Showing 111001 words to 114000 words out of 121250 words

Chapter 38 - ALKIBLA complete

Start ads

24 Aug 2025

471

Middle Ads

dama ta jima da canzawa,abubuwan da suka faru dazun suka dawo masa,rakin data dinga yi,magiyarta da ban hanqurin data dinga masa tana cewa ba zata qara ba,shi kuma yana tambayarta ba zata qara me ba,dukkansu shida ita ya tabbatar mahaukata suka zama tuburan,ita ciwo ya isheta,shi kuma duniyar data jefashi ne yasa ya kasa fahimtar komai.


Sallah ya sauka yayi yana miqa godiyarsa ga Allah,ya sani cewa ubangiji ya gama masa komai,sai kuma neman taimakonsa kan bauta masa da tsare haqqoqinsa,sannan ya kuma ya shiga lamarin xamantakewar aurensu,ya bashi ikon da zai riqeta bisa doron shari'a,kan gaskiya amana tausayi da kyautatawa.


Tana bude idanunta dashi ta soma tozali,ya sanyata a gaba yana qare mata kallo,saitayi rub da ciki da sauri tana boye fuskarta,yana murmushi shima ya haye bayanta,ya aza mata nauyinsa yana cewa
"Good morning zahraty amarya" sosai ya bata kunya bayan wadda takeji,nauyinsa takeji sosai,musamman idan ta tuna waye ya haidar a wajensu,amma gashi dare daya ya sauya komai a tsakaninsu,kamar bashi ba,kamar wani aka canza musu dashi,bata taba ganin fuskarsa a yanayin data ganta ba tsakanin jiya da yau.


Sai da yayi da gaske sannan ta miqe ta fuskanceshi,ya dinga tsokanarta,ya hanata sakat,ita kuma kunyarsa kamar qasa ta tsage ta shige ciki haka ta dinga ji,bai qyaleta ba yaci gaba da bibiyarta duk inda ta saka qafa cikin dakin,saidai bai fiya magana ba,amma ayyukansa na gaya mata komai,shi ya hada mata ruwa ta sake wanka,ya gyara dakin da kansa,don yace harsu tafi babu masu sharar da zasu sake shiga musu dakin,tayi mamakin yadda ya iya aiki da kansa,ashe dama a baya rashin ganin dama ne?,ko kuma sune basu fuskanceshi ba,itakam mamakin sauqin hali irin nasa take,komai nashi a sauqaqe yake yinsa,babu zafin nan,babu izzar nan da suke zatan masa ita.


Wayarsa ce tayi qara,ya qaraso ya daga,hajja ce take kira,bayan sun gaisa sai tace
"Lafiya na jiku shuru yau?"
"Eh...itace bata jin dadi sosai,ta sha magani ne,tana kwance" duk da ranta ya bata wani abu amma sai bata nuna ba,kawai tace
"Ayyah,qila tafiyar jiya ce da haka kawai ka kwasa mutane....ni dinma qafata ciwo take sai dana shafa magani,to Allah ua sawwaqe,ya bada lafiya"
"Amin amin" yana dubawa yaga harta kashe wayar ma,sai ya saki murmushi suka hada ido da zahra,itama murmushin kawai tayi,addu'a dama take kada Allah yasa asirinsu ya tonu wajen hajjan,sai gashi bata gane ba
"Ko zakije ku gaisa?" Ya fada yana kashe mata ido,kafada ta maqale,tasan bata isa taje ta fito ba hajja bata gano komai ba,don ko tafiyarta tasan ta sauya.


Wuni sukayi sur cikin dakin ba tare da shi ko ita sun fita ba,sai yayi amfani da wannan damar,ya dinga lura da ita tare da dasa mata sabuwar qaunarta cikin zuciyarta,bai yarda sunyi nisa da juna ko raba mazauni ba,ya sanya nata sabo dashi da saboda jikinsa,tun tana kakkaucewa harta sallama.


Washegari shi da ita kadai suka fita wani waje,bayan sun biya sun gaida su hajja,yadda ta dinga sussunne kai da jin nauyinsu su duka ya alamtawa hajja me afkuwa ta afku,duk da ba haka taso ba,taso sai bayan anyi taron biki an kaita amma ba abun damuwa bane,tunda already matarsa ce.....da fatan alkhairi ta bisu sanda suke ficewa,saita lura mama ma idanunta yana kansu fuskarta na nuna farincikin dake qasan zuciyarta.


