Showing 30001 words to 33000 words out of 121250 words
financial crisis iri iri.
Tuni tayi masa aji sukutum da guda ga ajjiyeshi,gefe guda kuma shirye shiryen biki ake a gidan haiqan,kowanne sashe suna nasu shirin,itama bata zauna ba,ta shiga anayin komai da ita,don 'yan uwanta ne da bata da tamkarsu.
Wannan karon umminta da kanta ta kirata ta mata magana akan ibrahim,abinda bata taba yi ba akanta kenan
"Ki tayani da addu'a" shine amsar da zahran ta baiwa ummin nata,domin tasan abun babu dadi,koda itace kuwa,sun taso tare,karatu da komai tare,amma dukka sauran zasu tafi su bar diyarta?,duk da kasancewarta mutum mai yawan haquri da yarda da qadddara,tana da yawan ibada,abinda yasa take da wata nutsuwa ta musamman kenan
"Addu'a kullum cikinta muke,saidai aci gaba,ubangiji yayi zabi mafi alkhairi" abinda tace mata kenan ba tare data nuna damuwa ko a fuskarta ba.
*_ALƘIBLARSU |||_*🚶🏾♀️🚶🏾♀️🚶🏾♀️
Ana gab da sallar magariba suka dawo daga kai dinkunansu na biki,wanda ta hada dana hajja ummint ilham harda nata duka takai musu zoo road,kasancewar duka duka bikin sati biyar ya rage.
A gajiye libis take,saboda sun dan sha tafiya a qafa kafin su samu abin hawa,saboda yau ana wahalar abun hawa wanda batasan dalilin da ya kawo hakan ba.
Bandakin tsakar gidan hajja ta daura alwala ta shiga dakin hajjan ta tada salla,tana idarwa wayarta ta fara tsuwwa,ta shafa addu'ar da takeyi ta janyo wayar tana duba mai kiran.
Ibrahim ne,tsakanin jiya da yau sam basuyi waya ba ko sau daya,ita ta sha'afa ma dashi gaba daya,kara wayar tayi a kunnenta tana yin sallama,ya amsa mata,saidai sautin muryarsa batayi mata yadda suka saba magana ba.
Gaisawa kawai sukayi ta shigar masa da qorafin da taci alwashin gaya masa
"Ibrahim.....sam banga alfanu ko ma'anar ci gaba da tarayyarmu ba a haka.....aure shine ribar kowacce alaqa da dangantaka,ya kamata mu fuskanci reality,kayi abinda ya kamata" ajiyar zuciya ya sake cikin wani yanayi ya soma magana mai kama da ko in kula
"Abinda na kira na gaya miki dama kenan,don kada ki zargeni....kin ganni nan.....wallahi kakata ce wadda ta haifi ubana tayimin mata,ta kuma ce lallai lallai kona aureta kota tsinemin,ni kuma naga babu yadda zanyi ko don na farantawa babana,shi yasa na kiraki na baki haquri don dole nayi musu biyayya,Allah ya hada kowa da rabonsa" daga haka ya katse wayar.
Tamkar mutum mutumi haka tabar wayar a kunnen tana sauraren shuru,duk da cewa tasha qiyasta haka qarshen alaqarsu zata kasance,amma bata taba kawowa zatazo ta wannan sigar ba.
Sallamar salma ita ta taimaka ta dawo da ita hayyacinta harta samu nasarar cire wayar daga kunnenta,kallon fuskar zahran yasa salma ta fahimci akwai matsala,saita qaraso tana tambayar zahran lafiya?
"Mun rabu da ibrahim shima salma" ta amsa mata da yanayin data kasa tantance wanne ne?,baqinciki ne ko tashin hankali?".
Duk abinda salman ke fada tana jinta ne kawai ba tare da tana fahimta ba,har tayi ta gama,saita zama kamar wata mutum mutumi,abu na qarshe data ji shine qwalla dake saukowa a idanunta masu dumi,wanda yayi dai dai da shigowar hajja.
Wannan karon itama hajjan hankalinta tashi yayi fiye da baya,ta dinga salati tana salallami,ita kanta salma hankalinta ya tashi,wannan wacce iriyar qaddarace haka daya bayan daya?.
