Showing 90001 words to 93000 words out of 113608 words

Chapter 31 - TSINTAR_AYA

Start ads

09 Aug 2025

698

Middle Ads

haihuwa shiru.

Wata Raba yara sun tafi yawon farauta wacce take ta al'adace sukan d'auki kibau suje farautar b'eraye ko burguna da zomaye acen aka dawo mana da gawar duk au biyun, a yanda aka sanar damu Zaki ne ya ritsastu abinda muka gani ajikinsu tabbas yagace sosai wannan ya sanya aka je neman zakin amma babu labarin sa a wannan dawar, dan haka mukabar maganar sa akayita jajantawa sarki, Bayan shekaru uku sega ciki ya bayyana acikin Maryama wanda iko da mulki a lokacin ya tashi, har akam Mulkin taga Sarki Tahir yanaji da ita sabida cikin ta d'akko k'anin ta daga masarautar su acewarta tunda mahaifiyarsu ta mutu ake wulak'anta sa me suna JAY. Alokacin dayazo ganin girmansa ya sanya gaba d'aya Tahir yace ya dawo masarautar sarauni awurina inda nice na rainesa alokacin yanada shekaru goma nikuwa ina rainon Barra ya kasamce sun taso atare shine uban rainonta.
Babu wanda yasan da ciki ajikin Surbajo se ranar da akace Maryama tana Nak'uda anan itama aka sanar akan nak'udar take, nayi mamaki sosai dukda na dad'e ina zargin cikin nata amma ban nuna ba sabida ta b'oye kanta tun mutuwar yaranta, haka aka had'asu d'aki d'aya da ungozoma ta masarautar ta karb'i haihuwar su rana d'aya a tare!!!! Dukkansu kusan atare aka sanar da haihuwar su cewar Maryama ta haifi D'a Namiji ita kuwa ta haifi Tamace sedai ta macen ma takoma, fada ana murna ana kuka haka aka wuni akai kwana bakwai aka samu Namiji D'an bahillace kyakyawa sosai yana tsananin kamanni da yayan sa Marwan amma shi seyaci sunan Hammood, Maryama tanata iyayi itace me magaji hankalina yak'i kwanciya nidai banga gawar 'yar jinjirar surbajo ba amma kullum ita kuka take babu bakin magana daga bisani cutar Hauka ta kamata yanxu haka tana nan a masarautar yamma ana kula da ita, hakanan yanayin kamanin Hammood da yaran Surbajo a wancen lokacin ya sanya akayita gulmar cewar kamar Surbajo.ta haifo Hammood amma waya isa yace haka uwar tanata fara'a akan yaro jinin 'yan uwasa marigaya ya d'akko kuma kowa yasan ze iya kamanni dasu koda kuwa uwarsu suka yo. Ana haka Ungozoma tazomun da wata magana me girma amma senak'i aminta jikina yana rawa sena kwasa naje gun Maryama amma me daga ranar dana b'ulguta mata kwanan maganar se gaba d'aya ta dawomun kurma tak'i bud'e baki tayi magana nayi nayi wai tanaji amma ammata asiri bata magana akan haka ta kwanta ciwo har rainon Hammood ya dawo hannuna inda adole Jay ya dinga kulawa dashi. Iyakar abinda zance dai shine Hafsa Jay yana matuk'ar k'aunar Hammood yaran nan harya shekara 2 lafiyar sa k'alau kawai daga baya ya dena magana, haka seda ya shekara goma da taimakon addu'a ya soma ji amma baya magana, nafi shekaru goma da sanin maganar sa ta dawo amma narasa dalilin Jay na hanashi bud'e baki, ban yadda da kowa ba hafsah har Jay, banaji Maryama ita tahaifi d'an nan, Jay ya auri Barra kafin in gama gano cewar bashida hali me kyau dukda zargi nake amma yana tsananin bani tsoro bansan komai ba se zargi amma akwai abinda yake faruwa ta k'ark'ashin k'asa tun sanda ya k'ara aure na fahimci hakan, har yau Maminku batawa kowa magana amma tanayi da Jay, abun tamabaya anan shine akanme batawa mijinta magana tsawon shekaru a zuwan maganarta ya d'auke yayita yawo k'asashen duniya sunce lafiyarta k'alau muka barshi akan asiri ne, har yau batawa kowa magana se Jay shi d'inma a asirice bata san na saniba shin akan me? Har gobe batada kyakyawar alak'a da Hammood shin akan me, ga usman da tashi tawagar yace mulki na ubansa ne rik'on k'warya aka baiwa Marwan harya barwa Tahir a maimakon sa, gaba d'aya na rasa gane komai akan masarautar nan, badan komai nake kuka ba sedan ganin bansan halin da zuri'a ta take ciki ba, kullum addu'a ta anan itace kar Allah ya karb'i raina senasan ainahin gaskiyar wacece mahaifiyar Hammood, menene tarihin ciwon Surbajo, mesa gaba d'aya Tahir baya maganar ta koda yakaita turai kowani wurin neman magani, waye Jay? Meyake acikin zuri'ata? Su waye suke neman ran Hammood? Wannan itace damuwata Hafsa" Cikin tausayi hawaye yana zuba a idan Hafsa tace