Karo kusan na hudu kenan tana hada ido dashi sanda suke zaune saman table din daga ita saishi,waje ne me kyau,wanda kallonshi kawai ya isa ya sanya zuciya ta debe kewar dake damunta,gabanshi shi babu komai face ruwan roba,sanda aka kawo menu ita ya zabarwa abubuwan da za'a kawo mata,wanda kusan duk abubuwan kwadayi ne,yatsunsa ya sarqafe kawai cikin na juna ya zuba mata idanu yana kallon duk wani motsi nata,kyau take qara yi masa,qaunarta yakeji har babu iyaka.


Karo na qarshe da suka hada idanu tadan kwabe fuska kamar mai shirin yin kuka,murmushi ya sakar mata yana girgiza kansa,gyara zamansa yayi still dai baibar kallonta ba,a hankali yace
"U r my first love" cikin mamakin furucinsa ta dakata daga kai ice cream din data debo bakinta ta zuba masa idanu alamun son qarin bayani,kai ya gyada mata
"Yes u r"Saita samu kanta da tattara dukkan hankalinta a kanshi,cike da mamaki take dubanshi
"Tun lokacin da aka haifeki na fara sonki,a lokacin da nike tamkar ɗa a wajen ummi,duk da na fara samun qanne a lokacin,amma sanda aka haifeki ji nayi sai a lokacin na samu qanwa,a sannan ni kadai kike yarda dani baya ga ummi kaf fadin gidan" yana fadin haka saita tuna sanda hajja ke bata wannan labarin,amma a lokacin ta zata hajjan na fada ne kawai saboda taji dadi a ranta,kota rage kaifin jin haushinsa da rashin jituwar dake tsakaninsu
"Sannu a hankali kina qara gama inajinki cikin zuciyata da gangar jikina,hakan yana yiwa ummi dadi,amma takan kwabeni kan...nayi a hankali,kada kulawar da nake baki tasa ki sangarce,saina fara sanya lura da nutsuwa,a sannan sai na lura da kin fara tabara saboda gata da kike samu daga wajen hajja itama,duk gidan kece ta gaban goshinta fiye da kowa,saboda sunanta da kikaci,sannan kuma cikin jikokinta kinfi kowa wuni wajenta,tunda jima sashenta shine wajen zamana a yawancin lokuta.


