Showing 54001 words to 57000 words out of 121250 words

Chapter 19 - ALKIBLA complete

Start ads

24 Aug 2025

460

Middle Ads

tsanani da tsauri da zaki yankema rayuwata a karo na farko!" Ta qarasa maganar kuka na qace mata,tsam ummin ta miqe a nutse ta fita daga falon ba tare data tsaya sake jin komai ko sake cewa komai ba,mutum na biyu da ya sake miqewa zai rufawa ummin baya haidar ne,don shi maganar hajjan jinta yake kaman tatsuniyar gizo da qoqi,don baiga dalili ko abinda zai saka wannan kwamacalar yiwuwa ba,kawai saboda ana son hukunta yarinya sai an jingina da tashi rayuwar?
"Kai aliyyu....dakata" abba babba mahaifinsa ya dakatar dashi,saiya koma hannun kujerar daya tashi cikin girmamawa ya zauna
"Gani abba" ya fada wata irin murya mai kauri
"Dukkaninmu nan daka ganmu(ya fada yana nuna junansu da yatsa)albarkarta muke nema....dukkanmu aljannarmu tana qarqashin qafarta,sa'annan babu wani abu da zata nema nan gidan duniya mu kasa yi mata shi,koda fansar ranmu ne zamu bada,ina fatan ka fahimci abinda nakeson fada?" A wannan karon zuciyarsa sake gaya masa take abun babba ne,saidai har yanzu zuciyar 'yan mazan a dake take,har yanzu baiji wani darrr ba,don haka ya gyada masa kai kawai ya dora da fadin
"Eh abba...."
"Amma yaaaya.....hajja ina ganin kamar wannan hukuncin baiyi tsauri ba?,ya kamata a zauna a sake duba abinda zai yiwu ko?" Cewar abban tsakiya wanda kukan zahran bai masa dadi a ransa kamar yadda baiwa sauran
"Kai muftahu....." Hajja ta fada da salon son dakatar dashi,dai dai nan haidar ya miqe tsam abinsa ya fice daga falon.


Da wani irin sauri itama zahran ta miqe tayi dakinta saboda ji da tayi ta kasa zaman falon,kamar idan ta tashi tabar musu falon ta tserewa wannan mummunan hukunci na hajjan,amma data shiga dakin saita kasa zaune ta kasa tsaye,kamar wata zararriya haka ta dinga jin kwanyarta na yamutsawa,ta dinga leqensu abban tana so suyi subar falon,tana da tabbacin barazana ce kawai hajjan keyi amma zata janye,tasan cewa da taje ta kwantar da kai ta lallabata shikenan za'a wuce wajen,duk da tafi kowa sanin halin hajjan tunda tafi sauran zama da ita,sau tari tana da kafiya da zafi kan wasu abubuwan,wanda idan ta juye maka zaka tsammaci ba ita bace.


Kansa yake gayawa cewa babu wani abu da zai faru sansa yake dosar nahiyar da dakunansu suke,dukkan abinda hajjan ta fada barazana ce kawai saboda tana tunanin ya qetare abinda ta gaya masa,tana so ne ta kaɗashi kawai saboda haka,saidai can can qasan ranshi ya kasa samun nutsuwar da yakeson samawa kansa,ya kasa gamsuwa da dukka kalaman kwantar da hankali da zuciyarsa ke jero masa,ya kasa daukar kowanne daga ciki,indai har kuwa hajja na nufin abinda ta fada da gaskene har cikin zuciyarta....to a karon farko wani mummunan al'amari zai iya faruwa wanda shi kansa bai sanshi ba,bai kuma san qarshensa ba.



