Showing 93001 words to 96000 words out of 113608 words
wa aikin sirri se'a kashe Usman ko'a korashi inyaso seya zamana kai kad'ai kayi saura, bayan nan kuma sesu maka kisan mummuk'e kaida me martaba gaba d'aya kaga fada zata tashi babu makusanci se Jay! Wanda shi kuma k'anin matar sarki ne ze yak'i mutanen fada da rabinsu mutanen sane ciki haffa D'an galadima da Galadima shi seya d'are kujerar mulki, ina fatan ka fahimce ni?" K'ura mata idanshi yayi da suka kad'a sukayi ja, cikin tsananin mutuwar jiki yace
"Hafsat yanzu abinda kikeso ki gayamun shine gaba d'aya matsalar rayuwata makullin rayuwar tawane yake bud'ewa kowa k'ofofi da zasu shigo su cutar dani, barni haka Hafsat banason jin sauran mutuwa zanyi idan kikaci gaba zuciyata fashewa zatayi akan Mulkin dabeko dameni ba" kallon tausayi tayi masa sannan cikin raunin murya tace
"Yas Mood bazaka tab'a gujewa jin zallan gaskiya ba, gwanda ka saurareni" Bece komai ba taci gaba
"Gabaki d'aya Jay auren Barra dayake bawai soyayya bace ba, bayan kai d'an sarki, usman d'an sarki me rasuwa sekuma Barratu data zamto 'ya awurin Bahar wacce hakan ya bata babban matsayin zama k'anwar sarki kuma wacce zata iya mulk'ar k'asar ta kai tsaye idanda namiji ce, to bayan babu magaji se Barra lallai Mijin Barra da aka rena agidan shine ze zama magajin sarki. Ina fata na had'a maka wannan puzzle d'in cikin sauk'in daze baka damar had'e sauren kai tsaye, koda yake na manta ban gaya maka ba, ita Zulaiha itace tsohuwar budurwar Jay auren ta is part of their plans ai, gabaki d'aya kaga anan bazaka fuskanci soyayyarta a tattare dashi ba alhalin itace take k'ara taka rawar gani wurin tabbatar da ganin cewar ita Barratu bata haihu ba, idan Barra ta haihu ai shirinsu ya lalace dan tabbas gado ze fad'a a hannun d'an mace su kuwa kansu kad'ai suka sani dan basuda power a tasu k'aramar masarautar.
"Ranar daya ceceni a hannun Idan fad'a k'amshin turaren sa ya k'ara tona masa asiri, ya ceceni ne dan kawai in dena binciken sa yana nunamun cewar yanayi ne dankai a yanda na fahimta, wanda hakan shine ya k'ara nutsar da zargina akan tabbas shi mugu ne! A sanda yake kokarin ganin bayanka kaikuma kanacen kana wahalar da kanka wurin ganin bayan D'an Galadima alhali shi babu k'iyayya a tsaninku zallan kishin kane yake sabida shikuwa so yake ya zama d'an gaye kamar ka, gani kake kamar D'an galadima baya sonka kawai shidai yanaso ne kowa ya tsane ka, dukda tarin mak'iyanka masoyanka sunfi mak'iyanka yawa wannan shine hasadar sa. Tunani kake D'an Galadima ya turoni awurinka amma sam ba haka bane, banaso inta janka da surutu, a wannan audio's zakaji da kunnenka yana bayarda order akan akashe ka, zakaji labarin dana samu akan Zulaiha daya zamana tana tsanar Jay sabida yanxu shi kuma Jay so yake Barra ta haihun sabida kita dalilin d'an ze hau kujerar bayan ba ranka, sab'anin da daya zamana shine da kansa bayason haihuwar da ita. Jay ne ya aika a kashe Baba Surbajo satin daya gabata sabida ya gano tana bani informations sosai har sukayi nasarar zuwa..." Hannunta ya rik'e seda ta zabura
"Yayi nasarar kashe ta? Tausayin kansu take yau kad'ai wani iri takeji aranta gameda Mood gaba d'aya rayuwar sa yanayinta ne aduhu! Shafa gefen fuskarta tayi da d'ayan hannunta
