Showing 102001 words to 105000 words out of 113608 words
handle d'in k'ofar d'akin yayi daidai da d'auke wutan da akayi, tsaki yaja ya soma lalube a duhu, wayar sa ya lalubo ya kunna torchlight take haske ya mamaye ilahirin d'akin, akaro na hud'u kiran Hafsa ya kuma shigowa, a darare ya d'aga kiran, had'e da cewa "Hafsah bani mintuna biyu wan.... "Yaa Mood karka shiga toilet d'in dan Allah" Datse kiran yayi wannan yarinyar bazata fahimci dole seyayi wanka ze iya fita ba, akan me taketa sauri haka? Yana kama handle d'in toilet d'in tana banko k'ofar d'akin kuma a daidai wannan lokacin masu kula da gen d'in gidan gana d'aya suka tashi gen d'in, fincikoshi tayi gaba d'aya suka fad'i akan carpet dake wurin ta buga bayanta ya fad'o mata, yamutsa fuska tayi sabida azaba sannan cikin inina da shesheka azabar gudun data sha tace dashi
"Jay ya jona maka wayar dazata ma shorking a toilet kana shiga, please karka shiga" D'agata yayi gaba d'aya ya tallafeta zuwa jikinsa bayan ya zauna "Me kike k'ok'arin gayamun?" "Munrigada munyi abinda duk wayar da Gimbiya Maryama zatayi senyayi ringing a wayana, kuma zanji dik me take fad'a! Yayi waya da ita da wani layin yake gaya mata ya gudo daga station yayi amfani da kayan dogarawa yae basaja yashiga part d'inka,inshort (A tak'aice) ya sanar mata cewar ya had'a shock da wani wayan charger da sucket na toilet d'inka kana shiga ka taka ze baka shock ka mutu, abinda yasa naketa ma waya kenan" Tsatsare ta da ido yai,lokaci d'aya idanshi ya kawo ruwa. Cikin tausayin kansa yace "Hafsah nagode kinji, bansan mezan ce miki ba wlh,irin wannan gudun dakika ce u almost risk ur life for me inda kuma ajikin handle na k'ofar toilet d'in shock d'in yake fa, na tab'a kinzo kin tab'ani" Nunfarfashi take mayarwa sauri da sauri sabida gudun datasha, a hankali tace "Ka bani ruwa please" Da hanzari ya mik'e bayan ya kwantar da ita akan pillow daya janyo sannan yaje ya dakko ruwan roba yazo ya tsiyaya a kofi ya mik'a mata, zaunawa tayi sannan ta karb'a tasha seda nutsuwar ta ta dawo mata sannan tace "Jay bashida hankali gaskia, something is definately wrong with his head, ban tab'a ganin wawa irin saba, yana residing @ Shabana hotel room 113 3rd floor, nariga da na gaya wa Data sunkuma je domin su kamashi, amma yanzu intelligence agency department ze zauna" Kallonta yake yanda take magana har yau secondry school ma Hafsat bawai gamawa tayi ba, amma kanta yana matuk'ar ja, how beautiful! Kasa hak'ura yayi ya sumbaci soft chick nata na hagu sannan batare daya ankare ba yace "I so much like you Hasah, ur my world" Tsatsaresa tayi da ido sannan ta kawar da kanta tare da sakar masa gajeran tsaki "Ur making me unconfortable ka dena please." Dariya kawai yayi sannan ya kira waya aka turo masa Electrician, anan ya tsare Hafsat yana rirrik'e da ita ko wani motsi nata seya tambaya lafiya har electrician ya iso. Bayani yayi masa a atak'aice lokacin Har Data ma yazo d'aukan rahoto shida me hoto inda atake sukaga mugun tuggun daya shirya suka warware sunata mamakin muguntar sa, Mood se k'ara godewa Allah yake da irin baiwar dayayi masa wacce la shakka Hafsat baiwa ce babba a rayuwar sa.
