Showing 18001 words to 21000 words out of 121250 words
nisa da hanyar barin falon,tana ta zumbura baki,sam bataji dadi ba data tuntu eshi da zancan,zata zubda mata aji ne kawai,kuma ma ai yana ji akayi maganar da ya sadiq amma baice komai ba,sai daya dan kurbi furar sannan ya amsata
"Ana aure dole hajja?,kika sani ko batayi masa bane?".
Kamar saukar mashi haka zahra taji maganar a qahon zuciyarta,don sai data kasa jurewa ta waiwayo ta dubesu,shikam shan furarsa yake kamar ma baisan me ya fada ba,cikin bacin rai tayi gaba da sauri ta shige dakinta,batasan dai me hajjan tace masa ba,amma ta jiyo muryarta tana magana,saidai bata iya tantance me take ce masa.
23/10/2021, 08:38 - ππ»ππ»: *KIJI TSORON ALLAHβπΎβπΎβπΎ,karki taba kayan daba naki bane,ba kuma mallakinki bane*
7
Saman madubi ta samu ta zauna cikin fushi ranta na wani irin suya
"Shifa ya haidar din nan rainin wayonsa yawa ne dashi,ya rainama mutane ajawali,meya daukemu ne?,duk laifin hajja ne,ai tasan bana hada shirgina dashi me yasa zata masa zancan matsalata,aikin banza kawai,don yaga mata na hauka akanshi snine hake raina ajawalin mata,koya dauka kowa baka yake,baisan suna mata suka tara ba,mtsewww......aikin banza kawai" a sarari tayi maganarta,kamar da wani a dakin take magana,taja tsaki tana gyara zamanta saman madubin.
Ji tayi xaman dakin gaba daya baiyi mata bama,gwara ta shiga cikin 'yan uwanta ko zata samu sassauci,saita zaro gogagge cikin hijabanta ta saka ta zira silifas dinta ta fito.
Har yanzu yana zaune falon riqe da babbar abokiyarsa wato waya,ya wani miqe qafafunsa saman center table,gefansa furar da yace a kawo masa ce,ya ajjiyeta ba tare da yayi mata wani shan kirki ba.
Harta giftashi bai daga kai ba,sai data kusa qofar fita taji yace
"Ke!" Tasan da ita yake,dole ta dawo
"Ki tabbata gobe a makaranta kika kwana" abinda ya fada kenan a taqaice,dole ta amsashi da to,duk da kuwa ji take kamar ta rufeshi da duka saboda takaici,haka ta fita tana tura baki gaba,ita sam wallahi babu innamal din komawarta makaranta,so tayi ma ta laΖe da wannan ciwon taqi komawa gaba daya,don itakam gaskiya ta gaji,amma yana son rusa mata plan,to Allah yasa babu kowa a falon sanda ya fada bare a tilastata,shuru kawai zatayi da bakinta,suyita wasan buya harya koma hutunsa,tunda dak ai shima ba dawwama zaiyi ba,da wannan tunanin ta shiga sashensu salma.
A kitchen ta sameta tana kwabin doghnout,sosai taji dadin ganinta
"Gwara da kika fito ai,shi yana can wala'alla yana sha'aninsa keya barki kwance,dama yanzu nake cewa bari na gama kwabin nan naje na fiddoki,na kunna wayarki dazun naga kamar ma ya tura miki saqo" baki zahra ta tabe,tana jan daya robar kwabin ta tattare dogon hannun rigarta ta fara tayata tana cewa
"Can masa....gaba daya ma kamar Allah ya fidda minshi a raina,idan ma ya cuceni yaje shida Allah"
"Kawai yafi" daga haka suka shiga wata hirar,zahran na bata labarin abinda ya faru yanzu a falon hajjan,da kuma cewar da yayi lallai gobe ta koma makaranta
"Kinsan Allah ki rufawa kanki asiri ki tattara goben ki koma,kinfi kowa sanin halin ya haidar ko?" Salma ta fada tana dubanta
"Wallahi wannan karon saidai yaci kansa da kansa yasha baqin ruwa,don ni ko zan koma badai gobe ba ehe,ke saima anyi bikin huda dani" dariya salma ta danyi
"Zahra,zahra kafiya,to Allah ya kauda bacin rana"
"Amin" ta amsa mata,salman ta cire hannunta daga flower data gama kwabawar ta wanke a fanfo,tana goge ruwan a rigar jikinta tace
"Bari na dauko miki wayar" baki ta tabe ba tare data ce komai ba,salma ta juya ta fice.