Kusan duk wani makusancinta a wannan karon lamarin yafi shigarsa,babu abinda zahra ta rasa,kaf yaran gidan babu wanda keda kyau da sura irin tata,hakanan tarbiyya,abinda yayi su salma shi yayisu,asali da nasaba dukka daya,to amma tata qaddarar tazo daban da tasu,kuma babu wanda ya isa ya sauya mata,saidai addu'a nada qarfin ikon sauya komai da izinin Allah,wannan shine wasu daga cikin kalaman hajja data cika da damuwa matuqa gaske.
Ƙarfe tara na dare ta isa sassan umminta bayan kiran datayi mata kwanaki uku da faruwar al'amarin.
A dakin gadonta ta sameta ita kadai zaune gefan gado,bayan ta baro qannenta a falo zaune,zata zauna qasa ummin ta nuna mata gefanta gami da cewa
"Zauna nan"babu musu ta zauna din tana duban mahaifiyartata
"Zahra'u....kalleni nan" ta fada tana dubanta,kanta ta daga tana duban ummin tata,ta hangi da gasken gasken zata gaya mata koma menene zai fito daga bakinta din,saboda ba kasafai take kiran sunanta haka kai tsaye ba,da wahala ta kirata haka da wannan sunan kai tsaye,don sunan hajja ne fatiman,sunan dake da daraja a idonta,don haka ta sake tattara mata hankalinta
"Zahra'u....inason ki gayamin,tsakaninki da mahaliccinki wanne abu kike aikatawa da dukka manemanki suke barinki haka bagatatan?" Take idanunta ya tara hawaye,muryarta tana rawa tace
"Ban sani ba ummi,bani da masaniya"
"Ki gayamin inna wuro....tun wuri ki shaida min,meke faruwa?"
"Ki yarda dani ummi,wallahi babu wani abu" shuru ne ya biyo baya na wani dan lokaci,sai sautin sheshsheqar kukan zahran tsahon wani lokaci sannan ummin ta sake cewa
"Inason ki sake dagewa da addu'a,bawai ki zauna haka ba,ki gayawa Allah matsalolinki da buqatarki,a shirye yake ya amsa miki buqatunki,ya kuma yaye miki matsalolinki" kai take gyadawa a hankali,sosai tausayin 'yar tata ya kamata,sai tace
"Tashi kije...Allah ya shige mana gaba".
***********
Sannu a hankali kwanaki suke shudewa,lokacin biki kuma yana qaratowa,harya zamana saura sati hudu kacal biki,shirye shirye suka kankama sosai,yayin da zahra ta maida kanta busy ta kuma shiga harkar bikin kamar yadda ya kamata ta kasance a ciki,ta kowanne bangare akwai hannunta a ciki.
*_ƘADDARA ta riga fata....._*
ƙarfe biyar da wasu mintuna na yammacin ranar alhamis ne,tsaye suke a farfajiyar gidan suna amsar wasu daga cikin dinkunansu da telarsu ta gama ta kawo musu suna dubawa,babu jimawa suka sallameta,kowa ya ninke nashi ya saka a leda,suka koma tattauna sauran abubuwan da basu kai ga aiwatarwa ba wanda ya shafi bikin.
A hankali a hankali suka soma jin sautin salatin daga sassan abba babba,sak dukkaninsu sukayi suka kasa kunne,tabbas daga can sautin salatin yake fitowa daya nabin daya a jejjere.
Zumbur hafsat ta miqe fuskarta dauke da tsoro da firgici tace
"Kamar muryar mama....mama ce....ina zuwa" cikin sauri ta durfafi sashen nasu,yasira ta rufa mata baya,sauran kuma suka tsaya cak,kowaccensu ta kasa motsawa cike da fargaba jin abinda ya faru,da kuma abinda zai biyo bayan salatin......