"Na sauya mata wurin zama kafin suje kuma nasa ankama su, a bakinsu naji har abubuwan daban san dasu ba, kasan dalilin dayasa Jay yake hanaka magana? Kallonta kawai yake beyi magana ba, taci gaba
"Gaba d'aya yasan wannan masarautar bazata tab'a bari nakashashe ya mulketa ba, haka tsarin yake su kuwa wad'an cen sunasone su tabbatar kana magana su kashe ka, idan baka magana basa buk'atar sesun kasheka dan sunsan Idan Sarki ya mutu Usman za'a baiwa, shikuwa usman yana shirin kashe sarki amma yana tsoron ya kashe sarki ka bud'e baki! Theme biyu ne sukaje kasheku bayan kafito daga masallaci, da mutanen Jay alokacin dayakeda yak'inin ka bada salla a masallaci wannan ranar, se mutanen usman dasuma abinda sukajeyi kenan, harbi biyu akayi ranar kai mutanen Jay ne suka harbeka shi kuma Me martaba mutanen Usman ne suka harbe sa" Jinjina kansa yayi yaja majinan dake shirin zubo masa sabida kuka kafin yace
"Wacece Zulaiha? Auren soyayya sukayi da Jay tabbas amma daga baya yawan k'azantarta ya sanya gaba d'aya baya sonta nine ma nake rarrashin sa akan ya zauna da ita yaya yanzu kuma zakice tana masa wani mummunan aiki me kamada wannan? Nisawa tayi kafin tace
"Wannan shitasa akace mugu baida kama sam, wlh Mood gaba d'aya acikin duk wad'annan mutanen babu mutumin dayafi cutar dakai sama da Uncle Jay, sabisa ka yarda dashi amma shi burinsa kawai ya hallakar dakai yanzu dai saurari wad'an nan audios d'in" Ta k'arashe maganar tana kallon Ayatullahi, wanda shikuwa a take ya soma playing musu audi'os ko wanne da bayanin sa! Zuwa lokacin da yagama hak'ik'ancewa kansa Jay masifa ne kansa ya rigada ya soma sara masa bashida zab'in daya wuce ya kama kansa ya dafe, daga zaunen dayake jiri ya soma d'ebansa cikin tafiyar luu ta ya sulale ragwaf tamkar wani kayan wanki, sulalewarsa dayin kansa da dukkansu sukayi yayi daidai da harbin da aka yi ya ratso har cikin palon tako ina daga waje k'arar bundiga kakeji!
Mom Nu'aiym.
*TSINTAR AYA* FREE BOOK
*BILLY GALADANCHI*
*SHAFI NA TALATIN DA BIYU*
32.
Tsoro me tsanani ne ya kama Hafsat yayinda Data yace yana kallonsu a firgice, wannan harbin daya shigo ta window yabi, ginin bullet proof ne, harsashi bata iya huda ginin da kuma k'ofar sedai window d'in shi d'inma dan yana a bud'e ne, maza ku kowa daga kwance ya rerafa zuwa b'arin da ba window ku rab'u da gini" Ba musu aka soma gungurawa se Hafsat data kafe da hannun Mood dabesan me ake ciki ba yana zube a sume, Data ne kinkimesa ya kwantar dashi gefe take ya zari bundiga ya lab'e jikin window ya soma musayar harsashi dasu, inda yayi nasarar harbe bakwai daga cikinsu, uku tsuka gudu, har wannan lokacin Mood be farfad'o ba, Hafsat se kuka takeyi nak'in k'arawa tana jinjigar yayan nata dake tsananin bata tausayi, tare da ganin cewar tabbas ayau rayiwar ta ta k'are, sabida inba yanzu ba bata tab'ajin k'arar bundiga haka kamar saukar aradu ba se a film, ilahirin duniyar ta seda ta gigita, ganin komai ya lafa ya baiwa Data damar kiran waya police suka cika gidansa, sannan akayi k'ok'arin farfad'o da Mood, bayan ya farka aka kaishi d'aki yaso sosai barin gidan amma ina, Data kyakyawan tsaro ya tilasta aka baiwa gidan sannan ya fita farautar 'yan iska.
