Showing 45001 words to 48000 words out of 113608 words

Chapter 16 - TSINTAR_AYA

Start ads

09 Aug 2025

691

Middle Ads

yamma" Beko kalleta ba, tace tana kallon khairiyya "Sannu khairiyya gani" A haustine khairiyya ta kalleta

,"Kutmar uba, kina 'yar aikin gidan nan ki kalleni ki kirani khairiyya gatsai, shi kuma sarkin gaba d'aya kike kalla kina wani yaa prince, agidan uwarki ya zama yayanki ko yaya eee? ko motsawa beyi ba bare ta saka ran ze amsa ta, kallon sa Hafsat tayi aranta tace 'yar aiki a sarari kuma seta kalleta tace

"Pardon? shafa sumar kai khairiyya tayi data baje ya sauka a saman kafad'unta kafin tace

"Wai mekenan, zaki durk'usa kiji kiran me nake miki kiyi gaisuwar girmamawa kosena hallakaki tukunna"  Tsaye kawai Hafsat tayi tana kallon ta, ruwan dake gefen side table me asalin sanyi ta janyo cup d'in ta antayawa Hafsat a fuska da jiki gaba d'aya

"Da uwarki nake magana dabazaki yi abinda nace ba" Nan ma tunda Hafsat ta zabura dajin ruwan sanyi ajikinta bata kuma cewa da ita komai ba, kallon Hammood tayi

"Dear yarinyar nan wane irin dama aka bata ne wai? ni zata raina haka idan agaban bayi tamun haka bata wulakantani ba, kuma kana kallo bazaka ce komai ba" Kallon su yayi dukkansu da hannu ya soma magana wanda hafsat ta k'ura masa ido tana kallon sa, duk abinda yake fad'a tana ganewa, suwa yanzu tafara sabawa da yan da sukeyi da Bahar da Uncle Jay

"She's just a maid do as u pleases" Tab'e baki Hafsat tayi tana shirin kuka

"Ammu na, kizo zasuci zalina ban musu komai ba" Harara ya wurga mata ta juya da sauri zata bar wurin khairi ta damk'o kanta tayi dragging nata agabanta, marinta tayi seda d'an kwalin kanta ya zare tace

"Who are you calling Ammu here? are you mad? k'ara wage baki tayi irin na yara ta soma doddoka k'afarta a k'asa

"Kika mareni ban miki komai ba,Allah kuwan sena gaya ki da Ammu, muguwa dake" Sumar kanta ta kaiwa cafka azaba ta sanya Hafsat ta k'walla k'ara lokaci d'aya hawaye ya wanke fuskarta sunkuyewa tayi ta juya suka fuskantar juna ta murd'e hannun Khairii abinda ya sanya tayi k'ara, hannu bibbiyu ta sanya ta tureta taje cen ta fad'a jikin Hammood suka afka akan kujera gaba d'aya, aguje Hafsat ta kwasa zuwa part d'in su, Hammood ma ya mik'e da sauri ya kalli khairii data soma kuka

"Am sorry babe are you hurt? tana kuka tace "She's too much" Be tsaya ba yana soma aikin gudun nasa yace "Dont worry baby i will deal with her" Yasha mamakin yanda Hafsat ta lashe aguje ta tsere masa, daga isarta d'akin kawai ta shige ta banko k'ofar hartana murza masa key, segashi shima aguje yaje ya banki k'ofar, da sauri Bahar ta rik'eshi

"Kurma hauka kake meta maka zaka biyota da gudu haka" Kallon Bahar yayi da hannu ya mata alamar wai ta ture khairii ta fad'i" Tsaki Bahar tayi

"Ta tureta ta ture banza, shine ka biyota haka kaiga me mata, kasani ko karo sukayi, Hafsat dai batada abokin fad'a, wlh tallahi idan ba la'ana kakeso ba kar inji kar inga hannunka akan K'anwar ka,tun yanzu zaka fara tare fad'a akan matarka da 'yar uwarka, hauka kake" Kallonta yake cikin b'acin rai da hannu yace

"Tana sani tayi komai wlh, ba wani karo bata girmama tane" Dak'uwa ta sake a fuskar sa

"Ta girmama ta uwarta ce? nace ta girmamata uwarta ce? sabon sanabe da kinibibi,dame take tak'ama mulki ko sarauta? itama tana dashi" Juyawa yayi yana k'wafa, tace tana bugar k'ofar