"Lokacin da kika fara girma a sannan na zama saurayi" saita kalleshi,murmushi ya subuce mata,saboda fadar hakan da yayi ya tuna mata da abubuwa masu yawa,ta kuma gane dai dai lokacin da yake nufi din,shima murmushin ya sake mata mai sanyi sannan yaci gaba
"A lokacin na fuskanci kaf cikin sa'anninki da tsararrakin kin fisu tsiwa.....kafiya...rashin tsoro da kuma taurin kai,kuma kamar hakan ya faru ne saboda kulawa da hajja ke nuna miki,kinsan dalilin da yasa na aje soyayyarki?,wanda ya zama musabbin da har yau babu wanda yasan ina sonki?" Kai ta girgiza a hankali cike da daukin son jin ci gaban labarin
"Abu na farko da ya sanya naji ya cancanci na ajeshi shine ummi....ummi na nuna miki qauna da soyayya qwarai,hakanan ta azani a matsayin yaya a gareki,wanda ya isa da duk lamuranki,ya isa ya yanke hukunci cikin rayuwarki fiye da sadiq.....sai nayi tunani a karan kaina,matuqar naci gaba da sonki har aka kai sanda zaki sani koki fahimta....to ya zamana babu me tsawata miki kenan kan kiyi koki bari?,idan har na aureki kenan babu sauran wanda zai dinga taka burki akan al'amuranki?,komai zakiyishi yadda kike so?,hakan zaiwa ummi dadi?,ko kuma zaifi mata dadi idan naci gaba da tsaiwa kan rayuwarki ne?.....hukuncin na aje din shi nafi ganin dacewarsa,saboda haka na ajjiye dukkan wata soyayyarki da nakeji a cikin raina,na shiga treating dinki kamar sauran,na kuma qara matsa lamba fiye da baya,abunda ya kuma sawa naji na gamsu da hukuncin da na yiwa kaina,sabon suna da suka miki inna wuro,uwar masu gida ko?,hakan na nufin kiyi abinda kikeso,sannan lokaci qalilan daga dan fara tasawarki samari suka yiwa rayuwarki caaaaaa.....naso hajja a lokacin ta yarda da tsarin da naso kafawa a kanki amma fur taqi,saboda tana ganin na fiya matsantawa,bana duba maraicinki.....kinsan wani abu?" Saita girgiza kai a hankali,labarin da yake batan yana mata dadi sosai
"A duk sanda wani yazo ya kuma yaudareki ya gudu.....na fiki jin ciwon faruwar wannan,nakan jima ina jin raina yana baci,duk da nakanji kishi,nakanji bacin rai duk sanda kike tsaye da wani da sunan saurayi,to amma sai zuciyata ta gayamin,tunda ka aje soyayyarta ka zabi bata kariya,dole zuciyarka taqi ji taqi gani,dole ka daure ka zama jajirtacce,ka fuskanci dukkan wani qalubale,na karbi wannan magana,na kuma sake jaddadawa kaina hakan,dalilin da yasa na karbi zahra takwararki kenan,na soma nazartarta da halayyarta....."sai yadan tsaya yana aje numfashi idanunsa kan zahran yadda ta nutsu tana saurarensa tana kuma fahimtarsa
"Am sorry to say....tana da haquri....tana da sanyin hali,uwa uba nutsuwa da kamewa,sannan kuma sunanku daya,wadan nan dalilai sune kadai suka sanya na miqa mata wuyana,saboda nasan wadan nan halaye zasu dai dai da tawa dabi'ar da halayyar,zatona da hasashen saiya zama gaskiya,ta fahimceni fiye da yadda na zata,ta kuma banbance abinda nakeso da wanda bana so,a hankali sai zuciyata ta fara samun nutsuwa da sukuni,na kuma gamsu zahran ta dace dani,saidai duk da haka baki fita daga zuciyata ba....sau tari nakan tura mata saqo wanda a zahiri sanda nake rubutashi dake nake,saidai nasan cewa koda baki sani ba kai tsaye,kuna karbar wayarta,kuna kuma shiga inbox nata,idan akayi katari kika karanta to kamar na rage wani nauyi dake zuciyata,na kuma isar da saqona,don yawancin lokuta tana gayamin yadda kike nuna zallar mamaki idan kikaci karo da daya daga cikin saqonnin dana tura matan.....bazan boye miki ba....nayi missing zahra'u,na kuma shiga tashin hankali na haqiqa sanda na rasata,har nakejin ma kamar bani bane....kamar zan zauce....na jima....na jima ina dorawa kaina alhakin mutuwarta,saboda ta rasu ne a sanda naje makaranta ganinta,da wani yammaci,na dawo daga gwambe,na tsaya ta wudil ganinta,saboda munyi waya tun ina hanya.


"Sanda na shiga makarantar na sameta shuru,kamar irin anyi hutu dalibai sun kokkoma gida,to amma nasan ana tsaka da zangon karatu ne,ba lokacin hutu bane,waya na daga na kirata da zummar bata mamaki,don batasan da zuwa na ba,na gaya mata inda nake tsaye,cike da zumudi da mamaki tace gata nan fitowa,saina maida wayar aljihuna ina duban inda nake tsayen,wajene mai yalwar bishiyoyi dogaye da kuma tarin ciyayi mai tsaho,tunda nake zuwan mata makarantar lokaci zuwa lokaci bamu taba tsaiwa a wajen ba sai ranar,ina cikin karantar yanayin wajen naga bullowarta ta gefena,kamar kowanne lokaci cikin hijabinta,tana tafe tana murmushin ganina,saina bata dukka hankalina harta qaraso.....
"Me ya faru yau naga makarantar taku yau so silent" tambayar dana fara mata kenan
"Wallahi tun jiya da aka samu fitowar macizai ne,sai kowa ya tsorata ya lazimci zaman daki,don yau ko lactures ma ba'ayi ba" kai na jinjina sannan nace
"Amma da kin gayamin da bazan shigo ba bare na fiddoki daga daki" dariya tayi
"To na godewa Allah da ban gaya maka ba bare ka haramta min ganin fuskarka....komai muqaddarine ai daga ubangiji,koda ina daki duk abinda ya qaddara zai sameni saiya samenin"basai na gaya miki sauran abinda tace min ko nace mata ba...saboda tsaro ba don tsoro ba" ya fada yana murmushi,itama murmushin tayi tana girgiza kanta,idanunta a kanshi,ajiyar numfashi yayi
"Yau soyayya ta sani dogon magana.....a taimakamin da ruwa" hannunta ta sanya ta bude masa gorar ruwan sannan ta ajjiye masa,ya dauka a nutse ya soma sha,yana sha yana ajewa yashaqi numfashi har ya gama,ya aje robar yana sauke numfashi tsahon minti daya sannan ya dora.


