Showing 51001 words to 54000 words out of 113608 words
inta faman shan 'ya'yan itatuwa yana k'ara lafiya shisa kikaga gaba d'aya na duk'ufa da shansu" Kwantar da kanta tayi a saman cinyar Bahar kafin tace
"Ammu nikuwa wani abu yana damuna?" Kallon ta Bahar tayi
"Kaddai yawan ciwon kanne ko? Yamutsa fuska tayi tace
"Bashi bane Ammu, kawai akan rashin lafiyar Hammood ne, wainikam anya ba iska bane dashi, amma ayi mutum yana ji amma baya magana? Nisawa Bahar tayi kafin tace
"Hammude haryakai shekaru tara a duniya bayaji bakuma ya magana, makaranta ma seda yakai aka sakashi ta kurame, yanada shekaru goma a duniya akayi masa aikin k'walwa anan garin aka samu nasarar jin sa ya dawo sedai maganar ce tak'i yiyuwa, ita kanta maganar likitoci cewa sukayi damu daga lokacin da akayi aikin zuwa kowane lolaci ze iya dawowa yana magana kamar kowa tunda yake lalurar tasa bada ita aka haife saba, dankuwa harya soma yin magana yanada shekara da wata uku, Abbi Ummi duk fad'a yake, ni kaina yakan fad'e sunana Bare uncle Jay, tuni ake cewa UJay , yaro wasa wasa ya dena magana mun zata shiru shiru ne bayason surutu sekuma abu ya dawo kiyita masa magana baze waigoba sekin tab'asa, koda akaje asibiti sukace cutar kurumta ce akayita magani abun beyiba, jida farko ina kallon komai a matsayin wasa har ina ce masa kurma amma daga bisani sema abun ya shallake tunanin mu, akace a k'walwarsa ne jini ya shiga wani wurin akayi aiki so 2 amma ba nasara, seda yakai 9 aka sake aiki anan akayi nasarar ji ya dawo amma babu magana, Kurma ya wahala arayuwa Hafsat ina masa fatan macen dazata yi tattalin sa, dukda na kula jininku be had'u ba amma inaso kiyita hak'uri da kurma, yakai matsayin da be yadda da kowa ba a duniya sabida wahalar daya sha abaya, idanda yanada bakin magana daya gaya miki irin wahalar dayasha a hannun mak'iyan sa, har gobe sharri ake k'ulla masa agun mahaifin sa, sannan sun kasa aiwatar da komai akansa, kurma yayi kud'in da ko mahaifin sa banaji yanada rabin su, ya samu sa'ar k'warewa a harkar zane da taimakon Shammaz (Likitan yaso a littafin Sa'a tafi manyan kaya), yanzu haka yana kulanda babban kamfanin sa dake UK, ya k'ware a zanen motoci da jirage ke harma da kekuna, ya kware sosai a zanen komai ma daidai da kamfanin k'era tile Hammood ne yake zana desighn duk sanda zasu fito da new, ya shahara a harkar dukda haka nake tilastawa mahaifinsa bashi kud'i sabida kawai yaji kwanciyar hankali akan cewa yanada mahaifa, a Nigeria seda masu tsaro yake yawo, sannan bazaki gansu tare dashi suna yawo ba amma duk inda ya saka k'afarsa suna cen a b'oye. Mangalo dan Allah karki guji Hammude akan halinsa, karkice zaki gujesa sabisa lalurar sa ni nayaba da hankalin ki, wannan ya sanya nake masa sha'awarki dukda dai dayake ina duniya babu wanda ya isa ya miki dole" Nisawa Hafsat tayi kafin tace
"Amma kun k'ara bincikawa koda maganar tasa ta dawo? Dariya Bahar tayi"Ai sunce indai ta dawo muna zaman mu zamuji yana magana, so munata dai addu'a amma har yau shiru" Nisawa tayi
"Allah ya bashi lafiya me dorewa Ammu, inshaa Allah wata rana se labari" Shafa sumar kanta Bahar tayi "Hafsatu, Allah kuma ya bani ikon aske kan nan tatas a huta da rashin zama da hula ko kallabi" Turo baki tayi
"Allah Ammu ina kokari ma, amma kiyi hakuri zanke sakawa"
"Yauwa koke fa? Allah ya miki albarka yar k'warai" Ameen tace tana kara shigewa ajikinta, ta dad'e sosai bata samu wannan kalmar abakin kowa ba, kada Allah ya kashe mata ammunta da wuri....