Jay wurin da aka kawoshi ya kalla, mafi k'ask'anci acikin wurare, ko ina kashine sannan kuma ga mahaukacin zarnin fitsari! Tun farkon dare har zuwa asubahi banda tunanin rayuwar sa babu abinda yakeyi, meya tab'a aikatawa a rayuwar sa na alkhairi? Ilahirin rayuwar sa yayi tane a k'ark'ashin munafurci dacin amana, zuciyar sa batada kyau tun yana k'arami ya sani, duk abinda yakeso ko buri to tabbacin ba nasa bane ba, duk wani abu da wani ze mallaka shiyake k'wad'ayin samu! Tun yana abun a wasa har zamana da gasken gaske haka halayyar sa take. Zuciyar sa gaba d'aya setayi masa nauyi rayuwar sa setayi masa tsananin k'unci, lokaci d'aya se wata nadama mara iyaka ta shigeshi atake wani zazzafan zazzab'i ya lullub'eshi. Ya sani a duk duniyar sama bashida wata wacce yakeso sama da Barra, yasan yayita shirya mata yaudara amma tabbas soyayyar ta tana nan kwance a k'asan zuciyar sa, koda zuciyar sa ta gaya masa bayason Hammood, ya tabbatar k'arya take yi amma son da yake wa duniya ya rinjayi soyayyar su da har ta kai ta kuma kawo ze iya cutar dasu akan ya mallaki abinda yakeso mecece amfanin rayuwar sa. Yasan yana d'auke da mummunan ciwon zuciya amma ya yi imani da kalmar datake cewa cuta aiba mutuwa bace ba dan hakane be fasa neman duniyar sa tare kuma da neman lafiyar sa ba!! Sufyan shine mutumin daya fara zuwa wurin sa a wannan safiyar, sedai mamakin abin da aka gaya masa ya hana shi sukuni, atake ya tabbatar cewar lallai d'an adam ba'a bakin komai yake ba, Yanda sukazo da Jay jiya yanata turje turje yanzu kuma ace gashi bayama iya motsa d'an yatsar sa, ba shiri sika kwashe shi zuwa asibiti anan aka hau bincike nan da nan aka gano zuciyar sace ta kumbura sosai. Duk wannan rashin mutuncin nasa se dole aka kira yan uwansa wanda su Hammood ne. Maryama da farko an barta ta zauna agidan sarki kafin agama bincike amma daga wayar datayi da Jay akan kisan mood se kawai aka d'auke ta zuwa station dan haka su Barra sukaje masa asibiti anan ya hau neman yafiya kamar me, Hammood atake ya yafe masa, Barra ma haka, Zulaiha ta saci dukiyar sa ta gudu dan haka batanan har Jay ya shek'a lahira a wahale sabida zuciyar sa data buga.
*A gurguje please*
*Bayan sati uku*
Zuwa wannan lokacin an gama yankewa su Baba Usman da Maryama da duk wani me hannu a al'amarin hukuncin daya dace dashi a kotu. Dan haka kowa ya kama gabansa gidan yayi lafiya. Bilal yaci k'aniyar sa sosai dan kuwa am masa kaciyar k'arfin hali dukda momy ta tabbatar musu su mayar masa da dukiyar sa dan duk lalacewar da Bilal yayi itace sila, abu d'aya ne batada haKk'i a kansa shine muguwar halayyar sa mara kyau! Dan haka shida kanshi ya tuba yashiga taitayin sa ya komawa Allah.
***************
"Hafsah gaba d'aya abinda kike nufi ne bam gane ba, anyi anyi dake ki tare part d'inki babu abinda babu aciki sai ke, hatta hadimai da komai an zuba miki amma kin k'i ki tare kin mayar dani sakarai dabesan meyake ba, su Bahar sun zura miki ido kin mik'e k'afa kina abinda kika ga dama to wlh ki shirya yau zaki tare dan bazaki mayar dani sakarai ba" Turo baki tayi tana d'auke kanta gefe guda sannan ta ce da shi "Gaba d'aya so kake kamun tilas a auren ka sekace ana dole,nikam tunda nace banayi ana dole ne? Kallon takaici ya bi ta da shi sannan yace "Maganar banza zaki gayamun?" Tsaki taja masa gajere "kaine dai kaja koma meye auren namu na zobe ne da baze rabu ba?" Hannun sa yakai ya daki bakin ta seda tayi k'ara sannan ya ce "Idan har kika mayar dani sa'an ki duk maganar da ta fita a bakinki kikace zaki gaya mun kinsan Allah se na b'arar da rabin hak'orin ki, na gaya miki yau by 8 ki shirya ki tare tun muna shaida juna, na sanar da Bahar Saraki yana buk'atar matar sa" Tana rik'e da bakin ta daya daka ta ce "Doki ne ba saraki ba" Zabura yayi ze cafko ta ta ruga aguje tabar masa wurin seda tayi nisa ta tsaya ta waigo shi tace "Banya banya tunda kaci zali na" Gudu ya soma yi akan ya cafko ta ta k'arawa dokin ta linzami. Juyawa yayi yana dariya wato yarinyar nan gaba seta mayar dashi abun kwatance a masarau tar nan, gaba d'aya idan al'amarin wasu ne ta iya zama serious amma lamari idan ya shafe sa gaba d'aya koma masa takeyi wata irin yarinya 'yar shekaru sha biyu.