Kafin ta dawo ta gama kwabin itama ta wanke hannunta,harta samu waje ta zauna,ta dawo ta miqa mata wayar tana cewa
"Ga saqon nan,duba ki gani",still baki ta tabe kana ta sanya hannu ta karba din,ta buda saqon ga fara duba tsahonsa kafin ta koma farko da niyyar karantawa hafsa tayi sallama cikin kitchen din riqe da plate din abinci
"Gawa taqi rami,yanzu hajja tacemin aikin fito" murmushi tayi tana maida idonta kan wayar kana ta amsawa hafsa
"Ke kyaso na mutu tun yanzu?" Kai ta girgiza itama tana neman wajen zama
"A'ah ina fa.....salame zubamin miya don Allah inji umma,haka kawai suka mana tuwo da rana"
"Kya samu wata salamen ta zuba miki kuwa amma bani ba" dariya ta saki,tasan sarai bata son sunan
"Afwa tuba nake"
"Kina da hannu ai sai kizo ki diba" tashi tayi ta isa gaban tukunyar ta bude ta zuba miyar,daidai sanda zahra ta fara karanta saqon a fili
_assalamu alaiki,ina me neman afuwa da gafara daga gareki,nasan cewa na miki ba dai dai ba,amma tuntuni naso na samu lokaci mu tattauna kafin zuwan rana irin wannan amma Allah bai nufa,duk da haka ina mai baki haquri,ki sani matar mutum kabarinsa,kuma Allaj yayi keba matata bace shi yasa ban aureki ba,amma idan da hali kuma zai yiwu ki bani dama ki zamto mata ta biyu a wajena,ina dakon amincewarki_
_nuraddeen_
Wani ashar salma taso zundumawa sai kuma ta katse
"Lallai gayen nan yakai qarshe a rainin wayo"
"Tayani gani don Allah" inji hafsa tana kama haba,yayin da zahra ta saki wani murmushi mai ciwo,da kuma nuni da rainin wayon nuraddeen din ya bata mamaki,don daga haka ta zare sim din wayar kawai ta ballashi biyu ta watsa cikin sink din dake kusa dashi,ta kunna famfo ruwa ya korashi
"Na dauki tarayya ta dashi kamar mafarki,kuma ku saka hakan a ranku,mu shiga next chapter da Allah" ta fada cikin dakiya.
Shigowar yusra kitchen din shi ya tada sabon hira,haka nan suke da wuya kaga mutun daya shi kadai,saidai idan dukka basa gidan
"Na zaci munafuntata kukayi ai kuka zauna kuna wainar fulawa aka rasa me kirana"
"To ba ita akeyi ba kwaΙai...." Dariya ta saki
"Allah qamshin manja na dinga ji,kuma naji kamar daga nan ne,kwanan nan sha'awar wainar fulawa nake wlh,mu kuma cikinmu an rasa me soyawa,kowacce sai tace idan ta soya ba zata iya ci ba,ai shikenan"
"Ni kinma tunamin" hafsa ta fada tana ane farantin data gama cin abinci
"Gidansu zainab ahmad din nan?" Tayi maganar da sigar tambaya tana side hannunta
"Eh" suka amsa a kusan tare
"Wallahi suna wainar fulawa da daddare,harda me qwai dame kifi,ke kinji dadinta kuwa?"
"Wayyo Allah,har kinsa yawuna tsinkewa,yaushe zamuje"
"Yauma idan da kudinki"
"Mu bari sai gobe,yau ya usama yamin alqawarin kyautar dubu daya gobe"
"To kuwa muna aljihunki" inji salma
"Allah ya kaimu" ta amsa musu,daga haka suka sake shiga wata hirar kafin kowa su watse.
Bata koma sassan hajja ba,saita wuce sassansu wajen umminta,tunda ta kwanta ciwon bata ganta ba.
A hankali tayi sallama falon nasu,ita daya ce zaune qasan carfet,gabanta da wata babbar baqar leda tana ta fiddo kayan dake cikinta,wanda suka hada dasu madara bournvita,Klein,corn flaks,sabulai,mayukan shafawa,turaruka,maclien,cream salad,suger na qananun jakankuna da sauran kayan amfanin gida na yau da kullum.
Kayan tabi da kallo sannan ta samu waje ta zauna
"Ummi ina yini?" Kai tadan daga ta kalleta kana ta maida ga abinda takeyi tare da amsa mata
"Lafiya lau,ya jikin naki?"