Zubewa Baba yayi akan gwiwowinsa, tuba nake akan abinda Bilal yayi na rashin hankali, banida ikon lank'wasa Bilal Hajiya, nayi nayi ya maida miki kud'inki amma yak'i, dan Allah dan Annabi ki yafe mana rashin amanar dabamu rike miki ba" Sauke ajiyar zuciya Momy tayi
"Baba ba laifin Bilal bane ba, bashida laifi ko kad'an duk abinda ya faru laifi nane Baba, da banshiga hurumin Allah ba da yanzu ni daku da Bilal muna sha'anin mu babu abinsa ya samemu, amma nasanya son zuciya agaba dan Allah Baba ku gafarceni" Nan aka shiga neman yafiyar juna har suka sulhunta, Muhseen yana tsaye k'ik'am har suka gama sannan Baba ya wuce b'angaren su su kuwa suka wuce inda zasu. A hanya bayan sun dawo daga neman gafarar iyayen yan aiki Muhseen ya kalli Momy yace
"Mahaifina Bashida lafiya momy, bashida mata kuma.Mahaifiyata ta rasu shekaru hud'u baya, kullum nine a tare dashi, ina tausayin sa ga jikin tsufa ga kuma rashin mace, idanda zaki taimakeni damunje kun gaisa" Kallon sa tayi cikin jimami
"Kaddai baya iya tashi? share k'wallan daya gangaro masa a ido yayi sannan yace
"Yana iya tashi sosai ma, yana yawon sa sedai hannu d'ayane bashida shi, yana shan wahalan rashin hannun sabida da jikin stufa abun ya sameshi garin k'wak'ule gaban yaran mutane yayi karo da wanda baze hak'uraba ya guntule hannun" Da sauri ta kallesa
"Subhanallah Muhseen, yaran mutane kuma? Kawar da kansa yayi gefe yace "Ea fa, mahaifina mutum ne me tsananin dukiya da tarin kud'i, sesa matsalar sa d'aya son b'ata yara k'anana, bak'in cikin sa ya kashe mahaifiya ta, anyi anyi ya dena be dena ba seda ya kawo me gadi buzu yaci karo da mahaukaci ya tab'a masa farjin 'yarsa kafin na dawo ya sanya adda ya datse hannun sa" "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un wannan wace irin masifa ce, Allah ka rabamu da mugun ji da mugun gani" Nisawa yayi
"Dan Allah Maa kozaki je din" Tana sauke numfashi tace
"Ea muje babu damuwa wlh"
**************
Bayan isha hafsat shiryawa tayi cikin shigar k'ananun kaya riga da kuma wando sedai rigar ta kawo cinyarta, hula kad'ai ta saka tafice waje, duk yanayin sanyin garin dad'i sosai yake mata, wak'enta take tana zagayar interlock kamar kullum, yau kanta zafi yake mata, tanason sanin gaskiyar abinda yake tafiya arayuwar Hammood, ada be dameta ba sam amma yanzu dataga Ammun ta acikin damuwar halin da Hammood yake ciki taji tashiga damuwa sosai, mesa to zasu tasoshi agaba? karo tayi da mutum da sauri ta d'ago cikin bada hak'uri, karo tayi da Bilal lokaci d'aya plan d'inta ya bijiro mata, da sauri ta sakar masa murmushi
"Ya kake" ta furta tana tsatsaresa da ido, shi d'inma yana murmushin sa me sanyi yace
"Am cool dear n u? Tana meci gaba da murmushin ta tace
"Same here" Hanyar barin wurin tabi yad'an had'a da gudu ya sameta
"Fine girl bazaki bari muyi hira ba" Dariya tayi tana kallon sa
"Hira fa kace wane irin hira? d'age mata girarsa yayi "Labarin U.S zan baki, harma wataran in kaiki yawo" Jinjina kanta tayi
"Danaji dad'i kuwa, to meye labarin U.S d'in? Murmushin sa ya fad'ad'a
