Showing 66001 words to 69000 words out of 113608 words

Chapter 23 - TSINTAR_AYA

Start ads

09 Aug 2025

696

Middle Ads

hakane se yarinyar nan ta yabawa aya zak'inta, seya nuna mata iyakarta ayau, setayi danasanin zuwan sa a dumiyar ta me cikeda hazo!!! Wayoyin sane suka hau ruri kusan a tare, nan Uncle Jay ne d'ayar kuma Ummin sane gaba d'aya babu d'aya daga d'aga dankuwa yasan ko zancen me zasu masa!!!


Hafsat dake rik'e da wayarta a wannan lokacin tana karanta New's d'in itama murmushi tasake wanda ita kad'ai tasan ma'anar sa.

MOM NU'AIYM.

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

    *NA: BILLY GALADANCHI*

*Ohhhh gaskia Reader's kuna bani nishad'i, harga Allah inajin dad'in comment naku dakuma k'aunar dakuke nunawa wannan littafin na tsintar aya, Allah yabar tare..... Wannan shafin gaba d'ayan sa sadaukarwa ne ga duk wata me bibiyar littafin Tsintar Aya, kuyi yanda kukaga dama dashi.*

*SHAFI NA ASHIRIN*

  20.

Gabaki d'aya kanta ba k'aramin d'aurewa yayi ba, tayama za'ayi wannan maganar ta fita? Waye yaje ya buga wannan labarin meke damun wannan gidan jaridar dazasu buga labari kansu tsaye batare da wata hujjar ba? Mik'ewa tayi kawai tabar Fadar sarauniya cikin sassarfa har tana had'a hanya kai daga bisani ma da gudu ta had'a dashi, sedai lungu da sak'o na masarautar mutane sunyi gungu d'aya idan ba wayace a hannunsu  ba to jarida ce, wannan abin ne ya sanya ta k'arawa gudun gudu zuwa na fanfalak'i har zuwa lokacin data iso gidan Hammood, tana haki ta kalli hadiman dasuma jaridar suke kallo tace fuskarta a had'e

"Ina prince mood yake? Kallon ta sukayi sannan d'aya daga cikin su yace

"Ranki ya dade tunda ya dawo daga masallaci be fito daga ciki ba, kai tsaye b'angaren dayake mallakin sa ta nufa a k'ofar parlor sukayi karo yana sauri ze fita, hannun sa ta rik'o batare da b'ata lokaci ba ta juya ciki dashi, shikuwa haka ya dawo tamkar rak'umi da akala be iya hanata ba dukda so yake yaga k'arshen iyashegen ta dan ubanta... A tsakiyar d'akinsa ta sake masa hannu sannan ta waigo gaba d'aya suka fuskanci juna har lokacin huka take na gudun datasha dan haka seda ta d'anja fasali sannan tace

"Labarin dake yawo gaba d'aya a masarautar nan na tabbatar kaima ka ganshi, zuwa kawai nayi in baka shawara k'waya biyu, na farko idan ka fita waje pretend as if nothing happened, i mean bakaga komai ba zakayi kamar bakasan da wannan labarin ba, na biyu kuma karka k'aryata 'yan jarida, am only telling you this because i care in kayi sab'anin abinda na fad'a zaka wargaza komai, zaka basu lasisin ci gaba dayin barazana da rayuwar ka, bance dole sekayi abinda nace ba bankuma ce dole seka yarda daniba wata rana zaka fahimci inda na dosa" Tana kaiwa nan ta juya zata bar d'akin ya damk'o hannunta ya wulwulo da ita ta fad'a jikin sa suka tsaya kallon juna a hankali yace

"U really are a drama queen, so kike ki mayar dani sakarai ko? Aikinki yana kyau sosai, abu d'aya zan.....hannu takai ta rufe bakinsa sannan tace shhhhhhhhhh

"No where is safe in this palace, please no matter how angry you are karka kuma furta koda kalmar A ne a palace d'in nan" Tana kaiwa nan ta k'wace jikinta ta ruga gaba d'aya tabar cikin gida, amma me tana zuwa waje sega dandazon 'yan jarida sunkai su goma sha kowa yazo ne yin magana da Hammood, shi d'inma bayanta ya nufo tun daga bak'in k'ofa daya hangosu seyayi tsaye kawai ya jingina da k'ofar ya hard'e hannayensa a k'irjinsa yana murmushin dake d'auke d'auke da ma'anoni daban daban....., tamkar wacce k'wai ya fashe a ciki haka ta dinga takawa harta isa gabansu,waigawa tayi ta kalle sa yanda yake murmushi ya matukar kashe mata jiki T bataso ya b'ata mata shirinta taga alamar zarginsa akanta me yawane baze tab'a saurararta ba. Kallon su tayi tace