"Da sauqi alhmdlh"
"To Allah ya qara lafiya"
"Amin amin" ta amsa mata,sai shuru yadan biyo baya,wani lokaci ummin nata kaman tana mata halin fulani na kara da alkunya kamar na diyan fari,duk da cewa ba itace ta farin ba,amma itama abun ya shafeta.
"Haka abu kuma ya faru?,sai ki addu'a Allah yasa hakane yafi alkhairi" ta fada cikin yanayi na rashin bawa abun muhimmanci
"Amin" ta fada tana murxa yatsanta.
Bayan shudewar wasu sakanni ummin ta sake cewa
"Kinga irin hidimar yayanku,shi koda yaushe baya gajiya damu,kowanne lokaci alkhairinsa a tafe yake,ko iya hakan ya isa ya bayyanar da nagartarsa,fatana Allah yasa sauran 'yan uwanshi suyi halinsa"
"Ba amin ba,kura ce da fatar akuya" ta fada a ranta,amma a fili don ta farantawa ummin nata sai tace
"Amin" a taqaice.
Ita ta taimakawa ummin aka raba kayan zuwa ma'ajiyarsu,kowanne abu aka sashi a muhallinsa,tadan jima ranar wajenta,ita kuma a fakaice tana jan hankalinta tare da sake nuna mata girman haidar din,sai da suka gama komai sannan tayi mata sallama gab da za a kira magrib ta baro sashen.
Daga nesa ta hangoshi can inda masu gidan dake da mota ko babur suke ajiyesu,tsaye jikin motarsa,booth din a bude ana fidda kayan ciki zuwa sassa sassa na gidan,baki tadan tabe kana ta nufi sassan hajja.
Canma raba kayan ta tadda hajjan nayi,ita da shafa'atu husna da amira dukka jikokinta ne,sai tayi wucewarta cikin daki,bata tsaya ba ta zarce bandaki,ta daura alwala,saboda gab ake da akira sallah.
Kamar yadda taci alwashi kuwa a washegarin bata gayawa kowa yadda sukayi da yaa zaki ba,sai tayi kwanciyarta luf a daki,wuni guda,hajja tana ta mita da yawo tsakanin falon da dakin kan ta fito,ko kuma jikinne?,saitace lafiya lau take,tana ramuwar baccin da bata samu yi ba,har hajjan dai ta haqura ta qyaleta.
Sai bayan sallar magariba su yusra suka shigo,kowacce sanye da hijabinta
"Zamuje gidansu xainab ahmad,na gayawa yayarta ta soya mana wainar gamu nan zuwa"inji yusra tana isa gaban madubin zahran gana gyara wuyan hijabinta,fuska ta yatsina,don batason fita bare suyi karo dashi,tasan haduwarsu ba zatayi kyauba,tunda ya bata umarni taqi ji
"Kuje kawai kwa tahomin da tawa,banajin fita"
"Ki tashi kawai malama mu wuce,babu mai miki dakon komai" tashi tayi ta zauna sosai tana duban yusran
"Kinsan fa akwai jagwal,ya haidar,banaso mu hadu,so nake har sai ya koma tukunna"
"Dazu naga fitarsa ma....ina jin wajen ya zahra ma ya tafi,kinsan ko ba yanzu zai dawo ba" inji hafsat dake gaban madubi tana shafa powder,jin hakan yasa ta miqe ta zaro hijabinta ta ware ta saka,ta sanya slippers dinta sannan suka fito.
Da kallo hajja ta bisu sanda suke fitowa daga dakin suna 'yar hayaniyarsu,har sunyi gaba hafsat tadan dawo da baya
"Don Allah koda ya haidar zai tambaya ina ina kice kece kika aikemu" baki ta tabe tana dubansu
"Babu ruwan fadimatu zahra'u,ku qarke qalau"
"Hajja mu dake fa bata baci" ta fada tana dariya tayi gaba suka fice.
Kusan awa biyu suka kwashe,har kusan bayan isha'i sannan suka fito,suna tafe suna hirarsu har suka qaraso qofar gidan.
Salma ce a gaba,ita ta fara tura qofar gidan,da sauri ta dawo da baya har tana bige yasira
"Dalla meye haka...kefa kin fiya abun haushi wani lokaci"
"Ya haidar.....wallahi ya dawo,suna baranda shida dasu ya abu sufyan" sak kowaccensu tayi,aka koma kallon kallo tsakaninsu,aka rasa me magana har tsahon wasu sakanni.