"So ur this kind" Dariya siririya tayi "Kamun kamada wanda na sanine a Nigeria" Kallonta yayi
"Nikuwa kinga wannan kyakyawar fuskar ban tab'a tsammanin akwai irinta a Nigeria ba sam, dan ban tab'a ganin irin taba" Dariya ta kumayi
"kana kamada khairiyya sosai, kai d'an uwanta ne ? Shafar sumar kansa yayi "Yea she's my Lil sis" tab'e baki Hafsat tayi
"But you look younger, tafika fuskan girma" Dariya yayi "A gat a fine baby face u know, haka aketa cewa tuni, agarin nan zokiga 'yan matan dake bina tsabar kyauna, nifa kawai dan ina k'yank'yamin fatan turawan nan ne, hajiya da nayi kud'i" Dariya tayi
"Kai ai Yariman babban masarauta ne babukai babu auren mejan kunne" Dariya yayi
"I hate all those sarauta stuffs shisa nafi k'aunar zamana anan kawai, ka dinga maka manyan kaya kenan kaman limamin masallacin maka ina zan iya ka garin zafin azaba" Hara rarsa tayi
."Badai kada yanda zakayi gari nakune sarauta takuce, sarki kuma semun radaka ehe" Dariya yayi ya kula tanada son zolaya, barkwanci abakinta kaman jamfa a jos
"Idan zaki zama sarauniyar ai zan yarda koma gobe a rad'a kai koma yanzu ne" Kallon gefen fuskar sa tayi ta yatsine fuska
"Magana ta Allah kamun kyau da yawa, nifa bannson namiji yacika kyau, bakinka kamar na mata, ido a manya manya, dogon siririn hanci suma kamar jini arabi ina zan kaika, bi d'an daidai nakeso wanda bata haddasa hawan jini" Dariya yayi har yana rik'e ciki yanxu kam
"Kinganki wani kyau, kyau gashinan a gunki yana zuba muna kwashe wa" Dariya tayi bataso ya saba sosai da ita dan ita amfani kawai zatayi dashi don cimma wata manufarta
"Yanxu Ammu zata soma nemana, zanje saga ciki nagode daka d'eban kewa" Murmushi yayi
"kozan samu number waya, so bake wai kozan samu daman kafa gwamnati na agunki inga kozan iya komawa Nigeria" Bata b'ata lokaci ba ta bashi, kafin tamai sallama kukan Bahar ne ya d'auki hankalinta!! Da sauri tayi wurinta ta rik'eta
"Ammu lafiya dai? tana jan majina tace "Hoo ni Bahar, ina ganin tashin hankali, yanzu akamun waya wai Barratu tanata zubar da jini ga aman jini kuma, ina zanshiga inga haske, gwanda kawai in tafi gida, ku kirawomun Hammude ya sakani a jirgi gida zan tafi" Rarrashinta ta hauyi suka d'unguma part d'in, kallo d'aya yayiwa Hafsat ya d'auke kansa idan nan yayi jajir tamkar wanda ya had'iyi d'anyen attauhu, Bahar ya rik'e yana bata magana jin bayanin datake, an gaya masa tinda rana ya mata banza ne sabida bayason ta tashi hankalin ta, ya hana a gaya mata yarasa wanne wawan ne ya sanar mata
"Bahar wanne jirgi zamu samu zuwa Nigeria kai tsaye yanzu" Khairiyya ta furta cikeda k'osawa da kukan da tsohuwar keyi musu, cikin masifa Bahar tace
"Mad'aurin auren ubanki da uwaki zakije ki tambaya, ja'irar yarinya ni zaki gayawa D'ibar albarka la'ananniya, wlh ki fita a idona ba dake nake magana kinaji na" Ta kuma share majinar data zubo mata sanadin kukan datayi, Hafsat ya rubuta w
"Ki rarrasheta zuwa safiya, inshaa Allah zamu samu jirgin daze tafi da ita" Haka sukayita bata baki harta dena kukan bayan ankira mata barran sunyi magana da ita.