"Waye ya bud'e muku main gate, kuma waye ya baku izinin zuwa nan ku tashi prince hammood daga baccin sa? Speakers suka kawo kusa da ita da masu waya kowa dai da abinda yake amfani wurin yim recording

"Ranki ya dad'e me zakice game da gaskiyar wannan al'amarin daya faru gameda jita jitan da aketa yad'awa akan k'aryata kurumtar Prince Mood da mutane sukayi? Bataso kulasuba amma bari ta ari action tayi acting kamar actrees ta indian film!!!

"Akan meyasa ku kuna aiki amma kwata kwata bakusan aikin kuba, ita kanta jaridara data buga wannan labarin k'aryar semunje kotu dasu, dan wannan labarine mara tushe? Idan tushensa ? Kuntab'a gani meji yana magana yayi kurumtar k'arya? Akan me sarki me jiran gado zeyi putting up wannan act d'in? Wannan labari ne ya samo tushene daga mak'aryata mak'iyan prince, kunsan duk inda mutum me babban matsayi irin prince yake dole seya samu mak'iya, sabida haka nake baku tabbacin wannan labarin k'aryane, kuma ni matar prince ce, sabida haka kunji daga bakina, koyazo bashida bakin baku amsa koda akwai wanda ya iya maganar kurame ne anan nakirashi seya muku bayani da kanshi? Wanine daga cikin 'yan jaridar yace

"Amma Ranki ya dad'e majiya me tushe ta tabbatar ance yanayin magana da zab'abb'un mutane ne kawai akan wani babban dalilin daya barwa kansa sani, mezakice game da wannan" Murmushi tayi

"Mekakeso nace maka to? Idan har akwai zab'abb'un mutane a rayuwar sa tokuwa koda banzo ta farko ba zanzo ata uku, kuma ni kaina dazanji sautin muryar mijina danafi kowa farin ciki, inama ace Allah  ya amshi bakunansu yanda ya bud'e masa jinsa harshensa ma ya soma motsi aida munyi farin ciki, banaji idanda ace prince Allah ya bashi damar magana zamu b'oye wannan baiwar, dan kuwa har gobe bamu dena nema masa magani akan hakan ba" Wani daga gefe yace

"To Ranki ya dad'e ke a haka kina magana kika yarda kika aureshi matsayin sa na kurma wanda baya magana" Yanxu kam hawayene suka wanke fuskarta cikin fad'a tace

"Kurma ba mutum bane? Ko gani kake kafishi? Acikinku babu wanda ya baiwa kansa ilimin ji gani ko magana, kyauta ce Allah ya baiwa wanda yaso sabida haka ni koda gurgune yafiyemun mutane marasa nagarta irin masu yad'a labarin k'arya, dik wanda ya kumanbuga labari mara tushe akan prince da ahalinsa wlh kotuce zata rabamu, ku barshi yaji da abinda ya dameshi, kokuma nayi sanadin da gaba d'aya gidajen jaridunku da gidajen radio ku dama na tv zasu dena aiki har abada" Nan sukaci gaba d'a wurgo mata tambayoyin su amma bata kula kowa ba tasanya kaintabar wurin tana sharar k'walla, abun ya mata ciwo ainun mesa mutanen nan basuda adalcine akan komai? Meya tsare musu bata ganinsa da hayaniyar komai, baya shiga shirgin mutane, wayarta ta janyo ta duba acc nata taga ruwan dala aciki kud'ad'en da aka ware mata musamman dan biyan buk'atunta na yau da kullum, kawai daga zuwa Fadar sarauni wanka tayi ta shirya ta kira waya aka shirya mata driver sannan ta fita, bata tsaya ko inaba se tsohuwar makarantar datayi secondry school anan garin, batasha wahalar ganin malamin nasu ba, yasha mamakin ganin ta sosai kafin suka keb'e tana murmushi tace

"Sir taimakonka nake nema dan Allah" kallonta yayi sannan yace

"Bakida matsala Miss arrogant, ina saurarenki"