Jay zirga zirga yake a tsakiyar d'aki tamkar me yunk'urin nak'uda ilahirin jikinsa kuwa rawa yakeyi na yanda aka kama yaransa bakwai, dan an tabbatar masa dukkansu ba harbin mutuwa aka musu ba, maharbin k'wararre ne, idanda ze samu dama daga asibitin ze sanya a hallakar dasu gaba d'aya sabida gudun karsu tona masa asirin sa, tayaya abubuwa zasuke tab'arb'are masa kamar daga sama? Komai ya nemi muhalli ya darb'e wuri d'aya se jagulewa al'amura suke wannan wace irin rayuwa ce ta rashin 'yanci, tayaya Mood ze rayu da kwnan tonon asirin sa? Menene matsalar wannan tafiyar wai, wayarsa ya zaro ya danna kiran wata lambar kafin yace
"K'afa ya zakamun haka? Na sanar dakai ilairin gidan ku kashe su, Mood da Hafsat gaba d'aya inso samune a biznesu a gidan, yaya labari zezomun mara dad'i akan sun kasa? Cikin murya irinta 'yan daba K'afa yace
"Kad'an d'agamun k'afa me gida, wannan aikin daka bamu na kasada ne gashi ko kud'in k'warai ma baka biyamu ba, tayaya zaka tursmu gidan Detective gaba d'aya harsashi baya b'ula ginin gidansa, yanzu mekenan ka mana? Asaran Harsashi kokuma hasaran yaran aiki? Nazan d'agama k'afaba, duk yaro d'aya daya shek'a lahira akan wannan mission d'in sena huda cikinka da alburushi alk'ur'an" Cikin d'aga murya yace
"Kai har ka isa in fad'a ka fad'a, ni zakayi musayar yawu dani kaiga d'an jagaliya ko, daga kai harsu babu wanda ya isa wlh, sena girgiza tarihin kafuwar k'ungiyar ta addancin ku" Dariya irinta 'yan daba k'afa yayi kafin yace
"Kai bud'a danla gafara, ni zaka gayawa rashin suma aka?! Nafika jin tsinin balaga wlh tatas zan kwaye maka aiki, kasan fa sirrikanka a tafin hannuna suke ko? Kawai ka kiyayi kwayewar bayanka a hannuna, banza dako zuri'arsa be ragawa ba d'an ragga kawai! Yana kaiwa nan ya kastse kiran tare da cewa
"Ni Ranka ya dad'e zewa wowta kirawomun wannan Detective d'in sanar masa cewar K'afa ne zanzo muyi magana akwai aikin bud'a k'afa zan bada kai ne" Da mamaki yaransa me suna karan d'ori ya kallesa
"Oga anya haka zamuyi kuwa? Sosa sumar kansa yayi
"Gaba d'aya tun mutuwar d'an haza da kuma jikan malam na tsorata da harkar nan karan d'ori, kawai gwanda mu d'aga k'afa zamufi samun sassauci" Girgiza kai yayi shima cikin gamsuwa "Se Oga, hakan ma yayi sosai muyi hakan bara a masa waya kawai"
******************
Baya baya Barra tayi zuwa d'ayan d'akin tana sauke numfarfashi masu nauyin d'auka, gaba d'aya aduk halayyar Jay wannan b'anagaren ne bata yarda dashi ba, duk iyakar bayanan da Hafsa take mata duk tayi bincike tabbas hakane amma kisa, mijinta? Koda baya son nata kamar aka fad'a mata auren manufa yayi da ita bata kawo ze iya kisa ba, bare rayuwa ba d'aya ba, bazata iya bari wani yaji wannan maganar ba, zata rufe asirin Jay har k'abarinta bayan ta tallafi Family d'inta, wata zuciyar ce take raya mata taje tayi masa maganar kanta tsaye, amma tana tsoron abinda ze biyo baya a duniyar ta idan har Jay yasan cewar tabbas tasan bad'inin zahirinsa! Kamar daga sama ta ganshi akanta, hakan ne ya tsanantawa k'irjinta dokawa, mik'ewa tayi duk yanda taso adane bayanan sirrin dake zuciyar ta hakan seyaci tura dan kuwa firgici sosai ya nuna a fuskar ta, wanda baze tab'a b'oyuwa ba awurin mutum irin Jay da kamar shine ya raineta, gaba d'aya halayyarta babu wacce be sani ba. Takunsa ya k'arawa tsayi zuwa daf da ita yanda xuciyarta ke lugude kana jiyo sautin bugun numfashinta dukda k'arar na'urar sanyaya d'aki dake d'akin, tafukan k'afarsa duka ya d'aura akan k'afarta kamar yanda sukeyi a duk sanda zasuyi wata mu'amalar aure dake riskarsu daga tsaye, jikinta ne ya tsananta rawa gumi take har akan fuskar ta, d'age k'afafunsa yayi ya tura a k'ark'ashin nata ganin batada shirin yin hakan kamar yanda ta saba, sosai ya d'ageta sama ya kai hannayensa ya rik'o fuskarta sannan ya soma goga tsinin hancinsu wuri d'aya lokaci d'aya yana mata lilo tubda ya d'ageta da k'afafuwan sa, cikin wata murya dabata tab'a sanin Jay yana ita ba me razanarwa tare da nuna rashin imani k'arara yace