"Wannan al'amarine me rikitarwa, wannan duka labarin a dunk'ule yake abu ne dayake neman fashin bak'i akowace kalma, gaba d'aya rayuwar tundaga kan haihuwar a baud'e take, banaji Jay yana turbar damuke masa fata amma kuma Mami! Bantab'a kawota a macuta ba, sedai kuma a maganar farko ban yarda da itaba, akwai zambo a juyewar samartakar gauro, ki kwantar da hankalinki Bahar zanyi amfani da zamani insan me ake ciki a wannan rumfar me duhuwar gaske, ban saniba ko zamuyi aiki a tare? Bahar tana kallon ta tace

"Ashekarun k'uruciya ma ban tab'uka komai ba se yanzu da tsufa ya dabaibayeni" Murmishi hafsou tayi kafin tace

"Ki koma Nigeria Bahar, aiki yanzu yake akanmu, so nake ki bibiyi dalilin b'arewar cikin dake jikin Anty Barra dan ni ban yadda da wannan aikin na rashin haihuwar taba" Da tuhuma Bahar ta kalleta

"Me kike tunani kuma ata ina zan fara? Murmushi me ciwo tayi

"Ki nemi likitan daduk ya dubata a asirce, yanada kyau ki fara amfani da ruwan darham na wannan daular, ki siyeshi da kud'i kisan menene asalin abinda ya b'arar da cikin! Barin Bahar U.S kuwa tazo gun 'yarta cikin hikima seta gabo wani abu, cewar tabbas Uncle Jay shine yake bata k'wayar hana d'aukar ciki a hikimce kuma duk indai zata samu seya zubar! Lokacin da hafsa nan a bada labarin Mik'ewa tsaye Hammood yayi

"Hafsa wai kanki d'aya kuwa? Mik'ewa itama tayi

"Idan ka fara haka a yanzu yaya zakayi idan kaji sauran labaran? Inyi tsammanin zaka zauce mana inna tabbatar maka cewar Surbajo dake a turu itace mahaifiyarka ta haihuwa!

*Mom Nu'aiym.*


*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

      *BILLY GALADANCHI*

        *SHAFI NA TALATIN*

*HAFSATY AN RIGIMA GA SHAFIN DARE NAN NA SAUKAR MIKI DASHI,NADAI CIKI ALK'AWARI KO?😂


30.

Maganar data fad'a ne ya k'wank'wasa kansa akan labarin daya gabaci wannan, hannayenta ya rik'o ita kanta seda ya bata tausayi jikinsa yana b'ari kansa yana sara masa yace.

"Hafsa please tell me more, banaso ya kasance tunanina ya tabbata gaskia ne, its being long danaga Baba Surbajo, nakanje gaidata Bahar tana turani wurin ta sosai, apart from Uncle Jay Baba Surbajo kad'ai tasan ina magana, that woman suffered alot, tana fama da matsaloli lafiyar ta k'alau but she still have to act like she's mentally ill, when ever i visit her, tanamun nasiha wa'azi and tana yawan gayamun cewan she's doing everything for me, Hafsa kin tab'a ganinta, muna kama sosai ko? Sadda kai k'asa hafsa tayi hawaye yana zuba daga idanta sabida tsananin tausayin hammood dataji ya kama, muryanta yana rawa tace

