Showing 3001 words to 6000 words out of 113608 words

Chapter 2 - TSINTAR_AYA

Start ads

09 Aug 2025

688

Middle Ads

sabida nauyinta amma ita tazo ta maimaita da bakinta" Jikin 'yar shara (Hafsat) ne ya fara rawa sosai sabida tsoro ta k'ure a toilet anata kiranta amma bata fitoba, seda momy taje ta fincikota sannan ta fito tanata zare ido, Baba Lami tace

"Ke 'Yar sha maimaita abinda kikazo kika gayamun Hajiya da yaro sunayi agidan nan" Jikinta rawa yakeyi sosai yanzu kam har fitsari ya soma fito mata tace

"Baba Lami dan Allah ki rufamun asiri" Mari Baba Lami takai mata

"Na rufa miki asiri kamar yaya? kina neman tona mana asiri kice in rufe naki, kimga hajiya zuwa tayi tana gayamun waikeda yaro Lalata kukeyi kullum cikin dare nan yake kwana sanda bama nan" Da mamaki momy ta kalli'Yar sha sannan tace

"Hoo yaron zamani, Lallai na yarda duniya tayi gurb'acewar dabazata gyaruba sesa gyaran Allah, kokin san dabakwa nan bilal k'ararta ya kawomun, fita takeyi idan na fita na zaneta namata fad'a shine zaki dawo da sharrin akanmu? ko shakka banayi wannan yarinyar dalilin kenan dayasa mutan garinsu ma bame sonta, amma ni bazance miki komai ba, bari Bilal yazo ya maidaki garinku tunkan kinb'atan suna agari, aniyarki ta biki Yar shara" Haka suka tasata agaba da uwar Bilal da momy suka mata tatas!

kuka ta kwanayi a wannan daren babu k'auk'autawa, washe gari bilal da duka ya tashi mata tamkar ze kashe ta, haka suka fita akan ze kaita garinsu insunso su kasheta, ita tasan cewar bilal baze barta ta rayu a farin cikiba, tanada yak'inin cewan abinda yakeso ajikimta baze hak'uraba harse ya karb'a.


*MOM NU'AIYM.*

  *TSINTAR AYA* FREE BOOK.

*BILLY GALADANCHI*

*Sak'on gaisuwa zuwaga Babbar Antyna, mace me karamci kuma me girmama, babba da yaro, Alkhairin Allah yakai miki a duk inda kike  Anty mejidda musa*

*Makaranta Littafin tsintar Aya nagode da rububin son dakuka nuna masa tun a shafin farko, Allah yabar k'auna.*

*SHAFI NA BIYU*

Dariya ya kwashe da ita sanda ta shigo motar jikinta yana b'ari, sanda ya fita a gidan ya saisaita kan motar sosai akan titi sannan ya waigo ya kalleta yana wani kashe ido

"Tsuntsu daga sama gashashe, wato lallai 'yar sha bakida hankali, tsammani kike wai Baba zata tab'a yadda da zancenki,kokuma kina tsammanin kamar akwai abinda ze tab'a hanani cimma burina akanki, wlh sekin gane kurenki a hannuna" Batace masa komai ba banda kukan datake kanta asaman cinyoyinta.Batayi tsammanin cewa zekaita garin nasu ba, amma ga mamakinta setaga ya d'auki hanyar garin nasu se faman wak'e wak'en sa yakeyi tamkar wanda akawa bushara da gidan aljanna!

     Harsuka isa be kuma koda kallon inda take ba, gidan nasu babban gidane sosai me yalwar shiguhu kala kala, kana kuma ko wane b'angaren bayan ka wuce shiguhun runface ta bunu da kuma d'akuna wasu ginin laka wasu kuma bukka ce, tsarin gidan kana ganinsa zaka shaida cewar irin gidan daya had'a dukka kowa da kowa ne, ma'ana Extended family.... Tun a soro na k'arshe Bilal yake rafka sallama har ya bazama cikin gidan, harya cire rai da za'a amsa masa sekuma kaman daga sama ya soma ganin mutane tamkar ana yayyafin su suna fitowa, Atare d'aukacin mutanen wurin suka had'a baki wurin ambatar 'yar shara! wanda hakan ba k'aramin k'ara rikitar da ita yayi ba cikin tsananin firgici take kallon kowa idan ta ya sauka akan Baba jere daya tsatsareta da ido tamkar ze cinyeta d'anya. Bilal gaggaisawa yayi da mazan ta hanyar musabaha sannan yace