"Sir nasan ban isa na samu ilimi akan computer ba tunda dacen ma baso nake ba, as u know dai sam banason karatu, amma a ire iren kallon american films danake naga idan sunason su gano abu suna amfani da abubuwan dasuka shafi computers wurin gano abubuwa da dama kaman su trackers dinnan, CCTV camer'as irin wanda basa buk'atar dogon wiaring na wutar lantarki da dai sauran abubuwa, to ban saniba ko kanada ilimi akan hakan" kallon mamakinya sakar mata

"Ke kuwa Miss Arrogant meya kaiki? Me zakiyi da wannan abubuwan? Mirmushi tayi

"Malam dik wanda ya taimakeni akan wannan aikin nawa zan bashi dala dubu d'aya"  Kallon ta Malam yayi

"Hafsat a nufinki dubu d'ari biyar da goma sha biyu? Ke ina kikaga wannan kud'in? Wani murmushi tayi

"Malam idan ka had'ani da wanda ze taimakeni zan baka dala d'ari biyar, albashinka na wata nawa kenan a kwana d'aya" Mik'ewa yayi tsaye

"Idan dai zaki bani  wannan kud'in muje na had'aki da Zubairu mass com danshi k'arshene sosai  a wannan b'angaren" Tana murmushi tace

"Muna zuwa zan bakasu bawai se anjima ba Sir" Yana washe yace

"To Miss Arrogant muje" Haka suka fita ya shiga gaban motar dogarawa ya zauna ita kuwa tashi k'atotuwar jeep baka k'irar land cruiser prada akaja suka tafi.

Basu wani sha wahalar neman Zubairu Masscom ba, anan dai bata b'atawa uncle nasu lokaci ba ta sallameshi ya tashi yana godiya tare da mamakin yaushe 'yar shara ta samu duniya har haka take yawo tare da dogarawa cikin manyan motoci na alfarma?




Hammood kai kawo yake da jaridar yamma a hannunsa yana nanata karatun maganganun da Hafsat ta fad'a, wato tsakani da Allah dai Yarinyar nan so takeyi tayi wasa da hankalin sa, ta gama fallasa asirinsa kuma sannan yanzu takeso tayi amfani da hikima da dabara wurin kawar da tunanin sa akan cewar itace ta fad'a, yaya ze aminta da wannan? Banko k'ofar d'akin da akayine yaja hankalin sa ya juya yana kallon Khairiyya da gaba d'aya wunin ranar be sanyata a ido ba, a hankali ta tako zuwa inda yake fuskarta gaba d'aya tashin hankali ya bayyana tace

"Me kakeso ka mayar danine wai Hammood? Anya baka baiwa Hafsa dama da yawa ba kuwa? Tafita a media tana yayata cewar ita matar kace, kai sa'anta ne tana 'yar aiki? Bayaga haka menene ya sanya ajeta zargin maganar da ake tunanin kanayi? Me zakacemun game da wannan? Kaucewarsa yayi kawai batare dayace komai ba, ta rik'o hannunsa

"Menene gaskiyar abinda yake tsakanin ka da Hafsat? Mesa zata shigo har b'angaren ka? Akan me kake nema ka mayar dani shashane wai? Dafe kansa yayi dake barazanar rabe masa gida ba, mesa zuciyarsa takeso tayiwa Hafsat biyayya ne nak'in cewa kowa komai akan maganar nan? Akanme ze zauna a haka? K'wace hannimun sa yayi yayinda ta sanya wata mahaukaciyar k'ara ta zauna a bakin gadon tana k'ara me sauti, be sairateta ba yabar cikin part d'in zuciyarsa babu dad'i, sak'on waya ya turawa Uncle Jay kamar haka

"Ya dace kazo ka gayawa khairiyya maganar auren nan, tasoma zargina tanamun tambayoyi akan Hafsat, banaso tsegumi ya tashi daga cikin gidan zuwa gaba akan bana mata adalci" yana gama tura wannan sak'on ya nufi wurin mahaifinsa dake kiransa.

***************
-Zama zakiyi suna wulak'antaki akan wata, ki bincika kiji wlh aure aka d'aura musu, kwata kwata prince be miki adalci ba, kiyi gaggawar yin ramuwar gayya tun kafin lokaci ya k'ure miki-

Dafe kai khairii tayi wannan shine karo na barkatai da ake turo mata ire iren wad'an nan sak'unan tun bayan dasuka sauka a k'asar nan, cikin fusata wannan karon ta tura reply da