_kuyi manage da wannan,mu hadu gobe in sha Allah dan jin meke faruwa?......_
23/10/2021, 08:40 - 👍🏻👍🏻: 12
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ƘAWA DA KECE RAINI_💄💅🏽
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau'in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki gaba daya ZAHIRINKI DA BAƊININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
*kayayyakinmu sune kamar haka*
FACE AND BODY SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500
*Ku dubamu a handle namu na Facebook da Instagram*
Ummu Dufail
*ko ta number wayarmu kamar haka*
07067943479
*_muna turawa kowacce jaha dake fadin nigeria da yardar Allah_*
*_INGANCI DA RAHUSA SHINE TAKENMU_*🤞🏾🤞🏾🤞🏾
_____________________________
Minti biyu saiga hafsat ta fito tana hawaye hannayenta a ka,dukkansu suka nufeta cikin sauri kuma cikin tashin hankali,don dukkansu sun kasa shiga sashen har sai data fito
"Yaa zahra.....yaa zahra,ya zahra ta mutu" ta fada tana rushewa da kuka.
Sak kowaccensu tayi tana jin maganar tana shigarta,babu wadda ta kawo faruwar hakan cikin ranta a cikinsu,zahra ce tayi qarfin halin cewa
"Yaa zahran da take makaranta?,me ya sameta haka?,rashin lafiya tayi?"
"Maciji.....maciji ne ya sareta"
"Innalilahi wa inna ilaihi raji'un" kowaccensu ke maimaitawa.
Cikin ƙanƙanin lokaci duka matan gidan suka shirya suka fito saboda nuna kara ga mama,uwa uba kuma ga surukuta da take shirin shiga tsakani,gidan ya zamana babu kowa,daga 'yammatan sai yara,su dinma zaman jugum jugum sukayi,kowanne a cikinsu yana tuna yaa zahran da irin kirkinta,haquri gami da sanyin hali.
Yasira ce taja doguwar ajiyar zuciya tana cewa
"Allah sarki yaa haidar,ko yaya zaiji?" Ta fadi maganar tana tuna yadda suke da zahran tashi,kusan kaf wanda yasan haidar bai taba ganinsa yana soyayya ba sai akan zahran,wata iriyar soyayya suke shida ita,ita tana girmamashi da girmama ra'ayinsa hadi da bashi kulawa,hakanan shima ya iya tattalinta da nashi salon na iya kula da 'ya mace cikin sanyi,wanda ba kowa ne zai fahimta haka ba sai mai dogon nazari.
Sai washegari su suka je gidan makokin bayan sun girka abinci mai yawa sun tafi dashi kula kula,ko acan ma kusan baya ga mahaifan zahran haidar shine mutum.na gaba da aka tausayawa,kowa yaje ya masa gaisuwa ya dawo saiya fadi irin halin daya ganshi,wata mata dake matuqar kama dasu mama,wanda da alama danginsu ce tace
"Dole aliyyu ya shiga wani hali,a gabansa ajalin zahra ya risketa,kuma a gabansa ta mutu,ai dole,mutuwar masoyinka gaban idanunka aiba qaramin al'amari bane da zaiyi saurin barin zuciya da tunani nan da nan".
Shuru inna wuro dake gefe tayi tana nazarin al'amarin,tabbas jikinta yayi sanyi sosai,komai saiya sake fice mata akai,musamman sanda ake dawo da kayan zahra daga hostel,yau ga komai na zahran amma babu ita,tana can duniyar da babu wanda ya isa ya dawo da ita,ta tafi kenan tafiya ta har abada saidai tarihi.
A hanyarsu ta dawowa hafsat ke sake basu labarin yadda abun ya faru,ashe a makaranta tsautsayin ya sameta,a sannan haidar din yaje wajenta,ta juya da niyar zuwa hostel ta dauko biro da takarda zata rubuta masa list na abubuwan da take buqata na biki,yaga gilmawar macijin.....kafin ya isa gareta yakai mata dauki harya sareta,rashin samun allurar akan kari shi ya kawo ajalinta,don suna hanyar wata barrack,duk da ba tasu bace amma yana da alfarma ako ina,wanda yake da tabbacin acan za'a samu allurar,ta mutu cikin motarsa,baima yarda ta mutun ba saida aka shigar da ita clinic din aka bincika aka shaida masa rai yayi halinsa.
Shuru kowa yayi yana jinjina al'amarin,tare da kadaita girman ubangiji,isa da buwayarsa,babu wanda ya taba kawowa zahra mutuwa koda ita karan kanta,ta mutu ta tafi a lokacin da masoyanta ke buqatarta,dangi keta shirin aurenta,ashe shirin zaman makokinta ake
(Allah kasa mu cika da imani,ka kyauta qarshenmu,kasa mu mutu alokacin da kake mai yarda da amincewa damu amin summa amin🤲🏽🤲🏽).
