Showing 81001 words to 84000 words out of 113608 words
k'arawa fad'i
"Hakane na zama anty, yanxu ina muka kwana,?" Murmushi yayi
"So nake ki nutsu mu saurari labarin ta" gyaran zaman ta tayi kafin tace "Malama Hafsat Bismillah" Seda tayi gyaran murya sannan tace
"Na tasone a hannun kakata wacce ta haifi ubana, tun sanda na bud'i idona na ganni duniya nake kuma shaida mutane babu abinda nafi sabawa dashi sama da fuskar kakata, bansan waye Babata ba amma tabbas yanayin d'acin harshe na yana tabbatar mun da cewar babu saukar d'and'anon nono uwar haihuwa acikin sa, yanayin yanda gabb'an jikina,zuciya da ruhina suka kwad'aita dason jin dumi irin na mahaifiya ya tabbatar mun dacewar tabbas ban tab'a sanin d'imin jikin uwar haihuwa ta ajikina ba, wacce na bud'i ido da ita itace Baba suwai kakata kenan. Na taso gidan yawa gidan shugaban wani babban gari na fulani me zaman kansa, gaba d'aya ba ruga bace babban garine me d'auke da sassa sassa na fulani acikin ruga iri iri, wanda duk wannan suna k'ark'ashin kulawar Kakana Baba Jere wanda shine limamin garin shine kuma babban me gari na duka yankunan garin da kuma rugagen dake mak'otaka da ahalin garin sa. Acikin gidan namu akwai tarin samari da 'yan mata wanda idan wannan ba uwarku d'aya ba tokuwa d'an qanin uba ko wan uba ne, acikin fulani dana sani gidan Baba jere kad'aine basuda gadon kiwo ko noma sedai k'ira, mak'era ne da suka shahara a wannan fannin sedai irin fulanin nan ne dasam basuda d'igon addini a al'amuran su, gaba d'aya komai nasu yana tafiya ne bisa wata wahaltacciyar al'ada mara tushe,ko kak'i kokaso tilas ne kabi wannan al'adar, koda na tashi bansan sunana Hafsah ba sedaga baya 'yar shara shine sunan danasan yake mallakina, bayaga haka banida wani suna agidan, kyara da tsangwama yanda kukasan a duniya niba mutum bace wata halittace ta daban, inada shekaru shida a duniya akazo neman yara masu son aikatau kawai se Baba suwai ta rok'i alfarmar Baba jere yabarni in tafi burni aikatau nan take kuwa yace dama ya tsani d'aga ido yaga 'yar shara acikin gidan sa, dan haka in tattara in tafi har yau kalaman sa sunamun amsa kuwwa sanda yafito ya kalleni ina musu sallama yace
"Garin da ubanki ya tafi be dawo ba Allah ya sanya dagacen kibi bayanshi 'yar shara" Bansan menene asalin tarihina ba seda na shekara biyu a birni a lokacin ina aiki wani gida na wata malamar makaranta ina mata rainon yarta dan haka dani take zuwa makaranta, aji biyu take d'auka a wancen lokacin nikuwa seya zamana duk karatun da akewa yaran yana nan daram akaina bayako motsi kuma banida wata wasa abakina se karatun nan, ganin haka malama ta sanyani aji d'aya a primary, dukna girmi yan ajinmu dankuwa nafi shekaru shida haka na dage Allah ya sanya inada tsananin k'ok'ari matsala ta d'aya ce inada kafiya, fad'a ga kuma rashin kunya, sam bana lank'wasuwa wanda wannan ya sanya ina aji shida a primary a lokacin ina shekaru sha biyu kawai na rasa aikina agidan malama, ina gama common interance ta mayar dani gida akan wai banajin magana ana fad'a ina fad'a, nan Baba jere yamun duka ya kusa sumar dani, daganan duk inda akazo d'eban yara 'yan aiki sekiga ance nayi girma har Allah ya kawo Hajiya Barira garin ita kuwa ta dawo ne dame mata aiki akan tayi shege bataji kuma ita batason yara, ana haka aka ce gani nan take Baba jere ya hau gaya mata mugwayen halayena, inda tace aid'a na kowa ne, dan haka ita taji ta gani ba akan 'yar aiki bama ta d'aukeni a matsayin 'yar rik'o, zata