"Hajiya Barira ce tamun umarni akan in dawo da 'Yar shara gida, tace in sanar daku kuyi hak'uri da k'in zuwan datayi da kanta ta dawo da ita, tanajin kunyar kune ta kasa rik'eta kamar yanda tayi alk'awari, tace hakan ya biyo bayan cikin shegen dake jikin 'Yar shara ne harna tsawo wata biyu, bazata iya abun kunya ba ita kam, sabida haka na dawo da ita tushiyar ta" Tas wurin ya d'auki salati yayinda lokaci d'aya duniyar ta soma juyawa da 'yar shara tana shawagi da ita, wannan wane mummunan k'azafi ne Bilal yake shirin manna mata, sama sama tajiyo muryar Baba jere yana cewa

"Kayi tafiyar ka Bilal, zamu mata hukuncin daya dace da ita" Haka.ta ruk'unk'une wuri d'aya tana gunjin kuka amma sam ta kasa magana har Bilal ya juya sekuma ya dawo kusa da ita ya sunkuya ya ajiye mata wata leda, ga kati nan ajiki lambar wayana, idan azaba tayi azaba kika yanke hukuncin bani kanki seki nemeni a waya kud'ine acikin wannan biredin sekiyita tattalinsa dan nasan kwana bazaki k'ara agarin nan ba zasu koraki" Batace masa komai ba, babu kuma wanda yaji maganar dasuke se ita kad'ai sabida yanda yazo daf da ita yana magana k'asa k'asa...... Haka ya tafi banda kuka babu abinda 'Yar shara takeyi.Kallon tsana Baba jere yabita dashi sannan yace

"'Yar k'wai bani kayan wuta da alamar k'ira" Inna suwai ce tayi azamar kallon sa, murya yana rawa tace

"Jere me zakayi? kallon ta shima yayi

"Bakiji tayi shege ba, yanda nayi da ubanta haka itama zan mata" Idanta ne ya kawo ruwa babu musu ko gaddama a atsakanin su, babu wanda yake ja da hukuncin jere shine me garin garin gaba d'aya kuma biyayya agaresa batada hijabi awurin su dole sesunyi jikinta yana karkarwa ta zube akan gwiwowinta

"Jere ka dubi girman Allah ka sassauta mata, karka manta azabar k'irane yayi sanadin Djoro, kabar 'Yar shara itakam ita kad'ai ne a tsatson Djoro dazan kalla inji sanyi" Wani kallo ta wurga mata yanzu a hautsine

"Bana buk'atar tsatson Djoro a zuri'a ta, Yanda Allah ya kashe Djoro Allah ya kashe D'iyatai daya bari, Idan zan mata k'ira har a tafukan hannayenta zan manna mata sabida azaban wutan yajewa d'an shegen dake shikinta shima ya mutu atare da ita" Kuka ta saka da iyakacin k'arfin ta ruga ta rungume 'yar shara, zuwa lokacin da aka kawo kayan k'ira aka hura huta aka soma d'o'd'in k'arfen iyakacin gigicewa Hafsat ta gigice, batasan me ma'anar hakan ba, amma menene ya kashe mahaifinta ance rashin lafiya yayi, itama ciwon zasu zasu saka mata kome? k'aramar akwatinta ta janyo ta cura wayarta aciki sannan a hankali ta ware biredin nan ta zaro kudinta ta cura a rigar mamanta tanabin kowa da kallo, katin da lambar wayar Bilal yake aciki ma sanda ta d'auka ta adana ajikinta se zare ido take, batasan me za'a mata ba amma tabbas tasan akwai alamun zata dauki yar mitsitsiyar akwatinta ta kwasa aguje inhar ya kasance azabace! Lokacin da k'arfen yayi azabar zafi se wasu maza tagani datakeda yak'inin yan uwanta ne sukazo suka daddafeta tun a nan ta soma ihu mik'ar da k'afarta akayi aka dafe Jere ya daddage ya manna mata k'arfen a tsakiyar tafin k'afarta!!! Wata uwar k'ara data k'walla tsabar azaba seda ta saki fitsari a wando ba shiri, haka ya mata tambari biyu a kowace k'afa zuwa wannan lokacin ta suma batasan inda kanta yake ba, k'ara dafa k'arafan yake yana ik'irarin manna mata a hannu Inna suwai ta rungumeshi tana kuka akan yabar ta a haka, kallon ta yayi yana yamutsa fuska

