Showing 42001 words to 45000 words out of 121250 words

Chapter 15 - ALKIBLA complete

Start ads

24 Aug 2025

465

Middle Ads

ta fahinta,don haka taci gaba da binta a baya suna tafe zafin rana na dukansu.


Basuyi nisa ba suka soma jin hirar wasu mata biyu a bayansu
"Kai mutuwa....mutuwa masu gari,babu ruwanta da babba ko yaro,tsoho ko tsohuwa kawai dauka take"
"Hmmm....kedai Allah yasa mu dace,mutuwa ma irin wannan ta abdul ai tafi ratsa jiki da daga hankali,mutuwar saurayi?,sati biyu kacal da kai kudin aure ashe ba za'ayi auren ba,babu ma abu mafi tausayi irin yarinyar daya kaiwa kudin,kamar zata shide wallahi abun tausayi"
"Ai da tausayi,Allah yasa mu cika da imani".


Cak zahran da hafsan duka suka tsaya,a sace zahra ya waiwaya ta dubesu,dukkansu babu wanda tasan fuskarsa a cikinsu,suna tsaye sukazo suka giftasu,da alama ma basu ankara da tsaiwarsu ba,sukayi gaba suna ci gaba da hirarsu.


A zafafe zahra ta soma takawa tana koma zuwa layin da suka baro,hafsa ta cafki hannunta
"Ina zaki?"
"Zanyi magana da auwal" daga haka ta zame hannunta ta koma.


Suna nan inda ta barsu,harda qarin wasu abokan nashi wadanda yakanje dasu lokaci zuwa lokaci,dukkansu tasan fuskarsu sunsan fuskarta.


Auwal din ne ya soma ganinta,saiya miqe,kafin ya tarbota harta iso wajen,cikin tsananin nuna jimami yace
"Sannu zahra....ashe kin iso,ya mukaji da wannan abu daya samemu?" Dukka sauran abokan sai suka soma yunqurin yi mata gaisuwa,a qalla sunkusa su biyar,hankalinta ta maida kan auwal
"Zuwa nayi na maka godiya kan zalunci da munafuntata da kukayi,na gode sosai,ubangiji ya saka da alkhairi" cikin yanayi na rudewa ya soma magana
"Munafuntata kamar ya?" Tana ji a ranta baqincikin da datake ji ba zata iya rufeshi ba
"Da kun gayamin kai da abdulyassar ban dace dashi ba,da kun gayamin yakai kudin aure...dana fahinceku na kuma rabu dashi ta sauqi bawai ta irin wannan hanyar ba".


Sai auwal din ya dora hannu saman ka yana cewa
"Kai innalillahi,Allah ya tsinewa munafuki.....wai mutum ma na qarqashin qasa,ko awanni biyu bai cika ba amma ba zasu bar gawarshi ta huta ba....to duk wanda ma ya gaya miki qarya yake,kawai 'yan hada husuma ne wadanda basaso a zauna lafiya,masu zuwa lahira da qoqon dambu....ko ba haka bane mansir?" Ya fada yana maida dubansa ga daya abokin nasa wanda daga auwal din sai shi a wadanda abdulyassar din yafi zuwa dasu
"Haka yake....hakane auwal"
"Baya ga key holder din dana gani!" Ta fada a zafafe
"Au....wannan fa friends ne suka hada suna tsokanarsa saboda yadda sukaga ya tsani yarinyar....just for fun akayishi,shine mutane suka sauya zancan?"
"Dakata!" Ta fada da sauri tana daga masa hannu ganin yanason raina mata hankali
"Dukkan abinda bawa ya shuka shi zai girba,kaje....na barku da Allah" da haka ta juya ta soma barin wajen,tana ji abokan nasa na qwala mata kira hankali tashe,saidai babu wanda ta waiwaya ta kalla bare ta koma,saima ta tsaida musu napep ta haye hafsat tabi bayanta.