"Fito abunki Hafsatu Manga 'yar sarki, wacce maza ke rarrashi, inga wanda ya isa ya tab'aki fito abinki, waccen la'ananniyar ake cewa kin ture, yaushe kika tab'a tsokanar magana ma bare a miki sharri" Fitowa tayi tazo tana fiki fiki da ido, cikin shagwab'a tace

"Ammu kinga yaa prince ko, matarsa fa ban kula da itaba mukayi karo nina na buga goshi amma kinji me yake cewa ko" k'wafa Bahar tayi

"Barni da la'anannu duk zasu gane kurensu".

Koda ya koma part d'in bega khairiyya ba, yaje d'akinta ya tarar ta rufe da key, yayita knocking ta masa banza, iskanci nema wannan yabi k'atuwa da gudu d'uwawunta yana wani b'atar b'atar, ita ze renawa hankali? Gayen nan ya gane itafa auren nan neman rufin asirinta kanta kawai ya sanya ta yishi dough dai ta kula tanason zama wuri d'aya dashi he's so caring and loving also, amma batason ko kusa taga yana shiga shirgin hafsat.

******************

Bilal ganin ba wanda ya damu da nemansa kawai ya sanya ya dawo garin, gida ya nema ya saya abinsa yaci gaba da harkar kasuwancin sa daya dakatar yana k'ara yaga duk wata macen datazo gabansa, har gobe yana mamakin yanda akayi abarsa ta zama lagwanin dayasha kalanzir a ranar dayaso yasha zumar khairi, kuma ko yanzu in yabada hanta seya huta da ni'imar shegiyar, but seriously he's missing momy fa, ba wasu kud'in dake zuwar masa daga masa sedai na kasuwanci shikuwa ina zeyi almubazzaranci ya shiga uku...Bilal kenan.

Momy na zaune a parlonta itada 'yan aikinta, damuwa ta mata yawa, an sanar mata anyiwa khairii aure, amma su basuda tunani, kodai bata gayawa kowa bane? da wannan d'anyen jikin zasu mata aure, wanan tunanin shine abinda yafi cin mata rai sama da tunanin Bilal, shi kamma batada niyyan d'aukan wani mataki a kanshi, ta zalince sa tasani, amma ya d'eba da zafi, ba raping nasa tayi ba, ko seducing nasa laifine? tasan koma menene tunda Allah ya haramta ta halasta setaji wuya Allah ya kare mata martabar khairin ta, Allah ya baiwa mijinta hak'urin jure yanda ze sameta, k'irjinta ne ya doka tunawa da yanda take mayarwa iyaye yaransu da Bilal yake lalata wa su yaya sukeji ne? anya idan abinda takeji sukeji zasu rayu kuwa? watak'il duk bak'in ciki ya cikasu, in hakane dole naje in rokesu gafara.da sauri ta zaro wayarta tayi dilaing wata number yana d'agawa tace

"Muhseen kazo gida ina neman ka dan Allah" yana russunawa yace

"Ok ma zanzo yanzu".....A k'ofar parlon suna fitowa da mahaifin Bilal sukayi karo Baba!!!

********************
Sati biyu da zuwan su Hafsat U.S abubuwa da yawa sun faru ciki hadda komawar ta makaranta ss2 d'in, batada wata damuwa seta khairiyya, wacce a yanzu ita kuma damuwar ta Hammood ne, yak'i ya kusance ta sesai yazo ya mata wasanni suma sama sama, hug kiss on the forehead,on her lips,chicks sometimes amma iyakar sa nan, tunani take ko bashida lapia mesa baze nemi hakk'in sa agunta ba? kodai shima out of pity ya aureta amma baso a ransa?, Hafsat kuwa damuwar khairiyya takan ragu a duk sanda taje school ta samu new friends har su biyu, d'aya cylia sunanta 'yar America ce d'ayar kuwa sunan ta Chidimma bayerbiya ce a lagos take Nigeria, wannan k'awayen nata kuwa wayewa tana neman blasting kansu danji suke da kansu musamman chidi datayi shekaru biyu a U.S d'in tare take zama da family nata kowa yana nan, abunda ke b'ata ran hafsat duk befi wannan gajeran skirt d'inba iya cinya, gashi abubuwa suna nema su mata yawa sabida su basuda yalwar mata masu k'ugu irin nata, dan haka tanashan kallo..... Yau suna zaune awurin wani shan coffe itada cylia sun dawo daga school suka d'an tsaya sabida sanyi susha coffee, suna hirar su kawai sukaga wani kyakyawan saurayi a kansu kana kallonsa kasan ba bature bane yafi kamada larabawa yana murmushi yace