rik'eni amana dukda halina, haka muka kwaso muna dawowa Burni na nuna mata takardar primary na nace nifa so nake in zama lauya Baba jere zan d'aure, haka na shiga bata baki harta sakani secondry school aji d'aya nake zuwa abuna, na zama yar gidan masu kud'i bana mason ace yau inje k'auyen mu, haka nazo bayan nakai S.S 1 se wani al'amari ya soma faruwa dani mara dad'i, dama cen daga secondry school danake zuwa kullum se an kawowa momy k'arana, nayiwa malami kaza rashin kunya nayiwa malami kaza rashin kunya, wannan ya sanya momy setake sanya D'an me gadin ta wato Yaya Bilal daya xama d'an gida kamar ni yakemun duka wannan ya sanya a duniya banida wanda nake tsoro sama da yaa Bilal, sabida muguntar sa yaga damar ya sanyani tsallen kwad'o idan banyi ba kuma inci duka, hakan ya tilastani rage yiwa malamai na rashin kunya sekuma abun ya dawo kullum se anmun tsakani da wani a class d'inmu danni sam banida hak'uri kona kwabo ni kaina na sani, haka akayita gwagwarmaya dani momy tanata hak'uri har zuwa lokacin da Yaa Billal ya tsiro da wata d'abi'ar banza a kaina" shiru tayi tana kallon su wanda dukkansu ita suke se Hammood ne dake k'arawa matsowa kusa da ita cikin tashin hankali
"Wane irin d'abi'a ne wannan? Meyake miki duka? Share hawayen idanta tayi ta girgiza masa kanta
"Tab'amun jikina yake yana cewa zeyi iskanci dani, kuma idan ban tsayaba ya dinga marina yana cewa seya k'ullamun sharri, koda wane lokaci Allah ze kawo dalilin daze hanashi cimma mugun burinsa akaina, ta wata hanya mafi sauk'o, tsoron abinda yakemun ya sanya duk sanda nadawo saga school kafin momy ta dawo daga gun aiki nake sauri inbar gidan zuwa gun wata bishiyar bayan layin mu indai yana gari, be tab'a sanin inda nake zuwa ba, da haka har wata rana yazo yadinga yagalgalar jikina yana dukana, katsam sega momy ta dawo lokacin dabata saba dawowa ba, ba wannan lokacin na saba jiyo sautukan zantuttukan banza da iface iface marasa kan gado agidan ba tsakanin Momy da Bilal amma tabbas a wannan ranar na gano ihun meye nakeji, hankalina ya tashi akan yanayi mummunar alak'ar dana fahimta akwai tsakanin su, dake banida hankali nima se kawai naje na samu Baba Lami wadda itace uwar Bilal na zayyane mata komai nan naga rashin dattako dan kuwa atake taje ta gayawa momy wai ina mata sharri itada Bilal momy bata fad'i mummunan kalma ko d'aya akaina ba kawai tace bilal ya mayar dani gida, dama kuma yasan k'auyen mu kuma shine yake kaini, akwai lokacin daya soma koyamun mota acewar momy inna iya inyana school koda cefane na rik'a yi mata amma seyazo da iskancin sa seban iya sosai ba na dena zuwa kawai, dama Bilal yana cike da haushi na yanzu kuma gani gashi abanza ance ya kaini k'auyenmu" kuka ta tsaya ta d'anyi wanda da sauri Hmmood ya matso ya rik'e hannun ta, meya miki dayaje kaiki gida? Tab'aki ya kuma yi? Wani abun ya faru ne" tana share k'wallah tace
"Banaji mahaifiyata da akace ta mutu batamun addu'a har wannan lokacin, sabida Bilal bayan ya kaini gida seyace da kakana inji Hajiya Barira wai a mayar dani sabida nayi cikin shege, wannan ya sanya kakana da dama baida imani yace yanda yayida uban haihuwata haka zemun nima, kayan k'ira ya d'akko seda suka d'auli wuta ya mannamun a tafukan k'afana wanda daganan bansan meya faru ba se farkawa nayi na ganni abakin titin garinmu yashe, haka nasha dukan ruwan sama na tuna kafin Bilal ya tafi ya bani kud'i da katin sa waina nemesa a waya danyasan in aka koreni dole naje na bashi kaina, amma duk wad'annan abubuwan ba abinda na tsira dashi face suturun jikina" Da sauri yakai hannu ya d'aga k'afarta ga wannan tabon nan kowacce k'afa wuri biyu, zuface ta keto masa yana jinjinawa rashin imani irinna wadancen mutanen, murmushi tayi sannan taci gaba
