Showing 39001 words to 42000 words out of 113608 words
har gidan Uncle Jay bayan ya masa bayanin sanda sukaga Khairiyya ita da wacce ke cewa uwarta ce sekuma ya baiwa Yaseer dama ya zayyanemu abinda yakeda yak'inin shine ya faru, Ant Barra ta tausaya mata ainun tace tana kallon Jay
"Jay anan gidan babu wanda ze zargi komai akan khairiyya, yadai dace mu d'akkota ta dawo nan inyaso senake kulawa da ita zamanta acen bashida wani amfani koda yake babu wanda yasan da gidan amma dai idon fada idon masifa ne idone na duniya ko ina yawo suke" Saukar da kanshi yayi a k'asa yana wani nazari kafin daga bisani ya gyad'a kansa cikin gamsuwa da bayanin datayi.
******************
Lokacin da Khairiyya ta farka babu kowa a d'akin se ita kad'ai, sosai takejin jikinta yana mata zogi, har ranta tanaji cewa bazata iya tafiya konan dacen ba, a zuciyar ta kuwa tayawa take zata kashe kanta har abada, gwanda ace bata duniya akan wannan mummunanr bak'ar rayuwar data fad'a, motsin tab'a k'ofar dataji shine ya mayar da hankalin ta zuwa wurin bazata iya tuna komai ba, yaushe tazo nan? waya kawota nan kuma? kallon sa tayi ganin kurma ba k'aramin tayar mata da hankali yayi ba da sauri tasoma kok'arin mim'ewa zaune sedai azabar dataji ya tilasta mata k'walla k'ara ta koma da azama da kwanta lokaci d'aya idanta ya kawo ruwa a hankqli tace
"Wayyoo Annah its really painful" da azama shikuwa ya matsa ya rik'e hannunta, da ido suka kalli juna lokaci d'aya hawayen idanta ya gangaro, bakinsa ya motsa amma be iya cewa ko k'ala ba, da azama ya zaro wayarsa ya rubuta
"Please dont cry dear, u'll soon get better" Haska mata screen d'in yayi ta kawar da kanta batare data kalla ba, hannun sa ya sanya ya waigo da hab'arta ta kalleshi ya nuna mata screen d'in wayarsa, badan taso ba ta kalla, kallon sa tayi bayan ta gama karantawa sannan tace cikin kuka
"Banaso na warke, so nake in mutu wlh, i just want to meet with Annah na before i die, zan gaya mata wasiyya idan na mutu kada su bari momy na tazo kusa da gawana, she's evil, she's a monster i hate her" Kallon mamaki ya mata, sannan ya hasko matar datace mahaifiyar tace, da sauri ya goge wance ya rubuta
"Subhanallah khairii, she's ur mother remember? take back ur words now! ya k'arashe maganar yana tsatsare ta da ido, tana karantawa ta d'auke kanta tace
"Noo never, i will never take those word's back! i hate her she's evil, she's a selfish mother, ta wargazamun rayuwata, ta cutar dani, ta zalinc.....Da sauri yakai hannunsa ya rufe mata baki suka soma kallon juna, a hankali tasanya hannunta ta ture hannunsa dake bakinta tace
"Dan Allah ka saurara kaji mezan gaya maka, idan naci gaba da rik'e maganar nan mutuwa zanyi kafin inje gun Annah na" Da idanshi ta fahimci yana sauraren me take fad'a dan haka a hankali ta fara bashi tarihin rayuwar ta.
