Showing 78001 words to 81000 words out of 113608 words

Chapter 27 - TSINTAR_AYA

Start ads

09 Aug 2025

711

Middle Ads

k'areba se kawai suka d'auki matakin rataya laifin akaina ta hanyar kawo shedun k'arya" kallon juna suke suna wani murmushi atare kawar da kanta tayi sannan taci gaba

"Raina fansa ne akan ubana dankuwa Me martaba ya 'yantani a matsayin 'yarsa tuni, Raina fansa ne akan mijina dan kuwa yasha matuk'ar wahala arayuwata kuma shine ya d'akko ni a lokacin da ake neman yagan rigar mutunci yamun sutura, idan na mutu agarin ceton sa ban damu ba, ka k'addara nid'ince na sanya akashe su, amma kuma tare da had'in bakin wasu acikin fadar nan, wannan shine Assighment dazan baka matsayin ka na babban me bincike alaji Data" Gyaran murya yayi har lokacin yana murmushi kafin yace

"Ban fahimci wanne Assighnment ba aduk wannan labarin da kika bani a baud'e" Murmushi tayi kafin tace

"Ka nemo su waye makasan sarki da d'ansa acikin fada bayan ni" Nisawa yayi kafin yace

"Idan ina binciken mutum akan kowane irin laifi ina duba zuciyar sane lolacin dayake magana, bana duba kalamansa, amma narasa yanda akayi kika raba zuciyata kashi biyu a wannan lokacin, na farko kalamanki suka d'auki mafi rinjayen kaso a k'walwata da zuciyata, na biyu kuma harbawar zuciyar ki ya tabbatar mun da cewar keme gaskiya ce hakane?" Murmushi tayi

"Ehm Ehm banda azarb'ab'i bance dakai inada gaskia ba, nadai gaya maka hanya mafi b'ullewa ne amaimakon ka b'ata lokacinka wurin jiran in baka wata amsa danni babu amsar dazaka samu daga gareni a wannan lokacin" Shiru yayi yana nazarin yarinyar be tab'a had'uwa da mutum mara tsoro irinta ba, meke damun kanta haka?

"Idanda zaki bani had'in kai, da munyi wannan tafiyar atare Malama Hafsa, banaso muyita zagaye nida ke, na soma fahimtar kalaman ki dakuma gaskiyar ki" batace masa komai ba yace yana kallonta har lokacin

"Idan zaki bini zan dawo anjima na d'aukeki samuje gidana inada mata hadda yara biyu so karkiyi wani tunanin,akwai muhimman abubuwan danakeso mu tattauna a tare masu buk'atar sirri" Shiru har lokacin batace masa komai ba, seda kusan mintuna uku suka wuce sannan ta sauke nannauyar ajiyan zuciya tace

"Banaso fitana atare dakai ya samu saukar idon polisawan wannan wurin, ka sani idon fada akwaisu a ko'ina na tabbatar anan d'inma akwai mutanen su dan komai zan bikane amma zuciyata batada nutsuwa akan bazaka cutar dani ba sam! Murmushi yayi sannan yace

"Kinada tsananin kaifin basira da k'wazo wannan shine abinda ya ankarar dani akan gaskiyar ki, ya kuma kwad'aitamun son yin tafiya atare dake, idan haka kike tunani zan murd'e kalamai na daga yanzu zuwa yin basaja na wuccin gadi kafin mu samu gaskiyar ke wacece! Murmushi tayi dankuwa tsaf ta gane kalaman sa kafin tace

"Abin ze amfanar da mutane da yawa Detective, kawai inasone ka sani kaima ka shigo wani hannun dayake a rub'e bashida sanayya kota ina tashin wari yake abinsa ka kiyaye" Cikin gano zancen ta yace

"Hakane zan tafi amma ki sani bazan tab'a saurara miki ba idan har ya tabbatar cewar ke mai laifice, dan kuwa kin kasa kawo wasu k'wararan hujjojin dazasu nuna cewar bakida hannu a wannan tafiyar, detective ze baud'e hannunsa yakaiki d'akin horon dayake mallakin humumar su ya azabtar dake cikin k'una" Murmushi tayi

"Ina fatan wannan basajan ya zame maka alkahiri, ina maka tsoro kayi sakacin da santsin miyan yauk'i ze jaka zuwaga gangara" Mik'ewa yayi

"Gwara ki tanadi hujjojin kariya dakai, dan kuwa daga yanxu bazanmiki yare irin wannan ba, had'aki zanyi da horo mafi muni, sarki da d'ansa rayuwar suce a tsakiya"

