Showing 69001 words to 72000 words out of 113608 words

Chapter 24 - TSINTAR_AYA

Start ads

09 Aug 2025

699

Middle Ads

dare bazata iya gane waye ba suka k'urawa juna ido acikin duhun dukkaninsu suna iya jiyo yanda sautin bugawar zuciyoyin junansu ke bugawa da k'arfi, zuwa wani lokaci dabaze wuce minti uku ba ya sake ta sannan ya fita daga lungun yana fitar da sautin hakin k'arya daga huhunsa yana tambayar wasu

"Kunyi nasarar ganinsu kuwa? Ni ban same suba" D'ayan yana kallon sa yace

"Bibiyar su a yanzu baze amfanemu da komai ba, shugaba ya suma dan haka mu koma kawai kafin k'ubgiyar kwantacciyar maciji ta ganmu ta gane sirrinmu" Haka suka juya zuwa d'akin taron na sirri zuciyoyin su babu dad'i suna mejin rad'ad'in abinda suka fad'a agaban wad'an nan. Dafe zuciyarta tayi dake k'ok'arin faso k'irjinta ta fito ta soma sauke numfarfashi sama sama tsananin tsoron data shiga, jikinta ba k'aramin rawa ya hauyi ba seda ta denajin takun sawun tafiyarsu da mintuna biyu zuwa biyar sannan ta zare mask ta cire bak'ar rigar dake jikinta, ta zubesu anan sannan ta fito daga cikin wurin tana waiwaye...... gab dazata shiga part d'in Bahar aka rik'o hannunta a zabure ta k'walla k'ara da sauri ya rufe mata baki da hannun sa cikin rad'a a kunnenta yace

"Daga ina kike cikin wannan daren" gano cewar Hammood ne ba k'aramin kwantar mata da hankali yayi ba, tace cikin sauke numfashi

"Alhamdulillah" sannan tayi lamo ta lafe ajikin sa, shikuwa hakan datayi ba k'aramin tasiri yayi ajikin saba, sungumarta gaba d'aya yayi nan d'inma lafewa tayi a k'irjin sa tana sauke gajerun numfashi a wahale, ji takeyi tamkar wani macecin rayuwarta yazo, kai tsaye cikin gidan yashiga dogarawa masu tsaron k'ofar basuce dasu komai ba, har d'akin dayake mallakin ta ya shigar da itabya ajiye ta akan gado, hannu yakai ya janyo mata hular dake kanta ta rufe sumar data lek'o ata gaban kanta, yana nazarin yanayin ta yace

"Daga ina kike yanzu? Kawar da kanta tayi daga dubansa sannan tace

"Kai daga ina kake yanzu? Murmushi yayi kafin yace

"Kinada ban mamaki Hafsat, kina ganin kamar ke kinfi kowa wayau ne kome? Tsammani kike kamar kin samu power dazaki iya kayar dani, ki sani nan masarauta tace kuma duk wani wanda yake k'ulla sharri ko alkhairi akaina inada masaniya akansa, lokaci kawai na baiwa kowa daze yabawa aya zak'inta a hannuna, wlh bakina dana rufe na tsawon shekaru sena fansheshi akan mak'iyna cikin k'asa ga wata watanni shida, idan kikaje ki gayawa manyan ki su shirya, kuma sunyi sake d'an zaki ya girma, a shirye nazo kuma tabbas sena kayar dasu nine da nasara, suna tak'amar suna iya wargazani, nikuma ina tak'amar zan iya wargaza dukkan shirin su, sena zame musu k'arfen k'afa fiye da yanda Takawa me martaba sarkin masarautar hankaka ya wargaza azzaluman masarautar sa. Duba littafin TAFARU TA KARE dan samun yanda ta kaya a wannan masarautar. Sena tabbatar na rugurguza anniyarsu kuma wallahi, summa tallahi billahi ni Hammood nayi alk'awarin koda raina ze zama fansa sena wargaza sirrin mak'iyana sannu a hankali" Mik'ewa tayi zaune sannan tace tana kallonsa ido cikin ido