"Inaso naga me turon wannan sak'on ido da ido, zamuyi maganar sirri" Tana aika sak'on wanka tayi ta shirya tsaf irin shirin 'ya'ya dakuma matan sarakuna sannan ta jeru da kuyangin ta ta nemi a jagoranceta zuwa Fadar Sarauni dan bazata iya kai kanta ba dama dama so d'aya taje....... Gaisuwa irinta girmamawa sukayida Bahar sannan tace

"Ranki ya dad'e magana nazo muyi akan Hafsat" Hafsat dake cikin d'akin bahar k'irjinta yayi mugun dokawa ta k'ara matsawa sosai jikin k'ofar d'akin dukda label ba halinta bane amma wannan karon setaji ta kasa nutsuwa, bahar ta tsatsage hak'waranta ta kalleta tace

"To kumadai Gimbiya to meke tafe dake yau kenan? Murmushi khairii tayi sannan tace

"Rad'e rad'in magana nakeji da kuma k'ananun maganu daketa tashi ana gaya mun wai saura sati biyu muzo garin nan aka d'aurawa Hafsat aure da Mijina, nikuma na tabbatar duk fad'in masarautar nan ke kad'aice bazaki gayamun maganar daba gaskiya bace ba, shiyasa nazo inji daga majiya me tushe" kallon ta Bahar tayi sannan ta kawar da kanta tace

"Kafin zuwanki masarautar nan wani al'amari ya faru me d'aure kai wanda shine ma sanadin mik'aki aure da mahaifinki yayi awurin hammude, to al'amarin ya faru ne akan wannan Hafsat dakike gani, kuma an rigada anshirya yi musu aure atare tun kafin naki dan haka shine yanzu aka cika alk'awarin" kallon mamaki khairii ta mata sannan tace

"Auu wai dama Wannan itace karuwar tasa da akace yayiwa fyad'e ko yayiwa cikine kuketa kare kare, shine tsabar ci baya kuka aura masa ita dan kutuwar zuciya, shine sabida ni banida daraja aka had'ani da karuwa zuwa U.S aka mayar dani wawiya dabatasan me takeyi ba? Lallai ma kuncika" B'ata fuska Bahar tayi sannan tace

"Ke idan rashin Daraja kikeji kisan dawa kike magana kinji dan ninan bansan komai ba se darajata,duk wata hatsabibiya la'ananniya bata isa ta tako k'afarta har nan tace zata gayamun la'anata ko rashin daraja ba, idan bakinki ya kuma bud'ewa kika k'ara tunanin aika muggan kalamai akan Hafsat d'ina wlh zan d'ebe darajar dake kanki in wurgar a bola" Cikeda rashin kunya ta mik'e

"Yarinyar batada wani suna daya wuce karuwa, dan kina uwar sarki ko kakar yarima se akace a gagara gaya miki gaskia? Kun zalinceni nima inada yanci ai" Mik'ewa Bahar tayi sannan tace

"Rashin darajar ta isa haka khairiyya yanxu kinga fita anan, kuma karki kuskura ki kuma tunanin zuwa inda nake daga yanzu har abada, nime daraja duk wanda kikaga yana rab'ata tokuwa tabbas babu la'anta akansa d'an daraja ne, ke kuma bakida darajar dazaki fad'a ni kuma in fad'a dan kuwa nayi sa'a da kakar ki" Fuuuu Khairri ta fita daga d'akin tana k'unk'uni kwashe da alkhaybba me tsananin sauyin tsiya, a k'ofar fita daga d'akin tayi karo da Hammood shikuwa ya baro wurin sarki yazo gun bahar! Wani kallo yabita dashi dashi kad'ai yasan ma'anar sa lallai wannan yarinyar ba saiti a kanta!!
Sheshekar kukan Hafsat ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin dayaje, inda Bahar ma taje ta tsaya a k'ofar d'akin tana kiran hafsat, takawa shima yayi dan tun zuwan khairii yake bayanta yasan kukan me Hafsatun keyi, anan ya sanya hannunsa ya murd'a handle d'in take awurin kuwa k'ofar ya bud'e a hankali ya tura kansa aciki ganinta yashe acikin a saman tile ya sanya ya tura jikinshi duka aciki, wannan ne karonsa na farko dayaga tana kukan gaske, tabbas kalmomin khairii sun mata zafi, Bahar bata bi bayansa ba yanayin sa kad'ai ya isa ya nunar mata cewa yaji komai, sunkuyawa yayi ya d'auketa cak ya d'aurata akan gado sannan ya sunkuya daidai kunnenta yace

"Do not take what she said to your heart, i appologize on behalf of my queen" D'ago jajayen idanuwanta tayi ta sauke a kanshi sannan tace

