saita dan ya mutsa fuska
"Mtsweww,kaina ke ciwo"
"Dole ai,wannan kukan da kikayi ai ba kadan bane"da haka suka taka zuwa wajen gidan.


A yanzun layin a dinke yake da jama'a,da alama har sun dawo kenan,haka yasa sabuwar qwalla suka zirarowa zahra,yanzu haka abdul nacan kwance,nacan kwance qasan qasa,babu kowa saishi kadai,babu kowa sai halayyarsa da ayyukansa.


"Zahra duka shagunan layin nan a rufe suke" taji hafsat na fada,kai ta gyada tana share hawayen fuskarta
"Eh na gani,amma layin nan kamar layin gidansu rabi'ah ishaq ko?,da kika tana rakoni?"
"Eh tabbas,aiga gidan nasu can ma qarshen layi"
"Yauwa,mu qarasa nasha ruwan a can kawai"
"Ok" hafsat ta fada,kai tsaye suka miqe zuwa gaba,wanda gidan ke jerin gidajen dake jikin gidansi abdulyasar din,tsakaninsu da gidansu abdulyasar din gida biyar ne kacal.


Da sallama suka shiga gidan,wata mace dake duqe bakin fanfo tana wanki ta daga kai tana amsa musu sallamar
"Ku qaraso mana" ta fada tana dagowa daga duqen da tayi.


Gaidata sukayi sannan suka shaida mata su din qawayen rabi'ah ne
"Ayyah,kuma gashi bata dade ta fita ba wallahi"murmushin qarfin hali zahra tayi
"Babu komai,dama ruwa muka shigo zamu sha_ta qarashe maganar ta duqawa kamar wadda zatayi ruku'u saboda yadda kanta keci gaba da sara mata
"To babu damuwa,bari A kawo muku" saita yi gaba daga can qarshen tsakar gidan,ta bude wani fridge dan qarami dake qasan rumfa tana cewa
"Hala daga gidan rasuwar gidan su abdul kuke?" Hafsat ce ta amsa mata
"Eh wallahi" cikin nuna jimami da alhini ta sake cewa sanda take ciro ruwan
"Ai mun tashi da tashin hankali yau,mutuwar matashi yaro,babban abun tausayin ma,yau satinsa biyu cif da kai kudin aure....." Kalma mafi girma da muni data daki zuciya da kunnuwan zahra,kalmar da taji kamar a wani mugun mafarki aka furtata,kafin ta dawo hayyacinta sautin muryar hafsat cike da zallar mamaki ta furta
"Sati biyu da kai kudin aurensa?"amsa musu tayi sanda take rufe fridge din tana dawowa zuwa garesu
"Wallahi Allah,bari kawai....daxun yarinyar da ya kaiwa kudin tazo,abun gwanin ban tausayi,bakiga kukan da take ba,tana faduwa ana dagata,dukkanmu sai data sanyamu qwalla,sai data sake saka hajiyarsa kuka sosai,qarshe kasa zama tayi sai gida aka maidata,kinga keyholder din kai kudin akan window na ma,ni ko amfani da ita bankai ga yi ba" qarashen maganar yazo dai dai da zamewar zahra daga durquson da tayi zuwa zama dabas a qasa
"La haula wala quwwata illa billah" kawai zahran ke fada cikin zuciyarta,bakinta zuwa maqogaronta ya sake bushewa raqayau kamar bata taba kurbar maqwarwa daya ta ruwa ba tunda Allah ya halicceta,tana jin sanda matar ke miqo ruwan amma saita kasa amsa,maimakon karba ma saita miqe tsaye kawai ta nufi qofa,bataga wani sauran amfanin zamanta ba kuma,tana jiyo hafsa na mata godiya gami da sallama.


Tuni ta miqi hanya ba tare dako waiwaye ba,ita kanta hafsat din sai cimmata tayi a hanyar
"Zahra....da kin tsaya ya shamsu ya dawo ya maidamu" kaita girgixa idanunta na sauka kan gungun abokan abdulyasar dake zaune qasan wata rumfa,can ta hango auwal a tsakiyarsu,wani abu ya caki zuciyarta,tsanar auwal din ta kamata,tabbas babu shakka yasan komai,yasan duk abinda ke wakana tunda amininsa ne,dashi aka hada baki,dashi aka rufeta
"Muje kawai hafsa,ma hadu a hanya" a yanayin data ga ta shiga,tasan cewa koda bayani tayi mata babu lallai

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login