"Nikanje gayar da ita sosai Hammood she help me with alot of information, she's ur mother she loves u so much yaa Mood,  she endue everything alot of pain just so you live, am sorry to say amma gaskia Uncle Jay da Mami bazasuga annabi ba" Had'e jikinsa da nata yayi yana wani kuka me sauti tare murza bayanta da hannayensa da k'arfi, sosai ya matseta dankuwa taji zafin matsar gunjin kukansa ya sanya ta sake wani kuka meban tausayi ita kanta se yanzu abubuwa suke dawo mata sosai, lallai an cutar da Mood, acikin k'ank'anin lokaci Allah ya taimaketa tasan komai dole ta kwantar wa Mood da hankali, wannan shine time datake jira tayi calming nasa, cikin murya k'asa k'asa tace kusa da kunnenshi

"Ka saurareni , ka kwantar da hankalinka muyi mahana Yaa Mood, ka d'auka duk abinda zakaji jinsa shine mafi alkhairi agareka kaji" Data ne ya mik'e ya janyo hannun sa shima ya soma ban baki "kayi hak'uri Hammood, dama haka rayuwar nan take ups and down ne sukayi yawa acikinta, dik abubuwan dazakaji tamkar a film kawai akeyinsu wlh anan ma anayi a duniyar zahiri sukan faru, balantana rayuwar sarauta mutane da Mulki da kuma Kud'i suna iyayin komai a kansa, akwai labarin wani gidan sarautar dana sani d'a ya kashe mahaifin dayake gargarar mutuwa yana fama da ciwo shekaru kusan biyar be mutu ba kuma be bashi sarautar ba kawai yaran nan ya kashe uban yace ya gaji da jiran sa tunda shi mulki yake so, ashe naka bame sauk'i bane ba? Ehm Hammood" kwantar da kanshi yayi ajikin Data tamkar wani k'aramin yaro yashiga sauke gaurayen ajiyan zuciya, seda Hafsa ta hadiyi zuciya sannan taci gaba

"Lokacin dana ziyarci Baba Surbajo kallo d'aya na mata k'irjina ya doka sabida tsananin kamannin datake da Mood,lokaci d'aya na harbo bakin zaren, sabida ita kuyangar dataje da maganar awurin barra batada cikakken ililmi akan meya faru a wannan daren da lokacin haihuwar, bayan na zauna kusa da ita na gaisheta bata amsani ba haka kuma bata nunamun hankalin ta sosai yake ajikinta ba, seda nai gyaran zama nace ina kallon ta

"Baba ina wuni, ya lafiyar jikinki? Bata amsani ba har lokacin wannan ya sanya kawai na zauna na kama kanta nayi addu'a tare da mata fatan samun lafiya sannan a tak'aice nace da ita

"Baba nizan koma, sabuwar 'yarkice Bahar tace inzo in gaisheki, me martaba ne yake matsayi  uban rik'ona a yanzu ta sanarmun rashin lafiyar ki tace kema uwatace ina miki fatan alkhairi" Da wannan naga ta bini da ido, kallon datamun ya dasa wani abu a raina harnabar wurin bata dena kallo naba, a k'wayar idanta na hango tsantsar k'auna, tabbacin cewar tana tsananin jin duk abinda nake cewa, a hakan na kasa bacci a wannan daren ban yadda batada lafiya akai ba, inada yak'inin garas take,mesa take pretending? Kasawar hak'urina ya sanya najewa Bahar da maganar lallai Baba surbajo lafiyar ta k'alau kokuma dai ta warke, da farko bata yardaba akan cewar cutace datak'i samun waraka fin shekaru talatin aduniya amma dana k'ara komawa namata addu'a sanda zan tafi seta rik'e hannu ta k'ara mayarwa akanta alamun tana buk'atar addu'an fiye da yanda nake mata, dan haka sena k'ara k'aimi na d'auki tsawon sati d'aya ina zuwa ahaka harna soma samun damar tana mun magana, lokaci zuwa lokaci sedai na kula cewar a sirrance takemun magana dan haka wata rana senaja bahar mukaje wurinta acikin talatainin dare, wanda na jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya a wannan daren, na farko A ranar nafara yin arba da mutan k'ungiyar aci duhu, aranar kuma mukayi nasara Baba Surbajo ta bamu cikakken labari akan lokacin haihuwar ka, tace damu.....