Rasuwar zahran yasa aka qara wata daya kan yadda aka tsara bikin,zuwa sannan ana saka ran zuciyoyi sun huce,an dan samu nutsuwa da dangana akan lamarin.
*_SAUYIN RAYUWA_*
Tun daga sanda abun ya faru gaba daya tamkar an sake canza haidar din daka wanda dacan suka sani zuwa wani na daban,ya sake zama miskili na qin qarawa,bai damu da zama ko rayuwa cikin mutane ba,magana saita zama dole ko ta shafi aikinsa,ya sake zama mutum mai zafi qwari da gaske fiye da baya,har kowa cikin gidan na shakka da dari dari na taboshi ko shiga cikin sabga ko huruminsa,bama su da suke qannensa mata ba,harda su ya musty kowa shiga taitayinsa yake idan ana maganar ya haidar,hakanan ya sake rungumar aikinsa,ya rabu da komai.
Hakan ya damu hajja qwarai,harta ringa qorafi,tana ganin ya sanyawa kansa damuwa mai yawa kan mutuwar zahra,ta fuskanci ma kamar yana dorawa kansa ne alhakin mutuwarta,da farko hakan hasashenta ne,amma data dameshi da qorafi da mita,da kuma son jin ta bakinsa saiya tabbatar mata da hakan
"Da banje gurinta ba a sannan,da ban fito da ita ba,da abinda ya sameta bai sameta ba,da tuni taba raye har yanzu" baki hajja ta sake tana kallonsa cike da mamaki,abun nasa ya zarce inda take tunani
"Ina hankalinka yake ne zaki?,ina imaninka da tauhidinka ya tafi?,shin ka manta kowacce rai bata tsallake ajalinta?,ka manta cewa kowacce rai saita dandani mutuwa?,ka manta kowacce rai na tare da qaddararta?"
"Duka nasan da hakan....kuma ina yawan gayawa kaina haka,saidai har yanzu na kasa cire tunanin cewa nine sila".
Ganin abun bana qare bane yasa tace su sashi kawai a addu'a,ubangiji ya sanyaya masa zuciyarsa,ya cire masa wannan tunani daga qwaqwalwarsa.
Biki akayi gagarumi wanda yabar tarihi cikin zuri'arsu,baqi na kusa dana nesa duka sun hallara,ansha hidima sosai,a hakanma an rage wasu abubuwan saboda rasuwar da akayin,amma hakan bai hana wasu hidimomin ba,tunda yaran bana sashe daya bane ba.
Xahra tamkar zata raba kanta gida hudu,saboda kowacce idan ta tashi ita take nema,baga yasira ba,baga yusra ba,baga hafsat ba,hakanan ba ga salma ba,a qarshe dai bayan amare kowacce an miqa ta gidanta sai data kwanta zazzabi na kusan kwana biyar.
Gaba daya daga bikin xuwa daurin auren babu wanda haidar yazo,ya kira ya musu Allah ya sanya alkhairi,ya kuma ce aiki ne ya tsareshi bazai samu zuwa ba.
Abba babba shi da mama zasuyi fada hajja ta hana
"Akul!,kada naji kada na gani,ku qyaleshin tunda yace aiki ne,kudai naku kuci gaba da yi masa addu'a,tsanantawa ba naku bane,Allah yayi mata rahama,shi kuma ya bashi dangana"da haka suka haqura da qorafin da sukayi niyyar yi.
Duk wanda yaga zahran cikin hidimar bikin cewa yake
"Kema Allah ya fito miki da na gari" takanyi murmushi ta amsa cikin ranta,ba domin abin ya dameta ba ko ya ɗaɗata da qasa ba,yayin da 'yan gaza gani,yan bani na iya,masu kokawa da qaddara da qarfin tuwo kance
"Ummm.....zahra kenan,ko kema kin bi sahun wasu yammatanne masu jiran mai kudi gida da mota,maka duk sati...kada dai kyau ya rudeki ki cuci kanki" suma takan bisu da dariya kawai,don a sannan bata da lokacin bata lokaci,hakanan bata da damuwa dasu tasan kuma ba hakan bane bare maganar ta dameta,yayin da wasunsu kance
"Uhmmm....zahra matar manya,da alama naki bikin na dabanne,saimun shirya sosai,dama irinku ai sai da babban kai" suma duka aji daya take saka su da masu magana ta biyu,dukkaninsu ba matsalarta bane su din,shi yasa basu da wata amsa daga gareta.