Wani yawu mai tauri take hadewa cikin motar,gaba daya ji take zuciyarta ta bushe ta qeqashe,lamarin maza ya fice mata fit a ka,me yasa ne basu da *ALƘIBLA?* me yasa kowanne da kalar zaluncinsa ga 'ya mace?,saboda muna da rauni?,saboda ba zamu iya aurar da kanmu ba saidai a auremu?,me yasa mazan zamanin nan suka zama fitina ga rayuwar 'ya'ya mata?,me yasa duk wani bala'i,shiga ha'ula'i da tashin hankalin mace mafi akasari kan ɗa namiji ne?,baki auren ba baki huta ba,kinyi auren baki huta ba,sai yaushe diya mace zata hutama ranta?,ba a iya kanta ba,akan mata 'yan uwanta da yawa taga irin hakan,me yasa suka maidashi kamar anko ko gasa,sun maidashi abun kwalliya,YAUDARA!....shin basa tunani ne?,basa tunanin cewa suna wataran iyayen wasu ne?,basa tsoro da fargabar kada abinda sukayi a fanshe kan diyoyinsu wadanda basuji ba basu gani ba?,inda ta godewa Allah....babu wanda ta saidawa mutuncinta,babu wanda yayi nasarar tarwatsa mutuncinta,yau inda acw ta aikata hakan ta tabbatar nadama da dana sanin da take ciki ta zarta ta yanzu,sai Allah yasa bata watsar da tarbiyyarta ba,bata bari rudi da zaqin soyayya ya jata ta aikata babban kuskure mai tarwatsa rayuwa ba,kuskuren da bashi gyaruwa har abada, yanzu kam takai qarshe.....takai maqura,enought is enough....ta dauki iya abinda zata iya dauka,ya isa haka!,ya isa!......


Ire iren wadan nan tunane tunane su ta dinga yi har suka qaraso gida,wanda ko tsaiwa a biya mai napep din kudinsa batayi ba,batasan ya suka qarke da hafsat ba.


A falo ta tadda hajja tana karyawa,bata bi ta kanta ba ta wuce dakinta da wani irin sassarfa,gaban mudubi ta tsaya,ta cire hijabi ta kuma cire doguwar rigar jikinta,daga ita sai vest da under wear,kanta take qarewa kallo lungu da saqo,sai a sannan kukan ya qwace mata,da gudunsa kuwa kukan yazo,kukan da zaka tabbatar da cewa yana fita ne daga tsakiyar zuciya,yana kuma tafe da wani irin qunci da baqinciki
"Me na rasa?,meye bani dashi?,meye illata!,ku gayamin!" Ta fada a fili hawaye na gudu tana kuma tambayar kanta da kanta.


Ji tayi an rungumeta,hajjanta ce
"Me haka zahra'u?,ki nutsu mana,kita maimaita Allahumma ajirni fi musibaty,wa akhlifni kairan min ha" da muryar kuka ta kama addu'ar tana ta maimaitawa har ta soma samun nutsuwa,don haka hajjan ta zaunar da ita gefan gadon tana shafa bayanta kadan kadan tana tayata nanata addu'ar.


*_wajen daya kamata a tsaya mu fafata kan wanda yafi iya yaudara cikin samarin nan uku yayi,da kuma matakin daya kamata budurwa ta dauka idan ta samu kanta cikin irin wannan situation din,idan kuna da buqata ku sanar min domin bude grp musamman saboda haka,karku manta,dama munce akwai fafatawa da tattaunawa kan mai zafi kan kowanne littafi,ma'assalam_*
23/10/2021, 08:41 - 👍🏻👍🏻: 16

*KIJI TSORON ALLAH☝🏾☝🏾☝🏾☝🏾,kada ki dauka ko kiyi amfani da kayan da ba naki bane,ba kuma mallakinki bane!*




A hankali aka turo qofar dakin,hafsat ce jiki a matuqar sanyaye,idanunta kan zahran,zuwa sannan kukan da takeyi ya ragu sai ajiyar zuciya
"Zahra.....sawwama nason magana dake,tana falo"
"Sawwama?" Ta tambaya tana kallon hafsat
"Eh sawwama ta layin shago tara" ta ganeta,duk da babu alaqa tsakaninsu,saidai gaisuwar mutuci saboda babu tazara sosai tsakanin unguwanninsu
"Lafiya?" Zahran ta tambayi hafsan tana kallon yadda yanayin fuskarta ta sauya fiye da dazu
"Daga gaisuwar gidansu abdulyassar take" shuru tayi yana juya maganar,to meye ya faru?,saita miqe kawai kai tsaye ta fice zuwa falon.