"Gaba d'aya Allah yana bayana yana dafamun a irin lokutan danake tsananin buk'atar hakan, nayi farin ciki danayi nasarar gano amsa kuwwar d'an mage, ban tab'a sani inada hikimar gano wannan hanyar ba, zan jirayeka zuwa duhuwar ina maka fatan samun nasara" Seda yakai k'ofa sannan yace

"Daga yanzu babu wata magana me kamada dad'i a tsakanina dake, idan baud'e yayi baud'e zaki iya samun tsaraba harta duka kisan wannan, bayaga haka kiyi hankali wurin gayamun magana dan kuwa daga wannan lokacin mun gama tausasa kalamai se saukar horo me tsanani" Bata bashi amsaba ta fahimci da haka yakeso ya rabata da wurin tana fatan police biyu dake tsaye basu fahimci komai ba, dan bata yadda da kowa ba a yanxu!

************

Ranka ya dad'e hak'uri zakayi ka kwanta zuwa lokacin dazaka samu lafiya, kayi hak'uri ko zuwa jibi ne" kallon mitumin yayi a k'ufule ya saba darashin yin magana har yanzu bakinsa nauyin bud'ewa yake masa, idan ba ambaton Allah yake ba seya wuni beyi magana ba

"Yaya zasu mata sharri, akan zasu sauke akan ta, meta musu k'arya sukeyi kuma inaso inga matata yanzu yanzu" Nisawa Uncle Jay yayi kafin yace

"Hammood kokasan ba inda zan barka kaje, kana hauka ne wai, su hukumar aiba mahaukata bane ba dazasu yanke mata hukunci babu wani bincike" kallon mamaki yayiwa Uncle Jay

"Uncle ban gane me kake nufi ba, so kake in barsu suyita dukanta, kokuma so kake sauro da k'udan cizo yayita cizonta, agun kwanciya ake kashi ayi fitsari gaskia zuwa zanyi in dawo da ita" Khairiyya da kishi ke shirin hallakawa tayi gajeran tsaki sannan tace a k'ufule

"Yarinya tana neman ranka, kai kana neman ka ceceta, gaskia Hammood kanada matsala, i will make sure she rot in jail" d'aga ido yayi daga kwancen dayake yace

"Kidena alak'anta hafsat da maganar nan, batada wani alak'a da ita kuma ita ba muguwa bace ba, zargi ne aka jefa a zukatan ku akanta kuma kada ku bari ayi nasara akan hakan" Wani tsakin taja

"Ko shakka banayi asiri ta maka, an jik'a an baka kasha, kasan me kake ciki kuma fita ba inda zakaje da wannan raunin" Mik'eea yayi zaune yana k'walla k'ara yana dafe wurin kafin yace

"Khairiyya idan bazaki fad'a alkhairi ba to kiyi shiru dan Allah, babu i repeat babu wani wanda ya isa a duk fad'in duniyar nan ya hanani fita idan ba Allah ba, yanzu zanje i want to bail her out" zata k'ara magana Uncle Jay yace

"Khairii please, ki rabu dashu, Hammood tunda yamun musu abin yafi k'arfin sa, just let him go" Tashi zaune yayi da ssuri Ummin sa ta rik'esa tana kallon sa, shi d'inma kallonta yayi

"Ummi dan Allah karki hanani, yarinyar nan nini kad'ai nasan abinda nakeji akan halin nan datake ciki, tayi mana sadaukarwa bazan tab'a bari ta shiga wani hali ba akan rashin gaskiya! Zama ta koma tayi sannan da ido tayiwa Uncle Jay alama akan yace masa wani abu

"Ka bamu mintuna goma mu nemo wanda zasu baka tsoro" Tashi yayi tsaye kafin yace

"Abinda banaso kenan, hankali ze dawo akaina, da abun hawa na kasuwa ma zan fita" Damuwa sosai ta bayyana a fuskar ummi ta sadda kanta a k'asa cikin son b'oye damuwar ta, seda yakai k'ofa sannan ya waigo ya kalli mahaifiyarsa

"Ummi kimun addu'a" Murmushi ta sakar masa wanda bekai zuci ba sannan ta gyad'a masa kai" Dawowa yayi ya karb'i kud'i hannun Uncle Jay sannan yabar cikin d'akin da tunani kala kala aranshi.