**************
"Lokacin dana tashi bansan kowa ba se Annah na, itane ta haifi mahaifina so she's my granma, Anna love's me so much a yanda take fad'a tace tanajin tausayina, sabisa mamana ta tafi ta barni when i was very young i mean a little cute Annah's pet, bansan wani damuw aba nida brother na Bilal, kawai nasan sauran siblings namu ba mamanmu d'aya ba, and mu muna rayuwa ne awurin granny su kuma sauran a main part na gidan wurin sa sarki yake da family nashi, inada son mulki sa izza, inada jinkai kamar yanda naji ake fad'a kowane lokaci, nayi primary school na a k'asar nan, amma a UK nayi High school na wurin yaa Bilal a lokacin yana college acen, ni 'yar gatace sosai sanda na kammala secondry school naso inci gaba a UK but Annah tace sam ita indawo gida kawai haka na hak'ura na dawo nan da zama ba samu admn nashiga 100 level ban saniba ashe duk mutunci na danaketa kariya a UK shirme nake, ban saniba ashe budurcin nan danake tak'ama dashi mahaifiya ta sayar dashi tun kafin in gama sanin darajar sa aguna! Sanda nake zuwa jami'a a met with a guy Sunansa Bilal, had'uwa na dashi na farko dana biyu duk fad'a a na uku ne muka soma zama ftiends, wannan kafin nan kawai se maganar aurena dakai ya fito, Jinkai da isa ya sanya naji bana son auren wani abu wai kurma, da haka dana gaya masa ya xigani ..............
............ tas ta kwashe komai ta gaya masa ta k'ara da cewa
"My mother sold out my dignity, she let him with no option but to take away my virginity which i value the most, i just hate her i hate my self, how can she be so heartless? she's inhuman she's an animal, she should have marry idan tasan bazata iya rik'e kantaba, now u ce because of what she did i lost everything am a looser!! ta k'arashe maganar cikin d'aga murya tana kuka" Bashida bakin magana a wannan gab'ar, besan ta ina ze fara ba, tausayin ta ya kashe shi, amma wannan Bilal d'in idan ya had'u dashi seya kaishi lahira, wane irin haukane zaka nunawa yarinya tsiraicin uwarta tana aikata masha'a, wannan yaran ya cancanci a kashe sa ma. Hannunta ya rik'o se kuka take ta kallesa girgiza mata kansa yayi alamar ta dena kuka sannan ya zaro yawar da dauri ya rubuta
"U know i can't talk ko? Haska mata yayi ta karanta kafin ta girgiza masa kanta, mayar da wayar yayi zuwaha dubansa kafin ya rubuta mata
"Please zanyi rubutu a jotter ki daure ki karanta" Nanma daya haska mata d'aga masa kanta tayi alamar "to" Da sauri ya zaro k'aramar jotter da pen ya duk'ufa rubutun kusan 19mns kafin ya mik'a mata ta karb'a tana daga kwancen sannnan ta soma dubawa
"Khairii pleasee wannan maganar ya zama sirri a tsakanina dake, karki sanar da kowa har Annah ma kinji, wannan mummunan labarine mara dad'in ji, wabban labarin idan ya bazu ke kanki se fita ya gagareki, ba komai ake gayawa kowa ba Khairii, ki rufawa mabaifiyar ki asiri ina yace dake ta tuba ? toki yarda da tubanta ki k'addara cewar koda babu wannan abun daya shiga tsakanin ke da mahaifiyarki da wannan yaron se hakan tafaru dake, just be grateful to Allah daya kareki ma, karki d'auka cewar addu'ar dakike bata karb'u ba a lokacin, keda kanki kince bakisan mesa ya fasa raping naki da gaske ba so kikasan wanne kalan ciwon ne ajikin sa Allah ya kareki? so please karna kuma jin kin gayawa mamanki wannan munanan kalaman, ki yafe mata tunda k'addarane baya wuce kan kowa, sannan kuma wannan maganar na kasheshi daga yanzu nan nidake ban yarda ki gayawa kowa ba. maganar mutuwa kuma karna kuma ji addinin musulunci ya mana umarni da yarda da kaddara ta alkhairi dakuma akasin ta ke musulma ne, kisan me kike ciki, wasu yaran zakiga basukai 18 bama amma samari sama da goma suke raping nasu at thesame time su me kikeso suce? ehm? d'agowa tayi bayan takai k'arshen jotter d'in sannan tace
"Amma mesa momyna zatayi haka? yaya kakeso in rayu ina kallon mugun abub da Bilal ya nunamun a allon computar sa, duk yanda naso na manta wannan abun ya gagara fita daga kaina, bazan tab'a iya rayuwa a rumfa d'aya da mahaifiyata ba daga yanzu har abada" Gyaran murya yayi sannan ya rubuta bayan ya kuma ansar jotter
"Ki k'addara cewar duk wannnan abun daya faru mafarki kike, d'auka cewan sharri ya mata, kin manta harkar technology ne wai? munkai wani babban matsayi da zaki iya tarar wa cewar fuskarta kawai ya saka ba ita bace d'in, ki nutsu mana, wannan umarni ne khairii karki fitar da maganar nan daga d'akin nan ki bunne ta har abada kinji ko? Haska mata yayi jotter na hannunsa, seda ta gama karantawa sannan tace
"Ba damuwa inshaa Allahu bazan gayawa koda kaina bane amma mezancewa 'yan gidanmu?