"Hii Am Bilal" Kallon sa Hafsat tayi ta d'auke kai Cylia ta bashi hannu suka gaisa ya zauna suka soma hira da cylia, duk yanda yaso Hafsat ta saka bakinta bata saka bakin taba har suka tashi daga zaman dasukeyi.....

Washe gari weekends ba school tana zaune a garden tana duba wani book nata sega Khairiyya tare da wannan gayen na jiya dayace sunansa Bilal, kallo d'aya ta musu ta tabbatar yan uwane sabida kamar dasuke, mik'ewa tayi zatabar wurin Bilal ya rik'o hannunta

"Hey pretty, me kike a gidan k'anwata" Warce hannunta tayi "Bakada hankali ne kake rik'emun hannu" Sake kamo hannunta tayi wannan karon tana warce hannunta ta sauke masa lafiyayyen mari a fuska mamaki ya sanya kawai yabita da kallo se khairiiyya ce tazo zata mareta yauma kamar ranar tureta tayi taje zata fad'i kawai Bilal ya rik'eta, tana juyawa zata gudu kawai Mood tagani agabanta, nan danan ta soma neman hanyar b'ullewa, seda sukasha zagaye tayi nan ya tare tayi cen ya tare sannan ta arce ta gefen sa ta runtuma a guje, dariya Bilal yayi yana jallon khairii

"Gidan nan baze tab'a zama boring ba, dole zan kwaso kayana inzo inta zama, whose that gal, i saw her yesterday at my coffee shop tak'i magana, k'anwar mijin kine? I like her!!! sosai kalmar yayan nata ya daki k'irjin ta tace

"Haba yaa Bilal, she just slaped u fa, kaga tarbiya anan kai sa'an tane? Allah ya tsareka da son waccen mayyar, tsintarta fa akayi" D'age kafad'unsa yayi "What ever" Tsaki tayi ta soma k'unk'uni ya rik'o hannun ta

"Share su, zokiji k'anwata zoki bani labarin dakika ce kinji..

*Hahhhhh to Readers ina fatan kuna lafiya, na gaisheku kyauta, bari inbisu da gudu inga zasuje kafin jibi dan nasan semun wuce gobe muna gudu lolxxx....

*Mom Nu'aiym.*

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*NA:BILLY GALADANCHI*

*Hajiya Maryam (Sakatariya) Nagode da irin k'ok'arin dakike mun, Allah ya k'ara d'aukaka da laifin basira, littafin Ido da tsakuwa yana tafiya yanda ya kamata, masoya Billy Galadanchi ku bibiyi litattafan Haj maryam akwai tarin fad'akarwa acikin su.*




*SHAFI NA GOMA SHA HUD'U.



Tana shirin shiga parlor ya rik'o ta, da sauri ya ajiyeta agabansa, tsatsareta da idansa yayi ita d'inma shi take kallo lokaci d'aya idanta ya kawo ruwan sanin cewar Bahar bata nan,muryan ta yana rawa tace

"Allah Yaa Mood sune suka tsokaneni, wannan yaran ne yake tab'ani, d'an iskane yanata rik'emun hannu na, nace ya dena ya kama ya rirrik'eni shine ni kuma sena.... sekuma ta k'asa k'arasa durta kalmar marin data masa, hannunta daya matse tak'e k'ok'arin ta wace cikin kuka tace "Yaa Mood please am sorry bazan k'araba daga yau kaji" Har lokacin hannun yake dad'a matsewa amma be sak'eta ba idanshi kuma yana kanta yama rasa mezeyi mata, wace irin mara kunyace yarin yar nan wai? yazata kalli babba girman Bilal ta antaya masa mari dan kawai ya rik'e hannun ta, she's so mean wlh, hannunta dake hannunsa yajata har gaban Bilar ya direta a durk'ushe yana had'e rai da hannu yayi mata alamar