***************
Koda ya iso station d'in ya tarar da motar Baba Usman da wasu muk'araban sa, fasa shiga ciki yayi ganin akwai yalwar duhu awurin seya lab'e agefen bishiyar da Baba usman yayi parking, yana nan tsaye har aka shafe minti sama da goma sannan segasu sun fito, tsayawa sukayi suda D.P.O. Baba usman ya mik'a masa kud'i ya karb'a sannan yace yana kallon sa

"D.P.O banaso abaiwa yarinyar nan dama ko k'afar dazatayi wani bayani, idanda daganan station d'in zaku turata jail batare da alkhali yabita kanta ba danaji dad'i, amma ko yanzu idan alk'alin naku ne semu siyeshi mu siye lauyeyun su murd'eta, kasani idan asirina ya tonu naka asirin ma ya gama tonuwa" DPO yana 'yar dariya yace

"Ai ka rabu dani da ita kawai, narasa waye ya turo Detective Data akan binciken ta, mutumin dayayi yak'i da mutanen harma da aljanun gidan madubi, dabadan shiba da duni zansan yanda zanyi kawai na hanata xuwa gun shari'a, abin ma dayazo da sauki tunda kace batada galihu batada kowa" Baba usman yana dariya yace

"Ance ba'a siyen Detective data da kud'i, idan nabi ta kansa da nera ya taka ya wuce zan sace matar sa, ko 'yar sa inyanada su inga ta tsiya" Dariyar mugunta DPO yayi kafin yace

"Ranka ya dad'e inama ace nice nakeda irin tunanin ka, dana mori ilimina" Dariya jin dad'i yae kafin yace

"Mu zamu koma, ka tuntub'i detective d'in kaji idan yayi musu zamu karb'e case d'in daga hannun sa" Sallama sukawa juna sannan suka wuce shiya koma, sauke ajiyar zuciya Hammood danya samu wata shaidar akan Baba Usman yayi recording na komai a wayarsa, kai tsaye cikin station d'in yashiga bayan sun gaisa dashi yace

"Office na DP0 nake nema" kallon sosai sukayi masa kafin d'aya daga cikinsu yace malam lafiya?

"Sunana prince hammood daga masarautar Daulatul Dinar" Take suka fara kai masa gaisuwa, yamutsa fuska yayi sabida yanda wurin bullet d'in ke masa ciwo sosai yace yana kallon d'aya daga ciki

"Lead the way" da azama ya shiga gaba shikuwa yabi bayan sa. Bayan sun gaisa yace yana kallon D.P.O

"Kada kayi tunanin zakayi wasa da abubuwan dake hannun ka, domin duk abinda kuka tattauna kaida Ubandoma ina jinku kuma nayi recording na komai a wayana, harna turawa aminaina ta whatsapp kusan su goma, yazame maka dole kayi duk abinda nakeso batare dako k'wandala ba kuma idan bakayi ba, in wulak'antar mafarin ka" jikin d.p.o yana rawa yace

"Yallab'ai babu yanda xanyi da matsalar Yallab'ai Ubandoma, idan ma banyiba ze b'ullo ne ta wata sigar" Gyaran zama yayi kafin yace

"Daga yanzu duk abinda nace ka gaya masa shi zaka gaya masa, sannan kuma duk abinda ya gaya maka kake gayamun ta hanyar lambar wayar dazan baka b'oyayyiya sabida a wannan suna bibiya ta, na biyun sa kuma wlh idan ka sake wanima yaji nazo nan wurin ko naji hirarrakinku senayi mafarin rufe ganin ka da k'asa" Nan take ya amsa da angama ya rufa masa asiri kodan aikin sa, sun tattauna sosai ya samu sirrikan su kafin ya buk'aci ganawa da Hafsa inda kai tsaye suka gabatar masa da ita har offishin D.P.O


Mik'ewa yayi tsaye ya matso da sauri inda take ya kama hannunta inda atake D.P.O ya basu wuri, hannunta yake murzawa wanda yaga alamun shatin sanda rud'u rud'u ajiki cikin tashin hankali ya kalleta

"Waye ya dakeki a hannu haka? Murmushi tayi ta shafi k'afad'arsa

"Ya raunin hannun ka, harbi da zafi ko? Sannu yaa mood, hankalina yana wurin ku kaida Me matraba da wannan Muhseen d'in" K'ara shafa hannun ta yayi sannan yace

"Cewa nayi waye ya dakeki Hafsah? Murmushi tayi kafin tace

"D.P.O naji kaman suna kiransa ko, so yake ince nice na saka a kasheku, tayaya zan amsa laifin daba nawa ba, kuma tayaya zance nasa akashe mahaifina da mijina? Kuma kaga dukan nan Allah da zafi" kawai seta soma sheshekar kuka ga alama dama kukan takeso tayi tuni amma taurin kai ya hanata tayishi agaban su, iskar bakinsa yasanya yana hure mata hurin da hannunta ya tashi cikin kulawa