"Bayan na samu ciki sena dinga b'oyon cikina, badan komai ba sedan dalilai guda biyu na farko dai sabida an tabbatar mun da cewar Maryama itace ta sanya aka kashemun yarana guda biyu, nayiwa Me martaba maganar a wancen lokacin amma se gaba d'aya ya nunamun be aminta ba gulmar gidan sarauta ne! Na biyu kuma an tabbatar mun dacewar tace bazata k'ara barin ciki yayi k'wari ajikina ba ga wannan cikin nima bansan dashiba har seda ya soma motsi, nayi mamaki sosai danko girma bayayi, haka nida kuyanga ta ta wancen lokacin muka rufe maganar, ga mamakina rana d'aya ina lissafin ciki wata bakwai sega nak'uda gadan gadan, kuyangata taso sosai ta karb'i haihuwata da kanta amma se haihuwar tazo da gaddama yasa dole ta sanar a Fadar me martaba inda ala dole aka had'ani da Maryama wacce a lokacin itama tana gargarar haihuwa. Dukda azabar datake ciki hakan be hanata d'agowa ta kalleni ba tace cikin bak'in ciki

"Yanda kika b'oyemun wannan mugun cikin dake jikinki sena nuna miki iyakarki idan har na haifi Mace ke kuma kika haifi Namiji" Bance da ita komai ba kawai na kawar da kaina abinda nakeji a lokacin ya isheni, haka inaji ina gani aka sallami masu taimakona ya rage dagani se ita sekuwa Ungowar zomar dabata amsa umarnin kowa sena Sarauniya Maryama. Itace ta fara haihuwa kafin ni sedai Na mace ta haifa, akan idona ta kawar da kanta gefe sanda aka nuna mata yarinyar sannan tace

"Banason ganin ta tazone takanas danta wargazamun shirina, so take ta lalatamun duniya ta, tanason kafawa bayana mummunan tarihi, inzo in k'are da haihuwar mace! Akan me gwandamun mutuwar ta da rayuwar ta akan rayuwar ta" Ungowar zoman ce ta soma bada hak'uri tana ban baki, a lokacin nikuwa wata azababbiyar nak'uda ta tasomun wacce tasa nakusa fita hayyacina koma ince na fita hayyacina! Cikin ikon Allah sena haifo yarona Namiji santalele me tsananin kamanni da yayunsa marigaya, koda na dawo hayyacina abinda suka bani shine abinda yafi bani tsoro Maryama ce rik'e da yaron tana murmushin mugunta, ta kalleni kallo me kyau tace dani

"Surbajo ya rage naki ki zab'i d'aya daga cikin biyu abinda zan fad'a, kindaiga iyani dakene se Ungozoma a d'akin nan ko? To kodai ki amshi wannan yarinyar data rigada ta mutu a matsayin abinda kika haifa kokuma wlh tallahi summa tallahi billahi in kashe yaron nan har lahira yanzu yanzu in sauya akalar zancen, zance kin haifi mace kin kashe danna haifi Namiji, kuma kin had'a harshi muna k'ok'arin k'arb'arsa kika kashe shi zan sokawa kaina wuk'a a kafad'a duk ince kece kika sokamun, kinga dai gaba d'aya bayan kinyi asarar d'anki zakuma kiyi asarar mutincin ki k'arshe kema a kasheki a banza" Cikin bak'in tashin hankali na mik'e jiri yana d'ebana nace cikeda rauni

"Maryama wace irin mara imani ceke wai? Yanzu jinjirar nan kasheta kikayi? Hankali a tashe na karb'i yarinyar hannun unguwar zoma ina kuka ita kuwa seta baiwa unguwar zoma jinjirin hannunta tace

"Yauwa yanzu kinga 'yata tana hannunku, tsaf dani na shiga wanka in kimtsa kaina in fito na tarar kin shak'eta har lahira ta mutu kin kuma ce nice na kashe miki 'ya'ya shisa kika kashe tawa! Ya kikaga wannan wasan? Ina sharar k'wallah nace

"Keda Allah Maryama, Allah yafiki wlh, muguwar mace kawai" Wata dariyar shak'iyanci tayi ta amshi jinjirin nawa ta matse masa hanci a haukace nayo kanta nayi wurgi da gawar jinjirar ina k'ok'arin k'watar yarona a hannun ta, kawai se gani nayi ta baiwa Ungozomar yaron da sauri ta k'wallah uwar k'ala take matan dake waje da kuyangi sukayo d'akin tana kuka ta kasa ciro jinjirar ashe a tafasashen kaskon ruwan zafi ta fad'a ban kulaba Allah ma ya sani, ganin sun shigo ta nuna yarinyar tana kuka tace