Tunda Bahar ta sanya ta a gaba akan seta koma ta shiga rikici, sam bazata je wurin Mood ba zalin ta yake ci, seda aka kirawo momyn ta sannan aka yi mata tilas aka kaita part d'in ta da sunan amarya.
Bata b'ata lokaci ba wankan ta tayi ta shirya acikin rigar bacci kara nauyi me asalin santsi kalar purple, ta tufke gashin kan ta da roba fara siririya a tsakiya. Har lokacin da Hammood ya shigo da ledoji a hannun sa bakinta yana nan da tsini tana mita. Da sallama ya shiga d'akin yanda ta kwasa aguje ne ya tilasta masa tsayawa kallon ta, hijabi ta soma nema bata samu ba,ba wani zani a kusa kuma kawai setayi cikinsa ta k'ank'ameshi
"Dan Allah kafita kafin inga hijabi na,ko ka nemomun zani in d'aura kaji" kallon ta yake yana mamakin meye hakan takeyi? Ba yau ya saba ganinta da suturu maka mantan wad'an nan ba, mesa zatayi haka?
"Ki sake ni mana, meye hakan?
"Yaya zaka ganni a haka wai? dan Allah ka fita waje" Sake kayan hannun sa yayi yana dariya "Naji bazan gan ki a haka ba amma tayaya to?" K'ara matse shi tayi ga gam "Fita zakayi waje mana" "Idan so kike na fita ba sai ki sakeni ba in fita, nifa na gano abin 'yan iska kike mun" bud'e idanta tayi da sauri taja baya sega kuka wiwi "Sharrin dazaka mun kenan? Ina kaine ka shigo mun har cikin d'akina babu sallama, tunda kamun sharri banya banya... bakinta ya kaiwa duka "Idan kika k'arasa fad'ar kalmar nan sena b'abb'a laki anan, maza zoki tattare kayan nan" kallon jikin ta ta kuma yi sannan tace
"Zan tattare amma dan Allah ka fita" Ma tsawa ya dinga yi kusa da ita tanaja baya har suka manne a bangon d'akin, yanayin fuskar sa ba k'aramin tsoratar da ita yayi ba, ya wani had'a rai tamkar be tab'a dariya ba, hannun sa ya kai a saman waist d'inta ya saukar da hannun a hankali sannan yabi santsin rigar zuwa bayan tsararta ya murza a hankali, numfashin ta yana sark'ewa ta d'age kanta a sama tare da rufe idanta, a hankali ya gangara da hannun sa zuwa saman mazaunan ta, wanda abun ya zo mata a bazata da sauri ta kai hannunta tana shirin b'anb'are nasa,hannayenta duka biyu yaja zuwa saman ginin ya manne su da bangon ya soma lalubar bakinta, janye fuskarta ta soma yi tak'i tsaya amma ta kasa magana, da hanzari ya rik'o hab'arta ya manna bakin sa da nata ya soma kissing nata tamkar mayunwacin zaki, tun tana k'ok'arin k'watar kanta harta sare da wannan ta barshi yafi 15mns a bakin ta seda ta soma jin zafi a saman lips nata tamkar ze ciresu ya wurgar. Yana sakin ta ta soma neman hanyar guduwa rik'o hannun ta yayi, a zabure ta kalle sa cikin tsoro sannan ta ce murya yana rawa "Kayi hak'uri bazan k'ara fad'an banya banya ba d'in tunda baka so" Ganin abinda yakeso yayi tasiri akanta wato tsoron sa yasa yace
"In k'arajin bakin tsiwa anan kin gama raini, maza ki tattare kayan nan ki nemo plate kizo nan" Kallon sa tayi ta sunkuya tana tattare wa amma k'unk'uni takeyi, hannunta ya rik'o ta kuma kallon sa a zabure, yana tsare ta da idan sa yace "Me kike cewa? Zo nan naga alama bakin ki bawai ya nutsu bane" k'walla ne ya taru a idan ta "kayi hakuri yaa Mood wlh na tuba har yanzu baki na zugi lips d'ina suke mun" Mik'ar da ita yayi tsaye "Da yana miki zuk'i baza kimun mita ba hajiya, maza zo in k'ara hora ki" Warce hannun ta ta ruga aguje "wlh gun bahar zan koma, bazan zauna kanacin zalina ba mugu kawai" Zama yayi akan gadon sabida yasan halinta ba inda be k'ulle ba ya zare key's d'in ya tabbatar yau akan daru a zaune zasu kwana.
