Showing 51001 words to 54000 words out of 121250 words

Chapter 18 - ALKIBLA complete

Start ads

24 Aug 2025

454

Middle Ads

takai bakin qofa ta waiwayo
"Waye haisam?" Tambayar data daurema zahra kai
"Haisam kuma?" Zahran itama ta maimaita sunan ta sigar tambaya wa hajjan
"Eh shi" nazari kadan zahra ta fada,tafi kowa sanin cewa ta jima da yiwa kanta shamaki da duk wani da namiji bare tace ko yana da alaqa ne da rayuwarta,don haka ta girgiza kai
"Bansanshi ba hajja" kai ta jinjina
"Bari yayankun ya dawo" bin hajjan kawai tayi da kallo saboda ta kulle mata kai,waye haisam din?,kuma meya hadinsa da yaa haidar?,data kasa canka saita tattara tunanin duka ta watsar,koma waye kuma koma.meye matsalarsu ce,itakam ta jima sa cire sabga ko sha'anin maza daga tsarin rayuwarta,hakanan ta dade da ciresu daga cikin jerin matsalolinta da zasu dameta.


Tun randa ta dawo a daren hindatu ta nemeta basu ganta ba,washegari tazo gidan,ta gaya mata lafiya lau,kada ta damu karsu nemeta,zata nemeta da kanta.


Tunda hajjan ta fita take kwance tana saqa tana warwara kan yadda lamarin zai warware mata cikin sauqi ba tare da wata matsalar ga sake sawo kai ba,tunda tana fatan wannan ta mutu,a haka har bacci yayi nasarar yin awon gaba da ita.


*_ABINDA KA SHUKA_*



A nutse take tafiya kan hanyarta zuwa gida,tun daga nesa take hango mutum biyu,daya a tsugunne daya a tsaye bisa saman kansa,haka taci gaba da tahowa tana matsar inda suke harta qaraso dab dasu,sai a sannan taga fuskokin mutum biyun sosai.



Na tsugunnen abdulyassar ne,na tsayen kuma auwal ne,sam babu alamu na walwala ko farinciki kan fuskar abdulyassar din,face ma uban gumi da yake hadawa,fuskarshi amurtuke sosai.


Kai ta dauke zata gotasu taji an riqe hijabinta,saita juyo da sauri,auwal ne,ya soma magana cikin zallar damuwa kamar zaiyi kuka
"Haba zahra....yanzu kina ganin abdulyassar haka zaki wuceshi ba zaki kulashi ba?,don Allah ki dawo ki tambayeshi me yake damunsa?,wallahi kinga munyi munyi ni da hajiyarsa ya gaya mana abinda yake damunsa yaqi cewa komai tun daxu,babu yadda bamuyi dashi ba,munyi munyi ma ya tashi daga nan amma yaqi" hijabinta ta fincike daga hannun auwal din tayi gaba abinta,tana jin auwal din na kiranta,tana kuma hangen yadda abdulyasar din yaci gaba da zama awajen.......
(Exactly haka yarinyar tayi mafarkinsa kwana biyar da rasuwarshin,na manta ban kawoshi tun a sannan ba saboda ajizanci na mantuwa).


Firgigit ta farka daga baccin daya dauketa din,ambaton sunan Allah ta shiga yi tana tunawa daya bayan daya dukkan abinda ya faru cikin mafarkin,a yanayin da taga abdulyasar din yana cikin damuwa babu ko shakka,saita miqe ta soma cire kayan jikinta ta shiga bandaki tayi wanka ta fito ta shirya,har a sannan mafarkin na maqale cikin ranta,saboda haka koda ta fito falo ta zuba abinci tana ci hajja ta soma baiwa labari.


"Zai iya yiwuwa haqqinku ke tambayarsa,ki yafe masa idan kinsan a baya baki yafe masa ba" baki zahran ta tabe
"Ni na yafe masa mana hajja,yaji da haqqin sauran da bansan adadinsu ba,da marasa zuciyar tausayi da zasu kasa mancewa bare su yafe masa".