"Da k'yar na samu nahau wata mota tayi loding kayan masarufi sukace zan basu hamsin haka na yadda koda mukazo banida ko anini, na hadu da shakiyanci karen motar yace ajikina ze fanshe hamsin dinsa hankalina be kuma tashiba seda wani ya baiwa karen motar dari bakwai yake cewa aini me tsadane ga dari bakwai yabar masa ni, da k'arfin hali da rashin kunyar da ake cewa inada ita a wannan lokacin sesukamun amfani na fatattakesu na baiwa karen motar zoben azurfata nayi tafiyata ayanayin dako tak'a k'afana bana iyayi sabisa rad'ad'i da zabar k'una, a haka nayi yunk'urin komawa gidan momy da k'afa, na yanke shawarar bazan nemi taimakon kowa ba dukda nisan dake ga unguwar sabida naga kowama dan iskane, haka nake tafiya a d'age har dare a tsala cen k'afa ta d'auke sega zauna gari banza suka afka mun sesukayi rashin sa'a ina cikin al'adata, dan haka sumamun duka suka gudu abunsu, bansha wahalar neman taimako ba dan kuwa a wannan lokacin hammood yazo mun, daganan ya d'aukeni har gidan su a lokacin bankosan shi waye ba, zuwa wayewar garin ranar sena fahimci a gidan sarki nake, maganganun da ake akan cewar d'an sarki yamun fyad'e sune abubuwan dana yi karin safiyar ranar dasu! Haka nan wasu mutane suka sameni suka ce na basu labarina ban boye musu komai ba kuwa na zayyane musu labarin abinda ya sameni kamar yanda na baku, senaga suna dariya d'aya daga cikin su yace
"Ke daga yau daga yanxu ma duk abinda zakiji kibarshi a haka ma'ana karkiyi musu, za'azo ana cewa yarima hammood ya miki fyad'e ki tafi ahakan, indai kinason wanda ya taimakeki.ya rayu, indai kinason karmu kasheshi tokuwa ki mana biyayya inba haka ba nan bakida kowa kasheki kawai zamuyi mu kashe banza" wannan maganganun sune suja tilasta bakin gaza motsawa dukda kuwa inaso ya motsa akan fad'ar gaskiya, haka na tabbata a zillimi bana iya cin komai, har maganar aurena dashi tazo kunnena, wata ziyara da Ummin sa ta kawomun baki ta bud'e ta gayamun gaskiyar ita ba kurma bace in sanar da ita gaskiya kuma na gaya mata gaskia, daga baya ne labari ya sameni cewar tayimun magana dan kawai ta tabbatar turoni mak'iya sukayi setaji shiru har gobe babu tashin zancen, a gurguje abubuwa da dama sun faru, mutane da dama sun zo akan ran Hammood sa hannuna sukeso, wasu na amsa musu da to wasu na bisu da dabara wasu kuma na zagesu dama kamar yanda na fad'a na iya tsiwa. Bayan munbar k'asar sena fahimci hankalin fada gaba d'aya yana kanmu, acikin kuyangi da bayi ma akwai wanda takanas ko motsin me yayi sesun fad'a, sena shige acikin su, hatta Kuyangin Khairiyya akwai wanda sukeda aiki akan Mood kawai, bayan na fahimci komai da kowa nasan kowa abinda yake ka sa senayiwa Bahar tiryan tiryan daganan tayi waya da ummi inda atake muka had'e kai da Uncle Jay da kuma Barra acikin taimakon kai da kai gani mun tsamoshi a hannun mak'iya, kuskuren farko da Hammood yayi shine rashin yarda dani, na biyu kuma ya barwa kansa tunanin cewar inya bayyana kansa mak'iya zasu kashesa, ni kuwa nake tunzurashi da kalamaina masu zafi dan kawai nasanya ya dena shakka yafito yayiwa kansa fighting, uncle jay bayaso yayi magana amma ni inaso, da wannan na gayawa 'yan jarida tabbacin yana magana har akayi caa akansa dama haka nakeso, k'ungiyar danake da tabbacin akwai sena shiga acikin ta a b'oye...... tabasu labarin duk abinda ya faru sannan tace