"Barratu amma kinsan banason lab'el" Janye jikinta take k'ok'arin yi daga nasa tana b'ata fuskar ta
"Ban fahimce kaba? Ta furta har lokacin tana k'ok'arin zame jikinta daga nasa, farcensa me d'auke da k'umba me tsayi ya caka sosai a kuncinta seda tayi k'ara wurin atake ya fashe ya soma jini sannan yakai hannunsa kunkurun sa ya sanya yatsunsa ya caka acikinta ya matse seda ta sunkuya, turata yayi ta fad'i ta buga bayanta akan gado nanma k'arar tayi tare da cewa
"Wayyo Bahar" Dariya yayi kafin yace
"Itama na tura a kasheta, matsala ce wannan tsohuwar arayuwata, zanma iya cewa barazana ce arayuwata, na tabbatar zuwa wannan lokacin an gamamun sa ita, bake wai me basira ba, bakewai kin iya wayau ba, halinki wan nene ban saniba, ko cewa akai dake bansan duk bibiyata da kike ba, bakisan komai ba har yanzu jahilar 'yar sarki, ba abinda kika sani tukunna sena kashe duk zuri'arki zakisan koni waye! A firgice tayi hanyar waje ya rik'o hannunta ta k'wace ya kuma kamota ya cillar akan gado
"Bahar data tsufa dukta rukub'e, idan na kasheta ba rage mata hanya nayi ba, watak'il ma wuta zataje amma inna kashe ta taje aljanna, kinyi kuskuren zurfafa bincike akaina dakin barni kawai da kaina zan karb'i mulkin in barki amma yanzu sena gama dasa miki azaba bayan azaba sannan in turaki rami, Bahar kuma na tura a akashe tsohuwa me diddigi" Mari ta sauke akan kuncin sa
"Kai Jay Barratu cefa da Bahar d'inka, kanka d'aya kuwa? Kodai nace wai bakada hankali ne, shaye shaye ka fara? Mari me gigita duniya ya dire mata
"Ubanki da uwarki nasha ba shaye shaye ba, banza me mugun hali, kina tsammanin zan baro masarauta tane haka kawai inzo nan in zauna sabida ku kuyita ci gaba, wabban mission ne daze zama successfull ko bakay so, dan kuwa anfi shekaru Ashirin da shirin sa,danma na saba da sanki ne, danma na saba da cinki ne, danma kinada dad'i ne Barratu naketajan abun da tsayi dan kawai inta cinki amma dabadan haka ba, aikema da tuni kin zama tarihi" A masife tace
"Idanda kana sona bazakantab'a cutar da ahalina ba Jay, mun maka dukkan adalci akan me zaka butulce mana? Akan meye bazaka duba halaccin muba ka tafi ka barmu babu cuta babu cutarwa, idan wani abu ya samu Bahar wlh sena d'auki fansa akanka" Wata mahauciyar dariya yayi
"Barratu gani kike tamkar duk wata hanya da Hafsa ta d'auraki akai me b'ullewa ce wannan shine babban kuskuren ki a rayuwa, ni banida niyyar cutar daku kamar yanda Sarauniya Maryama takeso, nida so nayi wai inna b'atar da Usman, sena k'arasa yayanki wato sarki bayan haka shi dama Hammood is answerable to me as u know, sena d'are kujerar mulki, ita Maryama dake tunanin in gama wahala tazo inhau mulki amma ina matsayin puppet king, tana mulkana senayi shawarar kaita fadar Sarauni ta huta! Bayan nan ke zaki zama Gimbiya Barratu, Zulaihaty zata Zama Sarauniya Zulaiha shi kuwa Hammood tuni na cire masa sarautar a ransa zance dashi danshi nake komai kinga ze barni na huta, Bahar idan taso kawomun wargi ita soma nayi in d'auketa daga kusa damu zuwa bayan masarauta kinga nayiwa kowa adalci kenan ko? Amma ke sabida dak'ik'iyace ke bakida wayau seya zamana kin biyewa waccen Hafsat kunata kawomun wargi gaba d'aya kunbi duk inda nakawo ku toshe, a tsammaninki bansan kina yawon neman duk wani sirri nawa ba, namiki shirune san ayanda nasan kwanyarki bataja nayi tsammanin bazaki gane komai ba se yanzu na fahimci kuskurena, dan kuwa na fahimci Hafsat itace take jujjuya kanki yanzu, ita kuma kaine da ita shegiya tamkar itace ta halicci kanta" Haryakai k'arshen maganar sa idansa na kanta tana hawayen bak'in ciki tace