**************
Tafiyar Bahar Nigeria ya tilastawa Hafsat komawa b'angaren su Hammood, wanda sam batason abinda ze had'asu da khairiyya dan kuwa cin kashi khairiyya ke mata har'a gaban kuyangi da bayi, batason yanda take yarfata amma yata iya Bahar ce tace lallai bazata barta ita kad'ai ba. Yauma kamar kullum tayi shirin makaranta tsaf da ita, tayi kyau dukda bata saka makeup ba,k'amshi kuwa sekace wacce zataje gasar wanda tafi kowa kamshi a nahiyar africa, kai tsaye kitchen ta shiga ta dafa spicy noodles ta fito dashi a hannu cikin plate, time take kallo idan ta wuce 7 Bus ze barta gashi yanzu 6:48 am, ganin khairiyya a main parlor ba k'aramin haushi ya bata ba, ta tsani ganin wannan yar anacen antyn masifaffun duniya, bata kalleta ba tace
"Barka da asuba" Kallon tsana khair ta wurga mata sannan tace
"Bani wannan kije ki dafa wani, dama yunwa ta fito dani" Gwalo ido tayi tana kallon ta
"Zanyi late sosai a school,.yanzu 11 mns ya ragemun bus yazo, inban fitaba zasu barni" kallon kinma rainani ta mata sannan tace
"Zaki bani kokuma saina mareki" Tab'e baki tayi
"Nida abuncina kuma aci zalina a k'wacen" harara khairiyya takai mata kafin tayi magana Hammood ya fito, matsawa tayi da sauri kusa dashi
"Honey kaga yarinyar nan, na saka an dafamun Noodles inaso zanci yunwa nakeji, ta k'wace a hannun Illele wai ita zataci tace school na gaya mata yunwa nakeji wai sedai naci kaina" A fusace ya tako tazo ya karb'e plate d'in a hannunta yana shirin mik'awa khairiyya Hafsat ta saita k'afanta ta ruga ta bige plate d'inta ta auna aguje
"Mugwaye zakuci zalina, Allah yafiku wlh sedai duk mu rasa" Sarkin yak'in magudanan africa ta yamma aguje shima yabita,cikin ikon Allah yau agate ya damk'o hannun ta!!
*Mom Nu'aiym*
*TSINTAR AYA* FREE BOOK
*BILLY GALADANCHI*
*SHAFI NA GOMA SHA SHIDA*
Kawai tsayawa yayi yana kallonta sanda take haki alamar tasha gudu, yanayin idanta dariya ma yaso bashi, ya kula hafsat rigimammiya ce tak'in k'arawa, tanada neman tsokana ainun, batada tsoro sam sannan bata b'oye b'oye, idan dai akan gaskiyar ta take tokoda kasheta za'ayi zata tsayawa kanta, zuwa yanzu ya soma gane cewar bazata dena sakashi gudu ba, shikuwa gudun dama tammar jiransa yake, duk sanda yaga ta ruga idan ba binta yayiba ba dad'i yakeji ba, hannunta ya sake, itama seta tsaya tana kallon sa, turo baki tayi gaba
"Idan kaci zalina Allah yana kallon ka" D'an zabura yayi tamkar ze kuma rik'ota ta arce da gudun fanfalak'i batako waigo saba, daidai titi Bus d'insu ya tsaya, da sauri ta shige tana lek'ensa, shi d'inma tsaye yayi har seda Bus d'in nasu ya b'acewa ganin sa, yana juyawa ya koma ciki da murmushi d'auke a fuskar sa kawai yayi karo da Khairii, d'anja baya yayi ya akayi besan da zuwan taba, ko k'amshin turarenta ma beji ba, koda yake gaba d'aya daddad'an k'amshin arab oud na hafsat ya gama mamaye ilahirin wurin, had'e fuska tayi
"Abinda kace zakazoyi kenan, nifa na soma zargin kamar soyayya kuke da yarinyar nan, bini bini ka bita da gudu sekace kuna wasan tsere, nasan cewar gudu halittar kace a cikin jinin jikinka yake amma why always Hafsat? idan kudu kakeso kayi tare da wani banida nauyi ai as u can c, kawai ka shirya mu ringa wasan b'uya, am very good at hide and sk game, after that kuma kana zuwa wurin Hafsa u just grab her hand bazaka iya marinta bane meye na tab'ata tun farko?" Sororo ya tsaya yana kallon ta amma harta k'araci surutan ta bece da ita ci kanki ba, rab'awa kawai yayi ta gefenta ya wuce, bin bayansa tayi har suka isa cikin gidan bakinta be mutu ba masifa kawai take, shi hankalin sama baya jikin sa, gaba d'aya tunanin sa ya ebesa ya kaishi wata duniyar....A b'angaren Hafsat kuwa tunani take anya Man d'in nan kansa d'aya kuwa ? yaya ze rik'a wani kwasowa a guje duk sanda ta tserewa muguntar sa? yanayin gudu sekace d'an shekaru sha biyu, wata zuciyar tace da ita kekuma me 17yrs kina tik'ar uban gudu ace dake me? lokacin da suka tsaya station nasu Cylia suka d'aukesu bata hak'uraba seda ta baiwa cylia labarin Yaa Mood sarakan tsere, nan suka dinga dariya abinsu, duk abin nan har yau Hafsat bata tab'a gayawa k'awayen ta labarin wani abu daya shafi gidan suba, ita dai kullum Bahar ce abakinta granny d'inta sekuwa Yaa Mood wanda koda yaushe cikin bada labarin tserensa akeyi.