Har ya saka key zai bude gefen nashi wayarsa ta dauki tsuwwa,tun kafin ya ciro ya saki tsaki,don sai yaji qarar wayar kamar wani qarin damuwa ce cikin kwanyarsa,ya zaro yana duba mai kiran,general hamza ne,babu uzuri matuqar kira daga wajen irinsu ne,don haka ya daga,ya gaidashi cikin girmamawa kamar yadda ya saba
"Abu biyu yasa nayi kiranka aliyyu.....na farko akwai wani gagarumin al'amari daya tunkaroka,wanda kyanta idan ka samu dama ka sameni saboda kaji kai tsaye daga bakina.....na biyu kuma batu ne na auratayya" saiya dan saki murmushi
"Ina farincikin shaida maka cewa ina saka ran nan gaba kadan xamu hada zuri'a,zamu hada jini da familynka....,duka dai idan ka samu dama kazo na ganka" kusan bai fahimci dukka maganganunsa ba,ya sani kuma a yanzun yadda yake jinsa ba fahimtar zaiyi ba,don haka kawai yace
"Sir...in sha Allah zan shigo gobe da safe" godiya general ya yiwa aliyyun kamar ba shine samansa ba,sannan ya katse wayar......



_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_

_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_

_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
23/10/2021, 08:42 - 👍🏻👍🏻: 20

_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_

_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_

_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
___________________________



Ko gama fita su abba babba basuyi daga falon ba zahra ta fito da sassarfarta,kai tsaye ta fada jikin hajjan gami da riqe hannayenta
"Hajja....don Allah kibar wannan zancan,ki haqura dashi....." Sosai ta dinke fuskarta,wanda kusan hakan baqo ne ga zahra
"Ke zahra'u,ki bude kunnenki ki jini da kyau,babu fashi a maganata,saboda haka bana son ki sake cewa komai" kuka ta barke dashi tana sakin hannayen hajjan
"Toni hajja na haqura....na haqura da karatun wallahi indai sai an aiwatar da wannan sharadin"
"Ko kin fasa karatu fa aure babu fashi....idanma zaki sanyawa ranki dangana ki sawa ranki ahto,don dukkaninku na gaji da ganinku daga ke har shi kuna yawo haka tsigai tsigai dukka shekarunku sunkai,sannan wannan shegen takun saqar naku ma gwara a kawo qarshensa" sosai ta saki sautin kukanta tana cewa
"Wallahi hajja yanzu bama fada,don Allah yaushe ma rabon da kiga na kulasa,ki janye hajja don Allah" miqewarta ma hajjan tayi tana cewa
"Saikuma kiyi tayi idan jajen farar kaza halak ne" kafin ma hajja tayi nata dakin zahran ta rigata miqewa da gudu ta nufi dakinta tana fadin
"Wallahi bakya sona hajja.....bansan haka ba sai yau" baki ta tabe kawai ta bita da kallo harta shige dakin ta kulla qofa.


Qaramin murmushi hajjan ta saki tana girgiza kai gami da sakin ajiyar zuciya
"Duka kwayi ku gama 'yan nema,duk tsiya mutum ai bayaqi jininsa haka ba" tayi maganar a fili amma qasa qasa,cikin ranta tana jin sakayau,wani irin dadi da karsashi takeji,ji take kamar ma ta janyo rana ita yau din ayi komai a wuce wajen,don daurin auren yanzu ita shine a gabanta,koma meye ya biyo baya.


Tsaye yake a tsakiyar yalwataccen bedroom din nasa daure da towel yana sharce ruwan wankan dake diga daga kansa zuwa sassan jikinsa dake cike da gargasa,wata iriyar kasala yakeji sosai,banda haka tun sassafe yaso zuwa wajen general yaji neman da yake masa,amma gashi har kusan sha daya da rabi na safe yau din bai fita ko ina ba,duk da tarin abubuwan yi da ya shirya zaiyi a yau din.


Sai daya shafe kusan minti talatin yana shiryawa,cikin qanqanin lokaci ya fito fes cikin wasu qananun kaya da sukayi masifar amsarsa,saidai fuskar nan a dinke take tsaf,yakanji yanayi na bacin rai ya mamayeshi a duk sanda ya tuna zantukan hajja na jiya,duk da cewa yana sake gayawa kansa wasa ne,kuma bazai taba yarda ko lamuntar hajjan taci gaba da irin wannan wasan gaban yarinyar ba har yaja masa raini a nan gaba,don bazai dauki raini ba,wayarsa da key din mota kawai ya dauka ya fice a dakin.