"Na tab'a gaya maka cewar ur a coward ko? To yauma zan kuma nanata maka ur nothing but a cowar and just that, ni kake zuwa kana yiwa barazana nida banda k'addara bankosan da wanzuwar kaba, kazo kana fad'a da mace macen ma 'yar shekaru sha bakwai kai kuwa ka takewa talatin baya, kaje kayi fad'a da maza mana bani ba, yes am an informer yanda kake tunani haka ne, ina bibiyar rayuwar kane kuma sakani akayi bazan sauraraba kuma senaga bayan wannan coward life da kake living, do your worst and lastly ni kadena yimun barazana dan duk abinda nake ba fasawa zanyi ba, i promised wanda suka sakani sena tabbatar naga k'arshen wannan rayuwar da kake, So idan barazana zakayi kaje ka nemi magautanka maza bani ba" Bakinta ya matse seda idanta yayi ja amma batako yi k'ok'arin k'watar kanta ba, shi kanshi idanshi yayi ja jajir jijiyoyin gefen kansa duk sun fito rad'o rad'o fatar fuskarsa tayi jajir sabida tsananin fusata yace

"Ni kike cewa coward, ni kike gayawa magana yanda duk kikaso, meya kawoki rayuwata? Me kikeso ne? Idan kud'i kike zan baki amma ke fitinace a rayuwata, an turoki kiyi kusanci dani sabida kawai ki wargaza rayuwata, ke kikafi kowa cutar dani, kin b'atamun suna kin yimun tabo irin wanda baze goge ba har abada, kinzo kin rab'eni sabida burin wasu bakida alak'a da wannan masarautar akan me zakiyi haka" ya k'arashe maganar yana ture kanta gefe, Murmushi tayi me ban takaici sannan tace

"Ina tantama idan wannan sarautar ta dace dakai, what a fool king zamu samu agaba, kai bazaka tashi tsaye ba kana daga kwance me zaka iya, ni bana fallasa sirrin kowa sabida haka bazaka iya samun komai awurina ba, use ur talent if u have any, ka k'wace kanka, in haka ta kasance will makesure i gather mak'iyanka duka then we both will give a round of applause for you" Sumar kanta ya cafko cikin fusata kafin yace

"Nawa suka biyaki? Da nawa aka siyoki kizo ki wargazan rayuwata, miliyan d'aya 'yar talakawa biyu zuwa biyar, iyakar abinda ko wanne d'an iska acikin mak'iyan nawa ze iya biyanki kenan, toni zan baki miliyan hamsin kije kiyi rayuwarki amma ki fita a tawa" Buge hannunsa tayi ta k'wace sumar kanta tace tana zagayar d'akin tare da kakkab'e sumar ta daya cukurkud'a mata

"You see i told you ur nothing but a coward!! Tsammani kake zanbar muk'amina na zamtowa ta princess a wannan masarautar sabida wasu 'yan canjinka, kokuma an sanar maka dan ina mace k'aramar yarinya banida wayau, nifa muk'amaina sunfi k'arfin kaf dukiyar ka, kaga ni yanzu nazama sarauniya kashi biyu, sannan kuma ina auren yarima me jiran gado dan haka akwai chances zan haifa masa magaji shima wataran ya zama sarki har kake tunanin cewar zan bar duk wad'an nan in anshi wani 50.m daga hannunka, Allah ya tsari gatari da saran shuka, baze tab' faruwa ba inada wayo fiye da tunanin ka." Wuyanta yanzukam ya rik'o seda tayi k'ara amma ta dage tak'i bari tayi kuka

"Harke kina tunanin kin isa macen dani Hammood zan had'a shinfid'a dake, k'azama sauran gayu, muci gaba da bibiyar rayukan junanmu,indai ina numfashi a doron k'asa bazaki tab'a haihuwar yariman wannan masarautar ba, se idan bani bane zan miki cikin sa, dan kuwa kin saba" Hannunta ta sanya tana k'ok'arin ya sake wuyanta amma seda yakai k'arshen maganar sa sannan ya cillar da ita seda ta fad'i, mik'ewa tayi rik'e da wuyanta tana tarin wahala amma Hafsat sabar kafiya bakinta be mutu ba

"Be brave enough to fight ur haters and defeat them, as for me ur just a coward and nothing more, u can never defeat me not even in ur damn dream's....I know ur weakness kuma kai bakasan koni wacece ba har yanzu, curse and insult me as much as it pleases u, just know that kalamanka bazasu girgizani ba, bazasuyi tasiri akaina ba, wlh lokaci yana gab da zuwa dazakayi danasanin duk abubuwan dakake mun, so d'aya ni Hafsat na tab'a tsoron mutum, akan Bilal na tab'a tsoron mutum akanshi kuma na dena tsoron mutum kai baka isa ka tsiratar dani ba" Yanzu kam huci hammood ys soma yi, yana k'ok'arin yin magana Bahar ta shigo d'akin, tana salallami tana tafa hannu