**************
Gabaki d'aya anrasa gane kan meke damun Barra, Gadai ciki ajikinta amma gaba d'aya banda zubar jini babu abinda takeyi, Bahar ta shiga rud'ani dan kuwa har an dawo mata da Barratu a b'angaren ta, yau abun yafi k'arfin nako yaushe dan kuwa tun cikin dare jini yake b'ulb'ula daga jikinta, hankalin Bahar da Jay ya matuk'ar tashi hakan ya tilasta musu d'aukar ta su kaita asibiti, abin mamaki shine likitoci basa ganin komai, duk wani dake jikinta yana nan lafiya lau musamman cikin dake jikinta, ba laifi tana shan addu'a iri iri awurin bakuna masu yawa sosai, dan kuwa mahaifiyarta a tsaye take k'ik'am tana mata addu'a. Zulaiha da yayarta ce suka kawowa Barra ziyarar dubiya a asibiti wanda sosai suka jajanta yanayin ciwon Barra, barinsu d'akin keda wuya suka had'a hannu suka tafa, Anty Safara'u ta kalli k'anwarta tace
"Ba se idan mun yarda zata haihun ba, tayaya munzo mu k'wace gida mu kuma sake baki wata jaka tazo ta shiga gabanmu, dacen tasan zata haihun tajira seda kikazo kika kasa" Murmushi Zulaiha tayi
"Tokuma ai anty safara kinji boka yace ze kashe d'an cikin nata ni kuma ze bani ciki" Dariya suka bushe dashi Safara tace
"Ki bari Boka yana kashe mini canjina da yawa, shegiya tayita sumy sumy da ita kamar ta Allah, nina tabbatar tana shiga bokaye ace duk kayan matan dakike sha itace miji kewa cin tuwon mayunwaci, ke kuma sedai ya lasa ya mik'e" Cikin k'unan rai adaidai lokacin dasuka shiga mota suka zauna Zulaiha tace
"Bashi bake yake b'atan raina irin yanda dan salon iskanci yake lasar kona ina nata, sedai kiji ihunsu, Baby more of that, suck it well thank u baby, ur killing me, ba kunya a idan Barratu nan dakike ganinta, ni anan nake lalacewa wurin musu lab'el ta windon d'akinsa har taku nak'e d'auka da yamma naje in bud'e window dan inji me suke ciki da dare, amma kinsan matar nan wasu lokutan tsabar kirsa suna magana amma bakyajin me suke cewa, bama wannan ba har wani shiri akeyi duk ranar daya gama kwanakin sa biyu agidana zakiji ana zancen ranar daze koma wai romantic slow Sex zasuyi, aranar komai k'wak'warki bazaki me suke ba sedai kijiyo nunfarfashi ko surutun su ma bazakiji ba, har ranar cewa na masa muyi Romantic slow sex amma seda muka kwanta ya nunan k'iri k'iri wai am not co-operating cewa banma iyaba kwata kwata" Nisawa Ant Safara tayi
"Tsinannu yan iska, wlh basusan dawa suke zancen ba, a haka zatayi ta zubar jini harta shek'a lahira, yar iska" Haka suka bar asibitin sunata surutai...
Hafsat yau daga school coffee shop suka wuce, koda tazo d'abi'ar dasu cylia sukeyi kenan, babu ruwan su kullum suna hanyar coffee shop, chidi tana kallon Hafsat tace
"What u did to that our English teacher is not good, ur very strongheaded and sometimes arrogant, how can u do that? Tab'e baki tayi
"Shine d'an iska meye na wani tab'ani? Murmushi chidi tayi
"Kema kinsan al'adan sune hakan, mezai dameki hannunki kawai ya rik'e, kuma bayan haka abu yake nuna miki fa bare kice haka kawai ne" Kafad'unta ta d'age alamun ko'a jikina sannan tace
"Niku rabu dani abinda ya isheni ya isheni, tana zaunawa ta zaro wayarta, 3msd colls all from yaa Mood, shin shi meye na kiranta a waya? ze iya magana ne aishi kurma ne tana? shirin kiransa ta somayi back sega message d'inshi
"Your not at school, kuma bakya gida, kina ina? Dukda tana d'aukar wannan a matsayin freedom nata seda k'irjin ta ya soma dukan uku uku, ta kalli Cylia tana wara ido tace da yaren bature
"Cylia yanzu yayana yamun text cewan bana school kuma banje gidaba, nasan yau nashiga ukuna, hadda