"Kunga Surbajo ta haukace, sabida haihuwar mace Surbajo ki d'auki d'anyar jinjira ki wurga a ruwan zafi dan zafin kishi a dole sekin haifi magajin sarki, ni sanda banida d'a banda jika kike hayayyafa haka kikaga nayi musu? Take wurin ya d'auki salati aka ciro yarinyar, wata tace zataje ta sanar, nidai gaskiyar datamun yawa ta sanya banje komai ba, kallon marar Maryama tayi

"Ku rufa mata asiri,abarshi akan bisa kuskure yarinyar ta su 'buce mata,ni ina tausayin ta na tabbatar tab'in hankaline ya sameta amma kubar nan wurin da jinjiri na, karta hallaka shi, ban yarda koda kallom sa tayiba, kishi ze iya sakata aikata komai dan haka da sauri kubar nan wurin dashi" Inaji ina gani suka gudumun da yarona ko nono ban bashi ba! Haka ina zaman zamana akazo da Likitan gargajiya ya dubani yace na samu tab'in hankali, maryama seta ziyarceni da sunan dubiya tace duk na kuskura nace da hanakali na seta hallakar da Jinjiri na dake hannunta har lahira, indai inason ya rayu tokuwa sena kawar dakai daga gareshi! Akan tilas na rayua haka dan inason yaron dako ganinsa ban tab'ayi ba ya rayu a duniyar nan.

Sanda Hafsa tazo nan abada labari sadda kabta tayi a k'asa ta dinga rusar uban kuka tamkar babu gobe! Hankalinta a tsananin tashe, Hammood ma kukan yake su Data kowa yayi shiru dan a yanda Hafsa tayi laushi ga alama sesun bata break na 1 hour!!!

Mom Nu'aiym.

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

      *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA TALATIN DA D'AYA*

31.

Gabaki d'aya banda sautin kuka  Hafsat da saukar numfashin Hammood babu abinda kake ji, seda ta nutsu sannan taci gaba cikin raunin Murya.Baba Surbajo tace "Abinda yafi bani mamaki shine yanda gaba d'aya Sarki baya ziyartar inda nake, sanda se labaru nakeji barkatai akan Hammood, akace kurma ne aka dawo akace yanaji amma baya magana, akace Maryama ta kurumce alhali ni tana zuwa tamun tatas da bakinta me tsini tamkar jab'a tasha fiya fiya. Duk wannan bidirin da ake fa ina gaya miki awurin bayi da kuyangin dake zuwa mun aiki nakejin su, tsammani suke banajin me suke fad'a tunda na kurumce amma ni nasan tabbas akwai mugun abun da ake k'ullawa Hammood batare da sanin saba, wani lokacin zezo mun kamar baya cikin nutsuwar sa, wani zubin inyazo wurina seya wuni be tashi ba, yana nan dai muna kallon kallo, hardai rana d'aya na bud'e baki na masa inda ga mamakina shima mayarmun yayi anan nayita so in bashi labarin nan danake baki amma sam seya zamana bakina yanamun nauyi, inajin tsoron yanda ze d'auki abun, amma seya zamana na rok'eshi akan ya rufe sirri na nacewar ina lafiya nakuma sanar masa ya rage kawomun ziyara da rana dan kuwa ido ze iya kai sak'o kuma tabbas wani abu mara dad'i ze biyo baya akaina ko kuma shi, ashe ban tsiraba dankuwa maganar barin k'asar gaba d'aya nashi ya sameni, na kuma tabbatar dan kawai an gano yana zuwar munne, daga haka dai na dena jin labarin sa se bayan wasu shekaru ina nan zaune a zullumi da fargaba, haka har labari ya riskeni akan ya dawo ya zama babba amma yanada fad'in rai da jiji dakai, haka harna soma samun labarin yanada mak'iya anaso a kashe sa! Shiru Hafsa takumayi kafin tace

"Acikin k'ananan bayi da hadiman b'angaren ta ta samo mana labarin ainahin wanene Uncle Jay, kuma su waye 'yan k'ungiyar aci duhu dake k'ark'ashin kulawar idan fada! Nida kaina nayita ziyartar tarukan na idan fada, nayita aikawa wakilai na anan nagano wani abu, da farko dai shi Uncle Jay yayarsa itace ta sanyashi ya shiga wannan k'ungiyar sedai tsuntsu biyu zasu jefe da dutse d'aya, da farko dai babu wani magaji kuma jinin sarautar daze iya gadon wannan sarautar se Usman, shikuwa bashida d'a baikuma da jika sun shigar masa ne dan idan ta tashi sesuce kai suke

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login