"kona manna mata kokuma akaita kan hanya ta kama gabanta" Dama bata saka ran ze barta ta zauna ba dan haka da sauri ta amince akan a koretan tasan koba jima koba dad'e zata nemi gida, koda babu ransu kuwa. Kallon masu dafeta yayi yace

"Ko inuwar wannan karku barmun agidana, ku fita da ita daga garin nan kuje cen bakin titi ku ajiyeta itada kayan ta da komanta" Haka suka amsa masa suka kwasheta a some ita da kayan ta, akan hanyar su aka soma ruwan sama ga duhu ya soma sauka wannan ya sanya babu wata tazara da garin suka ajiyeta suka ajiye mata akwatinta suka juya inda anan dukan ruwan sama ya dawo da ita cikin hayyacin amma seme ta farka cikin tsananin azaba da radad'i sannan babu akwatin kayanta a ranta ta ayyana acen aka kwace mata, ta godewa Allah daya sanya bata saka kud'inta a jakar ba, amma me tana lalubar rigar mamanta seta ji wayam! bata sani wad'an nan yan uwan nata sunga sanda ta saka kud'i a wurin, sune suka zace wayarta da kud'in suka barta da akwati wanda kafin ta farfad'o wani mara imani ya kwace. Babu takalmi a k'afarta batasan ammata lahani ba seda ta mik'e nan take ta zube awurin sabida wata sabuwar azabar data ziyarce ta ga ruwa ana tsulawa ga dare yayi, kukan ma a wannan lokacin gagararta yayi, jefi jefi motoci suke wucewa gata a gurfane bazata iya taka k'afarta ba bare ta saka musu hannu su taimaketa!

**************
    *Washe gari*

Anan ta kwana cikin tsananin radad'i da fargaba me tsanani, ilahirin ruwan akanta ya kare a gindin wata bishiya, da asuba ma se taimama tayi tayi salla a zaune, har azahar ba yalwar mutane akan titin, tunanin abinyi takeyi ga azabar k'unar dake tafin k'afarta, haka ta mik'e tanaji tana gani ta soma tafiya akan duga duganta inda wutar bata kaiba, haka tayita tafiya se la'asar ta samu wata motar yaji ta d'auketa asama nanma da k'yar ta samu hawa sabida wuyar datake ciki,tare da alk'awarin zata bashi Naira hamsin idan sun isa gari.

     Yamma sosai ya dawo daga wurin motsa jiki ya tsaya yabi wurin da kallo, yau ina wannan yarinyar ne? idan baze manta ba ya ganta wurin yafi so bakwai, kota dena zama a k'asan bishiyar ne? meke damunsa na damuwa da ita sosai haka ya tambayi kansa? Bafa komai kawai tausayi take bashi ko ba'a fad'a ba yasan akwai abinda yake damun ta, besan fuskarta ba dan kuwa kullum kwanan duniya kanta a sunkuye yake amma ta masa tsaaye tsayin alif ajikin allo a zuci kome yasa oho! Nisawa yayi kawai  yaci gaba da gudunsa jikinsa yana nan a murd'e se gumi yake had'awa a sukwane ya isa gida amma kamar kullum a masallaci ya tsaya yayi sallah tukunna har isha sannan ya shiga ciki. A gaggauce yayi wanka ya shirya yauma kamar kullum, wurin Muhsin ze tafi suyi maganar abinda ya shafi kasuwan cinsu sabida harga Allah k'asar yake neman dalilin daze d'aga mata idan ba yabar k'asar ba D'an galadima ze sanya yazo ya aikata abinda bashi kenan ba, D'an galadima munafiki ne...

    'Yar shara kuwa a tasha da suka sauka anan dirama ta tashi akan kud'in motar da tace zata bayar idan sun iso, dan kuwa batada ko k'wandala banda uban zogin da k'afafunta ke mata na rad'ad'in k'una... wata iriyar kallon banza kwandastan motar ya wurga mata yana lashe leb'ensa sannan yace