"Bari na samo maka abun sha a wani kanti nan" ta fada ta soma takawa,da hanzari na tsaidata
"A'ah....ni ganinki kawai nazoyi,bana buqatar ci ko shan komai" kafada ta maqale
"Ban yarda ba....saboda nima irin karamcin nan naka nakeso na koya,saboda haka saina samu ladan baqona" daga haka ta soma takawa ta cikin ciyayin nan tayi gaba,a cikin zuciyata inason tsaidata amma kamar wanda aka daurewa baki na kasa,inasin ince kada tabi ta wannan ciyayin amma na kasa fada mata,inason ince mata ta tsaya na rakata amma dukka kamar wanda aka daurewa baki duk na kasa fada,ashe ajali ne,ajali ne ya kirata,don batayi wani nisa da idanuna ba naga gilmawar wani abu ta bayanta,na fuskanci maciji ne,idan nayi magana kuma zata iya rudewa,don haka na fara takawa da wani irin hanzari da zafin nama,dai dai sanda ta waiwayo tana kallona,sai fuskarta ta nuna mamakin ganina ina tahowa inda take da mugun gudu,bansan ya akayi ba saijin ihunta nayi ta durqushe cikin ciyayin.


Sanda na isa na sameta riqe da qafarta,ta hada gumi sharkaf tana juye juye,dana dauke hannunta saiga inda macijin ya sareta nan,na bata taimakon daya dace,na riqeta zuwa asibitinsu na cikin makaranta,saidai abun haushin abun takaici basu da allurar kashe gubarsa,raina ya baci sosai,amma ban tsaya biye musu ba,saboda kada bata lokaci ya jawo asarar ran da naketa gudu,na sanyata a mota kawai muka wuto zuwa kano.


"Irin gudun dana dinga tsalawa ni kaina nasan Allah ne kawai yayi motar ba itace ajalinmu ba nida ita gaba daya,tana cure waje daya set din gaba taba murqususun ciwo da azabar dafin daya zuba matan,hankalina rabi ga titi rabi a kanta,qarin abun haushin asibiti manya guda biyu mukaje suma basu da allurar a dai dai lokacin ta qare,sanda muka dauki hanya zuwa asibitin mu a sannan ta kalleni,launin idanunta yana canzawa
"Kayi haquri ya haidar....kayi haquri,kuma naga ranka ya baci,duk abinda Allah ya shiryawa bawa bai isa ya tsallake mishi ba" saita maida kanta ta kwantar,kalamanta suka dagan hankali,na tsaya gefan hanya sanda naga yanayin jikinta ya saki gaba daya.


Nasan a sannan ta mutu don zuciyata tana gaya min haka.....amma idanuna a rufe suke,saina tashi motata da mugun gudun da yafi na dazu na nufi asibitin,saidai abinda nake tsoro dai shi aka gayamin,zahra ta rasu,dafin yaci jikinta yakai inda ba'a so yakai......"saiya tsaya da bata labarin yana duban yadda hawaye ke zuba a idanunta,a wancan lokacin sam batasan yadda mutuwar zahra ta kasance ba,kawai dai tasan saran maciji ne,hakanan tana ganin haidar yaqi daukan qaddara ne kawai,amma data kwatanta mutuwar masoyi ko aboki gaban idanun abokinsa sai taga abun ba mai sauqi bane,dole ya shiga irin yanayin daya shiga din,kasa jurewa tayi,sai tayi qasa da kanta kuka na kubce mata.
23/10/2021, 08:50 - 👍🏻👍🏻: 42


Murmushi ya saki,sannan ya taso daga inda yake zaune,yaja kujera dab da ita ya zauna har gwiwarsa na gogar tata,hannunsa ya sanya ya dago fuskarta gaba daya,saiya girgiza mata kai alamun
"A'ah"yatsansa guda daya ya sanya ya dinga dauke mata hawayen,murmushi kwance saman fuskarsa,har sai daya goge duk wani hawaye da yayi saura,saiya hada goshinsa da nata suna musayar numfashi,qamshin turarensu na gauraya da juna
"A wancan lokacin kinyi fushi....kin nuna kishi saboda ganina da wata balarabiya.....wadda nake ganinta da muni sosai idan na hada da kyakkyawar fusakarki,da kuma yadda zuciyata ta rayu da sonki......ta samu dukka fara'ata ne da kulawa saboda yabonki da tazomin dashi,ta shaidamin tunda taga shigowarmu taji mun burgeta.....tana son qawance dake,dalilin da yasa ta biyoni kenan har kika ganmu tare....saidai kuma a yanzun gashi kina kuka saboda wata da na taba so na baki labarin mutuwarta...me yasa bakiyi kishin xahra ba?" Ta rasa amsar da zata bashi,amma dole duk me imani yaji a yadda zahra ta rasun ya tabashi,ta riga data wuce zahra ba zata taba dawowa ba,kishi da ita tamkar abun nan da hausawa ke kira da ihu bayan hari ne.