Kallo daya ta yiwa sawwaman tasan cewa lallai tasha kuka itama ba na wasa ba,gaba daya idanunta sun tasa har lebunanta,zahran ta qarasa a hankali ta zauna gefan sawwaman
"Ashe kema kinsan abdulyasar?" Kai ta iya jinjinawa kawai ba tare da tace komai ba,saboda wano ciwo dake taso mata a qirji
"Ashe bani kadai bace?....bani kadai ya yiwa haka ba?" Maganar da taja hankalin zahra kenan da ta daga kai ta dubi sawwaman,kallon da take mata yake nuna tana da buqatar qarin bayani
"Abdul yayimin alqawarin aure....infact ma yau sati daya da tura magabatansa gidanmu,amma abun mamaki sai nakejin yau sati biyu dakai kudinsa wajen wata walida....baya ga haka ashe kema...." Hannu ta dagawa sawwama murmushin takaici na fita daga fuskar zahran,a take wasu kalamai da abdul din yake yawan gaya mata suka dinga dawo mata aka tar kamar a sannan yake furta mata su
"Duk duniya akwai wata bayan ke?,duk duniya akwai wata diya mace data isa ta rabani dake?,me kike fargaba a kaina?,akwai wata mace data isa na bata lokacina akanta na tafi zance wajenta idan bake ba.....zahra duk kyan mace....duk ajinta....duk gayunta saidai tabi bayanki"
"Duk abinda kika fada haka ne....hakane sawwama" kuka sawwaman ta fashe dashi,wanda da alama zallar baqinciki da bacin rai yake cin zuciyarta
"Abdul ya cuceni,ya zalunceni...abdul..." Da sauri hajja data fito tace
"Kiy shuru karki sake cewa komai,kuyi haquri ku masa addu'ar Allah ya yafe masa kuskuren daya tafka" miqewa zahra tayi ta koma daki don ba zata iya ci gaba da tattauna wannan maganar ba,hajja da hafsat sune suka sallami sawwama.


A ranar ko kusa ko alama bacci bai gitta ta ba bare ya samu nasarar daukarta ba,duk juyin da zatayin abdul din take tunawa,kalamansa da salon yadda yaso sabuleta daga rayuwarta ta wata siga mai masifar ciwo,shima so yayi yayi mata irin yadda nasir da nuraddeen sukayi mata?,so yayi ya karya mata zuciya?,yayi gutsi gutsi da ita?,don ta tabbatar a yadda ta bawa soyayyar abdulyasar amanna da Allah ya barshi da ransa hakan ya faru babu tantama zata iya rasa lafiyar zuciya,saita goge hawayenta ta miqe ta zauna tana gayawa kanta,wala'alla Allah ne ya sota da rahama ya daukeshi,ubangiji baiyi zataga wannan baqinciki da bacin ran da tashin hankalin ba,amma lallai ta yanke tsammani,hakanan ta debe haso daga dukkan lamarin maza,abun ba qarami bane,sha'aninsu ya wuce tunaninta.


Kwanyarta tana iya tuna mata sanda abdulyasar din yake musanyan waya da ita,ya aje mata wayarsa yacw ta bashi tata aga wanda yafi gaskiya a cikinsu,aga wanda saurayi ko budurwa zasu kira,ashe a sannan wala'alla sabon layi kenan yake sakawa?,ko layin da ba'a sanshi dashi ba?.


Sannan tana iya tuna sanda yakan rufeta da masifa cikin zallar kishi,yana cin alwashin duk randa yaga wani ya kulata ko ta tsaya dashi,ba shakka saiya masa diban karen mahaukaciya ya sadashi da qasa ya take wuyansa,kome zai faru indai a kanta ne saidai ya faru,tana iya tuna sanda yake tsaidata ya rakata makaranta ko wani guri da kansa,tana iya tuna sanda fafur ya hanata shiga kasuwa,ashe duk bogi ce?,qarya ce?,ashe bayan ita hadda sawwama wadda yakai magabatansa?,anya ko magabatan gaske ne bana haya bane?,anya kuwa bana bogi bane?,saboda babu iyayen arziqin da zasuje maka maganar aure wannan satin,wani satin kuma suje maka gidan su wata da saninsu,to bayan ita da sawwama mata nawa ya yaudara?,wannan Allah ne kawai masani.


Cikin daren ta yiwa kanta da kanta fada,ta gayawa kanta cewa da batasan abdulyasar ba,kafinshi kuma wasu sun yaudareta,ta kuma ci gaba da rayuwarta ba tare da komai ya sameta koya sauya ba,hakanan a yanzun ma zataci gaba da rayuwa babu shi,zata dora daga inda ta tsaya,ba zata bari damuwar wanda baisan da damuwarta ta dameta ba,damuwar wanda baya doron duniyar ma gaba daya,kai koda yana raye.....dukkan namijin da zai miki haka bai cancanci ki damu kanki saboda shi ba,saboda ya nunawa duniya cewa u r a zero behind decimal point,baki da wani amfani a tare dashi,keda babu duka daya,don me zaki damu da irin wadan nan?,me yasa irin wannan namijin zaki dora damuwarki a kanshi?,a daren,a kuma sannan ta yiwa kanta alaqawarin cire dukkan damuwar wani abun banza namijin daya yaudareta,ta kuma dasawa kanta takunkumin tserewa soyayya da kuma nisantarta bakin iyawarta,har sai taga abinda ya turewa buzu nadi,ko kuma abinda alqalamin qaddararta ya rubuta ya tabbata.