Kwana uku kacal da tafiyarsu sai kadaici da kewa ya soma damunta,dukka gidan taji ya daina mata dadi,bata taba tunani ko kawowa zata damu har haka da rashin 'yan uwan nata ba sai yanzu,duk saita sake zama wata so silent,bata fiya yawan hira dariya da raha da aka santa da ita ba.
Hajja ce mutum ta farko data fara lura da hakan,duk itama sai taji babu dadi,tasan cewa kewa ce ke damunta na 'yan uwanta da suka rayu tare suka taso tare,don haka tayi wani tunani,ta nemi abban gwammaja da babban danta abba babba ta zauna dasu,ta bada shawarar baiwa zahran damar ci gaba da karatu,idan yaso duk sanda Allah ya kawo mata manemi sai ta yanke tayi aurenta,don yafi wannan zaman da zatayi,domin zaman bashi da wani alfanu,hakanan babu abinda zai qara mata sai damuwa.
Dukkaninsu sunyi na'am,don result din zahran ba qaramin kyau yayi ba,don haka abban gwammaja ya nemi a bashi takardunta amma abba babba yace sam wannan karon shi zaiyi wannan aikin,hakanan abban gwammaja ya sallama din,tunda sun bashi damarmaki a baya sosai kan yarinyar,bai kamata a yanzu shima yaqi basu tasu damar ba.
Wani irin farinciki da bata taba tunanin zata jishi ba shi taji a sanda labarin ci gaba da karatunta ya risketa,duba da cewa ita sam bata da sha'awar ci gaba da karatu tun a baya,hafsat da yasira sun fita wannan kwadayin,tayi murna sosai,ta kuma tabbatar da qaunar da hajjanta ke mata ta daban ce,hakanan 'yan uwan mahaifin nata mutanene da samun kamarsu a wannan zamanin sai an tona,wannan shine ya zamto silar ci gaba da karatun zahran,mace ta farko a tarihin gidan data taba tsallakewa zuwa makarantar gaba da secondry.
*_SABUWAR DUNIYA_*
Kamar kowacce daliba,ta shiga makarantar cike da baqunta da rashin sabo,komai nata idan ka gani irin na farin shiga ne,sannu a hankali har ta fara gogewa tana kuma gane kan abubuwa.
Ƙawar farko data fara yi bayan zuwanta makarantar itace hindatu abubakar,babban abinda yaja hankalinta zuwa qawancesu shine qoqari irin na hindatun,duk da cewa sun fito ne daga mabanbantan gida masu mabanbantan dabi'u al'ada da kuma wadata,saboda hindatun iyayenta masu sukuni ne qwarai da gaske,don mota ta daban kuma ta musamman ake kawota makarantar kulli yaumin,a kuma dawo a dauketa,daga wayar hannunta zuwa suturu kawai zakasan 'yar babban gida ce,Allah ga hada jininsu da hindatu da wani irin qawance daya gauraya da qaunar juna,qauna kuma ta fisabilillahi,don da farko zahra taso janye jikinta daga abota da hindatun,saboda tsari da matakin rayuwarsu ba daya bane,da jajircewar hindatun qawancen nasu ya daidaita,kowa kuma yake amfani da irin nashi life style din ba tare da ya takura dan uwanshi akan yanayin nashi tsarin rayuwar ba.
Iyayen hindatun 'yan boko ne na gasken gaske,ba irin 'yan bokon muna boko ba,kusan hatta kakan hindatun asalinsa dan boko ne,irin 'yan bokon da turawan mulkin mallaka suka koyar tun duniya tana kwance,don haka idan ana gadar boko xa'a iya cewa sun gadon,don kuwa hatta da dabi'unsu da al'adunsu irin na nasara ne,akwai 'yancin da zabar rayuwa cikin gidansu