"Idan kin yarda in bashi kud'insa in rufa miki asiri, kekuma ki biyani daga baya" jikinta yana rawa ta amince da hakan aganinta zata samu kud'insa seta biyasa daga bayan koma a inane, dan haka ta masa godiya shikuwa ya biya kud'in cas bisa ass. Godiya ta masa azuwan idan ta samu zata biyasa kud'insa shikuwa yace alambaran kwana zasuyi atare ya fanshe hamsin d'insa, tun suna magana a cikin rad'a har maganar ta tashi atasha aka zagayesu, atake ya murd'eta akan itace ta masa alk'awarin ze fanshe ajikinta, gashi ta gaji da tsayuwar sabida akan duga duganta take tsaye, wani mutum ne yace da kwandastan

"Shinkai Zubairu dakata, nawane kud'in nata" Seda ya kalleta sannan ya kawar da kansa yace "D'ari bakwai ne" Mutumin ne ya zaro d'ari bakwai ya mik'a masa sannan yace yana kallon sa

"Bata amince da kaiba, dan haka gankud'inka nan ta biyaka, wannan yarinyar yar luwai caras da ita bazatabi k'azami kuma karen mota irinka ba zubairu, kumama akan wannan gajeran farashi, yarinya muje nizan baki dubu biyu" Cikin kuka tace

"Niba karuwa bace dazaku rik'a cilli dani tamkar wata k'wallo, wannan salon wani wulak'ancine kuma, ni a k'auyen d'an biram suka d'akkoni akan idan munzo zan basu naira hamsin, yaya kuma zezo yace d'ari bakwai ne? banisa hamsin amma inada zoben azurfa na tabbatar zekai dubu biyun da kai kake ik'irarin zaka bani, sabida haka gashi kaje ka sayar kabiya karuwa irinka badai niba" Ta k'arashe maganar tana cilla masa zoben ya daki k'irjinsa ya fad'i a k'asa

"Abinda kukamun se anwa 'ya'ya ko matanku ko k'aninku wlh, na barku da Allah shine ze sakamu  mugwayen banza" Ta juya tana d'ingishi ta fita tabar cikin tashan yayinda su kuwa sukayi cirko cirko suna kallon ikon Allah.

     A bakin junction taje ta zauna ta sunkuyar da kanta, ga dare yayi koda babu waya a hannunta ta tabbatar cewar tara na dare yayi idan ma be gota ba, koda ganin yanayin yanda mutane suka rage kai kawo kasan cewar dare ya ruga sosai, Ganin zata b'atawa kanta lokaci ya sanya ta mik'e ta soma d'ingishin datake gidan momy zata koma, itace rufin asirinta gwanda zama wurin Bilal idan Allah yaso baze samu abinda yakeso awurin taba amma wadannan mutanen ba Allah a ransu ko dukkansu farmata zasuyi, tana wannan unguwar datasha yake da nisa sosai da gidan momy amma haka zata taka, bazata hau wani abin hawa batada kudiba dan batasan yanda za'a k'arb'eta ba agidan, da wannan shawarar taci gaba da d'ingishi tana takawa a hankali.........

  Hamood be bar wurin Muhseen ba se k'arfe sha d'aya da 'yan mintuna, babu yalwar abun hawa kazalika jefi jefi zakaga mutane suna yawo, kuma duk wanda ka gani zakaga alaman sauri a tattare dashi, yanayin yanda take tafiya ya shagaltar dashi, d'ingishi takeyi alama sun nuna cewar da dugaduganta take takun tome yasa? yasan wannan kalan hijabin da zanen jikin amma a inane ma? yaya take tafiya babu takalmi a k'afarta? da wad'an nan tunane tunanen yaje gida batare daya tsaya wurin yarinyar ba sedai tambayoyi marasa amsa fal a kansa.

'Yar shara tayi tafiya sosai har k'arfe d'aya na dare ya tadda ta babu alamun zata isa gidan Momy, hankalinta ya soma tashi sabida ta kula cewan daga ita se karnuka akan hanyoyin datakebi d'in, sannan idan ta kaucewa titunama bawai b'ullewa zatayi ba, kana ko yanzu a yanda take hange akwai nisa sosai da inda take hari..... Takun dataji a bayanta ne ya sanya tayi hanzarin waigowa mazane sunkai su bakwai, a yanayin yanda ta gansu kuwa babu alamar mutunci a tattare dasu, wannan ya bata damar k'ara mai a tafiyar datakeyi dukda bata iya taka k'afarta sedai d'ingishi, tun suna k'ara saurin dasuke har suka soma gudu kad'an, ganin haka itama ta k'arawa dokinta linzami ta soma gudun cikin azabar k'una da radad'in da k'afarta keyi,dama gashi tana lokacin al'adarta wannan ya sanya mararta ta murd'e mata wuri d'aya lokaci d'aya jini ya kuma b'alle mata ga dama matarin data saka tuni ya jik'e sharaf! gudun fanfalak'i suka somayi atare suna ihu suna sowa suna mata dariya tsuntsu daga sama gashashe shine abinda suketa fad'a!