"Dame ya dakeki? Tab'e baki tayi irin na yara

"Sanda ne babba baka ganshi ba, niba abinda na masa so suke su kasheni, nace su kasheni amma ni kowa yasanni bana k'arya bakuma zan fara k'aryaba sabida karsu dakeni" Zuciyarsa tazo masa iya wuya yama rasa mezeyi kallon juna sukeyi kowa da abinda yake sak'awa har lokacin kuka take, k'ara kallon ranin yayi farcenta d'aya harya kumbura

"Shidawa yazo? Ya tambaya yana k'ara hura mata iska agun

"Baba Usman ne, shugaban k'ungiyar aci ta duhu da fada"

"Ya akayi kika san shine" Tana me share k'walla da gefen kafad'arta sabida ya rik'e hannayenta tace

"Dama inaso in gaya maka komai kafin su kasheni" Had'e jikin sa yayi da nata

"Kisa wai kike magana, kinada hankali kuwa? Waye ze kasheki? Kukan ta ta k'arawa sauti

"Wannan mutumin da suke kira DPO wanda ya kawoni nan dakuma Baba Usman sune sukace sauramun kwana uku a kasheni" Runtse idansa yayi sanya fahimci sunyi nasarar tsoratar da ita, k'ara matseta yayi da hannun sa me lafiya

"Babu wanda ya isa ya kasheki ina numfashi, k'yalesu kedai duk abinda kika sani ki sanar dani"zare jikinta tayi a nasa sannan tace

"Wani zezo na aminta da aikinsa da gaskiyar sa sunansa Detective Sufyan Data, munyi akan zece dasu zeje dani special investigation centre nasu ya tuhumeni, amma gun matarsa ze kaini, inada manyan shaidu awurin wani dakuma kaina, ze taimakeni yace inna gaya masa komai ze fitar dani lafiya" kallonta yayi

"Nasan Data ai, dama dashi ne naso in had'a yayi mana bincike, zan masa waya yaxo ku tafi, gidansa akwai tsaro ba abinda ze sameki acen, amma kinsan wannan dukan da aka miki sena rama, Allah har Baba usman sena saka ammasa fiye da wannan" Murmushi tayi tana kallon sa

" Laa Babba ne fa? Shima dariya ta bashi yace yana kallon ta

"Hafsah mesa kika sanya rayuwarki a hatsari har haka, mesa baki tab'a yimun bayani akan komai ba, se Uncle Jay ne ya gayamun komai da komai d'azu" tana kallon sa ta shagwab'e fuska

"Kaine kace baka sona ai, kuma ka tsaneni, Bahar kad'ai ke sona se Ummi" Murmushi yayi kome yasa wowtar Hafsah take burgeshi?


Mom Nu'aiym.


*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA*
26.

Sanye ajikinta wata farar rigace shara shara me santsi, ta tufke gashin kanta a tsakiya, ta sanya wata shara sharar hula itama fara akanta, fatarta dake shek'in wani haske tana asalin glowing abar d'aukar hankali takai hannu ta murza gefen fuskarta lokaci d'aya tana lumshe idon ta

"Yaa Sufyan bacci nakeji, tara ya gota fa, kake shirin fita? Hannun sa yakai ya tallafota jikinsa daidai kunkurunta

"Laurah wannan babban al'amari ne daya zamar mun dole senayi fitar dare, a k'aida kowa yasan 8 ana gama sallan isha ina gida, to wannan fitar basaja ne kin gane? Nisawa tayi kafin tace

"Dabadan kayi nasarar tarwatsa gidan madubi ba, da bazan barka kafita ba, amma duba da yanayin sharrin dakafi k'arfin sa na tabbatar kaime bautar Allah ne, da wannan nakeda hak'ik'a akan cewar aduk inda kake Allah mabuwayi yana tare dakai" Sumba yakai mata a agoshi sabida yanayin gajarta irin nata yana dariya yace

"Acikin shekaru hud'u Laurah baki ya bud'e, girma ya kawo kanshi" Zame jikinta tayi tana murmushi sannan tace

"K'waila tasha raino zakace" sarai yasan neman maganar sa take amma bebi ta kanta ba, murmushin sa kawai yake yafita yabar gidan.