Murmushi ya saka yana cewa
"Na fahimta....amma har yau kinsan ban samu makwafin zahra ba?" Cikin mamaki ta zare fuskarta daga nashi tana duban idanunsa,saiya dage mata dukka girarsa
"Eh....ban sake samun wadda tacemin ALIYYU HAIDAR INA SONKA BA,ban sani ba ko baqinjini gareni?" Dariya sosai ya bata,yanayin yadda yayi maganar ma abun dariya ne,sai tasa hannu ta toshe bakinta,yayin daya harde hannayensa a qirji yana qare mata kallo,dariyarta kadai ta sanyashi farinciki shima,gami da saukar masa da nutsuwa
"Aikam saidai idan har shin haidar din ne baiso a gaya masa ba,a iya sanina akwai daruruwa ko ince dubban mata dake ta dakon randa xai basu dama su furta wannan kalma a gareshi....." Tararta yayi ta hanyar watsa hannayensa,kamar zai saki kuka yace
"Ni dukkansu ban gansu ba,bansan da zamansu ba,zahran hajja kawai na sani,kuma ita kadai nake jira da dakon randa zata gaya min hakan....." Itama bata barshi ya qarashe ba yaji saukar kalaman kamar ruwan sama saman zuciyarsa
"Ya haidar kadai nakeso....shi nake qauna har abada" idanunsa ya ware cikin mamaki yana dubanta
"Say it again please"🙏🏽,duk kunya saita cikata,ta maida kanta wani sashen tana murmushi,sai ganinshi tayi ya koma inda ta maida kan nata
"Please....inason na sake ji" wani qwarin gwiwa ya bata daga cikin idanunshi,saita kalleshi sosai
"Ina son ya haidar,ina sonka...ina sonka" gaba daya ya tattareta cikin jikinsa,ya manta ma suna waje ne,sai data ankarar dashi,ta tabbatar da a 9ja suke da tuni sun tara 'yan kallo,da qyar yayi controlling kansa,ya komqa ya zauna dab da ita,muryarsa cike da wani irin softness ya kamo hannunta ya riqe tsam cikin nasa sannan yace
"Hakan yana nufin....kin mallakamin rayuwarki?,kin zama ni na zama ke?,zakici gaba kuma da kasancewa tawa har abada,munyi amanna wa juna zamu rayu da juna duk rintsi duk kin yarda da wannan?" A kunyace kan irin salon kalaman dake fita daga bakin yayan nata,da salon kallon da yake mata ta gyada masa kai,saiya girgiza kai
"Banison body language.....pls ki gayamin da bakinki"
"Amince.....na amince ya haidar" lightly yayi kissing saman hannunta,ya rasa da wacce kalma zai sake magana,kawai sai yaci gaba da riqon hannunta cikin nashi yana kallon kayarsa kamar za'a qwaceta,har sai da tayi waving hannunta saman fuskarsa
"Bansan me zance miki game dani ba,abu daya zuwa biyu kawai bakina zai iya gaya miki,da kanki zaki dinga bawa kanki amsar irin mijin da kikayi katari dashi,sannan ina miki albishir din cewa......zaki shiga sahun matan da sukafi dukkan mata sa'ar miji a duniya" daga haka ya miqe yana riqe da hannunta,itama saita miqe suka soma takawa cike da wani irin xallar farinciki dake yawo dasu a duniyarsu.


Kwan daya tak suka qara suka fara shirin dawowa,ya bata dama ta siya dukkan abinda take da buqata,siyayya me yawa da batasan me za'ayi dasu ba.


Kamar yadda suka tafi tare haka suka dawo,sun tadda 'yan Tarbarsu danqam suna jiransu,family ne mai cike da hadin kai da qaunar juna,babu wani bambanci da xaka gani tsakaninsu.


Tun a airphort din ta ankare da yadda 'yan gidan nasu keta gulmarta ita da ya zakin,saboda duk inda yayi yana maqale da abarsa,baya jin kunya ko nauyi sam,motsi kadan nata idanunsa da hankalinsa yana kanta.


Da zasu tafin bai bar kowa ya shiga tashi motar

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login