Sosai hajja tayi mamaki washegari da taga sakewa a tare da zahran,wanda sam batayi tsammamin ganin hakan tattare da ita ba,bata tanka mata ba sai taci gaba da biye mata,can qasan ranta tausayin zahran yana ratsata,duk inda ta gifta sai ta bita da kallo,haqiqa ta hadu da jarrabawa mai tsauri da wahala,amma kullum fatanta ya zama nasara ce a rayuwarta.


A irin hakan zahran ta lura da kallon da hajjan ke mata,ta fahimceta sarai,amma sai tayi murmushi
"Wai ya kiketa kallona tsohuwa?,kodai na miki kyau ne?" Kai hajjan ta gyada sannan tace
"Ina miki fata da addu'ar wannan ya zama karonki na qarshe da zaki sake fuskantar qalubale irin wannan kaf rayuwarki" saita rausayar dakai kawai,cikin zuciyarta tana amsa da amin.


Wannan karon ma umminta kasa jurewa tayi sai data titsiyeta
"Innawuro.....ki gayamin gaskiya idan akwai wani abu a qasa...."
"Wallahi ummi bansan komai ba,bansan meke faruwa ba" shuru ummin ta danyi na wasu mintina,sannan a sanyaye tace
"Kin tabbatar ba saida musu mutuncinki kike ba?" Sosai maganar tayi ma ummin kanta nauyi da zahran,saidai ya zamana dole ta yiwa zahran wannan tambayar,saboda uwa bai kamata a muhallin irin wannan da kike bincike da qwaqwwafi ba ki dinga boye wasu maganganun,wai don kawai kunya da nauyinsu,kan zahran a qasa tana fitar da qwalla tace
"Allah ya tsareni ummi,ubangiji ya tsare miki ni,kuma har abada bana fatan ya bani ikon ko damar da zata sanya nayi fatali da tarbiyyar da kuka gine ni a kanta,wallahi wallahi koda tunanin aikata hakan bai taba zuwa kaina ba bare na aikata ummi,ki yarda da 'yarki" nannauyar ajiyar zuciya ta sauke
"Na yarda dake.....ba kuma wai ina zarginki bane,amma ya zama dole nayi aikina na uwa na bincika da kyau,na tabbatar addu'ar da kullum ba dare ba rana da nake miki keda 'yar uwarki dama sauran dukkan yaran dake gidan nan ba zata fadi qasa banza ba,na yarda jarabtace kamar yadda take rubuce a rayuwar kowanne musulmi.....kici gaba da addu'a,kada dimuwa ko zafin jarrabawa yasa ki kasa cin ribar haqurinki....karbi wannan" ta fada taba miqa mata wata doguwar takarda,addu'o'ine a rubuce a cikinta,addu'o'i ingantattu masu ma'ana,wanda suke dauke da kalmomi masu girma da tsarki gami da kambama ubangiji,wadanda su kadai sun isa sanya nutsuwa a zuciyar bawa da samun biyan buqata daga wajen ubangijin talikai.


Godiya ta yiwa ummin sannan ta baro sashen,tun a ranar sata soma addu'o'in ta dinga jin sukuni da nutsuwa yana ratsata,ta sake jin zuciyarta wasai kuma fes,haqiqa ubangiji yayi gaskiya da yace ku saurara,da ambaton Allah kawai zukata suke samun nutsuwa,lallai babu abinda yakai ambaton ubangiji sanya nutsuwa a zuciyar mai damuwa.


Cikin satin ta hada kayanta ta koma bakin karatunta,tunda komai ya daidaita an koma makaranta,ta kuma fuskanci karatunta da kyau,ta watsar da duk wani damuwa da hayaniyar soyayya,babu wani da namiji da take tsaiwa ta kalla sau biyu ma bare ta saurari kalaman bakinsa,duk ta musu kudin goro gaba dayansu.