"Wani dare a k'ungiyar munkai ziyara nida Hammood a tare inda aka tashi kamamu shinema ya ceceni, amma seyayi canjiya da uncle Jay shi uncle jay seya koma yana gaya musu be ganni ba, Uncle Jay tsohon d'an kungiyar Ne wanda yake nuna musu atare amma ina zargin sa akan bayason Hammood ya gaji wannan sarautar sabida dalilai masu yawa, ban yanke masa hukuncin komai ba senaga yanda ta yiyu, se iya yiyuwa hujjar dayakeda ita me k'arfi ce. Na fahimci cewar khairiyya 'yace awurin tsohuwar marik'iyata wato Hajiya Barira, na fahimci anaso ayi amfani da ita a cutar da hammood abinda ya sanya nayi gangancin fita kenan wanda hammood keta bibiyata kuma nasan da hakan, nayi sanasar tattare muhimman sirrikan Idan fada, sedai kuma sun murd'e abin ta hanyar daban zata ba, inada shaidu sosai, inada hujjoji inada sautikan muryoyin su a ajiye suna maganganun cutarwa agaremu baki daya, ganin na kamasu a saukake shine sukamun wannan sharrin" kallon nutsuwa Data ya mata
"Mesa kika gayawa 'yan jarida yana magana" Tana kallon cikin idansa tace
"Sabida yana magana, akan me ze rayu a kurumce akan wasu banzayen mutane, akan me yana namiji ze zama wani irin mace ma ta fishi, akanme ze rik'a rayuwa ta rashin 'yanci alhali shi saraki ne, koni nan danake mace aka d'aura aurena da d'an sarki inajin izza tana fizgana akan me yarima ze mayar da kansa sakarai? Danme yasa Uncle Jay ze tilasta masa datse harshen sa? Akan me ? Nisawa Hammood yayi kafin yace
"Akan me kika sadaukar da rayuwarki akan tawa ? Mesa zaki taimaki wawa kamar ni? Murmushi tayi
"Wawane ya fara taimako na dole in biya bashi, bayaga haka kai yayana ne ka manta? Above all kuma akwai k'auna" Murmushi Data yayi kafin yayi gyaran murya yace
"Kin d'auki hanya me kyau sosai sedai kuma hanyace mafi hatsari agareki, sedai dabadan keba bansan yanda za'ayi abubuwa su warware acikin sauk'i haka ba, yanxu da kikayi nasarar gano komai da kowa menene taimakon gaggawa dakika shirya bamu sabida bamuda lokaci, bamu kad'ai muke shiri ba harsu nasan sunacen suna shirin yak'i babba damu" Kallon sosai tayiwa Hammood kafin tace
"Dabadan mahaifiyar khairiyya ba dabazan kawo wannan lokacin a wannan garin ba harna samu wayewa, da k'arfin dukiyar ta nayi nasarar samun ilimi na addini dana zamani, itace take ciyar dani banda so dakuma k'auna babu abin ta nunamun, har lokacin danayi yunk'urin tozartar da ita in tona mata asiri ko bak'ar magana bata gayamun ba, tayi zaman amana dani, ta d'aga darajata har kawo wannan lokacin tayaya zanyi kishi da 'yarta data rayu batare dajin dad'in uwartaba har zuwa aurenta, ni abokiyar zaman khairiyya ace nasan sirrin mahaifiyar ta mafi muni, nakuma san nata mafi muni duk a matsayinta na kishiyata anya anmata adalci kuwa? Tayaya zata rayu a farin cikin sanin cewar abokiyar zamanta tasan labari mafi muni akan mahaifiyarta da wani b'angare anata, da wannan nakeso kafin na bayar duk wasu hujjoji da kuma shaidu dana tara in sanya sharad'i na" kallon ta sosai Hammood keyi lokaci d'aya zuciyar sa ta shiga luguden tashin hankali, me yarinyar nan take nufi, Data dake nazarin ta yace
"Toohh wannan wane irin sharad'ine haka? Gyaran zaman ta tayi sannan tace