Tana kammalawa tace bari taje wajen umminta,don tunda tazo bata je wajenta din ba,saidai yanayin yaddata amsheta,da yadda ta amsa gaisuwarta ta ya daga mata hankali ya bata mamaki,ta kuma shiga wasu wasin anya kuwa ba wani abu taji kan case din daya dawo da ita gida ba?,tunda haidar din mutuminta ne,to amma ita kanta tun ranar bata sake ganin haidar din ba,asalima kamar taji suna waya da hajja na masa fatan alkhairi kamar ma tafiya yayi wani waje,wannan abun saiya sake sanyata a rudanin data fita,ko sansa ta koma sassan hajjan saita kasa sukuni.


*_BA ZATA!_*
_baya da ฦ™ura_


Masu karatu muje zuwa
_Da gaske iya qarshen matsalar kenan wa zahra???_ ๐Ÿšถ๐Ÿพโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿพโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿพโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿพโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿพโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿพโ€โ™€๏ธ

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_

_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_

_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_

_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_

_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._

_MUNA KUMA SAYARWA AKAN โ€˜DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_

_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_

_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_

_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_

_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _

_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234ย 803ย 081ย 1300/+234ย 808ย 540ย 5215_

_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._

_RANO NET..!!!!_
23/10/2021, 08:42 - ๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป: 19
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_

_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_

_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_

_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_

_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._

_MUNA KUMA SAYARWA AKAN โ€˜DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_

_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_

_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_

_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_

_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _

_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234ย 803ย 081ย 1300/+234ย 808ย 540ย 5215_

_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._

_RANO NET..!!!!_
_____________________________



*_BA ZATA!_*
_Baya da qura_



Tana tsaka da sallah sau biyu inna gaje na leqowa dakin da zummae ganin ta idar din?,a zuwa na uku ne ta sameta tana zaman tahiya,saita tsaya tana dakon zahran har zuwa sanda ta kammala ta kuma yi sallama.


"Uwar masu gida anason ganinki a falo" inna gajen ta fada tana duban zahra,saita saki addu'ar da takeyi tadan ja tsaki
"Anty uwani ko?,ni sam banison zuwanta gidan nan wallahi,haka kawai baka taka mata ba baka zubar mata ba ta saka maka idanu" kai inna gaje ta kada
"Ba ita bace,hajja ce....da alhaji babba" haka kawai taji wani faduwar gaba da batasan meye dalilinta ba,haka nan sai jikinta yayi sanyi
"Tom,ina zuwa" ta fada tana qarasa addu'o'inta ta shafa sannan ta miqe.


Tun kafin ta qaraso gabanta ke dukan uku uku saboda fuskokin data hanga cikin falon,abba babba abba yusuf,abban tsakiya haidar da kuma hajja,sai umminta daga gefe
"La haula wala quwwata illa billah" shine abinda take maimaitawa,take dukka qafafunta sukayi wani irin sanyi kamar ba zasu iya daukar gangar jikinta ba,hakan yasanya tafiyarta ta koma slow harta qaraso cikin falon.


Cikin girmamawa kamar kowanne lokaci ta gaidasu,suka amsa mata fuskar kowannne babu komai a samanta,ko kuma ace ba zaka karanto wani sauyin yanayi tattare da ita ba.