"Iskanci da kenan ma wannan, dan neman la'anta yanzu kai Hammude shine bazaka bari a yiwa yarinyar nan wankan al'adaba ka shigo kana neman hayyak'e mata tun bata tare ba? Da sauri Hafsat tabfad'a jikinta

"Ammu na kice ya fitamun anan, hakanan kawai ina bacci ya fad'omin a d'aki" Hannu Bahar takainta daki k'irjin sa

"Rashin Darajar zaka nunawa k'aramar yarinya? Maza ka fita anan kafin in maka yayyafin la'anta rasa kunya b'eran tanka, shiyasa mana kaketamun zarya anan sekace zariyar dillali tun dawowar ku, ashe zaryar ta neman d'eban albarka ce" Bece komai ba ya juya yana k'ara jinjina makircin Hafsat aranshi yanacin burika iri iri...

**************
Manyan muk'araban k'ungiyar aci duhu sun yanke shawarar had'uwa da khairiyya inda suka gama magana akan zasu had'u da member d'aya acikin su, anan suka yanke shawarar zasu kame me bibiyar su dan kuwa sun tabbatar kowaye tunda meeting d'in na jiya akanta ne seya kuma bin diddigin son sanin me zasu tattauna da ita..........
Tun safe Hafsat ta shirya tsaf ta nufi hanyar zuwa barin masarautar sedai kuma duk abinda takeyi idan Hammood kacokam yana kanta, dan haka fitarta seda yabi bayanta ta hanyar tracing location nata through her mobile phone number ta Nigeria, wanda duk ammata setting a wayar ta indai har ana tracing wayarta asan insa take to wayar zeke nuna mata, da wannan tayi branching wurin wani bawan Allah me saka caji ta bada wayar cajin k'arya tace zataje ta dawo kawai tayi tafiyarta aranta tana murmushin mugunta tace lallai Hammood idan yasan wata ai besan wata ba. Kai tsaye hotel d'in ta wuce taje reception nasu ta zauna tana dannan wayarta data saya me new sim wanda bama ita tayi register layin ba gaba d'aya tana nuna cewar hankalin ta baya wurin kowa se abinda take, obseving ta gamayi gaba d'aya masu shige sa fice musamman cleaners, wani cleaner data kula tunda ya shigo ake barkwanci dashi shita bi bayansa zuwa upstairs, seda ya shiga rom 1 second floor itama tayi azamad fad'awa d'akin kallonta yayi ganin ta rufe d'akin sannan yace

"Baiwar Allah lafiya? Murmushi tayi masa sannan tace

"Taimako nake nema" gyaran tsayuwar sa yayi

"Amma seki rutseni a d'aki, bake nagani reception a zaune ba? Mesa bakimun magana ba acen reception ba se nan" murmushi tayi masa sannan tace

"Maganar ce take buk'atar sirri" Jinjina kansa yayi

"To Bismillah ina jinki" murmushi tayi sannan tace

"Aikine zan baka kuma aikin riba biyu ne, na farko zaka samu ladan taimakawan da zakayi a ceci rayuka da dama na biyi zan biyaka kud'in aikinka" Murmushi yayi

"Hajiya kenan shi aikin lada ai baya buk'atar biya a duniya, guxurine na lahira ai" Murmushi tayi kafin tace

"Hakane idan bazaka damuba nawane albashinka as a cleaner duk wata? Gyaran sandar mop dake hannun sa yayi kafin yace

"Kai dayawa fa dubu ashirin ake bani duk wata, dukda bawai ta wadaceni da iyalina bane amma alhamdulillah da kafin na samu aikin ma ko karin kumallo bama samu yanzu ko alhamdulillah kobamuci me dad'i ba mukanci so d'aya a rana kuma wani zubin niman kwashi abincin da ake ragawa innazo cleaning naje da abuna gida" Gyrana mayafinta tayi kafin tace

"Anya zamuyi aiki dakai kuwa kanada surutu tambaya d'aya amsa ashirin" D'an matsowa yayi yace

"Am very good at keeping secret bana fallasa sirin wani" Jinjina kanta tayi kafin tace

"Idan kamun abinda nakeso kai tsaye zan saya maka babur,zan baka albashin ka na wata rib'i so goma kai tsaye zan kuma ciyar da gidanka da ingantaccen abinci na wata shida" Kallonta yayi a tsorace

"Hajiya kisa zaki sakani ? Yanzu kam daroya tayi siririya

"Allah ya kiyaye ko kiyashi na biya akashe, ko d'aya kaga wannan? Ta nuna masa wani k'aramin abu a hannun ta tace

"Wannan recoder ce dazaka lak'amun a wani d'aki acikin hotel d'in nan, maganar da wasu zasuyi kawai nakeso na sani banda wannan ba komai, ka nemi kamar bayan gado ka lak'amun ita ka kuma zaromun ita bayan sunyi checking out" Murmushi yayi

"Dan wannan aiko kyauta sena miki, aiki indai bame had'arin gaske bane ba ai zanyi, base kin bani ko k'wamdala ba" Murmushi tayi a karo na barkatai

"Zanma biyaka amma menene sunanka?