"Tun daga kan sarki da sarauniya har duk wani wanda baya cikin k'ungiyar aci duhu ta idan fada rayuwar su tana cikin hatsari, ya rage na Hammood ya cecesu ta hanyar rubutamun saki har k'waya uku in bashi duk wani abu daze tarwatsa mutanen fadar sa danakedasu a hannu, kokuma yak'i ya sakeni in adanae hujjoji da shaidun danake dasu al'ummar dasuke iyayensa, da talakawan sa su mutu a banza akan sonkan sa, banaji wannan aikine me wahala agaresa yasha gayamu ya tsanani, bashida wata alak'a dani na mata da miji tun bayan auren mu bare yace mun saba, dan haka yanxu dabara ta ragewa me shiga rijiya" Yanayin sa kad'ai zaka kalla ka tabbatar wa kanka cewar wani sabon tashin hankali ya ziyar cesa, gaba d'aya ya gid'ime wata iriyar zuface ta keto masa ya kalli Data cikin tashin hankali yace
"Uncle Sufyan kanajin wani zance kuma na mata, wannan wane irin magana ne" Shiru Data yayi na wani lokaci sannan ya kalli Hafsa, seda ya had'a rai sannan yace
"Ke waya gaya miki aure abun wasa ne? Kokuma mu sa'anninki ne dazaki gindaya mana wannan sharad'in e ? Turo baki taki tanajin azuciyarta iya abinda take so kenan, sannan tace
"Nidai abarni da zab'i na kawai, Uncle mutumin nan yanda yakecin zalina, ya tugemun gashin kaina, ya dinga marina kuma ba sona yake bafa, daga kawai na tausaya masa na rabashi da abinda bayaso, ni idan yanaso in tattare komai in bashi ya bani takardana, in bayaso kuma kowa ya rik'e abinda yakeda iko dashi" Sosai data yake kallonta ee lallai batada kunya yarinyar nan, shi zata gayawa magana, kallon Laure yayi yace
"Laurah jeki kawomun biro da takarda" Jiki a mace ta mik'e taje ta kawo karb'a yayi ya baiwa Mood yace yana kallon sa
"Kasan dai akan mace bazamu sadaukar da rayukan dukka wad'an nan mutanen bako, dan haka kq rubuta mata saki ukun datake buk'ata yanzu yanzu" Sororo yayi yana kallon Data shi kuwa ya d'auke kansa daga dubansa cikin basarwa yana furta
"Kai muke jira"
*Nagode da addu'oinku, yara sun samu sauki Alhamdulillah, na lek'okuna daba samu sararin yi hakan, nasan idan muka shiga week days aka soma maganar aikin yarona daya zakuji ni shiru nagode da son so.*
Mom Nu'aiym.
*TSINTAR AYA* FREE BOOK
*BILLY GALADANCHI*
*SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI*
27.
Be rubuta komai ba se kallon Data da yake, wanda shi kuma ya gama karantawa matarsa abinda yakeso tace akan maganar, gyaran murya tayi sannan tace
"Wannan ciwone na 'ya mace babu wanda ze fahimceshi semu mata, tabbas Hafsat kinada kaifin basira kin cika 'yar halak me adalci kuma sannan ni kinyi matuk'ar burgeni da wannan sadaukarwar taki,zamu baku wurin kuyi shawara amma mintuna goma kacal, muje ciki Hafsat" Tana zumb'ura baki ta mik'e duk suka bisu da kallo, Data yana murmushi yace yana kallon Mood
"Yaro ka d'akko ruwan dafa kanka, wannan yarinyar dakake gani rigimammiya ce, tanada wayo sosai amma tanada wawta, idan muka mata uzuri muka duba maganarta tana kokari ne kawai ta zama me kirkin gaske, sedai kanta zata cutar keda bakida wani dangi tsayayye idan ka sake ta gidanwa zataje? Koda yake anyi adopting nata agidanku zata yita zama anan ko bayan kun rabu, yanzu kai me zakace game da wannan" Kallon Data yake sosai yana wani tunani kafin daga bisani yace
"Ni bawai son yarinyar nake ba, kawai dai ni son rabuwa da itane banayi, sabida wasu dalilai kaga ai kaima shaidane ta taimakemu da iyakacin k'arfinta, sannan batada wani jigo kuma batada gata semu se Allah" Gajeran murmushi Data yayi tunawa da yanda yayi akan soyayyar dayakewa Laure daya kasa ganewa seda ta kusa kashesa, bazece da Mood komai ba, ze barshi dan kanshi ya gane da kanshi
"Yanzu kaga bamuda lokaci, yaya zamuyi da ita? Kawar dakai