"Zaki tsaya nan for 2 days, gidan uncle d'ina zakije ki kula da kanki bayan kwana biyu zan kaiki hostel, daga nan zaki bari wani ya ganki idan anje anzo dake seki sanara hostel na school kika b'oye, idan har yanzu bakya son auren so be it, i will respect ur decision" Tana kallo dubansa tayi
"Noo, ina so wlh, never thought kai mutum ne me kirki haka, kayi hakuri akan abubuwan dana fad'a a baya akanka kaji" Murmushi ya sakar mata, kafin ya rubuta
"zan aureki next week idan kin yarda, Zanje US tare dake, so that u can forget ur bad memories and leave them here, we moveee" Kallon sa tayi bayan ta gama karantawa sannan tace
"Ur too kind for me, kafi k'arfina yanzu hammood, ka nemi daidai kai kawai, ni yanzu rayuwata batada amfani wlh" Girgiza mata kansa cikin b'acin rai sannan ya rubuta
"Na gaya miki ki dena maganar nan, zanyi fushi sosai idan kika kara tashin ta, aure kuma ko bakya so zan aureki ni ina sonki, akwai rauni sosai ajikinki sekinbi abinda likita yace, dough akwai nurse dazata ke kula dake kwana nan" Bata kalleshi ba bayan ta gama karanta, kanta na gefe muryanta yana rawa tace
"Thank you so much Hammood Allah yabar k'auna"
Gabaki d'aya cikin sambatu Momy kaf seda ta gayawa Muhseen komai, ya tausayawa kalan rayuwar datake ciki, ya mata nasiha sosai sannan yaketa kwantar mata da hankali, ya sanar mata ba abinda ya samu khairiyya ta kwantar da hankainta.
******************
*Bayan kwana biyar*
Labari ya karad'e masarautar su khairiyya akan dawowarta, lokaci d'aya kuma aka yayata a inda ta b'oye. shimuwa Hammood ya gama gayawa mutan masarautar sa cewar suje nemar masa izinin a d'aura aure ranar asabar, gashi yau juma'a. mahaifinsa se murna yake inda Bahar keta masifa wannan dalilin ne ya sanya ta aika aka kira mata shi ita shida kawun sa da anty Barra.
Seda ta gama k'are musu kallo sannan tace
"Magana zakayiwa yaranka yasan me ake ciki, ni yanda mukayi dashi shine ze fara auran wannan yanzu kuma haka kawai seya sauta magana, idan mulkin wad'ancen ke rud'arsa karfa ya manta itama Hafsatun tana tak'ama da wannan mulkin, babu ta yanda za'ayi yamata rashin adalci irin wannan" Nisawa Jay yayi dama yasan za'a rina wai an ari zanin mahaukaciya
"Bahar kiyi hak'uri, ni a nawa ganin wannan yarinyar ki barta ta samu sauk'i tukunna, ba dad'i ace an aura masa ita had'e da wata tun yanzu suna kishi sannan kuma ita batada lfiya, a nawa hakan ma ze iya cutar da lafiyar ta amma yanda duk kika ce" Tsaki taji
"Watsewar duniya, wannan ai salon la'ana ne, ke Barra ashe dama mijinki bashida tunani me kyau, ita wannan yarinyar idan kukayi haka ai kun zalince ta, tunda maganar tace a sahun farko kafin ta wannan, kai munafikine wlh Hammude, inba munafurci ba da farko ai cewa kace baka san ita waccen ko? yamutsa fuska yayi ta wurga masa pilon kujera
"Kai d'an ranin hammatan me shayi ni kakewa gyatsine, toka gaytsini uwar ka da ubanka, yarinya kuma sesai a had'a auren su duka biyun" Barra ce ta sharb'e zancen sa cewa
"Ammu ki fahimci yaron nan, wasu tsegubguma yaji shiyasa ze auri khairiyyan yanzu, anma ai yafi son Hafsat ma, kawai dan batada lafiya ne shi yanzu yace so yakaita asibiti a turai ta warke asha biki, wannan fa ba wani bikin daza'ayi kawai yaji gulmar anaso a masa sharrin bin mata a waje shiyasa yakeso yaje da mace, shifa da farko hasaft din yaso suje tare ma amma semuka nuna masa lalurar ta ko? idan da munsan haka da bazamu bari me martaba ya tura sakon son daurin auren ba kuma kinga gobene warwarewa ze zama kamar k'aranta dan Allah kiyi hakuri Ammu" Nisawa tayi cikin takaici
"Idan ta samu lafiya muna daga cen zamu dawi ayi biki bazan kalli bak'in cikiba wlh" Haka akayita bata baki, shida gogan bece komai ba har aka tashi a taron.