Shuru ne ya biyo baya na wasu sakanni,sa'annan abba babba ya soma magana
"Zahra'u..."
"Na'am abba" ta amsa cikin sanyi da raunin murya
"Mahaifiyarki tazomin da wani al'amari wanda yake da girma a wajenmu,bayan na saurari dukka bayananta da kuma hukunci da matakin da take buqatar a dauka.....nayi magana da aliyyu gashinan,na kuma ji duk abinda ya sani daga bakinsa,saina samu hajja na kuma tuntubeta game da lamarin....tayi mana bayanin komai itama,da kuma yadda kika gaya mata,saidai duk da haka mun nemi ta bamu damar yin magana dake,duk da cewa da farko taqi hakan,to a yanzu gamu gaki inna wuro,ina son ki dubi girman Allah ki gaya mana cewa shin da gaske a hotel haidar ya ganki?" Qas tayi da kanta,qwalla na taruwa cikin idanunta,kunyar kalmar takeji kamar qasa ta tsage ta shige,dana sani da nadama na sake cika zuciyarta,ta kasa cewa komai har sai da abba babba ya maimaita tambayarshi,cikin muryar kuka tace
"Eh haka ne abba.....amma wallahi wallahi abba,na rantse da wanda raina yake hannunsa abba ba wani mummunan abu bane ya kaini,munje ne yin karatu nida sauran qawaye na saboda test da muke dasu da yawa a satin....ko sanda ya haidar ya ganni amsar abinci ya fito dani...."
"Ya isa haka,yarinya aita gama magana....idan dukkaninku baku yarda da ita ba,bakuma yarda da abinda tace din ba ni na yarda da hakan,dukkanku na fiku sanin wacece zahra'u....bama ita kadai ba,addu'ar da nake na dare ba rana ina da tabbacin ubangiji bazai wofantar da ita ba,babu wani cikin zuri'ata da xai aikata alfasha da iznin ubangiji"hajja tayi maganar da alamun ranta ya fara baci,ajiyar zuciya abba babba ya sauke,duk da dama zuciyarsu bata taba basu zahra'un zata aikata wata alfasha ba,amma yanayin yadda take magana ya isa ya shaida maka gaskiyar abinda take fada din,hakanan kuma bayanin nata ya sake sanya musu nutsuwa a ransu,saidai dukka ba zasu nuna haka tashin farko ba,dole ne su tauna tsakuwa don aya taji tsoro,don haka abba yusuf ya soma fada sosai kan zuwan da tayi,wanda yace sam bata da wata hujja ta zuwa din,tunda ba tarbiyyar gidan bace,hakanan duk wanda ya ganta akwai kallon da zai mata da kuma yadda zai fassara ta,haka ya dinga fada sosai,saboda kusan duka ya fisu zafi,yayin da kanta ke qasa hawaye wasu nabin wasu.


Itama ummin nata nata kan yana qasa,bata zargin diyarta ko daya,saidai tana da tarin fargaba,tana tsoron zamani,tana tsoron qawaye,tana tsoron gurbacewar muhalli,tana sane da cewa a yanzun tarbiyya ta zama wani abu mai tsananin tsada wanda sai wajen wane da wane ake samunta,tsadar tata taki jallin da hirar wanda ya rabauta da samunta ake,farautar masu ita ake,tsada suke da kuma wuyar samu,tattalinta kuma abune mai hatsarin gaske,wanda idan ka tsira da ita ba tare da wani yayi nasarar fauce maka ita ba to abun ayi maka sambarka ne,tana fargabar yadda diyarta ta kafa tarihin soma karatun gaba da secondry cikin gidan ya zamana ta kafa wani tarihin na daban,tarihin da bata fata ko burin samuwarsa,a kullum kwanan duniya dama takan kwana da tashi cikin fargaba,koda yaushe burinta shine diyarta ya zamana tana gidan nata mijin kamar yadda aka tsara ko kuma aka gina gidan akan hakan,wannan zai fiye mata kwanciyar hankali fiye da ace tana can tana karatu,tunda jarrabawa ta soma samun diyartata bata taba samun nutsuwa ko sukuni na sakan ba,idanunta basa barci,zuciyarta bata hutawa,bakinta baya gajiya da yi mata addu'a ako da yaushe,a kullum takan wayi gari cike da buri da kuma fatan Allah ya fiddo mata da miji na gari,koda kuwa zai zama silar datsewar karatunta,a yanzu kam a wannan bigiren....tana jin ya kamata ta motsa,tana jin ya kamata ta magantu,tana jin ya kamata tayi wani abu da zai sama mata nutsuwa ko yaya ne.