Mom Nu'aiym.
*TSINTAR AYA* FREE BOOK
*BILLY GALADANCHI*
*SHAFI NA TALATIN DA BAKWAI*
*ƊAN ƊANO DAGA LITTAFIN SIRRIN MU*
Yadda kake tunanin rayuwa ba haka take ba,da lokota da dama kana iya gane SIRRIN wasu, Amma wani lokaci naka SIRRIN dake bibiyar Rayuwarka wahalar gane masa kake,Yau Uban daya haifesa ya kawosa Duniya shine da gansa ya masa sharri,Shi ne ya saka za'a kai shi gidan yari,Matar da yafi so fiye da komai nasa,wacce ta zame masa Uwa,Uba,Yaya,Ƙanwa,Aboki yau itace Mahaifinsa ya kwanta da ita har ta ɗauki cikinsa,Kuma yanzu shine ake cewa shi yay mata CIKIN,da me zaiji? Da nakasar da take damunsa?ko kuma da BAƘON YANAYIN daya tunkaro sa?Wannan SIRRIN MU ne bai kamata ace kowa ya jishi ba,SIRRIN MU ne nida mahaifi na,SIRRIN MU ne nida Matar da nakeso, SIRRIN MU ni da Aljanun da suke tare da ita.
_JAMA'A WANNAN MARUBUCIYAR CE DAI WACCE TA NISHAƊANTAR DAKU A LITTAFIN *MOON* DA *UNCLE NE* GA KUMA *THE NEW EMIR* SBD NIN DAƊIN MASOYA YASA SAI TA GAMA PART ONE ZATA FARA SAKINSA WANDA ZATA NA BAWA ƳAN *VIP* POSTING 2 KULLUM A RANA ƳAN *NRML GRP* KUMA POSTING ƊAYA A RANA NASAN KUSAN *NIMCYLUV* TAURARUWAR MARUBUCIYA MAI TASHE😂
ZAKU IYA PAYMENT TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423
Sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616
400 for nrml grp
600 for vip
Nima BILLYGALADANCI na shiryar tsaf domin karanta littafin *SIRRIN MU*
37.