Sassansu ya fara shiga ya gaida mahaifiyarsa da momy abokiyar zamanta,a can ya samu anty uwani ta dubeshi bayan ya gaidata
"Kana nan dai zaune kana sake cinye shekarunka a gida,tun mutuwar yarinyar can zahra'u,banda abinka ai dole haka zaka haqura,ka sake zabar wata cikin dangin mahaifinka kuma tunda an gwada na mahaifiya,ko 'yar uwarka ma suwaiba ai baqi zatayi ba aliyyu sai a jarraba ko?" Kallo daya ya mata ya kauda kai,tamkar ma badashi take ba,shi dama ko can ba wani shiri suke sosai ba,don bai sakar mata fuska,ita kuma shakkarsa take,bare kuma 'yarta da ko kallo bata isheshi ba,yana shirin fita mama tace masa
"Idan ka dawo kazo ina son magana da kai"
"To" ya amsa mata ba tare daya kula da a dawo lafiyar da anty uwanin ke masa ba.


Yana taka sassan hajjan amma ji yake kamar ya koma kada ya shiga,saidai bazai iya ba matuqar yana garin,da haka ya iske babban falon tsohuwar,babu kowa ciki amma yana jiyo motsi daga kitchen,saiga jidda jikarta na fitowa hannunta riqe da wasu farantai.


Cikin girmamawa ta rusuna ta gaidashi,ya amsa zai tambayeta tsohuwar kenan sai gata ta fito daga dakin zahra,wadda ta kulle kanta tun jiya,ko abincin dare bata ci ba,ga na safiya ma da taqi budewa bare taci,sai da qyar hajjan ta samu ta bude qofar ta ritsata da tea tana qwalla tana roqarta ta janye zancan tayi kurba hudu.


Daga tsaye yake gaidata saidai ya dan ranqwafa,fuskarsa babu walwala ko fara'a,ta amsa masa tana zama gami da cewa
"Tun dazu nasa aka kaimaka abun karin,anje anyi bugu anyi bugu baka bude ba"
"Eh....bacci nake lokacin" baki tadan tabe kadan sannan ta dan daga murya tana qwallawa husna dake kitchen kira kan ta hado abun karyawa ta kawo masa
"Barshi kawai....sauri nake zan fita" ya fada yana dakatar da bayanin da takewa husnar
"Madalla....idan ka dawo kazo zanyi magana dakai"

***********Kai tsaye a yau din aka masa iso cikin katafaren falon general hamza,wanda ya tsaru qwarai,ga hotunan iyalinsa nan manne a kowanne bango na falon nashi,wanda ya wadatu da iskar ac mai ratsa jiki.


Zaune suke su biyu tak cikin falon daga haidar din sai general,gaban aliyyun cike yake da kayan ciye ciye iri daban daban,saidai yadda yakejin zuciyarsa babu sukuni baijin sha'awar cin komai
"Kaci wani abu mana haidar" general ya fada yana murmushi
"Alhmdlh daddy....a qoshe nake"
"To shikenan....ba laifi" ya fada yana zaro takarda daga cikin takardun dake gefansa,wadda akayi sealing nata cikin envalope ya miqa masa
"Wannan.....kada ka bude sai bayan kaje gida ka nutsu tukunna....yanzu magana ta biyu zamuyi dakai" kai ya gyada bayan ya amsa takardar ya aje saman cinyarsa
"Nasan kasan haisam zuwa yanzu,don na gabatar maka dashi" kai aliyyun ya sake gyadawa yatsunsa soke cikin na juna yana duban general gami da saurarensa
"To haisam dai ya sameni da zancan yaga wata yarinya yana sonta....ya kuma tabbatar min da 'yar gidanku ce,duk da bansan ya akayi suka hadu kuma yasan yar gidan naku bace,amma dai yacemin sunanta zahra" ya qarasa fada yana duban haidar.