Sai da suka gama fadan sannan sukayi mata jan kunne da gargadi mai qarfi,saida suka gama gaba daya sa'annan umminta da tunda aka fara batace komai ba tayi magana
"Hajja.....yaya(haka suke kiran abba babba tun tale tale,dukka matan qannen nasa
"Na'am halima muna saurarenki"
"Yaya dukkan fada da qoqarin da kukeyi akan zahra'u duk da cewa diyarku ce.....amma ya zama dole ga duk wanda ya gani ya yaba muku...idanma har akwai abinda yafi yabo din kun cancanci samunsa,a yau sau daya tak ina neman wata alfarma....alfarma guda daya da nake fata da kuma burin xan sameta daga gareku" shuru ya dan ratsa kafin abba babban ya bude baki yace
Fadeta halima....in sha Allah ba zata gagara ba"yayi furucin tare da yaqinin haka yake cikin zuciyar mahaifiyarsa hajja,domin halima takai mace,duk inda mutum mai tsananin kawaici kan diyoyin cikinsa da sanin ya kamata yakai takai,suna da tabbacin tunda har yau ta iya buda baki tayi magana to ba shakka lamarin ba qarami bane a zuciyarta.



"Inason a dakatar da zuwan inna wuro makaranta....ma'ana a dakatar da karatunta" sosai zancan ya daki zahra,don bata taba kawowa umminta da bakinta zata nema hakan ba,fitar furucin daga bakin ummin nata ba qaramin razani da gigita ya sanyata ba,domin tana qaunar karatunta a yanzu,qaunar da a baya batayi masa ba,ta damu dashi damuwar da abaya batayi masa ba
"Ba wanda zai dakatar da ita daga karatunta bayan bamu tabbatar da laifinta a kanta ba"
"Don Allah hajja na roqeki to kimin alfarma ta biyu....taci gaba da karatunta,amma da sharadin zata koma bakin karatun nata ne da igiyar aurenta a kanta....." Dif dakin yayi tamkae anyi ruwa an dauke,ga zahra kuwa rudanin data shiga yanzu ya zarta na baya
"Don Allah hajja....kiyimin wannan alfarmar" muryar ummin tata ta sake ratsa shurun.


Dukka wata laka ta jikin hajjan tamkar an zareta,wani irin nauyi da tausayin halimatun ya shigeta sanda take zaune gabanta tana roqon ayi mata alfarma kan diyar cikinta,ayi mata alfarma kan diyar data haifa da kanta,diyat da duk duniya tafi kowa iko da isa da ita,tabbas! Halimatu mutum ce,cikakkiyar mace mai cikakken kunya da kuma tarin kawaici,kawaicin da bata jin baya ga halimatu sai khadijatu mahaifiyar haidar ce kawai za'a samu da irinta tattare dasu,bata taba ba!,koda wasa bata taba nema ko maida hukuncin hajja baya ba a kan zahran,kulkum abinda hajja ta aiwatar ko ta zartar dai dai ne akan zahran,halimatun bata da wani zabi ko nuni dangane da duk wani lamari da ya shafi rayuwarta,lallai a yau din ya kamata....ya cancanta ayi mata itama abinda takeso!,saidai kuma hakan na nufin yiwuwar rugurgujewar ko samun tasgaro ga karatun zahra'un tata,karatun da take da tabbacin a yanzun shine komai na zahra'un,kai.....bata tunanin wannan ra'ayi ko hukuncin halimatu ne,tafi zato da zargin aliyyu shine ya shirya komai ta bakin ummin,ya kuma ja bakinsa yayi shuru,bayan taja kunnensa,ta kuma jaddada da masa buqatarta,lallai itama zata nuna nata qarfin qwanjin,zata nuna nata ikon,kai lokacima yayi da zata cika mafarkin data dauki shekara da shekaru tanayi,lokaci yayi da zata cika burinta,lokaci yayi da baraka guda daya data rage zata dinketa tsaf!,koda hakan na nufin rikici da tashin hankali daga kowanne gefen.