"Apologize" D'auke kanta tayi dan bataji zata iya bada hak'urin, itafa dama hafsat she's very stubborn , ko a school zaka sameta ajerin masu zafin school abu kad'an ya k'ular da ita kuma acikin mutanen datake hurd'a dasu zakaga ba k'auyawa tanason waye wa, wasu sabida yawan rashin shiga harkar mutane datake suke cewa da ita she's very arrogant, juyo da fuskarta tayi suka kalli juna ya nuna mata Bilal ya kuma mata alamar

"Appologize" Nan ma bata dena kallon sa ba kuma batayi abinda yace d'in ba, zuciyar sa gaya masa take ya wanke ta da mari amma bayaso yake dukan mace ba halin sa bane ba, amma me yarinyar nan take nufi dashine haka wai? cikin fad'a sosai yanzu kam ya kuma mata alamar ta bada hak'uri amma bud'ar bakin ta se cewa tayi

"Shine ya dace ya bani hak'uri and thats what am waiting for, i did nothing wrong then why should i be the one to appogize, how can he just grab my hand d'an iskan inane shi daze kaman hannu na" Mamaki sosai ya k'aru a fuskar Mood what is this girl wai? ya tambayi kansa a sarari kuma masifa yaso ya fara da hannayensa Bilal yayi saurin cewa

"K'anwata am sorry, i really am, kinsan na rayu anan shenaru sunkai goma sha biyar, am used to, anan ba komai bane sam na manta da hakan shisa akeso kake zama tushiyar ka kodan gudun manta irin wannan abubuwan, amma God know's i mean nothing" Murmushi ta masa

"What ever" Tana shirin mik'ewa Mood ya saka k'afarsa ta durk'ushe awurin da hannu ya kuma mata alamar "Apologize now" Tab'e baki tayi

"Wainikam baka ganewa ne? shi yama fika hankali ya gane me nake nufi dan kaga ya bada hak'uri" Damk'o kanta khairii tayi

"Me kike tunanin kice? cewar Prince dak'ik'i ne kome? ke kanki d'aya kuwa? Yauma kamar ranar haka ta durk'ushe tajuya fskantar khairi hannun ta ya langwashe ta k'walla k'ara kuma dole ta sake mata sumar da har hular kanta ya fita ta barbaje, hannu bibbiyu ta saka ta tureta taje cen Hammood ya rik'e ita kuwa ta kwasa a guje sumar kanta daya baje kamar wata haihuwar indiya tana gudu sumar kan nata tana shawagi sabida gyaran datasha an kashe kud'i wurin gyaran ta sosai, dan kuwa Bahar ba baya ba akwai tsafta, Hammod tsaye yayi ya rik'e k'ugu yana kallon ta shi kuwa Bilal yana dariya yana tafa hannu yace

"That funny thing, she's very honest inason mutum me irin halinta, so staright forward, gaskia tafimu gaskia" Kallon takaici Hammood ya masa yama rasa mezeyi, kawai barin wurin yayi. Kallon 'yar uwarsa yayi yace

"Khairii be very carefull with that girl, nasan ki da fad'a da tsanar me kyau, that poor thing u see there ko, zatayi wuyar sha'ani a murd'e take kaman namiji karki rik'a cewa zaki shiga sha'anin ta kinji ko? Murmushin yak'e tayi sannan tace

"Yaaa Bilal i really want to get rid of her, na tsani ganin ta agidan nan wlh, yarinyar batada kunya" Yana murmushi yace

"And she's beautiful nasan ki da tsanar masu kyau karki damu da wannan my sister is the most beautiful of all, by the way who is she? badai k'anwar saba naga suna kama" Wara ido tayi cikin takaici

"She's just a maid ba, k'anwar safa Allah ya kiyaye" Dariyar sa ya kumayi yana tafawa "You most have gone crazy, maid? lallai kin manta ma, kinsan school datake zuwa a garin nan is the most expensive of all, yaran masu kud'i sosai ne suke zuwa wannan school d'in idan me aikine ita waya saka ta" Tab'e baki tayi

"Allah kuwa yar aikine, wai uwar sarkice take mugun sonta shine ta 'yanta ta kaga tana rainawa mutane hankali" Murmushi yayi

"Ohh is that so, but still she's cool ai" Bata kuma magana akan Hafsat ba tace dashi