"Honey dan Allah ka canja, dan Allah honey ka dawo kamar Honey Jay d'ina nada, ka sanar dani bakai bane wannan kace dani komai wasa ne ko mafarki nake kaji? Wayarsa ce tayi k'ara ya dena kallonta ya janyo wayar daga aljihun sa sannan ya kara kunne ya saisaita muryarsa, Bahar ce dan haka cikin girmamawa ya gaisheta tace
"Kuzo Fada kaida Barratu babu lafiya, daga mab'oyar daka kaimu anje harcen an kashe Sarki, nima da k'yar nasha wlh, yanzu haka harsashi seda yabi ta gefen hannuna ya wuce seda akamun dressing, muna cikin matsala Jay, kai kad'ai ka rage mana" Cikin Tashin hankalin k'arya yace
"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, me sukawa sarkin Bahar? Tana kuka tace
"Hatsashi suka d'ana masa a k'ahon zuci, gaba d'aya da tsaro me yawa mukazo fada ka kirawo Hammood a waya tin jiya be dawo ba, ni kirashi be d'aga kiranba" yana kuka yace
"Gamunan zuwa Bahar, Allah ya isanmu" Ya katse kiran tare dayin dariya yace yana kallon Barratu
"Hajiya Bahar ta kub'uta amma yayanki ya zama tarihi, abinda nakeso dake shine kokiyi shiru tamkar bakiji bakuma kisan komai ba a kaima kokuma wlh insaka a kashe Bahar, karki Kuskura koda Hamood ne ya gano wai wani halin nawa dabe saniba, ki zab'a rayuwar raggan uwarki ko rufe wannan abin dakika sani, kindai ga ko yanzu yayanki na kasheshi kai tsaye" Tana k'wallah tace
"Koma me zakayi kayi amma abu biyu nake rokon alfarma awurinka, na farko babu ruwanka da mahaifiyata ka barmun ita a raye har lokacin ta yayi, na biyu kuma.babu ruwanka da rayuwar Hammood ka barmunshi a raye, Mulki kuma idan har zaka bani matsayin Sarauniya inhau babban matsayi ka barni in rayu dakai kakuma bani dama in haihu namaka alk'awarin zamma taimakeka ta hanyar d'aurawa Hafsa manyan laifukan dazata barnan araunace yanda bazatayi marmarin waiwayarmu ba har abada,shikuwa Hammood zamu nuna masa be isa mulki ba se zuwa gaba kad'an! Kallonta yake cikin ido sosai yanaso ya gano gaskiyar zancenta a idanta kuma tabbas daga zuciyarta take furta kalaman cikin tsananin mamaki yace
"Bakiji kin tsaneni ba akan kashe yayanki danasa akayi? Share hawayen idanta tayi
"Banso ace kana kisaba Jay ina tsananin sonka bazan iya rayuwa in babu kai ba, amma kuma banaji kaine ka kashe yaya Tahir, gawar daba takaba kawai ka k'arasar amma naji tsananin ciwo jay, mesa zakayi tunanin ashe Bahar bayan duk tsananin son danake maka, da tun farko kace dani Mulkin kakeso.da tuni munyi yadda zamuyi Yaya Tahir ya baka kujerar" kallonta yake tabbas Barratu tana sonsa kuma zata iyayin komai akan sa, amma be zata abun yakai haka ba, cikin jimami yace
"Kiyi hak'uri hak'uri Barratu, banaji bana gani, bazan yafewa koma waye ze hanani isa akan mulki ba ciki kuwa hadda ke, dan haka yanzu ya zakiyiwa Hafsa" Murmushi tayi me ciwo
"Zan d'aura alhakin kashe yaya Tahir awuyan Hafsa, tunda ba'a kama makasan ba, zamu tilastawa d'aya daga cikinsu zuwa yace shine yayi kisan kuma Hafsa ce ta turasa, amma zamuyi arranging yanda zamu kamashi, inyaso semu bashi kamar 5.m seya confessing bayan an kamashi zamu masa dabara ya kub'uta, kaga Hammood tukunna besan komai akanka bare yayi bincike" kallonta yayi
"Amma kina ganin bata fad'a masa ba, sunafa tare tun jiya" B'ata fuska tayi kad'an
"Bazata fad'a ba dan bance ta fad'a ba, tin dama cen nace ta tufawa mijina asiri kaine dai baka sona" Rarrashinta ya somayi akan tayi hak'uri tare da neman yafiyar abinda yayiwa Yayanta Tahir! Nan tayita kukan mutuwar yayanta tace dashi tabbas dabadan shi bane seta tona masa asiri amma girman soyayyar datake masa baze bata damar yin hakan ba" Jay Se murna yake yayi nasara haka suka d'unguma fada...Jay yanata k'ok'arin