****************
Hafsat jin labarin auren da mood zeyi ba k'aramin dad'i ya mata ba, harga Allah ita batason auren sa, yacika jinkai.gwanda ta nemi ajinta d'an talakawa wanda zasu rufawa juna asiri, ba wannan me kamada mutanen farkon ba akan kafiyar tsiya gajin kai. shirin tafiyar ta ma take zasuje US a k'alla zata ga duniya cikin jin gata, ba zuwan banza ba, ta godewa Allah ma daya kasance gaba d'aya babu me tambayar ta maganar iyayen ta, kowa ma ya d'auka cewar tayi loosing memory kamar yanda D'an galima ya tsara.
*Bayan d'aurin auren Khairiyya da Hammood*
Atare aka shirya tafiyar su dan batama tare anan ba, dukda ya bada gida a garinsa amma bata tare ba, sabida kwata kwata kowa ya rasa gane kan khairiyya wasu suna d'auka dan ammata dole ne, ciki kuwa hadda Annah, kullum ita ke taya jikarta kuka, dan kuwa khairiyya ba abinda take banda kukan nan tun dawowar ta, dukta fita hayyacinta dan harga Allah har zuwa wannan lokacin batason hammood.
*Shin ina labarin Bilal*
Bilal ya samu lambar wayar abokin sa daga baya, seda ya kwana ya wuni sannan ya samesa duk yana b'oye a hotel, mahaifinsa se kiransa yake dan ya dad'e beje gidaba, ya sanar dashi zezo shisa ya jirasa yafiso yayi ya dawo su taho tare danshi banda Baba Lami besan komai ba akai. Lokacin da abokin ya tashi ziyartar sa a hotel seda yaje sannan ya kirashi yace yazo ya rakashu unguwa Bilal yaso yak'i fita ganin goman dare ya gota amma se abokin nasa ya nuna mata wata harka zasuje yi dan haka suka fita, acen ya tilastawa Bilal dole seyayi sighning takardun gidansa daya rage kwaya daya akan ya barwa abokin sa, sannan seyana bashi miliyan 30 ze bashi kud'insa dasuke da yawa sosai, ganin baze iya ba ga bindogogi har uku akansa ya sanya ya bayar daduk abinda suke so yabar garin washe gari zuwa tawa Niger republic.
Bilal be b'oyewa mahaifin sa komai ba dangane da abinda yafaru tsakanin sa da momy, kawai ya b'oye abinda yayiwa yarta ne, bak'in ciki ne ya kusan kashe Baba, Baba Lami ta cucesa danba ita bace ta haifi yaran nan shisa zataci gaba da hura masa iskanci yanayi? lallai ya yarda duniya ba amana, akan abun duniya kabar yaranka yana zina, kuma sannan a had'a baki dashi ayi sata dan wannan satace babba ai bako k'arama ba, cikin fushi ya rantse se Bilal ya mayar da kud'in nan koya tsine masa albarka ko k'wamdala baze bar Bilal dashiba na momy, ko yanzu ya tab'a Allah da yawa momyn aiba dole ta masa ba bare yace, Bilal jin haka ya zab'i tsinuwar iyaye akan ya maida kud'in dan haka yace ai Nigeria da fad'i gwanda ya koma ya sauya gari.