Zahra ce ta soma jan tsaki,sannan ta soma yin gaba tana jan hannun hafsat
"Tsoron wai na meye,muje don Allah,fuska kawai xamu masa" qarfafa musu gwiwan da tayi yasa suka soma takawa zuwa ciki.
Zaratan samari ne guda hudu saman wasu fararen kujerun roba,aliyyu na biyar dinsu,dan qaramin teburi ne a gabansu dauke da lemuka da cups,sai dan qayataccen qaramin flask din tea da kofunansa.
Kana dubansu xaka gane akwai abinda suke tattaunawa,saidai aliyyun kacokam hankalinsa nakan wayarsa kamar kullum,lokaci lokaci yana dan sanya bakinsa ba tare daya daga kanshi daga wayar ba,hakan yasa sukaji dadi,sannu a hankali suka fara takawa zasu wuce zuwa sashen da yafi kusa dasu.
Kaman an umarceshi ya daga kansa,idanu biyu sukayi dasu,take kowacce tasha jinin jikinta,yayin da zahra ta fara qoqarin boyewa sosai ta bayansu yadda bazai iya ganinta ba.
Sunan hafsa ya kira,ta amsa kana cikin hanzari ta nufi inda yake,bata wuce sakan biyar ba ta dawo
"Ya haidar yace kuzo" ta fada tana narai narai da ido muryarta na rawa,tilas suka taka zuwa inda suke zaunan,suna hangoshi daga inda suke yana ci gaba da danna wayarsa,yayin da sauran abokan nasa suka dakata da maganar da sukeyi din,wasunsu suka dauki drink suna sha,wasu kuma suka tsiyaya black tea.
"A'ah,yammata.....daga ina haka?" Daya daga cikin abokan nashi mai suna saif ya fada cikin sakin fuska,kasa amsa masa sukayi,sai suka maye gurbin tambayar tashi da gaisuwa cikin sanyin murya dake nuna tsoro,ba wadda ta isa tayi gigin yin wani abun da bai dai dai ba,don dukkansu sun haddace dokokinsa da abinda bai dauka,suna girmama abokanshi sosai kamar yadda suke bashi girma,saidai akwai dan bambanci,kusan sunfi sakewa dasu fiye dashi,don a cikinsu akwai masu sakin fuska ba kamar shi ba.
Shanyasu yayi suka ci gaba da hirarsu,wanda mafi akasari abinda ya shafi aikinsu ne na soja,a qalla sun kusa awa guda a duqe qafafunsu har soma tsami,sai da daya daga cikin abokan nashi qasa qasa yace
"Man,ka ajjiye mutane fa,ka sallamesu idan baka da abun cewa" tsaki yaja yana gyara zamanshi,ya sauke qafarsa da tun dazun daya ke saman daya ya zauna sosai kamar wani saraki sannan ya jefa musu tambayar daga ina suke,cikin rawar murya hafsa tace
"Hajja ce ta aikemu nan baya...."
"Kunci sa'a ta gayamin,amma daga yauu....kada ku sake na sake ganinku kamar i yanzu a waje....ku bacemin a gun" da sauri dukkansu suka miqe,hakan ya sanya ta manta da cewa boye masa take ta miqe itama da sauri.
"Ke!...zonan" ya fada da wani dakakken sauti daya sanya cikinta bada wani sauti na quuuu,ko ba'a fada ba da ita yake babu neman qarin bayani
"Ba daku nake ba.....ku bace daga nan kafin na tashi" ya baiwa sauran umarni,hakanan tana ji tana gani suka wuce suka barta.
A hankali take takowa zuwa inda suke kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,duk yadda taso baiwa kanta qwarin gwiwa amma ta kasa tattaroshi,batayi tunanin zai ganta ba sam
"Kina cikinsu dama zahran hajja?" Daya daga cikin abokan nasa mai suna fahad wanda sai yanzu yayi magana ya furta,wani kallo aliyyun ya watsa mishi kafin ya maida dubansa a kanta yana jifanta da wani kallo yace
"A ina nace miki yau ki kwana?" Shuru kamar ba zata amsa ba sannan tace
"Makaranta"
"Da kyau!,me kike a gida yau din?"
"Babu komai"
Kanshi ya gyada shuru na wasu 'yan mintuna,sannan ya zira hannunshi a aljihu ya ciro key din mota ya wurga mata
"Ki cewa labaran ya kunna miki ruwa ya baki mesa" muqullin tabi da kallo tana maimaita abinda ya fada cikin qwaqwalwarta.