Baiyi wani mamaki sosai ba najin zancan musamman idan ya tuna da abinda ya faru ranar daya taso zahran zuwa gida daga hotel,saiya gyadawa general kai
"Eh....qanwata ce"murmushin farinciki general ya saki
"Ma sha Allah....muna da uwa a bakin murhu.....yanzu dai ni hamza ina nemawa yarona auren zahra'u....duk da ban gaya maka ba....haisam ba dan cikina bane,amma baida maraba da dana dana haifa,saboda dan qanwata ne data rasu awa daya tak bayan ta haifeshi,so a wajen iyalina ya taso,baisan wani uba ba bayan ni,bai kuma san wata uwa ba bayan mai dakina" kai haidar ya kada cike da gamsuwa,ta wani gefen kuma sai yaji kamar an rage masa nauyin dake cikin zuciyarsa,saboda hango mafita da yayi ta hanya mai sauqi kan zancan aurensa da zahra,indai har nema mata mijin ci gaba da zuwa makaranta ne zaisa su laqa masa auren da bai shirya ba,auren da baiji ba bai gani ba,to ga miji nan ta samu,saisu sake masa mara yayi fitsari,duk da yaron bai wani kwanta masa ba tun a wancan ranar da sukaso samun matsala da juna,don haka da karsashinsa yace
"Indai ni zan aurar da ita....to na bashi,saidai bazanyi saurin fadin hakan kai tsaye ba,zan isar da saqonka zuwa garesu,kuma ina da fatan cewa za'a dace"
"Ma sha Allah,ma sha Allah" general keta fada cikin nuna farinciki,sun taba hira da haidar din kan abinda ya shafi aikinsu,sannan haidar din ya masa sallama ya fito.


A farfajiyar gidan sukayi kacibus da haisam,a wannan karon fuskar haisam a washe bakinsa a bude ya nufi aliyyu da dan hanzarinsa yana miqa masa hannu gami da cewa
"Barka da warhaka" wani kallo aliyyun ya masa yayi gaba abunsa ba tare daya bashi hannun sun gaisa ba,ya qarasa motarsa ya bude ya shiga ya tasheta ya fice daga gidan.


Iska haisam ya kaiwa naushi,me ya yiwa guy din nan tun karon farko ne haka suke samun sabani?,amma koma meye zai lallaba su bashi auren zahra,kome zaiyi masa zai iya shanyewa indai zasu bashi zahran,saboda ta gama yi masa a rayuwa,bai taba ganin macen data masa dari bisa dari ba irin zahra'un.


A hankali yake tuqin kamar wanda baida lafiyayyen injin mota,da hannu daya yake murza sitiyarin motar,daya hannun kuma ya aza yatsunsa saman labbansa yana dan shafasu a hankali,yayi nisa cikin tunani da kuma lissafin yadda abubuwa zasu kasance da yadda zai tunkari su abba da maganar haisam,shi a karan kansa cikin idanunsu yaga gasken gasken son qulla lamarin daga garesu,amma kuma ta wani fannin yana da hope na cewa zasu karbi zancan haisam din.


Shawara ta qarshe da zuciyarsa ta bashi itace,ya tunkari yarinyar kai tsaye yayi mata tayin amsar haisam din koda baiyi mata ba matuqar dukkansu suna son zame kansu daga al'amarin,idan yaso daga baya sayi dukkan mai yiwuwa su warware zancan haisam din,da wannan shawarar ya qara gudun motarsa,tafiya kadan ya sanya signal yahau club road bayan ya baro titin gidan general.


Bai dawo gida ba sai bayan sallar isha'i,sai daya fara sauke abu sufyan da suka wuni tare a gida sannan yayo gida.


Kai tsaye sassansa ya nufa,yana shiga ya zaro wayarsa ya kira musty yace ya sameshi daki,babu jimawa ya iso,order din abinda zaici ya bashi yayo masa a wani gidan cin abinci dake kusa da tasu unguwar ya hada masa da key din motarsa,yana murna ya fice kuwa da sauri,don yana masifar son aiken ya haidar din,ko banza akwai qaruwa,baya amsar canji da sauransu.