"Aminullah" ya bata amsa a tak'aice

"Ba damuwa yanzu ungowa wannan dubu d'arice ka rik'e kafin aikin ya kammala, sannan kuma.Aminullah banda garaje kasan akwai CCTV ko ina a wannan hotel d'in dan haka sekayi k'ok'arin amfani da style wurin sak'ala shi yanad gum kana d'aya wannan bak'in bayan ze manne jikin koma meye" Jinjina kai yayi

"Amma hajiya hanzari ba gudu ba, bani zanyi aikin yamma ba kozan dawo se gobe da safe" Jinjina kanta tayi

"Bakasa matsala bani number ka zan saving sannan saganan semuke commumicating"

"To hajiya wanne d'akin ne?

"Room 11 ne a 3rd floor" Jinjina kansa yayi kafin yace zan gama da wannan da wuri sena haura, nagode sosai" Daganan sukayi sallama ta fito kai tsaye wurin shopping ta nufa.

Hammood kuwa daya isa location nata na k'arshe yasha mamaki da ganin wurin tome zatayi anan kuma a ina take? Ganin dai tabbas indai wayarta tana hannunta ta tona wurin ya sanya ya sauka ya soma tambayar kosunga k'anwarsa waye waye anan me saka cajin ya tabbatar masa tabar wayart charge ne tace zataje da tawo, dawowa yayi cikin mota ya soma murmushi

"Yarinyar nan shu'uma ce, tana sani ta ajiye wayar ta, waime ta d'auke sa ne, how much does she know about him by now? she's very cleaver tadad'e tanayi be ankara ba se yanzu!!

Zuwanta shopping tana zagaye a hankali tana d'ebar abubuwan buk'atarta kanta a k'asa kawai wani k'amshi dabazata tab'a mantawa dashi ba ya daki hancinta, da sauri ta d'ago idanta sukayi karo dana momy, cikin tsananin jin dad'i da k'auna tace

"Momy" Momy kuwa da take wa Hafsat kallon sani ganin ta k'ara haske da murjewa tace tana kallonta "Kamar Hafsat ko" Fad'awa jikinta hafsat tayi

"Momy nice baki gane ba dududu kwana nawa? Rungumarta momy ma tayi kafin tace

"Allah sarki 'yata, nayi kewar rashinki, naje garin kuma labarin danaji bemun dad'i ba, acen naji sharrin da Bilal ya miki abin ya d'auren kaina sosai, na gaya musu gaskiyar niba haka ya faru ba, kece ya rage na nemi gafararki hafsat, muje gida, dama kekam ina shirin sanar dake dukmanin abinda ya faru tun daga farko har k'arshe" Murmushi Hafsat tayi kafin tace

"Idan na dad'e banje gidaba zasu nemeni momy, ki bari gobe zanzo" rik'o hannunta tayi to muje mota zan baki labarin duk abinda ya faru acikin minti uku zuwa biyar" Hafsat bazata iya yiwa momy musuba dan haka ta bita har mota, anan taji labarin daya girgiza ta kuma ta tabbatar khairiyya itace kishiyarta a yanzu dama tayi imanin akwai inda tasan khairiyya, kenan Bilal fyad'e yayiwa khairiyya? Kuka kam atare suka shashi itada momy daga k'arshe suka rabu bayan exchnaging number waya suna yiwa juna alk'awarin sake had'uwa, dan hafsat ta nunawa momy cewar bazata iya bata labarin taba a yanzu sesun sake had'uwa sabida tana sauri, dan kuwa momy tace tanaso hafsat ta dawo gidanta da zama gaba d'aya.... Aran Hafsat tace Momy wannan bame yiyuwa bane yanzu.