***************
A jirgin zuwa US Mood a VIP yakaisu, inda kujerar Hafsat take fuskantar ta khairiyya, khairiyya batada labarin hafsat amma kallo d'aya tayi mata taji ta tsaneta, ta dad'e sosai bataga mace wacce tafita kyau ba, wannan haukar wacece ita kuma, takula yarinyar iko takeji dashi se shishigewa wannan Bahar d'in takeyi, kasa hak'uri tayi ta rubutawa Mood text tun kafin jirgin ya tashi
"Who is this girl? mesa zamu tafi da ita, bayi da kowa suna baya why is she with us? Murmushin gefen baki yayi ya replying nata da
"She's nobody, just a maid, kawai Bahar tanason ta kusa da ita ne shisa kika ganta anan" Kallon sa tayi da mamaki bayan ta karanta sannan ta kalli Hafsat
"Batamun kamada 'yan aiki ba sam, kalli yanda tasaka gwala gwalai" Tsaki yayi kad'an sannan ya manna mata reply
"Bahar tanason 'yar aikin sosai sabida marainiya ce, itace take mata wannan kashin kud'in, she's a maid and nothing more just treat her as one" Murmushi itama tayi bayan ta gama karantaw lallai zataci ubanta a hannuna, yarinya sekace aljana tsabar kyau, ta tsani me kyau a rayuwa, batasan mace me kyau sam.....Daganan jirginsu ya cira dama ana announcing saka belt sabida ana shirin yin boading.......
*Masu karatu banaji kun soma son wannan littafin tukunna, banaji munyi nisa ma a wannan tafiyar yanzu muka fara fa, yanzu book ze fara bada wuta, shin anya abinda hammood yayi ya kyauta kuwa ? yanaciwa hafsat zarafi da yawa a nawa ganin fa. Mu had'u a shafi na gama don farantawa juna rai nagode da kulawa amun afuwar rashin post kwana 2 please.*
Mom Nu'aiym.
*TSINTAR AYA* FREE BOOK
*NA: BILLY GALADANCHI*
*SUMOOD TACE TANA GAYAR DA DUK 'YAN MATAN HAMMOOD, KU SANI ITACE UWARGIDA*
*SHAFI NA GOMA SHA UKU*
Hada ido sukayi atake khairiyya ta wurgawa hafsat harara tana wani yamutsa fuska, hafsat mamakin duniya ne ya kamata aranta tace sabon salo gemu a kafad'a lokaci d'aya wani gajeran murmushi ya sub'uce mata wanda akan idan khairiyya, abun yayi matuk'ar baiwa khairiyya haushi uban me takewa dariya tana 'yar aiki? ita dai hafsat saukar da kanta kawai tayi asaman kafad'ar bahar tana turo baki irin na shagwab'abb'u, cikin kulawa Bahar ta kalleta tana murmushi
"Yarin yar nan idan mumaje k'asar nan naje na dawo za'asha fama, kefa sam bakya girma ko? k'ara turo bali ta sak'alo hannunta ya zago cikin na bahar sannan tace
"Ammu, bacci nakeji fa" Tab'e baki Bahar tayi
"Halin ja'irancin ya motsa kuma, se kace kina jinjira kina zuba wannan shagwab'ar dan kinajin bacci" Nan da nan idanta ya kawo ruwa
"Ammu nifa baccin gaske nakeji zo zan kwanta so nake nayi pilo da cinyarki" D'auke kai Bahar tayi, k'wallan idanta ya gangaro
"Ammu dan Allah fa" Sauke ajiyar zuciya Bahar tayi sannan tace
"Tozo ki k'arasani, ubanki yana biyana kud'in jinyar k'afana idan kika b'allani da sakarcin ki" Tana murmushi tana share hawayen ta
"Dududu how many kg nake waighying haba Ammu"
"Naji zo ki kwanta d'in" Ran Khairiyya ya b'aci gata ita za'a nunawa gata ita dakeda Annah, in yanzu takeson ganin Anna kuma ta k'irata a waya tace tanaso su had'u acen tanaga se hirgin Annah ya riga nasu U.S, d'an gajeran tsaki taja wanda Hammood ma ya jita sannan ta