Agogon dake ajiye agefen bed side drawer d'insa ya kalla, k'arfe d'aya saura kwata, mesa ya kasa bacci, yarinyar batayi kama da cewar tana cikin nutsuwa ba, mesa yakeji a ransa tamkar ya baro wani aiki me muhimmanci atiti beyiba gameda yarinyar, ya ganta a yanayi irin na rashin lafiya yakuma ganta tabbas tana neman taimako, ba wannan bama ya ganta lokacin da dara yaja k'afar mata sosai tayi k'aranci akan titi shin mesa be tsaya yaji meke damun taba? zabura yayi sannan ya zari key na motar sa, gajeran wando ne ajikinsa iya gwiwa sekuma riga mara hannu med'an fad'i, hanyar waje kawai ya nausa aguje yauma kamar kullum, hadiman dake hidima a b'abgarensa wanda basuyi bacci ba se gulmarsa suke.....

A hankali yake tafiya da motar sa haryakai inda yake tsammanin ganinta, direction datakebi anan yabi amma sam ko alamarta babu, beji ya karaya ba haka yaci gaba da zagayen titunan yana k'arewa wuraren kallo, cen ya hangota a kwance sedai wannan karon babu zani ajikinta babu hijabin duk gasunan agefen ta, da hanzari yayi parking motarsa yafito aguje ya k'araso inda take, bin yanayin ta yayi da kallo yana me haske ta da hasken fitilar wayar hannunsa, hannunta taja ta rufe fuskarta inda zata karewa musamman idanta, sannan taja hanninta d'aya tana k'ok'arin rufe jikinta dake a tsiraice ko pant d'inta yana gefe cen a yashe iya rigarta ne kawai ajikinta kuma itama duk an yaga ta, alamomi tas sun nuna fyad'e aka mata tunda gashi harda jini sosai ajikinta, zaninta yayi hanzarin zara ya rufa mata sannan ya juya bayansa kawai ya koma motarsa.


*Idan baku manta ba na gaya muku bazan samu daman yin posting kullum ba, bayan kwana d'add'aya zankeyi da izinin Allah.*

*Mom Nu'aiym.*

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA UKU*

Sumar kansa ya shafa zuwa k'eya cikin tsananin damuwa da fad'uwar gaba mara misaltuwa, mekenan ya faru wa 'yar mutane? yaya zeyi da ita a yanzu? wannan laifin sane ko me? mesa dacen datake tafiya acikin dare tana d'ingishi be tsaya yaji inda zataje ba? menene amfanin zuwansa yanzu? ina ze kaita? Asibiti? they will surely ask of police report ta ina ze fara? besan komai ba, acikin dare yaganta akan ttii anyi raping nata sai kuma me? shi daga ina yake? iska me zafi ya furzar daga cikin bakin sa sannan ya juya ya kuma kallon ta. Wayarsa ya janyo ya kira Muhseen be d'aukaba dama baze d'auka d'inka ba dan yasan baze masa magana ba, dan haka ya masa txt na wurin daze sameshi yanzu amma shiru shiru babu alamun dawowar sako har zuwa mintuna goma,yanada yak'inin cewar tabbas Muhseen bacci yake. k'ara mayarda dubanshi yayi zuwa ga yarinyar k'ok'arin d'aura zaninta take daga kwancen, sanan kuma seja baya take dashi, ganin yana nufota ya tilasta mata mik'ewa da k'yar tana kuka tare da motsa labb'anta sedai sam baya jin metake cewa, gyaran zaman zanin take kokarin yi amma ina se jiri ya d'ebeta ta tafi luuu zata fad'i a sume, da hanzari yayi azamar rik'ota sannan ya zube akan gwaiwowinsa d'auke da ita, kallon fuskarta yake tabbas suma tayi, lallai abun yafi k'arfin tunanin sa, be b'atawa kansa lokaci ba ya zurata a mota ya finciki motar se gida, nanma kwasarta yayi hannu bibbiyu zuwa b'angaren sa yanzu ma aguje kamar kullum, sedai wannan karon kana gani kasan a uzurcen gaske yake, be

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login