Ta k'ofar baya yabi, wata iriyar k'oface ta sirri wacce bazaka tab'a sanin akwaita awurin ba, Likitan yaso shammaz (Littafin Sa'a) shine yabi dare ya gina masa wannan k'ofar ta sirri... yayi tafiyar kusan mintuna goma kafin ya isa wurin wata motar ya bud'e ta ya shiga batare da yayi magana ba, kai tsaye police station ya nufa inda ya tarar D.P.O anata rafka gumi yana bakin kantarsu a tsaye, hannu ya mik'a masa suka gaisa sannan yace

"Detective Data" D.P.O ana muzurai akace

"Na gane sosai sir" hular daya sako wacce ke had'e da riga ya ture taje bayan wuyansa"

"Inaso zanyi magana da suspect tamu" Muryansa yana rawa

"What is the use? Tana tare da prince hammood shisam be yadda akan ita bace take neman ransu" Murmushi Data yayi

"Interesting, haka ma wani babban taimakon ne, because inaso nayi bincike da tushe, and right now am taking the suspect with me" kallon sa cikin tashin hankali

"Wai yallab'ai mesa baka tab'a bari muyi aikin mune? Waya turo ka kuma wannan karon" K'ank'ance idansa yayi

"C.P Mai doki ne ya turoni (ACP mai doki yake magana na littafin gidan madubi, yanzu ya tashi daga ACP ya zama babba shine commissioner.) Sosa k'eya D.P.O yayi kafin yace

'If that is the case, i will like to help" Murmushi yai masa

"Kai D.P.O Maharazu ka san waye ni kuwa? Bana son taimakon ka kamar yanda banason shishigi, wannan aikine na intelligence agency me zaman kansa, ka gayawa masu baka wasu kud'i kana shirin murd'e al'amura suyi hankali da kansu, maza abisa kansu inada tarin dukiya bazasu iya sayana ba, inada tarin gaskia k'aryarsu bazata rikitar dani ba, inada tarin basira datafi k'arfin masharranciyar basirar su, now lead the way? Juyawar dazasuyi sega Hammood a fusace janye da hannun Hafsat kallon A.C.P yayi sannan yace

"Waye acikin ku yakai hannun sa ajikin matana saraki ce fa? Kallon tuhuma duk yaran sukayiwa ogansu sannan wani jikinsa yana rawa yace

"Amun aikin gafara yallab'ai nine na daketa, alokacin anata so tayi magana tak'i tayi" Da mamaki Hafsa ta kalle sa, sannan ta narke fuskarta cikin shagwab'a tace

"Allah sarki me k'arya d'an wutane fa, wancen ogan nasu shine ya samu sandar sa me zafin tsiya, ya d'aura hannayena asaman bench ya dinga rotsamun seda na suma na farfad'o" ta k'arashe maganar tana sauke fuskarta asaman d'aya kafad'ar hammood me lafiya, hannun sa yakai yana patting bayan ta a hankali

"Koma waye wlh sena rama mata, sekunci ubanku a hannuna 'yan sandan kawai, kune kuke b'ata mana k'asa, haka ake bincike inaga ta kanku zan fara" Data ne ya matso ya mik'a masa hannu sukati musabaha sannan yace

"Ranka ya dad'e babban son ya akayi kazo nan bayan raunin dake jikin ka haka? Murmushi yayi cikin girmamawa sanin cewar Babban abokin Uncle Jay kenan ya sanya yace

"Am sorry Uncle Sufyan, hankali na yana kan yarinyar nan, she sacrifice alot for her family, and mak'iya are busy trying to accuse her of something big as this, yarinya da kind soul irin hakan nan ai gobe bazataji dad'in k'ara taimakon kowa ba" Nisawa Data yayi

"Polisawan k'asar nan gaba d'ayan su kaso 75 acikinsu sunada raunin saitin kai, Allah kad'ai ze mana maganin su" Anan suja tattauna kafin su shiga mota subar gidan, gaba d'ayan su gidan Data suka isa ata wannan b'oyayyiyar k'ofar. Da kansa yayi kiran matarsa lokacin 11. Yayi tazo ta gayar da Hammood yana mata murmushi yace

"Ga d'an gidan Jay fa, yaran da ake xuwa aita mana kuka akan sa, kai Jay wlh ya iya shak'iyan ci, shida matar sane, tana buk'atar taimakon ki Anty Laurah matar Data" Murmushi tayi

"Yanzu nice anty dan Allah? Ta furta tana shagwab'a, dariya yayi "Jibi zatayi 18yrs ina ke harkin cinye cake naki na 19, so ke antyn tane ai ko yaya? Murmushin ta ta

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login