Cikin wani irin amo da salo daya tabbatarwa da duk wanda ke dakin da gaske hajja ke magana,da gaske hukunci take zartawa mai zubin KAIFI DAYA!,MAGANA DAYA!,cikin salo na umarni kai tsaye tace
"Kin wuce ki nema alfarma akan diyarki halimatu,baki ma taba nema ba sai yau,kuma zaki samu da izinin Allah,zahra ba zata koma makaranta ba saida igiyar aurenta akanta....zahra zata koma makaranta cikin satin nan a matsayin matar aure....a matsayin matar Aliyyu,rana ita yau nakeson inga zahra'u a matsayin matar aliyyu!" Takai qarshen zancan tana sauke idanunta kan abba babba,wanda hakan ke nufin cewa tana da buqatar ya zartar da umarnin data bayar kenan.


Da wani irin sauri aliyyu ya dago da kanshi,wanda tunda aka fara dambarwar wayarsa ke hannunsa yana sarrafata cikin qwarewa,kanzil baice ba sai a yanzu da yaji fitar furuci mai nauyi daga bakin hajjan,furucin da ko cikin duniyar mafarki bai taba hakaito kwatankwacinsa ba,sai yaji sam hukuncin ma bai samu zama a kwanyarsa ba,lafazin nata kamar wani wasa ne ko raha a kunnuwansa,haka yaci gaba da gayawa zuciyarsa,saboda haka saiya sake rusunar da kansa yana ci gaba da danne dannen wayarsa abinsa,saidai kuma wannan karon sam zuciyarsa taqi yarda ta bashi hadin kai yaci gaba da abinda yakeyi din,gaba daya ta karkata ga sauraron abinda ke gudana a falon.


Ta fannin zahra kuwa numfashinta ne yayi qaura daga gangar jikinta na wucin gadi,tana son kiran sunan hajja ta kasa,tana son roqon hajja alfarma amma ta kasa,tana son tace a'ah amma dukka ta gaza aikata hakan,har zuwa sanda hajja tace
"Kai ka bata zaki....kuma kaine zaka gyara....dolenka" furucinta na biyu daya sanyashi shiga taitayinsa,ya kuma sake alamta masa hajjan fa da gaske take,abinda take fada da gaske takeyi,saiya aje wayarsa gefansa,karon farko shima da yace
"Me na bata hajja?,me nayi ni din?"
"Duukkan abinda ke faruwa anan kaika bazashi har ya kawomu ga zama a nan...."
"Bashi bane hajja.....kada ki masa hukunci ba bisa laifinsa ba,haidar bai gaya min komai ba,kuma ya bani mamaki daya boyemin...tunda ba don kunnuwana sun jiye min ba haka zai rufeni?,bayan shine mutum daya tilo cikin matasan gidan nan da yake da dabi'ar tsawatarwa da tsaiwa tsayin daka kan halayyar qannensa,don me zai watsar akan zahra'u?.....na roqeki hajja ki soke qudurinki.....kiyi haquri,amma zan iya cewa ba'a kyautata masa ba matuqar akace shine wanda zai aureta"
"Halimatu.....indai na isa a gidan nan,indai nina tsugunna na haifeku(ta fada tana nuna su abba yusuf)to rana ita yau inna wuro zata zama mata ga zaki....ku riqe wannan"
"Hajjaaaaa!" Zahra da wannan karon ta samu nasarar fisgo kalaman bakinta ta furta cikin wani irin rauni,hawaye na sauka saman kuncinta
"Don Allah hajja.....don Allah kiyimin kowanne irin hukunci amma banda wannan....wannan din ba gata bane hajja......shine hukunci mafi

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login