Ko wannan karon a k'ofar shiga Fadar Sarauni sukayi karo da Hammood,kallon juna sukayi sannan tayi gaba abinda batare datace masa ci kanka ba, a fusace yabi bayanta zuciyar sa tana harbawa, yayi sa'a Bahar bata parlor dan haka yabita har cen cikin d'akinta, kallon juna suka tsayayi tace tana zare abayar dake jikinta da dankwali ta dawo iya riga da wandone a jikinta

"Malam lafiya"

"Daga ina kike ? Ya tambayeta yana muzurai murmushi tayi

"Mesa kakeso ka sani ? Dakabi bayana bakaga inda naje bane dakake tambaya na" kallon ta yayi yarasa wace irin mara kunyace Hafsat

"Kinsan dai daga fitarki har dawowarki kina tare ne da tsinuwar Allah da mala'ikunsa ko? Kina matar aure kike fita babu izinin fita, daga yanxu ban yarda kije konan dacen batare da izinina ba" Wata dariyar raini ta masa

"Ban gane me kake nufi ba ? Tun yaushe ka bani izinin fita tunda har kai kayi kwance? Yazan biye maka mu lalace?

"Me kike nufi da kalamanki?

"Oho a tambaye ka" Rugowa yayi se damk'e ta ta kauce masa ta arce aguje zuwa waje yabiyo bayanta, a parlor ta zagaye bayan bahar shikuwa segashi aguje

"Nashiga Uku Ni Bahar Sarauni, yau naga d'ebar albarka la'ada wuri, kai yanzu dan bakada mutunci shine bazaka dena bibiyar yarinyar nan ba, Allahu bazakamun abinda kakeso agidaba, gobe zan kaima ka matarka" Mak'e kafad'a hafsat tayi cikin muryan sangarta tace

"Mugune Bahar, karki kaini wurinsa dan Allah, ya dinga jamun suma na idan banyi abinda yake so ba"

"Aikuwa idan ya kuma ja miki suma senaja mai la'anta yaseen, kwanakin nan rashin Daraja Hammude keji, ita waccen matar taka bazata iyaba bane ba? Kake bibiyarmun jikata da sabon dalon d'angwalar yaji, banason renin hammatan me shayi kamaji na gaya maka" A harzuk'e yabar gidan bayaso yayi magana amma tabbas seyaci kaniyar hafsat.

*************
Dukkansu su uku atare sukayi shirin fita, Hammood, khairiyya da kuma Hafsat, khairiyya da Hafsat munsan destination d'insu mararraba hotel zasuje, hammood ne bamusan inda zashiba, ga kuma idan fada dasuma suka d'auki destination d'aya dasu khairiyya..........

*Sorry na muku kad'an, ba charge a phone d'ina, gashi naso sosai inga yau ko Hafsat zata tsira......to mu had'u gobe dai inshaa Allah.*

*Mom Nu'aiym*

  *TSINTAR AYA*  FREE BOOK

         *BILLY GALADANCHI*

     *SHAFI NA ASHIRIN DA UKU*

23.
Tunda wad'annan mutanen suka fara shigowa se gaba d'aya hammood yabar reception sabida shima bawai ya fito haka kawai bane, tsaf acikin motar sa seda ya sauya kaya zuwa wata matacciyar yadi da hula kayan daud'ar jikinsu kad'ai ta ishe su, gaba d'aya yayi dressing irin na me garin k'auye da wani karkataccen madubi bayau ya saba basaja irin haka ba, dan kuwa gaba d'aya motar dayake kanta ba wacce aka sanshi da ita bace, wata iriyar starlet ce me sanya ciwon jiki, gaba d'aya rawanin dake kansa ya wani cukurkud'e wuri d'aya gashi a karkace, wannan shirin ba k'aramin b'atar da kamanin sa yayi ba fiyeda yanda ya kawar da kamanin Hafsat, shi kanshi shirin barin wurin yake dan haka kusan atare suka shiga abun hawa, ita tahau napep shikuwa ya shiga wannan kwarab'abbiyar starlet danake da tak'inin ta girmewa shekarun haihuwar sa, kallon matar yake data shiga keke napep d'in, tun d'azu me napep d'in yake wurin bayan ammasa bayanin wani abu an nuna masa waya, kuma wanda yabi bayan matar yashiga napep d'in bawai tare suke da matar ba, sannan kuma yaga yana wata magana dame napep d'in kafin fitowar ta, kenan parking d'in natane dama ita ake jira? Dama motarsa a kunne take hakan yasa yayi azamar zuwa domin yayi overtaking nasu amma me seyaga matar ciki wuyanta  ya tafi baya tamkar matacciya har mayafinta

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login