Kayan jikinsa ya fara cirewa ya zubasu a ma'ajiyar kayan datti,duk yadda wasu mazan keda aqidar watsa daki sam haidar din ba haka yake ba,da wahala ki samu dakinsa a wargaje da kaya,komai nashi tsaf tsf kamar wata mace,yana fitowa musty na dawowa,yace ya jirashi zai fito yanzu,saiya zira jallabiya golden colour mai gajeran hannu,bayan ya feshe jikinsa da turarukansa masu sanyin qamshin sai ya dawo falon.


Sai daya zauna gaban ledan da mustaphan ya aje sannan yace
"Idan ka fita....ka turomin yarinyar nan" dubanshi mustapha yayi
"Wace yaya?" Tsaki ya danja yana bude ledar
"Fatima"
"Ohk to" ya fada yana miqewa da sauri gamida aje masa muqullin ya fice.


Wani tunani da yayi shi ya sanyashi daukan wayarsa dake ajiye ya kira mustaphan
"Ka kiratanne?"
"No yaya....yanzu dai zan shiga"
"Manta kawai,bar kiran"
"Ok to" saiya datse kiran ya ajiye wayar ya jawo tarkacen takeaway din ya soma ci,saidai sam abincin bai masa test a baki,saboda ba sabonshi bane cin abincin waje matuqar yana gida,don haka cin abincin bai wani nisa ba ya aje ya wanke hannunsa ya sake daukar wayarsa ya fice zuwa sassan mahaifiyarsa.


Yana tafe zuwa sassan hajja bayan ya baro sashen mahaifiyarsa yana tuna maganganun da suka kusa kwashe awa guda sunayi da ita,wai da gasken kenan hajja take?,har maganar takai kunnen mamanshi?,har tana jaddada masa matsayi da girman hajjan a idanunsu?,da cewa hukuncinta dai dai yake da hukuncinta kona mahaifinsa?,da ire iren wannan tunanin ya isa sassan hajjan.


Sai daya jirata ta fito daga daki yana zaune yana kallon labarai a gidan tv,fuskarta babu yabo ba fallasa ta zauna daura dashi,shima saiya bar dukkan abinda yakeyi din ya tattara hankalinsa kanta
"Kince kina nema na,gani....amma kafin naji abinda zakice,bari na sauke nauyin saqo da alqawarin dana dauka" ya fada yana gyara zamansa sosai cikin kujerar yana duban hajja
"Nasan kinsan boss general hamza ko?" Kai ta gyada a nutse,idanunta kyam akan aliyyun,saiya lumshe ido ganin ta fahimta da wuri
"Yaronsa ko ince dansa....yaga fatima yana so....dazun naje wajen mahaifin nasa,yace na roqa masa alfarma wajenku kan a bawa dan nashi dama" daga haka ya tsagaita yana kallon hajjan.


Ga mamakinsa saita saki wani dan qaramin murmushi
"Wannan wasan kwaikwayon kuma ka shiryo?....kana tsammanin saboda ka sanya sunan general a ciki na kasa aiwatar da abinda nayi niyya na bawa dansa?" Kai ya kada
"Bazan miki qarya ba hajja....kinfi kowa sanin waye ni" kai ta gyada
"To naji....shikenan,aje a haka....baka shaida masa cewa mun mata miji ba,kuma kaine mijin?,gida bata qoshi ba ai bazamu baiwa dawa ba ko?,ba zamu zaka kyandir ba....mu haska wasu mu qona kanmu" sosai yake kallonta yana jin rudani nason lullubeshi,ya tabbata dai da gasken tsohuwar nan take,tanason hautsina masa dukkan lissafinsa da wani zaman lafiyarsa
"Amma hajja....for god sake yarinya tayi laifi ita kadai za'a hada harda ni cikin hukuncin?....me nawa ni a ciki?,hukunci ma irin wannan na aure?....kiyi haquri hajja,amma gaskiya bazan iya karbar wannan tsarin ba,babban kuskure ne ka yankewa kanka hukuncin amsar wani abu da bai dace da tsarin rayuwarka ba saboda wani matsantawa daga familynka,saboda zaka rayu ne tare da sakamakon wannan hukuncin daka yanke....bawai tare da familyn naka ba....,idan ma kin yanke hukuncin nan ne saboda ki

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login