"Is mom still calling you? yana kallonta yace

"Kin manta na gaya miki tafi 4weeks bata neman a waya ha, dama ba d'agawa nake ba, inaga ta huta abinta" Nisawa tayi kafin tace

"Yaa Bilal what am about to tell u now is the most terrible and traggic story da inaga ka tab'aji arayuwar ka, but i have no option there is no one i can share this secret with except u, bayita dannan zuciyana akan karna gayawa kowa but the is ko" tayi shiru tana kallon sa da hawaye a fuskar ta shima ita yake

"Its really killing me inside wannan abun shine zeyi ajalina idan nayi shiru" Da sauri ya kalleta "Subhanallah khairr, wannan wane irin magana ne?" Zaunawa tayi shima ya zauna tana share hawayenta tace

"Wannan auren nawa dakake ta tambayar dalilin dayasa aka yishi agurguje bakanan bakama sani ba to dalilai biyu ne suka sanya kaga anyi auren nan, Na farko mijina kurma ne sanda aka bashi aurena na nuna bana so harna gudu daga gida wanda na tabbatar an gaya maka wannan, na biyu kuma dalilin dayasa na amince ina dawowa da maganar auren sabida ammun fyad'e ne" Cikin tashin hankali ya kalleta

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, khairiyya yaushe haka ta faru ban saniba? share hawayen ta tayi

"Babu wanda yasan ammun fyad'en dagani se wanda yamun fyad'en se momy se kuma mijina" Mamakin sane ya k'aru
"Momy kuma da mijinki? why ? nisawa tayi sannan a hankali ta soma labarta masa komai har kawo aurenta da Hammood ta k'ara da cewar

"Ni abinda yake damuna shine gaba d'aya na rasa meya hau kaina na gayawa Hammod sirrin mahaifiyar mu tabbas bana cikin hayyacin kaina, gaya masa sirrin momy yafi damuna akan maganar abinda Bilal yamun, ze iya tausayamun akan ba laifina bane amma mutuncin mahaifiya fa, anya Yaa Bilal inada kai kuwa? meya kaini gaya masa? mema yasa na masa bayanin wani abu? gabaki d'aya narasa yanda akayi nayi wannan katob'arar, narasa meke kaina, narasa inda hankalina ya tafi, mutuncin mahaifiya na sayar na tona mata asiri duk sanda na tuna wannan abin it keeps hunting me" Nisawa yayi yana d'auke hawayen idansa kafin yace

"Am so sorry khairiyya, duk wannan abun ya faru dakene sabida am not a good brother, da ina kusa dake bazaki bi shawaran wani banza ba, nice na wofintar dake nabarki bana tuntub'ar inji me kike ciki,ki gafarceni k'anwata kinji, wannan abun da Bilal ya miki na godewa Allah dabe samu sa'a duka a kanki ba, dana shiga uku, momy kuwa banaji abinda take ya shafeni ko wanda tayi itada Allah abu d'aya na sani dolene mu mata biyayya, dolene mu saurareta mu mata wa'azi, dolene mu kwantar mata da hankalin ta, dolene ayau musan me take ciki, bata kyautaba data lalata yaran mutane amma shima k'wad'ayayye ne and for abinda ya miki wlh senaga bayansa acikin ruwan sanyi, seyasan cewa ni Bilal sunan mu kawai iri d'aya amma hali yasha banban, abinda kika gayawa mijinki ki manta dashi kawai haka Allah ya tsara ba tsarinki bane ba, amma dolene kiso Hammood idan de ke 'yar halas ce, dolene ki masa biyayya ki kuma so duk abinda yakeso He sure is a good husband"Nisawa tayi cikin jimami

"Now i am relieved, now i can rest, now i can sleep in peace, at last na gaya maka abinda yake cina, maganar momy dakake cewa yaya zan b'ullowa labarin toh? nifa ta gagara ma ko kirana a waya" Murmushi yayi yace

"Allah sarki Momy, bazata ita kiraba ai, Allah ya k'yaleta tanata aikata masha'a tazata taci bulus ashe akanmu abin ze k'are kada ki damu kinji, zan kirata a waya anjima zan bata numberki na nan ita da kanta zata kiraki, ki dena damuwa kinji" Jinjina masa kanta tayi alamun to sannan sukaci gaba da tattaunawa.

***************
Mood bebi takan Hafsat yayi tafiyarshi yabar gidan, sanda ya dawo ma

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login