"Ur repeatedly making thesame mistake all the time, So kake ka tona mana asiri,i told you not to talk ever again amma kaman bakajini ba, ko ina idone akanka ko rogar jikinka kada ka yadda dashi just go to your queen and let me be please"

"Idan.....rufe bakinsa tayi da hannunta sannan tace shhhhhhhh "Dont you dare say a word just leave please" Bece komai ba se yatsansa daya kai ya share mata hawayen idanta sannan ya mike, ya koma gun Bahar, zaman kuka ta saka masa

"Yau naga rashin Daraja Ni Tumba, yanzu kai Hammude dama da wannan mara darajar kake rayuwa, wacce la'ana tayi yawa akanta har bara ganin girman babab" Da hannu yaketa bata hak'uri amma daga k'arshe kukan dai yabarta tana yi seda hafsat ta ajiye nata kukan ta soma ban hak'uri.

******************
Yau a wurin meeting ma Hafsat ce ta shirya zataje a maimaikon Ameena, k'arfe d'aya da rabi na dare ta fito da shirinta mask ne kawai bata saka ba yana hannunta, muryar dataji a gefenta ne ya tilasta mata tsayawa ta lab'e basu ganta ba dankuwa daga gefenta suke, tana kallo suka nufi indabta nufa, itama da sauri ta sanya mask d'inta tabi bayansu cikin sand'a, haka suka taka atare susu biyu ita kuma ita kad'ai! Seda meeting yayi nisa sannan ta tsinkayi muryar da bazata tab'a mantawa da itaba tana cewa

"Wannan video sunada yawa a hannuna, banaji dan ammata barazana wata tsiyace, idan har sak'onninmu basu shigeta ba to wannan shishi kad'ai ne makamin mu" Nisawa wani daga ciki yayi sannaj yace

"Ai sak'on k'arshe ta amsa mana dame mukeso? Kuma na bata adresshing inda zamu had'u gobe, a mararraba hotel room 113rd floor" Babban cikin sune yace

"Ka samu wuri me kyau gaskia, karka bata damar jin tsoro ka gaya mana dukkanin sirrukan Mood dabata sani ba, ga k'ara da wannan abun na cewar uwarsa zalintar sarki tayi shi shege ne, gaba d'aya ka lalata matashi aranta" Murmushi wannan yayi sannan yace

"Allah yaja daran sarki na k'ware sosai a wannan harkar, ka kwantar da hankalinnka" Gyaran zama sarki yayi sannan yace

"Mutane 12 muka gayyata a wannan taron, yaya nake ganin wuri sha hud'u suke aciki lallai a tabbatar da an damk'e masu mana kutse kuma kamar ko yaushe a kashesu anan a binnesu anan, bazasu tsiraba" Cikin Hafsat ne ya bada wani sautiiii k'uuu daya sanya kowa seda yaji dankuwa tabbas Ameen ta sanar mata yau ba'a gayyaceta meeting ba tace ai bazasu gane ba setaje, kenan ta kira mutuwar ta kome? Tana tsakiya da wannan tunanin ta tsinkayi muryar Ogan yana cewa

"Kowa ya fad'i lambar sa muji idan munyi gayyata dashi, kowa da lambar da muka bashi kuma kunsan bama bada lamba a jere kamar ni yanzu nine lamba ta dubu bakwai da casa'in da hud'u" Anan kowa ya fara mikewa yana fad'ar lambar sa har akazo akan wani yana mik'ewa seya sanya hannunsa ya rufe bakin Hafsat da kuma hancinta da hannunsa ya watsa wata powder take ya cizgi hannunta sukabar cikin hall din a guje, itadai Hafsat batasan ko waye ba biye kawai take a guje tayi gujin har ranta ya b'aci, gashi kuma binsu ake da gudun fanfalak'i!!!!

MOM NU'AIYM.

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

*ASSLAMU ALAIKUM,KAMAR YANDA NA FAD'A DAGA FARKO DAI HAKANE, BA KULLUM ZANKEYIN POSTING BA, IDAN NAYI YAU BAXANYI GOBE BA, DUK RANAR DAKUKAGA NAYI YAU NAYI GOBE TO NASAMU CHANCE KENAN INA FATAN ZAKUMUN UZURI*

*SHAFI NA ASHIRIN DA D'AYA*

21.

Wata hanya ya d'auke tare da d'auke hankalin masubin bayansu, hannu ya sanya ya rufe mata baki bayan sun shiga lungun ga duhun

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login