*_BAYAN WANI LOKACI_*


Zaune take cikin dakin kwanan dalibai wanda ya zama mallakinsu ita da hindatu batula da jannah,yayin da nadiya da farida suke daki daya daura da nasu suda wasu mutum biyun,to amma idan baka sani ba zaka zaci dukkansu daki guda suke,saboda kusan komai a nan dakinsu zahran sukeyi,hatta da abinci daya sukeyi,duk da basi fiya ma girma abinci ba,saidai suyo takeaway,idan kaga girkakken abinci to aikin zahra ne,sau tari sukan mata qorafin tana walahar da kanta da wani girki,ta bari kawai suyo takeaway suci,takan ce
"Ni ban saba bafa,abincin da zaka girka da kanka yafi albarka,sannan kayan anincin da nazo dasu daga gida saina jibgesu su lalace?,ko kuma na maidasu gida idan an tambayeni nace qawaye suna siya min ina ci?" To su dinma idan ta dafa kowa dafifi yake wajen ci,saboda ita din ba baya bace wajen iya girki.


Kamar yau dinma dakin nasu cike yake da hayaniyar 'yammata,kasancewar suna cikin ranakun qarshen mako ne,kuma wannan karon kusan dukkaninsu basuje gida weekend ba,ita zahra saboda CA da zasu fara,kuma a satin zasuyi kusan gudan hudu,shi yasa taga gwara ta zauna waje guda tayi karatu sosai.



Yau dinma ita ta dafa musu abincin,kowa yaci ya qoshi,da suka kammala saita taja takardunta da system dinta saman gadonta ta barsu nan tsakar dakin kan carfet din da suka malale dakin dashi
"Yar allazi boko" taji su suna tsokanarta,bata kulasu ba sai murmushi kawai datayi taci gaba da karatunta,batason ta tsaya tankasu su dauke mata hankalinta,suma sukanyi karatun,amma saidai baiko kai nata ba,sukance sun gaji basu iyawa,da sun taba iya yadda zasu iya suke ajewa su shiga sabgarsu.


Yanzun ma hira suke masu charting nayi,harda qawayen su batula daga wani dakin,ana tsaka da haka taji mardiyya qawae farida ta luqa ashar
"Ferry....zoki gani....maza maza zo kiga" da sauri farida ta aje tata wayar ta matso kusa da mardiyya,saita zare glass din fuskarta,da qarfi ta furta
"What.....muhsin ne fa,wata fa naga ya dora yana furta kalaman soyayya a qasan pic dinta,kan bala'i" saita fada tana dauko wayarta da sauri tana duba wajen status dinta
"Zo kiga,ni bai nuna ajerin nawa status din ba,babu status dinsa" dariya wata rabi'ah dake zaune kusa dasu tayi,ta tashi ta zauna tana cewa
"Wai baku gane meke faruwa bane,ai na taba gaya miki farida tun kwanaki kika qi yarda,kinzo kina wani jin kin isa kinkai,wai waye ya gaya miki ma cewa a yanzu ana cika baki kan namiji?,ai wannan lokacin ya wuce,lokacin cika baki da alfahari,da basu amanna dari bisa dari.....everybody listen to me" ta fada tana gyara zamanta sosai a tsakiyarsu tare da miqe qafafunta,hakanan maganar da rabi'ah din ta soma fada ta dauki hankalin zahra,bata sauke littafin hannunta ba amma hankalinta na kanta
"Luggar mazan yanzu.....zasu iya yin budurwa dari ko dubu ta watsapp....kuma zasu iya dora hotonta a status...amma kuma,duk sanda zasu dora hoton daya,tofa zasu cire dukkan sauran su sanyasu a jerin wadanda a ranar ba zasuga status dinsu ba,ba zasu ciresu ba har sai hoton yayi disappering,ko kuma ranar naki pic din zasu saka,saisu cilla waccar cikin inda suka ciroki ke kuma a fito dake,donki gani,kiji dadi,ki kuma qara amanna dasu...so dukka abun bugene,duk ta yadda suka biyo miki ki bi musu ta haka,kada ku saurara kunji....kuyita musu yadda suke muku kawai,dakun samu na dauka ku dauka ku watsar dasu" ta qarasa fada tana sheqewa da dariya.


Maganar status din ta baiwa zahra mamaki,wato kullum sabon salo suke fiddawa?,saidai fatan samun shiriya,amma kuma zancan gogayya da samari barkatai sam shawarar batayi mata ba,saita tabe bakinta kawai taci gaba da karatunta,gefe guda hayaniyarsu tana cika mata kunne,da Allah ya taimaketa zuwa wani lokaci suka fara raguwa da kadan kadan,har dakin ya rage daga ita sai hindatu wadda ta haye gado ta kwanta zata dan rage bacci a cewarta kafin ta tashi tayi karatu.


Turo qofar dakin da aka sakeyi da qarfi yasa zahra dagowa tana fatan ba sune

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login