Ta fahimci abinda yake nufi tsaf,wato taje ta wanke mishi mota kenan koko yaya?,so yake ya disgata gaban abokanshi,data sake daga kai ta kalleshi ya maida qafafunsa yadda suke yaci gaba da sabgarsa.
Tsam ta miqe riqe da muqullin ta juya ta soma takawa
"Fahad.....kana so ka jawa mutane raini wajen yaran nan,na gaya maka tun ba yanzu ba banaso ko?" Ta jiyoshi yana fada cikin miskilanci,sai taja qaramin tsaki tana tunanin aikin daya sanyata yanzun,kuma tabbas yana hangota indai motarshi da take hangowa muqullinta ne a hannunsa,bama shi ba har duka abokan nashi suna iya ganota.....
_kuyimin afuwa jina shuru kwana biyu,hidima ce ta biki ta riqeni,naso muku bayani amma hakan bai samu ba,Allah yayi mana jagora_
23/10/2021, 08:38 - ππ»ππ»: 8
*KU MATSO MAZA KUJI LABARIN*
*_Oumahmad collection's_*
*_Shin kina buqatar waje daya tattare dukkan abubuwan buqata da kike son saye ba bata lokaci ko rarraba waje?_*
*to ga OUMAHMAD COLLECTIONS*
*_wadanda ke saida_*
_kayan kitchen_
_kayan sawa nau'i daban daban_
_jakankuna da takalma 'yan ubansu_
_wayoyin hannu kala daban daban na zamani_
_mayafai na gani na fada_
_kayan sawar yara na alfarma_
_kayan daki daga qasashe daban daban,irinsu dubai,china,India,turkey,Malaysia_
_ADRESS DINSU_ππ½ππ½
*_Kano hotoro_*
*Ko ku dubasu a facebook da sunan*
*_Maryam muhd_*
*Ko kira kai tsaye ta lambar waya kamar haka*
07014488636
*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*π€π½π€π½π€π½π€π½π€π½
__________________________________
*KIJI TSORON ALLAHβπΎβπΎβπΎ,KARKI TABA ABINDA BA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BANE*βββ
Kamar yadda yace bata fasa ba ta isa wajen labaran din,ta kuma buqaci ya hada mata famfon kamar yadda aka saba idan za'a wankewa wani cikin gidan mota,sai daya gama ta kalleshi
"Ance ka bani klien"
"Ah'ah....ai indai motar yallabai Aliyyu za'a wanke yana da carwash dinsa da ake wanke masa dashi,bari na dauko miki" har ya juya zai tafi ta dakatar dashi da sauri tana cewa
"Klien yace a bani,shi zaka daukomin" jimm yayi kadan sannan ya gyada kanshi yayi gaba,babu jimawa ya dawo dashi ya miqa mata,ta bishi da kallo har sai da taga bacewarsa sannan ta taka zuwa wajen mai musu aike aike cikin gidan,wanda wani lokaci yakan zauna a gidan na wasu kwanaki idan yana da ayyuka da yawa har zuwa sanda zai ragesu kana ya tafi gidansu
"Soson qarfe nakeson ka bani aro don Allah hayatu" ta fada tana dan waigawa taga yana ganinta?.
Ba tare da tunanin komai ba ya shiga ciki ya dauko ya miqa matan,ta karba tana jin dadin samun soson sannan ta durfafi motar tana qwafa,gami da qiyasta irin barnar da zatayi masa,yau saita fanshe dukka haushinta akan motar,koma me zai faru ya faru.
Sosai ta zambada klien cikin wani ruwa dake cikin botiki,saboda taji ance ba'a wanke mota da klien,don tana kodar da fentinta,to ba motar ba,shi kansa me motar da zata iya saita kodar dashi,taga kya da gayun da yakewa taqama,kamar wani yafi kyau,itakam ta tsani yadda mata ke kodashi,tana ganin kamar suke tunzurashi ma suke yake sake jin kansa wani,kofi ta ciko ta miqe da niyyar soma watsawa motar
"Zahra'u" taji an ambata sunanta daga bayanta,saita waiwaya,abba babba ne,riqe da maqullin mota da leda a hannunsa
"Na'am abba?....sannu da zuwa" kai ya gyada
"Yauwa....me zakiyi da ruwa kika tarashi haka kamar zakiyi wankin mota" saita marairaice sosai,ta sani cewa mafita tazo,duk da tana son taga ta bata wannan 'yar kyakkyawar motar