Ihu ta k'walla ganin batada hanyar fita, iyakar k'arfinta ta saka tana jan handle na k'ofar fita daga gidan amma gaba d'aya nauyin k'ofar kad'ai ya isheta, dawowa tayi tana zagayar d'akunan dake part d'in gaba d'aya ko ina a k'ulle, zama tayi parlor akan kujera tana kuka a hankali. Kukan magen sataji acikin parlon shine abinda yafi tayar mata da hankali fiye da komai, takure wa tayi wuri d'aya har zuwa sanda magen tazo ta soma lasar k'afar ta, uwar k'ara data k'walla ne ya janyo hankalin Hammood daya ware kayan baccin sa yana shirin sakawa bayan ya fito daga wanka, da farko har ya so zuwa yaji me take wa ihu se kuma ya banza tar da ita sabida sabin hali da akace yafi sanin gari! Yana shirin saka rigar sa ya ware hannayen sa asama kawai ji yayi amfad'o jikin sa anan ihu, mamakin yake anya kan Hafsa d'aya kuwa? Wannan wane irin shashan ci ne haka? Zare rigar yayi yanda ta ruk'unk'u ne shi ta bayan sa abin ba'a magana, towel d'in jikin sa ya ware ya zame k'asa, shida kanshi k'ok'ari yake ya sunkuya ya d'akko towel d'in amma yarinyar yanda kasan biri haka ta mak'ale shi tana ihu
"Wayyo Allah na mage, ka taimake ni karna shiga uku na" Tsawa ya daka mata wanda ya tilasta mata sakin shi ta bud'e idan ta, amma me tana ganin sa tsirara agaban ta kawai ta kuma k'walla k'ara ta ruga da gudu tabar cikin d'akin! Tana zuwa dai-dai k'ofar fita ta kuma yin karo da magen nan tana k'ok'arin shigowa d'akin, aikuma da gudu ta dawo takuma mannewa da jikin sa "Na tuba nabi Allah na bika yaa Mood, rashin kunya wlh na dena maka" Murnushi yayi ya rik'e ta, ya hango magen sa daya shigo da ita ya tabbatar itace ta firgi ta ta, tabbas shi d'an gata ne abubuwan sazeyi maganin ta dasu kad'ai yake samu. A hankali a kunnen ta yace "Calm down mana, mage nane zance ta tafi yanzu, zance ta barmun Dholl na ta huta irin wannan firgicin haka" D'an nutsuwa tayi ta waiga ta k'urawa magen ido har lokacin tana nan mak'ale dashi. Zaunar da ita yayi ya matsa kusa da magen ya sunkuya ya soma shafar bayanta a hankali "My Lulu u go please, kina firgitamun popcorn d'ina kinji" Magen kamar tasan me ake fad'a kawai ta juya tabar d'akin shikuwa ya tira k'ofar sannan ya dawo ya zauna kusa da ita yace "Mutanen dake kewaye damu zasu zata yanka naman jikin ki nake a wannan daren inaci, maza tashi sallah zamuyi mu godewa Allah daya nuna mana wannan ranar" Hararar sa tayi ta turo baki "Tabb'un jam, lallai ma yaa Mood ka iya zak'ewa, irin wannan abun a littafi akeyin sa bawai a zahiri ba, suma sabida su taya annabi kashe arna ne, kuma su neman lada suke bayaga haka auren soyayya sukayi, amma kawai kai daga zuwan ka auren had'i sekace nayi alwala muyi salla, alwalo ne ma ba alwala ba Allah bazan ba" Da mamaki ya kalle ta yanzu kam "Godiya wa Allah ne kuma bazaki ba Hafsa?" Seda ta juya masa baya tace "kullum cikin godiyar Allah nake akan ni'imo min sa akaina, amma banaji wannan auren naka ya isheni hadda suyin sallah, idan sallah kake so muyi nemo wani dalilin banda wannan" Had'a rai sosai yayi sannan yace yana mik'ewa "My Lulu musmusmus" ya k'arashe yana wangale k'ofar d'akin da gudu magen ta antayo aciki inda gaba d'aya Hafsah ta kuma rikice wa,ta nemi yin wurin sa, ya kauce ya d'auki magen ya wurga ta wurin da take ta haukace ma sa tayi "Kayi hak'uri,zan mutu dan Allah ka rabani da magen nan, Allah daga yanzu ma dena maka musu har abada, muje zanyi alwala in maka naka, sallan ma kayi baccin ka zan had'a nawa da naka inyi" Kiran magen sa yayi yai fitar waje sannan ya ce yana nuna ta sa d'an yatsan sa manuni "Naga alamar sena bud'e miki wani faifan littafin halaye na kinga sabo acikin jerin babin dabaki san da zaman sa ba,maza wuce ki d'auro alwala" Jikinta yana makyarkyata ta wuce taje tayi alwala tazo ta zura wani zundu memen jilbab sannan ta shinfid'a sallaya. Bayan sa tabi ya jagoran cesu salla raka'a biyu kacal sannan yaja dogon addu'a fin awa d'aya harta soma jin bacci ma, seda ya idar ya d'akko soyayyin kaji a wata kular data kula tana d'akin tun kafin yazo amma bata bud'a shiba ya bud'e side fridge ya d'akko lemuka da youghurt yazo ya ajiye agabansu yace taci,